Saturday 7 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA..4-5

*RUWAN KASHE GOBARA..!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_


  _*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_


   _Sadaukarwa ga k'awata Khadija Sidi_


_4_


~~~ Tsinke wayar yayi yana murmushi domin daga jin irin amsar da likitan yabashi yasan za ayi nasara,

Tashi yayi da kyar ya shiga toilet yayi alwala ya fito sai alokacin yayi salla, yana zaune akan abin sallar yana tunanin wannan mahaukaciyar, baffa da inna suka shigo,

"Lamido, me kuma ya sameka? Ina fata ba shaye shayen naka da ka sababa kaje kayi ka dauko wata lalurar ba?" Mahaifinsa yafada lokacin da yake kokarin shigowa cikin dakin,

Dagowa da kansa Lamido yayi,

"Baffa zazzabine fa kawai"

"Rufe min baki yaron banza, duk kabi ka gama zubar min da mutuncina agarin nan, baka da aiki sai shan kayan maye da lalata yayan mutane"

Sunkuyar da kai Lamido yayi domin dama ya kwana da sanin zai sha fada awurin baffan,

"Baffa tunda bashi da lafiya kayi hakuri.." Mahaifiyarshi tafara magana kafin baffan ya katseta,

"Ki barni dashi Zaituna,wannan yaron bashida hankali ko kadan, bashida tunani, kullum shi kenan acikin shan abubuwan maye, to ka saurara kaji, idan kaje can turai din ya rage ga naka ka tsaya ka nutsu ko kuma sabanin haka, nidai nagama duk abinda zanyi maka a matsayina na uba,ka duba kaga jiya har 12 baka dawo gidan nan ba kana can kana yawon gantalinka, to duniya dai ta ishi kowa riga da wando, wanda bai zo bama tana nan tana jiransa"

Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga cikin dakin cikeda takaicin halayya irinta danshi Lamido,

Inna ce ta matsa wurin lamidon ta dafa kafadarshi,

"Lamido dan Allah ka tsaya ka nutsu ka daina wannan shashancin kaji, baka koyi da dan uwanka wanda shi ya kasance nutsattse mai hankali, ka zauna kayi karatun ta nutsu kaji,Allah yayi maka albarka"

Tashi yayi ahankali batare da yace komai ba ya hau kan gadonshi ya sake kwanciya ya tukunkune acikin bargo domin wani zazzabin ne yake neman rufeshi.


*

  Ahankali ta bude idanuwanta, wurin datake tafara bi da kallo, kallonta ta mayar kan jikinta,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" tafada ahankali tana shafa kanta,

Ayanda taji gashin kanta acukurkude ya sanyata mikewa arazane amma babu shiri ta koma ta zauna sakamakon wani irin zugi da radadi da take ji ajikinta,

Bin ko ina take yi da kallo tana mamakin meya kawota nan,yanayin yanda wurin yake ya sanyata gane cewar tabbas wurin kasuwa ne,

Jin danshi akasanta ya sata dubawa jini tagani ajikinta sannan ga wani zafi yana ratsata,

K'arar hadarin da yake ta gudu a sararin samaniya ne yasata mikewa ahankali, kafarta babu takalmi haka ta doshi bakin titi tana dingishi, jinta take kamar sabuwar halitta kamar ba itaba,

"To nan inane? Ni kuma meya kawo ni nan? Kodai mafarki nake?" Wadannan tambayoyin ta jerowa kanta amma bata da wanda zai bata amsar tambayoyinta.

Titi ta mike sambal tabi tana tafiya ahankali batare da tasan inda zataje ba.





*_Ummi A'isha_*
[12/3/2016, 1:33 PM] Itz Ummi Shatu🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_



_5_



~~~ Tafiya taci gaba dayi ahankali ahankali cikin dingishi har ta danyi tafiya mai dan nisa, daidai lokacin aka fara yayyafi yif yif,

Haske tagani sosai ya haske mata ido wanda har bata iya hango gabanta,

Wata irin faduwa gabanta yayi zuciyarta ta harba da karfi, take ta sulale awurin ta fadi,

Cikin sauri mai motar ya fito da gudu yazo ya kinkimeta yayi cikin motar da ita,wuta yabawa motar ya nunku cikin gari, bai tsaya ako ina ba sai awani dan karamin asibiti mai zaman kansa,

Yana zuwa ya kira nurses mata guda biyu suka taimaka masa suka kinkimeta suka shigar da ita wani dan madaidaicin daki, shidai wannan bawan Allah waje yakoma ya zauna yana jiran abinda zaije ya zo domin likita yasamu zarafin shiga dakin da marar lafiyar tasa take ciki.


Sai da likitan ya kwashe kimanin sama da sa'a daya sannan ya fito hannunsa rikeda wani jan file,

"Kaine wanda ya kawo wannan baiwar Allahr ko?" Likitan ya tambayeshi yana gyara zaman farin tabaran dake manne a fuskarshi,

"Ehh nine likita, Allah dai yasa ba mutuwa tayi ba" yafada bakinsa yana rawa,

"Bata mutu ba sai dai inada wasu yan bayanai wadanda nake son sanar dakai amma yanzu ka biyoni zuwa office dina" likitan yafada tareda juyawa ya nufi office dinsa,

Bin bayansa shima mutumin yayi duk hankalinsa atashe,

Kujera likitan ya samu ya zauna tareda nunawa mutumin wurin zama,nan shima ya zauna yana fuskantar likitan,

"Bawan Allah ko zaka iya fada min alakarka da wannan marar lafiya da ka kawo? Da kuma dalilin dayasa ka kawota nan?" Likitan ya tambayeshi tareda kura masa ido kurr,

"Ehh to zan iya, dafarko dai ni sunana barrister elmustapha mamman, ina zaune anan garin yola awata unguwa wacce ake kirada sabon loko, tun tsawon lokuta masu yawa fiyeda shekaru biyu ina ganin ita wannan yarinyar abayan kasuwa da cikin tasha ko gefen titi tana yawo cikin hali irin na lalura wato tabin hankali to kuma dazu nadawo zan wuce ta gaban sabbin titunan nan kawai sai naganta tana tafiya amma kuma sai naga haka kawai ta yanke jiki ta fadi awurin, wannan dalilin ne ma yasa na taimaka mata na daukota nakawota nan"

Ajiyar zuciya likitan yasaki ya dan dafe kumatunsa da hannuwansa guda biyu,

"Tabbas naji bayaninka kuma na gamsu, wato a binciken dana gudanar nasamu damar gane cewa wannan yarinyar mai tabin hankali ce sai dai yanzu haka ta samu lafiya, sannan abu na biyu shine anyi mata fyade acikin wannan daren domin har yanzu da akwai sauran alamun hakan atattare da ita"

Ido barrister elmustapha ya zaro yana mai jijjiga kai, "hakika indai hakane to lallai acikin mutane akwai marassa imani, da ace zan samu wanda yayiwa yarinyar nan wannan mummunan aikin da wallahi sai na gurfanar dashi agaban shari'a, da sai na kwato mata yancinta, wannan ai cin zarafine in banda haka tayaya mutum zai yiwa mahaukaciya fyade" ya karasa maganar yana hucin takaici,

"Babu komai Allah zai saka mata, yanzu dai mun gudanar da dukkan gwaje gwajen da suka kamata muyi mata mun samu bata dauke da kowacce irin cuta, nasan nanda karfe 1:30 nadaren nan zata iya farfadowa" likitan yace dashi yana duba agogon hannunshi,

"Nagode dr yanzu ina son ka sanar dani duk wasu abubuwa wadanda ake bukata"

"Ba a bukatar komai sannan nima duk wata kulawa da za abata to zan yishine abisa kyauta, bana bukatar ko kobon ka, Allah ya bata lafiya"

"Mun gode dr Allah ya saka da alkhairi"

Hannu barrister elmustapha ya mika masa sukayi musabaha ya tashi yafita daga cikin office din.





_*Ummi Shatu*_

No comments:

Post a Comment