Thursday 26 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA..!73

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

      _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

      _Fatan alkairi gareku masu sunan k'awata,Khadija Ahmad (Kdeey) & Khadija Magaji bk,ina gaisheku aduk inda kuke._

  aishaummi.blogspot.com

    *_73_*

~~~D'agowa da kanta tayi ta kalleshi yanda ya rank'wafo kusa da ita har tana jin fitar numfashinsa,

Matsawa tayi ta koma gefen gadon ta zauna tana kallonshi, ko shakka ba tayi abinda ya fad'a mata d'azu gaskiyane har cikin ranshi sai dai bata son ta karbi ban hakurinsa cikin gaggawa gudun kar asake maimata gidan jiya,

"Kazo ka mayar dani gida..." Tace dashi ahankali bayan ta dauke idonta daga kallonsa,

Kusa da ya ita ya matsa ya zauna yana mai kallon kwayar idonta,

"Preety... Kece fa da bakinki kikace in baki hakkinki kamar yadda nake bawa kowacce mace acikin Gidana, to yanzu na shirya baki hakkin naki harma da sauran bashin da kike bina..."

Ji tayi kamar k'asa ta bud'e ta shiga dan kunya domin lokacin da ta furta masa hakan hankalinta ya gushe ne shiyasa, saurin kawar da kanta daga barin da yake tayi tana jin zuciyarta tana bugawa ahankali ahankali,

Binta da kallo ya fara yi wanda da bai samu zarafin yiba sai yanzu, idonshi ne ya kai kan jan lallen dake zane a tafin hannunta kasancewar ana igobe sunan matar yaya hassan anyi musu kunshi itada mai jego, ahankali ya mika hannunshi ya kamo nata ya soma bin kunshin da kallo,

"Woww.." Ya fad'a ahankali, hannunta ta fara k'ok'arin k'wacewa amma ta kasa saboda ya rik'eshi gam acikin nasa,

"Ka sakar min hannuna" tace dashi ba tare da ta jiyo ba,

Murmushi Lamido ya yi ya sake matsawa kusa da ita hadida rungumeta ta baya ya d'ora kanshi akan kafad'arta,

"Ikhlas banida bakin da zan baki hakuri domin nasan laifina mai girman gaske ne agareki amma duk da haka zance kiyi hakuri ki yafe min wallahi ina sonki, so mai tsanani"

Zoben hannunta ya kamo yana murzawa "kinga wannan zoben? Nine na saka miki shi bayan na cire wanda yake jikin dan yatsanki.."

Jikin ikhlas ne yayi sanyi aranta ta fara tunanin ashe kenan Lamido shine silar warkewarta domin tabbas shine mutumin da ya rabata da zoben da anty nafi ta bata ta saka acikin yatsanta wanda sakamakon haka ciwon hauka ya kamata,

Lumshe idanuwanta tayi ta yi luf ajikinsa tana sauraron kalaman da yake sanar da ita,

"Ina rokonki da ki yafe min duk abubuwan da suka faru, duk abubuwan da nayi miki laifinki ne saboda kece kika tilastani yin hakan amma wallahi ba dan bana sonki nayi miki ba"

Juyowa yayi da ita tana fuskantarsa, "nasan abinda nayi miki da ciwo da zafi da bacin rai amma ki daure ki yafe min please, ina sonki ikhlas, ina sonki fiyeda kowacce mace a duniya ki rike wannan a ranki kece macen da na fara so a duniya kuma har gobe baki sauya min ba dan haka ki daure ki yafe min..."

Hannuwanshi yasa ya tallafo kumatunta yana kallonta,

"Kin yafe min? Uhmm?"

Lumshe idanuwanta tayi tana jin lauassasun hannunshi bisa kuncinta ba tare da tayi magana ba,

"Ko baki yafe min bane..?" Ya sake tambayarta,

D'aga masa kanta tayi alamun ehhh,

Murmushi yayi ya dauketa cancak ya d'orata ajikinshi ya rungumeta tsamtsam yana jin wani irin farin ciki yana ratsashi,

"To me kike son inyi miki ki yafe min? Ko sai na biyaki bashinki sannan zaki yafe min?" Ya rada mata acikin kunnenta,

Kunya yasata ji dan haka tayi gaggawar cusa kanta cikin kirjinshi,

"Hakika yau ina cike da farin ciki domin na dade ina burin zuwan wannan ranar, ranar da zamu fuskanci juna nida ke ikhlas, babu shakka Allah ya soni da rahama shiyasa ya cika min burina ya mallaka min ke a matsayin mata"

Ikhlas dai lukus tayi acikin jikin Lamido ta kasa koda kwakkwaran motsi,

"Ka maida ni gida kaga yanzu sadiq ya tashi"

"Ai keda komawa gida sai gobe garama ki kirasu awaya ki fada musu"

"Yi hakuri dan Allah, daga fitowa sai ajini shiru ban koma ba?" Tace dashi fuskarta a shagwabe,

Wayarshi ya ciro daga cikin aljihun wandonshi ya mika mata,

"Ungo ki kirasu ki fada musu" ya dagota daga jikinshi yana mika mata wayar,

Fuskarta ta kawar taki amsar wayar, "kinga idan baki karba ba har na kashe wayar nan ba sake kunnawa zanyi ba sai gobe"

K'in karb'a tayi ta sake d'auke kanta hakan da tayi ya sake bawa Lamido sha'awa,

"Idan na k'irga 10 baki karb'a ba kashe wayata zanyi kuma babu ruwana tunda laifinki ne..."

Nan dinma shirun ta sake yi dan haka ya fara k'irgawa "1...,2..3...4...5...6...7...8..9..."

Kafin yace 10 tayi saurin mik'a hannunta ta kamo phone din,

Murmushi yayi ya rik'e hannunta wanda baya gajiya da kallonsa akoda yaushe domin kyaun da yayi,

"Ashe kina ji ai na dauka bakya ji"

Damk'a mata wayar yayi acikin hannunta yana kallon fuskarta,

Anty Farida matar yaya Hussain ta kira amma shiru bata daga ba hakan yasata tura mata text massage, massage din yana tafiya ta mika masa wayar idonta yana kallon k'asa,

Lollypop din da yake sha ya mik'a mata zai saka mata acikin bakinta,kawar da kanta tayi,

"Ni bazan sha kayan yara ba.." Ta fadi cikin shagwaba,

"Ni naji ni yaronne, nagode"

"Ni ai ba da kai nake ba saboda ban isa na cewa mai mata hud'u yaro ba"

Murmushi yayi ya riko hannunta "ni mata na uku ai banyi ta hudun ba ko?"

D'auke kanta ta sake yi bata amsa masa ba,hakan ya sashi sakar mata da dan malalacin murmushi,

"Nagaji sosai saboda driving din da nayi daga yola zuwa nan pls taimaka min nayi wanka kinji"

Kallonshi tayi saboda yanda ya langab'ar da kanshi kamar wani k'aramin yaro,

"Please pretty na" ya sake fada yana sake langab'ewa, kwayar idonta ta sauke akasa domin yau ta fuskanci Lamido shagwaba yake ji ba kad'an ba, yau yarintarshi ce ta tashi,

"Ko naje na hada ruwan da kaina?" Ya sake tambayarta, tashi tayi ba tare da ta sake kallonshi ba ta nufi cikin bathroom din kafin ta fito har ya cire kayanshi ya rage daga shi sai gajeren wando, tana fitowa suka yi karo a kofar toilet din yana kokarin shiga, dafe goshinta tayi,

"Washhh..!" Da sauri ya rikota jikinshi yana kallon goshin nata,

"Am sorry my dear..." Yace da ita ahankali, harararshi ta danyi tafara kokarin barin wurin,kunnuwanshi ya kama da hannunshi,

"Double sorry preety"

Juyawa tayi fuskarta dauke da murmushi....



   _masu karatu kuyi hakuri na yau babu yawa kun san jiki da jini kwana biyun nan lafiya bata isheni ba ina fata zaku yimin uzuri._

_Gaisuwa mai tarin yawa gareku Hajjaju & fa'iza nagode sosai da kulawarku._


*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment