Thursday 26 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA.. 74

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

aishaummi.blogspot.com

   *_74_*

~~~Cikin sauri ya kamo hannunta ya janyota baya yana murmushi, ita dinma murmushin take yi tana kallonshi,

"Ke ba zaki yi wankan bane?"

Kai ta daga masa,

"Why?" Ya tambayeta yana kokarin saka kwayar idonshi cikin nata,

"Ni nayi wanka dazu.." Ta bashi amsa, sakin hannunta yayi ya wuce cikin bathroom din yana murmushi kamar wanda aka yiwa bushara da aljannah yau haka yake jinsa,

Bakin gadon ta koma ta zauna tana jiran fitowarsa amma kuma duk atakure take domin bata taba zuwa hotel ba sai yau gashi ta taho su ammi basu sani ba yanzu idan ta koma ko me zatace musu?

Tana cikin wannan tunanin Lamido ya fito ya zauna a bayanta, juyawa tayi ta kalleshi yanda ya matseta sosai,

"Ya akayi?" Ta tambayeshi,

"Kije kiyi wankan" ya mayar mata da amsa,

"Ikon Allah nifa nace maka nayi wanka.."

"Allah sai kinyi wankan nan kinji dai nace Allah" ya fada tareda fara kokarin cire hijabin jikinta,

"Yau naji ikon Allah, wai jikinka ko nawa?"

"Nawa" ya fada yana kashe mata idonshi guda daya,

"Ko ni zanyi miki?"

"A'a nagode" ta fada da sauri,

"To tashi kije kiyi"

Mikewa tayi ba dan taso ba ta nufi cikin toilet din tana cicccije lebe domin bata so,

Rigarshi yasaka ya fita yaje motarshi ya dauko yar karamar jakar kayanshi da ya zo da ita ya koma dakin, towel ya ciro ya nufi bathroom din domin kai mata,

"Abban sadiq nidai gaskiya ka fita..." Ta fada cikin shagwaba,

"Towel fa na kawo miki, shikenan na fita" lankaye mata towel din yayi ya fita ya koma cikin dakin ya kishingida akan gado yana sauraren fitowarta.

Ta dade acikin bathroom din kafin ta fito tana daure da towel dinshi tasaka hijab tana rikeda kayanta a hannu, bakin gadon taje ta zauna tana goge jikinta da dan kwalin kayanta,

Tashi zaune Lamido yayi ya matsa kusa da ita,

"Kawo na tayaki.."

Kafin tayi magana har ya cire hijabin jikinta, bakin gashin kanta ya zubawa idanu yana kallo domin yana mutukar burgeshi, man shafawarshi ta dauka zata shafa nan yayi caraf ya rike hannunta,

"Ai cemiki nayi zan tayaki"

Kwace man yayi ya fara shafa mata ita kam duk yabi yasata jin kunya wanda shi kanshi ya lura da hakan domin kunyarta tana mutukar sake rikitashi, ahankali ya sake matsawa jikinta yace,

"Shy girl..."

Kasa jiyowa tayi domin salon shafa man da yake yi mata dabanne.

  Tashi zaune tayi tana bin dakin da kallo amma babu lamido, kasa kunne tayi sosai nan ta jiyo motsinshi a toilet, murmushi tayi ta shafi kumatunta da hannunta domin yau Lamido ya sakata tayi rayuwa mai dadi mai dauke da tsantsar nishadi aciki wacce bata taba yin irinta ba,

Motsin fitowarshi taji ta dan daga idonta ta kalleshi daga shi sai farin gajeren wando yana sharce ruwan dake jikin sumar kanshi,saurin dauke idonta tayi daga kanshi,

Gaban dressing mirror ya karasa ya fara kokarin shiryawa, babu zato ya hangota ta cikin mirror din tana zaune ta kura masa ido tana kallonshi,

"Yaya dai?" Ya tambayeta bayan shima ya bude manyan idanuwanshi akanta, girgiza masa kai tayi alamun babu komai,

"To ki tashi mana, ko kina sone na fita na barki ke daya a dakin?"

Cikin sauri ta tashi tana girgiza masa kanta ta shiga cikin bathroom tayi wanka ta fito lokacin Lamido yana tsaye yana salla, wuceshi tayi taje ta bude jakar kayanshi ta dauko farar t shirt mai gajeren hannu da blue din jeans ta saka ta dauki hijab itama ta fara sallar, domin sun makara sosai,

Lokacin data idar Lamido yana zaune ya kafeta da ido yana jiran ta, koda tayi sallama suna hada ido ya sakar mata hararar wasa,

"Kinga kin sakani banyi salla akan lokaci ba..."

Dauke kanta tayi daga kallonshi ta mike tsaye, "tunda ni na hanaka to kazo ka mayar dani gida saboda karka rasa ta isha kamar yadda ka rasa ta magrib"

Tashin shima yayi ya isa inda take ya kamo hannuwanta yana kallon kyakkyawan bakinta mai dauke da fararen hakora sosol hadida zagayayyen lips jajaye,

"Idan kin tafi dawa zan zauna?"

"Sai ka zauna kai kadai"

Murmushi yayi ya dauki key din motarshi  yaja hannunta,

"Kayan nan sunyi miki kyau ko nabar miki ne?" Ya fada cikin zolaya,

"Babu wani kyau kawai dai kana zugani ne" tace dashi a shagwabance,

"To naji kibari yanzu muje mu dawo inyaso sai kiyi min shagwabar"

Langabe kai tayi "kai abban sadiq dan Allah nidai na yafe"

Kokarin rufe dakin yayi bayan sun fita ya juyo yana kallonta "see you idle girl har kin fara k'orafi?"

"Ehh na yarda, nidai ka kaini gida yanzu nasan sadiq yana can ya tashi yanata kuka.."

"Babu wani kuka,bayan kin koya masa shan madara saboda rashin kirki"

Hannunta ya kama suka fita har inda ya ajiye motarshi ta shiga suka tafi wurin cin abinci,

"Preety ya kamata ki sakeni haka fa saboda gaskiya na jigatu"

Kawar da kanta tayi gefe "ni na isa na rikeka kai da kake da mata 3 kana niyyar yin ta hudu"

Murmushi yayi ya riko hannunta "inada mata uku amma kuma duk ciki nafi ji dake..."

"Ni kar kayi min dadin baki, idan kaje wurin wata matar taka ma nasan abinda yafi haka zaka fada mata"

Shiru yayi yaci gaba da driving din yana nazarinta, a dan zaman da suka yi dashi ya fuskanci cewar ita mace ce mai kishi sai dai tanada kokarin boye hakan amma wani lokacin kuma yanayin furucinta yana bayyanar da abinda yake cikin zuciyarta,

Murmushi mai sanyaya zuciya yayi "kenan tana kishina?" Ya tambayi kanshi acikin zuciyarshi,

"Pretty kenan! Ko da wasa karki sakawa ranki cewar zan iya fadawa wata mace maganganu masu kama da wanda na fada miki, ki yarda dani"

Daidai lokacin yayi packing agefen titi daidai wani wurin sayar da abinci da kayan makulashe,

"Ki zauna anan bari naje na siyo mana abinci"

"Ka taho min da ice cream"

Bakinta ya kaiwa kiss yana fadin "ai wannan bakin naki yana son ice cream,duk abinda kike so yau zan samo miki domin banida abinda zan iya biyanki farin cikin da kika bani"

Hannunta ta saka ta kare fuskarta, zame hannun nata yayi, "kin san how many marks kika samu?"

Sake rufe fuskarta tayi tana murmushi, ahankali ya rada mata,

"100/100 is your marks"

"Dan Allah ka bari" tafada tana murmushi,

"Shikenan tunda bakya so" yace da ita ahankali,

Sakinta yayi ya fita  daga cikin motar yana murmushi kamar yadda itama take murmushi, binshi tayi da kallo har ya shige cikin shagon, mintuna kadan sai gashi ya fito rikeda ledodi, cikin motar ya shiga ya mika mata kayan, ledar farko ta bude shawarma ta gani,hannu yasa ya gutsuro ya mika mata,

"Bude bakinki kici pretty" yace da ita yana kokarin saka mata acikin bakinta,

Bude bakinta tayi tareda lumshe idonta take Lamido yafara ciyar da ita abincin har sai da kawar ta kanta tace ta koshi, dayar ledar ya bude ya ciro robar ice cream ya mika mata,

"Zaki sha..?"

Cikin sauri ta daga masa kai alamun ehhh, mika mata yayi ya tsaya yana kallonta yana jiran yaga ta fara sha, tunanin ranar da suka sha soyayya a yola ya fara yi ranar da ya kaisu shan ice cream sam ya kasa mantawa da wannan ranar domin ranace wacce bazai iya mantawa da ita ba, gaba daya ya gama shagala da tunanin da yake yi babu zato yaji ikhlas na shafe masa kumatunshi da ice cream din hannunta,

Murmushi yayi ya riketa "kema kina son mu maimaita yanayin rannan ko? Nima ina bukatar hakan pretty, ina son hakan ta sake faruwa.."

Kankameta yayi suka fara kokawa ya kwace ice cream din hannunta ya fara Shafa mata a fuskarta, sun dade acikin wannan yanayi kafin daga bisani ya dauketa zuwa inda suka fito suna zuwa kan gado ya fada ya kwanta ya lumshe  idanuwanshi. Kusa dashi taje ta zauna tana jin sonshi yana yawo acikin jinin jikinta,

"Abban sadiq bacci zakayi?"

Mirginawa yayi ya zagayeta da hannuwanshi yana kallonta,

"Bacci yanzu? Ai yau babu baccin da zanyi"

"Idonka biyu zaka zauna har gari ya waye?" Ta jefa masa tambayar bayan ta zuba masa ido,

"Zancen kike so amma harke a rashin baccin" ya fada tareda sakinta ya koma ya kwanta, bathroom ta tashi ta shiga saboda batayi sallar isha ba, yana daga kwance yana kallonta har ta idar da sallar tazo kusa dashi ta kwanta.

  Har gari ya waye rana ta fito lamido yana manne da ita ya kasa matsawa daga kusa da ita ga wani dan malalacin zazzabi dake rinjayarshi daga shi har ita jikinsu ya danyi zafi kadan, wurin karfe 8 ya mike ya shiga toilet  yayi wanka ya fito ya shirya ya saka coffee colour din t shirt da bakin wando, agefen gadon ya zauna ya kunna wayarshi yana duba sakonnin da suka shigo wanda na matanshi ne sai xahar wacce itama ta turo nata sakon,

Ahankali ikhlas ta bude idonta tana kallonshi, ba karamin kyau taga yayi mata ba domin fuskarshi har wani irin sheki take yi,

Zuba mishi ido tayi taci gaba da kallon kyakkyawar fuskarshi wanda ko kadan shi bai san tana yi ba domin duk a tunaninshi bacci take yi, kallonshi take yi sosai acikin zuciyarta tana tunanin duk wanda yaga lamido kallon saurayi zai yi masa domin babu wanda zaiyi tunanin cewar yayi auren fari balle har ace yana da mata uku,

Babu zato caraf suka hada ido dashi, saurin dauke kanta tayi daga kallonshi, ahankali ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta yana kallon beautiful face dinta,

"Pretty kin tashi?" Yace da ita yana bin kunshin dake tafin hannunta da kallo,

Kai ta daga masa alamun ehh,

"Sorry ki tashi kiyi wanka"

Juyar da kanta ta sake yi, murmushi yayi ya juyo da fuskarta da hannunshi,

"Ki tashi ki shirya, kinji?"

"To ka daina kallo na" ta fada cikin shagwaba,

"To na daina" ya bata amsa bayan ya juya mata baya, tashi tayi ta sauka daga kan gadon tana cewa,

"Kar ka bude idonka please"

Hannuwanshi ya saka ya rufe idanuwanshi yana murmushi,

"Bazan bude ba wuce"

Sauri tayi ta shige cikin toilet din tana lekenshi, sai da yaji shigarta cikin bathroom din sannan ya bude fuskarshi, order din abinci yayi musu kafin ta fito daga wanka har an kawo abincin ajiyewa yayi ya fita domin sauran wayoyinshi suna cikin mota.

Fitowa tayi ta shirya ta fesa turarenshi ta saka kayanta, dan karamin tsaki tayi domin babu kayan kwalliya ita kuma tana son tayiwa lamido kwalliya domin ya taba fada mata cewar yana so,

Ranta a dan bace tana daura dankwali ya shigo cikin dakin, agabanta ya tsaya yana kallonta,

"Menene ya batawa pretty na rai?"

"Babu komai" ta bashi amsa tana girgiza masa kanta,

"Da akwai pretty, ki fada min ko inyi miki kuka.."

Hakan da yafada ne ya sata yin murmushin da bata shirya ba "saboda baka gajiya da kuka?"

Ta tambayeshi tana murmushi, hannunta ya kama zuwa wurinda ya ajiye musu abincin da aka kawo musu,

"Naji dadi tunda na ganki kina murmushi, kici gaba da yin murmushi domin yana yiwa fuskarki kyau"

Wani murmushin ta sake yi, zaunar da ita yayi ya bude breakfast din ya fara bata a baki, shine ya ciyar da ita har sai da ta koshi sannan ta tashi ta koma kan gadon ta kwanta babu jimawa bacci ya dauketa, komawa yayi ya zauna ya dan ci abincin kadan sannan ya koma kusa da ita ya kwanta, wunin ranar sunyi shine manne da juna har sai da yamma tayi sannan ta saka masa darun sai ya mayar da ita gida, ba dan yaso ba haka ya dauketa suka nufi gidan,

Yana rike da hannunta yana driving da daya hannun sai labari yake bata wai wani lokaci sunyi dare shida bash police suka taresu zasu tafi dasu police station wasu karnuka suka fito sunfi guda talatin nan police din suka baje suka barsu shida bash,

Dariya sosai ikhlas take yi domin labarin yayi mutukar bata dariya sannan bata taba tsammanin lamido ya iya surutu haka ba sai yau domin baya yi, har sukaje kofar gidan yaya hassan dariyar take yi, amma sai dariyar tata ta yanke saboda ganin yaya Hussain tsaye fuskarshi a murtuke sai muzurai yake yi,

Jiki asabule ta fito daga cikin motar, shima lamido fitowar yayi ya nufi yayan nata wanda daga gani babu tambaya domin kamarsu kusan daya da ita,

"Ke daga ina kike? A ina kika kwana? Dama ashe ke sokuwace shashasha ban sani ba?" Yaya Hussain ya fada cikin masifa,

"Um yaya dama, dama abban sadiq ne yazo shine...." Ta bashi amsa cikin rawar murya,

"Shine kika bishi ko? Saboda bakida zuciya baki san ciwon kanki ba, mutumin da ya gama wulakantaki agidanshi ya nuna miki cewar bai damu dake ba shine har yanzu zai zo yayi miki dadin baki ki yarda? To bari in fada miki kiji irin wadannan yan duniyar sun wuce duk inda kike tunani kuma wallahi ko bana nan ban yarda ki sake kulashi ba balle har ki bishi kinji dai na fada miki, dalla wuce ciki kibar nan ko na bugeki.."

Juyawa yayi ga lamido wanda yake tsaye yana kallonshi,

"Kai kuma ina mai gargadinka da ka fita daga harkar yarinyar nan domin muddin ina raye to bazata koma gidanka ba garama ka saketa ka daina batawa kanka lokaci idan kuma baka saketa ta dadin rai ba to kasani zaka saketa ta cikin bacin rai da tashin hankali"

Yana kaiwa nan ya juya yabar lamido awurin ya nufi cikin gida wurin ikhlas....!



_*Ummi Shatu*_

No comments:

Post a Comment