Tuesday 17 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA.. 71

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_


   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

     _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

  aishaummi.blogspot.com

   *_71_*

~~~Shiru dukkaninsu suka yi in banda ikhlas wacce ta fashe da kuka harda shassheka,

"To kuma menene abin kuka? Keda Allah ya rufa miki asiri, dama wannan addu'ar muka dade muna yi miki domin kada wannan yaron ya girma wata rana ya nemi ki nuna masa ubanshi ki kasa.." Hajiya tace da ita tana kokarin karasa shigowa cikin dakin,

"Ki daina kuka ikhlas wannan abun kiyi farin ciki ne domin yanzu hankalinki zai fi kwanciya.." Ammi ta fada tana kallonsu,

"Ammi baki san fa irin wulakancin da yayita yimin ba kawai saboda na nuna mishi bacin raina akan abinda yayi min" ikhlas ta fada cikin gurshekin kuka,

"To da waye yace miki ki nuna masa bacin rai? Ai bacin rai ya kare tunda har Allah ya rufa miki asiri uban wannan yaron ya bayyana.." Hajiya ta sake fada,

"Dan Allah hajiya ya isa haka... Ya za ayi ku rinka goyon bayanshi? Nifa akan wannan maganar wallahi ko kotune sai muje dashi domin a kwato mata hakkinta kuma bazata koma gidanshi ba har sai ya gane kuskurenshi.." Yaya Hussain ya fada cikin fada

"Adai yi hakuri abi komai a sannu" ammi tace da Hussain cikin sigar rarrashi,

"Ai wallahi sai ya gane kuskurensa sannan kuma bai isa mun bashi abdallah ba sai dai yayi duk abinda zaiyi,kuma wallahi indai ba itace tace zata koma ba to dole sai ya saketa"  Hussain ya sake fadi tareda ficewa fuuuuu cikin fushi,

"Dadina da Hussain akwai zuciya da zafin rai" hassan ya fadi,

"Barshi yayita yi dan me da masifar tsiya" inji hajiya,

"Allah dai ya kyauta" ammi ta fadi amma acikin zuciyarta murna ce fal wacce ita kadaice tasan dalilinta.

  Karfe 5 daidai lamido ya dawo gida, fadila da ihsan ya iske a falo suka yi mishi sannu da zuwa ya wuce dakinshi,

Wanka yayi ya fito ya koma falo inda fadila ta shirya girki domin ranar girkinta ne, zama yayi yaci abincin ya tashi ya fita salla, lokacin da ya dawo daga salla zama yayi a falo ya fara kallon ball har lokacin sallar isha yayi, masallaci ya koma yayi salla ya dawo ya sake zama a falo, harsu ihsan suka gama zamansu suka tashi shi yana nan a zaune sai da 9 tayi sannan ya tashi ya nufi dakinshi kamar wanda aka cewa ya dawo sai ya dawo da baya ya nufi dakin ikhlas domin yau sam baiyi ido hudu da itaba kuma baiji koda kukan sadiq ba,

Dakin nata ya bude ya shiga nan ya ganshi duhu dindim babu alamar haske, fitila ya kunna ya shiga cikin dakin rasss! Zuciyarshi ta harba domin dakin wayam babu ita babu sadiq,

Toilet ya bude ya leka nan dinma hakan take babu kowa, cikin sauri ya fita daga dakin har yana yin tuntube,

"Ina pretty ta tafi?" Ya tambayi kanshi bayan ya zaro wayarshi daga cikin aljihunsa, dakin ihsan ya nufa a sukwane ga waya kuma yana kiran innah,

Ko sallama babu ya fada dakin Ihsan, fitowarta kenan daga wanka tana daure da towel "my ihsan yau kinga maman sadiq agidan nan?" Ya tambayi ihsan arude,

Girgiza masa kai tayi "gaskiya yau ban ganta ba kwata kwata jiya dai mun hadu a falo zata shiga kitchen"

Juyawa yayi da sauri ya fita yana magana "ko ina innahn ma ta shiga? Inata yi mata waya taki dauka.."

D'akin fadila ya tasamma yana shiga yayi karo da ita itama tana kokarin fitowa,

"Fadila yau kinga ikhlas acikin gidan nan?"

"Ban ganta ba, lafiya?" Fadila ta bashi amsa, batare da ya mayar mata da amsaba ya juya yayi waje, wurin mai gadi yaje ya fara tambayarshi da yaushe ikhlas ta fita, nan maigadi yace tun safe ta fita da katon akwati,

Motarshi ya nufa ba tare da yace komai ba ya daukota a zabure ya fita, gidan barrister elmustapha ya je ya tura aka yi masa sallama dashi ya fito bayan sun gaisa ya tambayeshi ko ikhlas tazo?

Cikeda mamaki elmustapha yace "lafiya? Nidai yau banji ni'ima tace ikhlas tazo gidan nan ba"

"Shikenan sai da safe nagode"

Motar tashi ya koma ya shiga ya figeta ya nufi gidan innah yasan duk yanda akayi ikhlas can ta tafi, yana zuwa ya shiga ciki jikinshi har rawa yake yi,

"Innah ina ikhlas take?" Ya jefawa innah wannan tambayar daidai lokacin da ya shiga cikin dakinta,

"Ikhlas kuma? Ai ikhlas yau bata zo gidan nan ba lamido, ko wani abune ya faru?" Innah ta tambayeshi hankalinta atashe,

"Innah ikhlas bata gidana, ban san inda ta shiga ba" lamido yace da innah idonshi cikeda kwalla,

"To ka kirata awaya mana"

"Wallahi innah ko na kirata ba dauka zatayi ba"

"Ka kirata dai kaji"

Wayarshi ya zaro ya fara kiranta amma shiru shiru bata dauka ba harta katse yasake kira nanma shiru taki dauka da haka har sai da yayi mata miss called fiyeda goma,

Text massage yaga ta turo mishi kamar haka:-

   _Kadaina kirana haka domin bacci zanyi nasan abinda zaka tambayeni bai wuce a ina  nake ba, to ina Maiduguri gidanmu cikin gatana inda ake sona ake kaunata,Lamido ko kai kadaine autan maza to na hakura dakai bazan sake zaman aure da kaiba, idan ka samu dama kana iya turo min da takardar sakina.._

Ai lamido yana gama karanta sakon nan hankalinshi ya tashi kololuwar tashi take kwallar idonshi ta zubo akan kumatunshi,

"Innah kinji wai tana Maiduguri, wai bazata dawo ba sai dai na saketa..." Ya fada kamar Zararre,

"Fada kuka yi ko me? Menene ya hadaku?" Innah ta jero masa wadannan tambayoyin ajere, jikinshi ne ya fara rawa domin ya zama dole ya fadawa innah saboda ranar wanka ba a boyon cibi,

"Innah wallahi fushi take dani tun lokacin da na fada mata gaskiyar cewa nine mutumin da ya....." Shiru yayi kasa karasawa,

"Yayi mata me?" Innah ta tambayeshi cikin kaguwa,

"Innah ki yafe min nasan da lokacin da ina dan makaranta nayi rashin ji iri iri amma wallahi innah yanzu na tuba, wallahi yanzu bana aikata ko wanne irin laifi, tun lokacin da kuka yimin aure wallahi na shiryu amma innah ki taimaka min domin ikhlas itace rayuwata wallahi bazan iya rayuwa ba sai da ita..."

"To ai lamido ni na kasa gane inda maganar taka ta dosa"

"Innah fyade nayi mata tun shekaru wurin shida da suka wuce amma wallahi bada niyya nayi b...."

Tun kafin ya karasa innah ta daukeshi da mari har guda biyu ajere, rike kuncinshi yayi ya daga ido yana kallon innah domin tun tasowarshi innah bata taba marinshi ba sai yau,

"Akan wannan ne dama zaka zo ka sameni kana yimin surutu? Ka fice min daga daki ka bani wuri, ai gara kar ta dawo din domin indai hakane to baka da halin kwarai shashasha kawai, fice min daga daki" innah tafada cikin tsawa, juyawa yayi ya fita yana hawaye ya nufi dakin baffa,

Yana kishingide akan darduma yana jan carbi, tunda baffa yaganshi yasan ba lafiya ba dan haka ya mike zaune yana kallonshi,

"Lamido lafiya?"

"Baffa dan Allah dan annabi ka taimakeni, kada ka juya min baya kamar yadda innah tayi min, wallahi ina sonta itace ratuwata bazan iya rayuwa babu itaba.."

Dafashi baffa yayi "wacece?"

"Wacece kuwa banda matarsa ikhlas wacce yayiwa fyade saboda shi cikakken marar imani ne, shine kuma yanzu zai kwaso jiki yazo yace wai muje mu dawo masa da ita, to bari kaji ko zaka mutu ikhlas ba dawowa gidanka zatayi ba, hakan da tayi yayi daidai domin babu amfanin zama da fasiki idan ba ahali irin na lalura ba" innah dake bakin kofa ta fada tana huci,

A furgice baffa ya kalli innah "ban gane abinda kike nufiba? Kun sani a duhu"

"Gashi nan yayi maka bayani da bakinshi abinda ya faru.."

"Lamido wai me yake faruwa ne?" Baffa ya sake tambayarshi,

"Baffa wallahi ba laifina bane kaddara ce tasa har nayiwa ikhlas fyade..." Lamido ya fada yana kuka,

Cikin fushi baffa yake kallonshi "kuma to mu yanzu me kazo muyi maka?"

"Zuwa yayi muje mu dawo masa da ita mana saboda tatafi gidansu tace bazata zauna da fasiki ba" innah ta bawa baffa amsa ranta abace,

"Ni zanje na dawo maka da ita? To saurara kaji sai dai ka mutu amma zaman aure da wannan yarinyar kun gamashi, ni ba mutumin banza bane kuma bazaka mayar dani wofi ba dan da ace ma tun farko nasan ka aikata haka to da ban bari ka aureta ba amma yanzu ka jira takardar sammaci dan na tabbata yan uwanta ba zasu kyaleka sai sun gurfanar dakai agaban kotu" baffa ya fada cikin fushi tareda mikewa zai tafi, kafarshi lamido ya rike yana kuka,

"Baffa dan Allah kuyi min afuwa ku yafe min domin abinda ya faru kaddara ce..."

Fincike kafarshi baffa yayi ya kada kai ya fice daga falon innah ta mara masa baya suka bar lamido durkushe anan yana aikin kuka,

Mikewa yayi kanshi yana wani irin ciwo ga juyawa da yake yi, ko ba afada masa ba yasan hawan jininsa ne ya tashi domin yana dashi kuma ata sanadiyyar ikhlas ya hadu dashi,

Motarshi yaje ya shiga zuciyarshi sai bugawa take yi da karfi,ga hajijiya dake daukarshi, wayarshi ya dauka ya kira bash anan ya zayyana masa dukkan abinda ya faru, sosai bash ya jinjima lamarin acikin ranshi,

Kashe wayar lamido yayi ya finciki motarshi ya nufi gida, ikon Allah ne kadai ya kaishi gida domin titin ganinshi yake yi bibbiyu kamar wanda yasha kayan maye,

Yana zuwa ya shiga cikin dakinshi ya kwanta, kamar wanda ciwon ke jira yana kwanciya zazzabi ya kawo masa ziyara baya ga ciwon kai da ya sarke shi, juyi ya fara yi akan gado nan kuma ya fara amai har ya gangaro kasa daga kan gadon, wani azababben ciwon ciki da ciwon kirjine ya sako masa kai daga nan bai sake sanin halinda yake cikiba.

Fadila ce ta shiga cikin dakin nashi cikin shirin bacci nan tayi ido hudu dashi yashe akasa acikin amai bakinshi yana fitar da wani farin kumfa kamar wadda yaci guba, agigice ta ruga da gudu zuwa dakin ihsan wacce ita tuni tayi bacci ma,

"Ihsan, ihsan tashi, kitashi lamido zai mutu"

Zabura ihsan tayi ta diro daga kan gado domin jin abin tayi kamar a mafarki, tare suka sake runtuma zuwa dakin lamido, ganinshi yasa ihsan rudewa,

"Mun shiga uku me yaci?" Ihsan ta fada arude,

"Fadila dauki wayarshi ki kira koma wanene azo akaishi asibiti domin wallahi ni bazan iya driving acikin Daren nan ba"

Arude fadila ta dauki wayarshi ta yi dialling ita bata ma san kowa ta kiraba ashe bash ta kira domin shine mutum na karshe da suka yi waya, yana dauka ta fashe da kuka tana cewa "dan Allah ka taimaka mana kazo mu kai lamido asibiti kar ya mutu..."

Ai afirgice bash ya diro daga kan gadonshi, mintina kadan ya karaso gidan, su ihsan sai kuka suke yi sun sakashi agaba sun kasa koda tabashi, babu wata wata bash ya daukeshi a kafadarshi yayi waje dashi, hijabansu suka debo kawai suka bi bayan bash sunma manta da cewar kayan bacci ne kawai ajikinsu.

Wani dan karamin asibiti suka kaishi amma bash ba karamin gudu yayi ba kafin su isa abibitin, su ihsan kuwa sai faman kuka suketa yi kamar ransu zai fita,

Wasu nurses ne suka taimakawa bash suka shigar da Lamido wani dan daki wanda za a dubashi aciki, hankalin bash ba karamin tashi yayi ba domin ganin halin da lamido yake ciki,daya daga cikin nurse din da suka shigar da lamido ne ta fito tana kallonsu arude,

"Am sorry to say ina tunanin fa patient din da kuka kawo tuni ya dade da rigamu gidan gaskiya saboda guba yaci....".


*_Ummi Shatu_*

11 comments: