*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_
aishaummi.blogspot.com
*_72_*
~~~Ihu ihsan ta fasa itada fadila suka zube awurin suna burburwa yayinda bash yayi mutuwar tsaye, wani babban likita ne ya fito ya dakawa nurse din tsawa,
"Waye ya fada miki cewar ya mutu?"
Cikin inda inda nurse din tace "am sorry sir"
Juyawa yayi gurinsu fadila yace dasu "patient dinku bai mutu ba yana nan araye kuma insha Allah zamu bashi kyakkyawar kulawa har ya samu lafiya" yana gama fadin haka ya shiga cikin dakin da lamido yake.
Tsayawa suka yi cirko cirko suna jiran likitan da ya shiga duba lamido ya fito amma shiru bai fitoba har fiyeda tsawon awa daya, kuka sosai fadila da ihsan keyi rarrashin duniya bash yayi musu amma basu iya yin shiru ba,
Jungum jungum suka yi har wani lokaci, bash yana son ya kira baffa ya sanar dashi abinda yake faruwa amma baya son ya tayar musu da hankali dan haka yaja bakinsa yayi shiru, sai wurin karfe 2 nadare sannan likitan ya fito ya wucesu, zumbur dukkaninsu suka tashi suka bishi suna tambayarshi ya jikin marar lafiyar? Babu wata ingantacciyar amsa da likitan ya basu hakan ya sasu garzayawa dakin da lamido ke kwance duk ya fige yayi wani iri kamar wanda ya shekara yana jinya, gaban gadon ihsan da fadila suka karasa suna wani sabon kukan.
Kwana suka yi suna kuka har gari ya waye gashi har lokacin lamido baiyi koda motsi ba sai dai numfashi, ganin gari ya waye yasa bash tafiya gidan baffa, sashen innah ya shiga ahanya suka yi kicibus hannunta dauke da kulolin abinci tana kokarin zuwa sashen baffa,
"A'a bashir yanzu kake tafe? Sannu da zuwa.." Innah tace dashi tareda komawa da baya ta ajiye kayan dake hannunta,
"Ehh wlh innah, nine" bash ya fada yana sosa keyarshi,
Tsugunnawa yayi ya gaisheta ya dan fara inda inda domin ya rasa ta inda zai sanar da ita rashin lafiyar lamido,
"Bashir lafiya kuwa...?"
"Wallahi innah ba lafiya ba, lamido ne bashida lafiya tun jiya da daddare, a asibiti muka kwana nida su fadila.."
"To ni me zanyi muku kuma? Lamido bashida hali bashari, akan matarshi ne wai tatafi gida amma ai da laifinsa tunda..."
"Innah dan Allah kiyi hakuri muje kiga halin da yake ciki, wallahi lamido yana cikin wani hali"
"Jeka fadawa baffa tukunna inyaso muji abinda zai ce"
Mikewa bash yayi ya nufi sashen baffa innah kuma tana tsaye tayi suman tsaye kamar wacce aka dasa awurin, tana nan tsaye sai ga baffa ya shigo shida bash,
"Kina ina? Fito mu tafi muje mu ganoshi, lafiya ai ita ake yiwa" baffa ya fadi,
Shiga daki innah tayi ta janyo mayafinta ta fito suka fita, baffa sai tambayar bash yake yi da yaushe abin ya faru? Yanzu awanne hali lamido yake? Inna kuwa tafi kowa shiga cikin damuwa da haka suka karasa asibitin,
Dakin da lamido yake ciki suka shiga yana kwance ana kara masa ruwa fuskarshi tayi fayau, ga ihsan da fadila agefe sunata sharar kwalla idanuwansu duk sunyi luhu luhu, suna ganin innah suka tashi sukaje suka rungumeta suka fara wani sabon kukan, ita kanta innah sai da tayi kwalla saboda tausayi irin na uwa da d'a,suna cikin wannan hali likita ya shigo ya sake dubashi ya fita, bin bayan likitan Baffa yayi zuwa office dinshi ya tambayeshi abinda yake damun lamido,
"Alhaji damuwa da bacin rai shine abinda ke damunsa gashi dama yanada hawan jini.." Inji likitan ya bawa baffa amsa, mamakine ya kama baffa jin cewar Lamido yanada hawan jini domin bai taba saniba tashi yayi ya fita ya koma wurinsu bash.
A asibitin suka wuni har dare ya sake yi su ihsan kuwa har lokacin kayan baccine ajikinsu sun kasa tafiya su cire domin gani suke yi idan sun tafi kafin su dawo lamido ya mutu, koda dare yayi ma haka innah tayi tayi dasu akan suje gida su kwana amma fur suka ki suka ce anan zasu kwana.
Har akayi kwana uku Lamido bai san a inda yake ba, akwana na hudune ya dan bude idonsa amma baya gane kowa domin dishi dishi yake gani gashi kansa sai juyawa yake yi kamar hajijiya, duk da haka su innah ba karamin murna suka yi ba ganin ya bude idonsa,
Satin lamido daya a asibiti baffa ya kira bash ya tambayeshi dangane da maganar fyaden da lamido yayiwa ikhlas shekaru shida da suka wuce,
Nan bash ya zayyane komai sannan ya k'ara da cewa,
"Wallahi baffa lamido yana tsananin son ikhlas domin tun wannan lokacin ya kamu da Sonta bashida wata magana sai tata kullum burinshi ya ganta ya aureta kuma ta sanadiyyarta y kamu da ciwon hawan jini lokacin da marigayi ya aureta.."
Tausayin lamido ne ya rufe baffa domin abin a tausaya masa ne yayi dawainiya da son ikhlas na tsawon shekaru, ita kuwa innah harda kukanta saboda tausayin autan danta, tunda baffa yaji wannan maganar daga bakin bash ya cewa innah washe gari da sassafe zai tafi Maiduguri bikon ikhlas, hakan kuwa aka yi da sassafe ya tafi Maiduguri shida drivern shi,bayan sallar azahar suka karasa gidansu ikhlas.
Sun samu tarba sosai awurin ammi da hajiya, ikhlas dai dakyar kunya ta barta ta je ta gaishe da baffa sannan ta koma daki ta kwanta tana tuna lamido da irin wulakancinshi da rayuwar soyayyar da sukayi lokacin da bata tare agidanshi ba,
Waya ammi tayiwa hassan da Hussain akan suzo ayi maganar bikon ikhlas amma koda suka zo Hussain cewa yayi ikhlas ba zata koma ba domin wulakancin da lamido yayi mata yayi yawa maimakon ya barta da babban tabon da ya ji mata acikin zuciyarta na fyaden da yayi mata,shi dai baffa hakuri kawai yake basu bashida ta cewa, da kyar aka samu aka shawo kan yaya Hussain ya yarda cewar zata koma amma ba yanzu ba sai ta huta tukunna, duk da haka baffa yayi murna kuma yaji dadi domin dama baya son araba auren, a yammacin ranar su baffa suka koma yola amma har ya tafi basu nuna mishi abdallah ba.
Abu kamar wasa sai da lamido yayi sati uku a asibiti kafin hankalinsa ya dawo jikinsa ya fara samun nutsuwarshi,yana tuno da abinda ya faru ya kalli innah yana hawaye,
"Innah tana ina? Ba zata dawo ba ko? Ni dama nasan na rasata har abada"
"Zata dawo lamido ka kwantar da hankalinka tana nan dawowa" innah tace dashi cikin tausayawa,
"Dan Allah innah karku rabani da ita..." Yafada yana kokarin tsayar da kwallar dake bin kuncinshi,
"Babu wanda zai rabaku lamido, kayi hakuri kaji" innah tace dashi tana shafar sumar kanshi,
Sudai su fadila suna zaune suna jinsu amma basu tanka ba domin dama sun dade da gane cewar lamido yagama matowa akan ikhlas, haka suka ci gaba da zaman jinyarshi aranar da daddare xahar tazo dubashi ita da suhaimat nan aka shiga kallon kallo tsakaninta da su fadila amma kuma basuji haushinta sosai ba kamar yadda suke jin haushin ikhlas saboda sun fahimci cewar lamido yafi son ikhlas fiyeda kowacce mace acikinsu, basu wani jima ba suka tafi, washe gari da safe lamido ya dage shi lallai sai likita ya bashi sallama domin Maiduguri yake son tafiya wurin ikhlas, sallamarshi likitan yayi bawai dan ya gama warkewa ba, suka koma gida aka ci gaba da kulawa dashi.
Ikhlas kuwa yanzu hankalinta ya kwanta har ta danyi kiba kadan domin kullum tana tsakiyar hajiya da ammi suna hira ko ta tafi gidan yayunta susha hira wani lokacin har dare take kaiwa acan sai kwanciyar baccine yake dawo da ita gida, kullum tana ganin kiran lamido amma bata dauka ga text massage dinshi wanda kullum sai ya aiko mata fiyeda guda biyar amma ko sau daya bata taba gwada mayar mishi da reply ba gashi duk massages din na bada hakurine da na soyayya sai dai duk da haka wani lokacin tana jin kewarshi na damunta, amma har yanzu yaya Hussain bai ce ga ranar da zata koma ba domin shi ba danma baffa yaje biko ba to da niyyarshi ya raba auren,cikin haka matar yaya hassan ta haihu ta haifi yara biyu maza, murna awurin ikhlas kamar zata yi me,nan suka shiga budiri domin can ta tattara ta koma ta tare.
Kwanan lamido 5 da sallamowa daga asibiti ya fara shirin tafiya Maiduguri domin yaji dan sauki, yanzu kam ya shirya duk abinda za ayi sai dai ayi amma dole sai ya dawo da matarsa,sallama yayiwa su fadila da innah ya tafi.
A ranar da yaje aranar su ikhlas ke aikin suyar naman sunan matar yaya hassan sadiq kuma ta kaiwa ammi shi ta goyashi,gidansu ya fara zuwa ya aika akirata akace bata nan tana gidan yaya has an dan haka ya tafi can, suna tsaka da aikin yaro ya shigo yace wai ikhlas tazo inji yayanta, duk atunaninsu Hussain ne dan haka ta tashi ta fita da hijabinta a hannu aranta tana cewa,
"Naga dazun nan yaya Hussain yabar gidannan, yanzun ko me ya faru kuma?"
Tana fita taga mota irin tashi Lexus baka, jin yayi horn ya sanyata zuwa jikin motar ta bude ta Shiga, wani sanyin kamshine mai dadi ya bugeta, wa zata gani?
Lamido tagani sanye cikin farar shadda yar ubansu wacce tasha dinki mai aji, kanshi babu hula yayi mugun kyau hannunshi rikeda alewar lollypop yana tsotsa, kafeta yayi da ido yana kallonta domin har tayi dan kumatu alamun hankalinta ya kwanta,
Hade rai ikhlas tayi ta dauke kanta ta fara kokarin bude kofar motar,
"Haba pretty.." Yace da ita a hankali bayan ya matsa kusa da ita sosai,
"Malam ka bude min kofa zan fita, idan kuma takardar sakin ne ka kawo da kanka to ka bani saboda tafiya zanyi" ta fada cikin fada,
"Ba divorce letter na kawo miki ba pretty, apologise letter na kawo miki" ya fadi ahankali bayan ya zare lollypop din dake bakinshi,
"Dan Allah kiyi hakuri karki fita daga cikin rayuwata, ina yi miki tsananin son da koni ban san adadinshi ba, trust me pretty ban taba son wata ya mace ba wlhi sai ke, akanki na fara so kuma akanki na gama shi domin har yau babu macen da ta taba burgeni sama dake, sonkine yayi sanadiyyar da na kamu da hawan jini, rabuwa dake kamar rabuwa da numfashi nane domin you are my life.... I love you...!" Ya karasa maganar yana kallon fuskarta,
"Hmm nifa duk ba wannan na tambayeka ba.." Ikhlas ta fadi cikin gatsali,
"I know, kaiwai dai ina fada miki ne saboda kisan irin matsayinki awurina pretty, wallahi duk maganganun nan da nake gaya miki babu karya aciki,nafara sonki tun ranar da na fara ganinki, wannan tafiyar da kikayi kika barni har a asibiti ta sakani kwanciya saboda kece rayuwata kece farin cikina, kece burina, you are my everything..." Wasu zafafan hawayene suka gangaro daga cikin idonshi hakan yayi mutukar bawa ikhlas mamaki, shiru tayi ta kasa magana amma ta gama yarda da maganar da yake fada mata gaskiyace babu karya ko kadan aciki sannan son da yake yi mata bana yaudara bane sone tsaftatacce wanda babu algus aciki,amma duk da haka sai ta sake b'ata fuska ta hada girar sama da k'asa,
"Ni bance ka soni ba kuma bana son ka soni har abada, matanka dai wadanda kake so kake kauna to kaci gaba da sonsu da nuna musu kaunar...."
Murmushi yayi ya kalleta har lokacin fuskarshi d'auke take da tsadadden murmushi,maganganunta kamar da alamun kishi aciki, jikinta ya sake matsawa ta yadda har tana jiyo saukar numfashinsa akan fuskarta,
"Ko ki yarda ko karki yarda nidai ke kadai nake so kuma akanki zuciyata tasan zafin so, duk abubuwan da suka faru tsakaninmu wallahi laifinki ne, ikhlas ki tausaya min haka mana, so kike ciwon sonki ya kasheni? Idan ba so kike na mutu da sonki ba ya kamata ki yafe min haka domin kaunarki da sonki sun gama illata rayuwata..."
Kallonshi tayi ta gefen ido kawai sai ganinshi tayi ya sunkuyar da kai ya dafe goshinsa wanda da alama kuka yake yi, wani irin tausayinshi taji yana ratsata tun daga babban dan yatsan kafarta har zuwa tsakiyar kanta sannan ga wani irin shauki dake fisgarta, kasa magana tayi amma tana jin tausayinshi acikin ranta, sunfi minti goma suna zaune shiru babu wanda ya sake kwakkwaran motsi. Sai da lamido yayi kukanshi ya gama sannan ya zaro farin hankicif daga aljihunsa ya goge fuskarsa ya juya yana kallonta,
"Ki bani dama zan wanke laifin da nayi miki" yace da ita ahankali gashi muryarshi har ta dan dishe saboda kukan da yayi,
Tana jinshi ya kunna motar ya fara kokarin barin wurin amma bata iya hanashi ba, lollypop dinshi ya mayar cikin bakinshi yana driving yana sha, har sukaje Roxy hotel dake cikin birnin garin Maiduguri,
"Zo muje" yace da ita bayan yayi packing, babu musu ta fito ta bishi,tana tsaye tana kallonshi yaje ya biya kudin daki ya karbo key din dakin yazo ya kama hannunta suka wuce,
Room 90 shine dakin da ya bude suka shiga, kallonshi tayi ba karamin kyau yayiba shi dinma ita yake kallo da lollypop a bakinshi,
"Abban sadiq wai me zamu yi anan? Dan Allah nidai ka maida ni gida.."
Kallonta yayi ya dan sakar mata murmushi ya matsa kusa da ita
"Zan biyaki bashinki ne, duk kwanakin da nayi ba tare dake ba zan biyaki kayanki duka a yau...".
*_Ummi Shatu_*
No comments:
Post a Comment