Friday 6 January 2017

MARTABA TA 51-End

🏻: 👑 MARTABA TA👑

  Na
UMMI A'ISHA


51-52


~~~Hmmm A'isha kenan Allah dai ya bamu mafita pherty ta fada ahankali,

"Amma ni sai nake ganin yaya aadil yafi cancanta da aurenki pherty, duk da cewar nasan ke jawad kike so acikin ranki" Sadiya ta fada tana kallonta,

"Tabbas idan nace muku bana son jawad nayi karya, amma ahalin yanzu son da nake yiwa yaya aadil ya danne wanda nake yiwa jawad"

"Pherty nikuma idan nice ke jawad zan aura, saboda shi saurayi ne bashida mata, matashi mai karancin shekaru, zaku rayu sosai zaku ci soyayya, sannan kuma zaku more rayuwar aurenku fiyeda ace kin auri yaya aadil domin shi ko babu komai shekarunsa sunyi wa naki nisa, sannan kuma kinga yana da mata dole matarsa zata rinka kawo miki cikas fa" A'isha ta fada kamar zata saka kuka,

"A'a A'isha yaya aadil yayiwa pherty alkairi mai yawa kinga bai kamata tayi masa butulci ba, kuduba zancen nan nawa fa" Sadiya ta fada,

"Ya isa haka, time for prayer" pherty ta fada tana kokarin mikewa.


  Daren ranar babu wacce tayi bacci acikinsu haka suka kwana suna hirar jawad da aadil har gari ya waye, kowaccensu shiryawa tayi suka fita lectures bayan sun yi breakfast,

Karfe 11 daidai pherty ta fito daga lecture din da tayi amma kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar tana cikin damuwa.

   Hango jawad tayi tsaye jikin motarsa yana yi mata kallon kurulla, kallonsa ta danyi ta fara kokarin barin wurin da sauri yabi bayanta

"My queen" ya fada cikin tausashasshiyar murya,

Juyowa tayi ta kalleshi "jawad kayiwa Allah ka rabu dani dan Allah"

"Pherty kin san kuwa abinda kike fada? Taya zan iya rabuwa dake? Rabuwa dake tamkar rabuwa da numfashi nane pherty, kece rayuwata, wlhi bazan iya rabuwa dake ba"

Kallonsa ta tsaya yi ba tare da tace komai ba, yana sanye da riga da wando bakake abinku da farar fata sai kayan suka yi mutukar karbarsa,

Karasowa gabanta yayi ya tsaya,

"Pherty karki manta soyayyar mu, karki manta da jawad dinki pherty"

"Dama ta yaya zan iya mantawa da kai jawad? Ai bazan manta dakai ba tunda kayi sanadiyyar rabuwata da iyayena, kayi sanadiyyar rashin lafiya agareni, kayi sanadiyyar rushewar MARTABA TA, sannan kayi sanadiyyar....!"

"Ya isa haka pherty, ya isa dan Allah, wai pherty so kike na mutu ne? Eye? Nace so kike na mutu?" Gabanta ya karasa

"Ki kasheni pherty, nace ki kasheni tunda bakya sona"

"Ni bazan kasheka ba amma dai abinda nasani shine bazan taba aurenka ba, ko maza sun kare a duniya jawad bazan taba aurenka ba"

"Kika ce ba zaki aure ni ba?". Murmushi yayi mai kunshe da damuwa,

"Wallahi kuma ni zaki aura saboda nine nake sonki, aadil ba sonki yake ba domin nafiki sanin ko waye shi, pherty wallahi ni zan aureki mutukar ina numfashi" ya karasa maganar daidai lokacin da hawaye yake bin kumatunsa,

"Kaga malam idan kai baka da abinyi to ni ina dashi dan haka sai anjima" juyawa tayi da niyyar tafiya, cikin sauri ya janyo gefen mayafinta, tana jiyowa ta daga hannu da niyyar kai masa mari amma sai ta fasa,

"Meyasa kika fasa? Ki mare ni mana pherty, ki mareni amma wata rana zakiji kunya saboda kin mari mijinki,sannan ki ajiye acikin ranki wlhi ni jawad nine mijinki, ki saka wannan acikin zuciyarki"

Juyawa tayi tabar masa wurin cikin tashin hankali, juyawa jawad yayi ya koma ya dauki motarsa ya nufi hanyar ficewa daga cikin makarantar, daidai bakin gate din fita yaga motar aadil tana kokarin shigowa, glass din motarsa ya sauke ya dallawa aadil harara ya wuce, shima aadil din bin motar jawad din yayi da harara ya wuce ciki.

  A inda ya saba tsayawa yau ma anan ya tsayawa yana jiran gimbiyar tasa, yana zaune ya hangota tana tahowa cikin tafiyarta ta nutsuwa, tana sanye da jar atamfa ta yafa jan mayafi,tausayinta yaji acikin zuciyarta saboda tunowa da yayi da lalurar da take tare da ita,

"Assalamu alaikum yayana" ta fada tana murmushi

"Wa alaikissalam pherty na, amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida" ya fada cikeda zolaya

"A'a yaya bazan ma kashe muku da ba"

"To ai kin isa ne pherty na"

Murmushi ta dan yi bata yi magana ba,

"Kin San dalilin zuwana yanzu?" Ya fada yana kallonta

"A'a sai ka fada yayana"

"Zuwa nayi naji wanne irin gado kike so? Royal bed kikeso ko Italian bed, ko kuma dubai bed?"

Gabanta taji ya fadi tab yanzu zan kwana gado daya da yaya aadil watarana? Tambayar da tayiwa kanta kenan acikin zuciyarta

"Baki fada min ba, wanne kike so? Ina son zan bayar ne a siyo miki kayan dakin"

"Yaya ni duk wanda ya samu ina so" ta fada cikeda kunya

"To shikenan duk guda ukun zan siyo miki, ke ai yar gatace"

"Yaya sunyi yawa, dayanma ya isa"

"No,guda uku zan yi miki pherty na"

Murmushi ta kakaro dakyar tayi , "nagode yayana" ta fada idonta cikeda kwalla

"Kar kiyi kuka pherty na, kinfi haka a wurina"

"Nagode yaya".

  Bayan sun dan taba hira ne ya yi mata sallama ya tafi ita kuma ta koma hostel.

******

Gudu aosai jawad yayi daga makarantar su pherty zuwa gidansu, kai tsaye side dinshi ya wuce, kansa ya dafe tare da fadawa saman kujera domin jin kan nasa yake kamar zai rabe gida biyu dan tsabar zugin da yake masa, zunbur kuma ya tashi zaune

"What? Impossible, Xarah hakan ba zai taba faruwa ba" ya fada shi kadai kamar wani zautacce, tashi yayi ya fito ya nufi side din Ummi, yana zuwa ya tarar da ummin zaune ga tulin akwatuna masu kyau da tsada a gabanta, kallon akwatunan yayi cikin faduwar gaba, guda bakwai ne kalarsu pink colour,

Zama yayi dabas a gaban Ummi, "Ummi wannan kayan fa?" Ya fada cikin dar dar

"Kayan auren aadil ne da aka hado masa, kasan bikin nashi ya taho saura lokuta kadan ya rage"

Kafin yayi wata magana aadil ya bude kofa ya shigo, tashi jawad yayi ya tunkareshi yana zuwa yafara kokarin cin kwalarsa

"Sai yau na yarda kai ba dan uwana bane, ayau nagane cewa kai ba jinina bane, ko kadan bamu hada jini dakai ba aadil, kai ba dan uwana bane domin shi dan uwa yana taimakon dan uwansa ne a duk lokacin da ya bukaci taimako, ba irinka ba mai son zuciya da son kansa ba, ba irinka ba mai kokarin raba naka dan uwan da tashi rayuwar ba"

Wani mugun kallo aadil ya watsa masa sannan ya fara kokarin banbare hannun jawad din daga rikon da yayiwa rigarsa


"gaka nan mai son zuciya mai son kansa, yarinyar da kagama wulakantawa a baya sai yanzu zaka dawo kace ita kake so saboda kaga yanzu ta zama cikakkiyar mutum, to wlhi baka isaba ko bazan auri pherty ba bazan taba barinta ta aureka ba, gara nabawa bare aurenta akan nabaka, banza mayaudari kawai"

Ai jawad najin haka ya sake tunzura tare da fara wujijjiga wiyan rigar dake jikin aadil, da sauri Ummi ta taso ta fara kokarin rabasu,

"Kai jawad sa'anka ne? Cikashi, ka cikashi nace" ta fada cikin harshen fullanci

"Ki kyaleshi Ummi na koya masa hankali yau" jawad ya fada cikin karaji

"Idan kai baka koya min ba to ni zan koya maka, dama can kawai saurara maka nake yi" aadil ya fada shima a harzuke

Nan suka kaure da fada Ummi tayi tayi ta rabasu ta kasa, tun suna yi a falo har suka karasa dining area,sai naushi suke kaiwa junansu, wani wawan naushi aadil ya kaiwa jawad cikin sa'a ya sameshi a fuska, take jini ya fara fita daga hancin jawad

"Haba aadil kashe kanku zakuyi? Akan me?" Kuka Ummi ta fara, da sauri ya saki jawad ya nufi Ummi shikuwa jawad durkusawa yayi agun hancinsa yana ta zubar da jini.




Ummi A'isha
[5/10, 9:04 PM] Ummi A'isha🏻: [5/10, 9:02 PM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA 👑


  Na
UMMI A'ISHA


53-55


~~~Da sauri aadil ya saki jawad ya nufi wurin Ummi, "aadil kashe kanku za kuyi? Ko lokacin da kuke yara kanana ba kuyi kuruciyar fada ba kai da dan uwanka, sai yanzu da kuka girma kowa ya mallaki hankalin kansa" Ummi tafada tana kuka,

"Yi hakuri Ummi mun daina ba zamu sake ba" aadil ya fada kamar zaisa kukan shima,

Mikewa ummi tayi ta nufi wurin jawad wanda duk ya babbata wurin da jini jini ne yake fita a hancinsa sosai, hannunsa ummi taja ta nufi dakinta da shi daidai lokacin mahaifinsu ya shigo, ganin abinda ya faru ya sashi fara tambayar meke faruwa, ko kadan aadil bai iya bude bakinsa ba yana nan tsaye gaban dining area din yana ganin yadda jinin jawad ya zuba da yawa,

Jim kadan sai ga ummi tafito itada jawad din ta wanko masa fuskarsa amma har a lokacin jinin yana fita kadan kadan,

"Hajiya Fatima wai me ya faru ne?" Mahaifinsu ya tambaya cikeda mamaki

"Kagansu nan fada sukayi sai kace kananan yara gashi nan harda zubar da jini" Ummi tafada fuskarta cikeda hawaye,

Cikin mamaki mahaifin nasu ya dubi aadil "aadil fada? Kai da kaninka? Duk duniya kanada wanda yafi shi ne? To yanzu da ace ka haihu yaronka ya girma da agabansa zaka yi haka? Aadil kai fa ba yaro bane,  shekarunka talatin da wani abu, ace har yanzu ba kayi hankalin da zaka rike dan uwanka ba? Meya hadaku? Tambayarka nake meya hadaku fada?"

Shiru sukayi daga aadil din har jawad babu wanda yayi magana,

"Ba zaku fada min abunda ya hadaku fadan ba sai na sassaba muku?" Mahaifin nasu ya sake fada cikin fada,


"Daddy babu komai" aadil ya fada kansa a sunkuye

"Kai jawad me ya hadaku"

"Dady babu komai" jawad ya fada shima

"Kaji zancen banza, babu komai kawai zaku kama fada harda fasa jikin juna?"

"Alhaji akwai abinda ya hada su dan daga jin musayar yawun da suka yi nasan fadan nasu akan yarinyar da aadil din zai aura ne" ummi ta fada tana kallonsu

"Meya samu yarinyar? Akanta suke fadan? To in babu dama ahakura da auren indai zai jawo fitina a tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya ya fice daga cikin falon,

Yana fita ummi ta kallesu "ban taba ganin sakarkaru irinku ba, fada akan mace? Cikinku daya fa ko kun manta? Kai aadil yanzu ko wani kagani zai cuci dan uwanka ai bai kamata ka barshi ba balle kai da kanka, sanin kanka ne tun jawad yana karami ba a dukansa a fuska dan ko marinsa akayi hancinsa ya rinka jini kenan amma shine dan rashin tausayi yanzu kazo ka dake shi a hancinsa"

Dukar da kai aadil yayi sannan yace "ummi kiyi hakuri,hakan ba zai sake faruwa ba"


"Shikenan kaje maganar ta wuce" ummi tafada tareda ficewa daga cikin falon itama,

Tana fita jawad ya fara harararsa "wlhi har yanzu ban hakura da pherty ba kuma yanzune ma nasake jin sonta acikin raina"

Kallo aadil ya bishi dashi "kaje ka aureta ga wurin nan" yana gama fadin haka ya juya ya fice daga falon.


*******

  Bayan faruwar haka da kwana biyu aadil ya shirya yaje makarantar su pherty, ita sam bata san abinda ya faruba, bayan ya fito sun gaisa ne dai take ganin kamar yana cikin damuwa,

"Pherty na wani wuri za muje, kije ki debo kayanki kamar kala biyar dan sai kinyi 2 weeks sannan zaki dawo dan haka sai kiyiwa su Sadiya da Aisha sallama"

"To yaya" haka kawai tace ta juya ta koma hostel, tana zuwa ta dauki trolley ta fara hada kayanta aciki tana fadawa su Sadiya zasuyi tafiya da yaya aadil,

Bayan ta gama shirya kayanta ne suka rakata har wurin motar aadil suka yi musu Allah ya kiyaye hanya, kallonsa ta juya tayi lokacin da suka fara tafiya

"Yayana meke damunka ne?" Tafada tana kallonsa

"Pherty na lfy lau nake kawai dai bana jin dadin jikina ne"

Murmushi tayi sannan ta sake kallonsa "to yanzu dai ina zaka kaini?"

Murmushi shima yayi "gidan sayar da mutane"

"Ah yaya yaushe ka fara yanka kai?"

"Ai nadade ina yanke kan raguna pherty nace bata saniba"

Dariya ta fara harda buga kafa amma sai dariyarta ta tsaya ganin sun nufi hanyar kauyensu,

"Yaya aadil wai ina muka nufa?"

"Gidanku" ya fada agajarce

Shiru tayi bata iya cemasa komai ba illa tunani da tafara yi, yau shekararta hudu rabonta da garinsu, komai ya canja na tsarin garin tun daga kan tituna har zuwa kan gine ginen dake cikin garin.


Juyawa tayi ta kalli aadil saura kadan tasaka kuka, girgiza mata kai yayi,

"Kar kiyi kuka pherty na, na tabbata su mama suna nan suna addu'a Allah ya dawo dake garesu, domin duk abinda ya faru sun san kaddara ne"

"Nagode yaya, hakika kai nadabanne acikin mutane sannan kana da abubuwan da ba kowanne mutum ne yake dashi ba"

"Nagode pherty na wannan Kalmar taki tayi min zaki kamar sugar, oh no ba sugar ba kamar Zuma zakinta yake agareni,kin san zuma tafi sugar zaki"

Dariya tasa amma gabanta sai faduwa yake, saboda bata san yadda zata samu gidan nasu ba ko su mama na nan ko sun tashi oho.


Tafiya kadan suka shiga cikin garin kumo nan ta fara bin ko ina da kallo har suka isa unguwarsu, komai ya canja amma gidajen suna nan yanda suke in banda yan sauye sauye da aka samu "Allah sarki hawyn mama kawata ko tana nan ko bata nan" haka ta fada acikin zuciyarta daidai lokacin da suka zo kofar gidansu hawyn,

Akofar gidansu yayi packing ta fito, unguwar shiru kamar babu kowa, tsayawa tayi ta kasa shiga gidan sai aadil ne ya wuce gaba tana biye dashi a baya, lokacin da suka shiga gidan abbanta yana kishingide a tsakar gida akan tabarma yana jin radio ita kuma mama tana kitchen tana girki, sallama aadil ya rangada, tashi abbanta yayi daidai lokacin da yake amsa sallamar, zumbur ya mike,

"Hajiya Adama, Adama, Adama kina ina? Maza fito kigani yau Allah ya amshi addu'armu ya dawo mana da yarmu" abbanta ya fada cikin farin ciki

Da gudu mama ta bazamo ta fito, tana fadin "malam me naji kunnuwana suna fada min? Me nakeji malam?"  Idanuwanta ne suka kai kan pherty ai da sauri ta karasa wajenta ta rungumeta.


Kuka suka fara yi ita da maman nata

"Assha meye kuma na kukan? Tunda ta dawo ai bukatarmu ta biya" abbanta ya fada

Wuri aadil ya samu ya zauna kusa da abbanta, bayan sun nutsune aka gaggaisa nan aadil ya fara yiwa iyayenta bayani "baba ba tone tone za ayiba, ga pherty nan dai yau ta dawo sai dai ayi addu'ar Allah ya kiyaye gaba"

"Amin dannan, amin amin, wallahi ko lokacin da ta tafi nayi bakin ciki mutuka domin abinda ya faru kaddara ce kuma shima yaron da yayi mata cikin yazo ya nemi afuwarmu" juyawa yayi ga pherty "phertyma kiyi hakuri kinji nasan nabaki tarbiyya iya iyawata kuma kinyi aiki da ita kawai wata kaddara ce da jarrabawa ta samu rayuwarki"

Ita dai pherty itada mamanta basu ce komai ba in banda kukan da suke yi,

"Ba kuka za ayi ba mama godewa Allah za ayi" aadil ya fada yana kallonsu

"Abba bayan tafiyata daga gida wannan shine ya dauki dawainiyata yayi min komai na rayuwa ya kula dani har zuwa yanzu"

"Allah yayi masa albarka, Allah ya yi masa albarka, mun gode, mun gode madalla"

Nan aka barke da hirar yaushe gamo duk abubuwan da suka faru sai da pherty ta fadawa iyayenta abu dayane basu fada ba itada aadil maganar rashin lafiyar da take tareda ita domin bata son su tayarwa da iyayen nata hankali.

Aadil ya dade agidan Kafin yayi musu sallama ya fita, bin bayansa pherty tayi suka tsaya a soron gidan,

"Pherty na sai munyi waya, gobe zan koma abuja"

"Allah ya kiyaye hanya yayana,sannan banda kallon yanmata, gashi zaka tafi baka ga kawata hawwa ba"

Murmushi yayi "idan nazo next time zan ganta, ki gaishe min da ita"

"Zata ji"

"Yawwa amarya ta" ya fada yana dariya

"Kaima ai ango ne" itama tafada tana dariyar

"Idan na biya ta taki zan kwana anan, sai munyi waya pherty na, bye bye"

"Bye bye yayana". Tafada lokacin da yake shiga cikin motarsa,

Hannu ta fara daga masa har ya fice daga cikin layin nasu ta juya ta koma gidan nanfa suka cigaba da hira ita dasu mama ananne ma taji cewar yan unguwar basu san abinda ya faru ba kawai dai ance ta b'ata ne amma basu sanar da kowa abun kunyar da tayi ba, dad'i taji ya rufeta lallai naka sai naka,

"Mama ina hawwa?" Ta tambayi mama

"Hawwa dazun nan ma ta shigo, tana nan, ta kusa kammala karatunta itama a jami'ar tarayya dake garin katsina"

"Mama bari naje naganta, nayi missing dinta over"

Zuruf ta mike ta fice daga gidan ta nufi gidansu hawy, tana shiga ta hangota tsugunne tana wanke wanke,

"Sannu da aiki yanmatan mama"

Dasauri hawyn ta jiyo wa zata gani? Dagudu ta tashi taje suka rungume juna,

"Phertyn mama kece? Muje daki" hannunta taja ko ta kan mama basu biba domin tana daki, wanke wanke kuwa tuni anmanta dashi, zama sukayi suka fara bawa juna labarin duk abun da ya faru bayan rabuwarsu, nan pherty ta bata labarin aadil,

"Phertyn mama ko kin san cewar jawad yazo rannan kuwa? Har kirani yasa akayi na rakashi wurinsu mama, sannan yace shi yanzu aurenki zaiyi domin yana son gyara kuskuren da yayi a baya"

"Hmm hawy kenan ai jawad bashida aikin yi ne, domin nafada masa ni yanzu bazan aure shi ba yayansa zan aura"

Ido hawy ta zaro "wai dama shi aadil din yayansa ne?"

"Uwarsu daya ubansu daya"

"Tofa wannan abu akwai mamaki amma"

Hannun hawy ta kama ta dora akan mararta "hawy taba kiji fa, kiji yanda gefen marata yayi tauri kamar dutse, gashi doctor yace ba lallai ne na haihu ba, ko sex dinma dakyar idan zan iya, taya zan auri jawad? Aadil zan aura domin ko babu komai shi dama ba jikina yake so ba sannan kuma zai iya hakura ya zauna dani koda kuwa bazai samu wani abu awurina ba"

"Pherty kaddarar da kika hadu da ita kenan?" Hawy tafada idonta taf da kwalla,

"Kar kiyi kuka pls, ai ko jiya ma saura kiris na mari jawad wlhi"

Girgiza kai hawy tayi

"Gara da baki mareshi ba, jawad yayi nadama pherty kuma wlhi yanzu dagaske yake sonki, kamar yadda nasan kema kina sonsa, kawai kyautatawar da aadil yayi miki ne take hanaki nuna soyayyar jawad, amma ni nasan kina sonshi, to ga shawara ki daina bacci ki yawaita tsayuwar dare kina kai kukanki wurin ubangiji kan ya zaba miki abinda yafi alkairi, nima kuma zan tayaki da addu'a"

"Nagode hawy dama nasan ke ta dabance a gareni"

Murmushi tayi ta goge hawayen kan fuskarta

"Sannan magana ta gaba itace kar kisake yiwa jawad wulakanci pherty saboda kinga baki san abinda Allah zaiyi ba ta yiyu shine mujinki idan kuma ba mijinki bane sai a rabu salin alin, nasan abunda yayi miki da ciwo to amma kaddara ce babu yadda za ayi"

"Shikenan hawy nagode zan kiyaye insha Allah"

  Mikewa tayi "zan koma wurin mama domin ban gama ganinta ba"

"To muje nima ina nan shigowa"



Ummi A'isha🏻
[5/11, 12:36 PM] Ummi A'isha🏻: [5/11, 7:59 AM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA👑

   Na
UMMI A'ISHA

55-60


~~~ Dakin maman hawy suka je, itama kamar a mafarki ta ganta nan aka gaggaisa sannan ta koma gidansu.

  Tana zuwa ta dale jikin mama suka fara hira irinta d'a da uwa, daren ranar sun dade a zaune suna hira har sai wurin 2 sannan suka hakura, wayarta ta jawo saboda jin mama tayi bacci, tana budeta taga kiran yaya aadil babu adadi, agogo ta kalla anya kuwa ya kamata ta kirashi yanzu, kiransa ta fara yi ringing biyu ya dauka yana murmushi

"Pherty na yau nayi fushi, wato dan kin samu mama shine zaki manta da yayan ki ko?"

"Ni na isa yaya aadil? Na isa mantawa dakai, ban isa ba gaskiya hirace tayi yawa shiyasa ina fata kaje gida lfy"

"Lfy lau amarya"

Dariya tayi

"Yaya aadil kana son kirana da sunan nan alhalin kuma kaima angone"

Murmushi shima yayi, bayan sun dan taba hirane sukayi mata sallama domin gobe jirgin asuba zai bi zuwa abuja.

  Washe gari da safe bayan ta tashi tayi wanka ta shirya tana zaune a tsakiyarsu mama da abba tana yin breakfast suna hira sai ga hawy ta shigo, kallonta tayi tana murmushi

"Ta mama har antashi?"

"Eh Allah ya nufa" hawyn ta fada tana dariya

Daki suka shige bayan hawy sun gaisa dasu mama,

"Hawy ina labari?"

"Labari ai yana wurinki kawata, ina aadil?"

"Yau banyi waya dashi ba amma dai nasan ya koma abuja yabar gombe"

"Oh Allah ya taimaka, inasu Sadiya da A'isha?"

"Ai ina tashi da asuba bayan nayi salla dasu na fara waya"

"Allah sarki, Allah dai yabar zumunci"

"Amin" hira suka fara har suka gangaro ta kan hirar jawad amma ita pherty yanzu sam bata son taji an ambaci koda sunansa ma haka dai suka dade adaki suna hirar.


******

  Satin pherty biyu a kumo sannan ta koma gombe, taji dadin wannan zama sosai domin bata fuskanci wata matsala daga iyayenta ba ko kadan, tana shiga hostel su sadiya da A'isha sukaje suka rungumeta nan aka shiga hira har tsawon wani lokaci.

  Soyayyarta da aadil kuwa sai karuwa take domin kullum suna nan makale a waya, bayan sati uku da tafiyarsa aka harhada komai aka kai gidansu pherty, harda Salima matarsa a yan kaiwa kayan,nan aka bar rana kamar yadda yasa afarko, komai yaji a kayan jama'a sai yabawa suke yi.

  Nacin jawad kuwa bai hakura ba saboda yanzu kullum sai yazo makarantar wurinta duk da cewa ba wani sauraronsa take ba, da haka akwana a tashi har biki ya rage saura sati biyu nanfa su Sadiya da A'isha suka fara shirye shiryen biki, hawy tayiwa waya tazo sch dinsu dama aadil ya turo musu da kudade dan haka kasuwa suka shiga su hudun suka iyo siyayyar kayan biki harda kayan da amaryar zata saka.

  Ana biki saura kwana tara suka tattara suka koma kumo, shikuma angon sai saura sati daya biki zai zo daga abuja, ranar da sukaje aranar sai ga jawad kamar mahaukaci yazo gidansu, tana fitowa taga shine,

"Pherty bakida imani ashe? Bakida hankaline pherty? Wannan abun da kike shirin aikatawa wlhi mugunta ce tsantsarta, danme zaki auri aadil? Saboda kina son kasheni?"

Kallonsa tayi ya dan rame kadan kamar wani marar lafiya

"Kaine marar imani marar tausayi jawad, kaine kake shirin kisan kai sai kuma Allah ya juya maka al'amarinka da mummunan kudurinka kanka, na dade da fada maka bana sonka yanzu na tsaneka, ni bakai nake so ba yayanka nake so kuma shi zan aura, da shi zan rayu"

Tsugunnawa yayi ya dafe kirjinsa, kanta ta dauke amma koda ta jiyo sai taga jini yana fita daga bakinsa, da sauri ta kalleshi amma ba tayi magana ba, da kyar ya mike bakinsa duk jini ya kalleta

"Nagode pherty, tabbas kinyi min sakayya kuma nagani sannan nagode, zan tafi da sonki kuma zan mutu dashi, ina muku fatan alkairi keda mijinki masoyinki sannan Allah ya baku zuri'a dayyaba" yana kaiwa nan ya juya yana dingisawa idonsa cikeda kwalla bakinsa duk jini ya shiga motarsa, sai da yayi kamar minti biyar yana zaune yana kuka sannan ya iya fara tuka motar yana tafe yana aman jini yana kuka, ita kanta phertyn ta dade a tsaye kafin ta shiga gida tana zuwa daki kuma ta zauna ta fara kuka wanda ita kanta bata san ko na menene ba, matsowa kawayen nata suka yi suka fara tambayarta meya faru amma bata iya basu amsa ba.


******

  Allah ne kadai yakai jawad gida lfy domin yayi mutukar galabaita wani irin harbawa zuciyarsa take yi masa kamar zata faso kirjinsa ta fito waje gashi aman jinin da yake sai karuwa yake, yana shiga gida yayi packing ya fito yana dafe da kirjinsa, tafiya kadan kuma ya fara wani irin tari mai sarke kirji nan ya fara aman jini sosai, ahaka ya mike jiri yana daukarsa ya nufi side dinsa, sharafff ya fadi akasa sumamme daidai lokacin maigadi ya nufo wurinsa yana ganinsa kwance cikin jini ya nufi part din Ummi da gudu "hajiya, hajiya fito jawad ba lafiya" haka mai gadin ya fada daidai lokacin da ya shiga falon ummin, zuruf ta mike

"Yana ina?"

"Yana waje"

Dagudu Ummi ta fita ta nufi tsakar gidan, tana zuwa ta ganshi kwance bakinsa duk jini gashi ko alamun numfashi babu a tattare dashi, salati ta fara daidai lokacin motar dad dinsu ta shigo gidan, da sauri ya fito yana tambayar meke faruwa ganin jawad acikin wannan hali yasa yabawa driver da maigadi umarni su saka jawad a mota, dagudu Ummi taje ta dauko mayafinta ta shiga motar suka nufi asibiti.


Wani private hospital suka kaishi, nan likitoci suka nufi wani daki dashi, kuka Ummi kawai takeyi dad yana bata hakuri.

Kimanin awanni uku doctors din suka shafe suna kokarin ceto ran jawad amma abun yaci tura har lokacin bai farfado ba sai daf da sallar magrib sannan ya fara motsi nan kuma yafara tari yana aman jini, dakin Ummi ta fada ganin halin da yake ciki yasata sake fashewa da kuka.

  Wani babban doctor ne ya shigo hannunsa rikeda fayil ja, "ba kuka za kuyi ba, addu'a za kuyi masa, agaskiya abun nasa yayi worst, yana dauke da ciwon hawan jini, jininsa ya hau sosai irin hawan da ba aso, sannan kuma a halin yanzu yana fama da ciwon zuciya"

Wani kuka Ummi ta fasa mai ban tausayi tana fadin "jawad wacce damuwa kasa aranka haka? Haba jawad?

  Tashi dad yayi yabi bayan likitan zuwa office dinsa bayan sun zauna ne likitan ya fara yi masa bayani

"Am Alhaji yaron nan naka yana cikin wani hali gaskiya, yanzu babbar matsalar itace idan yatashi farkawa kila zai tashi da ciwon shanyewar rabin jiki saboda irin wannan faduwar dama itace ke haddasa wannan matsalar, amma za muyi iya bakin kokarinmu sai dai idan hakan bai samu ba sai a fitar dashi kasar waje"

Wani gumine yaketa tsattsafowa dad din baice komai ba ya tashi ya fita ya koma dakin da jawad yake.

Kwanansu uku a asibitin amma jawad ko motsi bai yi ba yana nan kwance kamar gawa, aranar aadil yazo garin koda yaje gidan bai samu kowa ba sai maigadin ne yayi masa bayani, wayar dad ya fara kira ya tambayeshi sunan asibitin yana fada masa yakarawa motarsa wuta ya isa asibitin, har a lokacin jawad bai motsa kai idan ka ganshi ba zaka taba tsammanin zai kara awa daya a raye ba saboda gaba dayansa acikin wasu karafa yake gashi ansaka masa abun numfashi wato oxygen tube, gefe kuma ana yi masa karin ruwa, Ummi na zaune fuskarta ta gama kumburewa saboda kuka, tayi jawur abunku da farar mace,

Ahankali ya karasa kusa da Ummi, "sannu Ummi, ya mai jiki?"

Cikin hawaye Ummi ta juyo tana ganin aadil sai ta sake fashewa da kuka mai ban tausayi

Riketa aadil yaje yayi nan shima ya fara hawayen, doctor dinne ya bude kofa ya shigo ya kallesu "kuyi hakuri kudaina kukan nan domin patient dinku baya son hayaniya asali ma isolating din masu irin lalurar su ake yi asauran hospitals nan dinma saboda kune shiyasa muka barku kuke tare dashi" kallon dad yayi

"Alhaji muna da bukatar jini domin akara masa"

Mikewa aadil yayi fuskarsa cikeda kwalla yace "muje a dibi nawa a kara masa"

Fita sukayi da doctor din suka nufi lab anan aadil din yake tambayarsa me yake damun dan uwan nasa, hawan jini da ciwon zuciya itace amsar da doctor din ya bashi, nan hankalin aadil ya tashi domin yasan yana dab da rasa dan uwan nasa gashi su biyu kacal iyayensu suka haifa, haka aka dibi jinin nasa leda biyu aka tafi domin karawa jawad, ba komai ne yafi daga masa hankali ba illa cewar da akayi kila jawad zai kamu da ciwon shanyewar barin jiki, dakin da jawad din yake ya koma ya samu Ummi

"Ummi wai duk mai ya haddasa masa wannan lalurar?"

"Wlhi aadil nima ban sani ba saboda jawad yanzu ya sauya hali dama can kasan shi ba mai yawan magana bane baya son hayaniya tun kuna yara kafishi magana shi sai ya wuni baiyi magana da kowa ba to yanzun kuma abinda ya tsira sai ya wuni a daki bai fito ba, nidai kawai ina zaune sai ga watchman wai nazo ga jawad can yafadi yanata aman jini, yanzu gashi doctor yace ciwon zuciya da hawan jini ne ke damunsa, ban san abunda yake damunsa ba har ya kamu da wannan lalurar" ta karasa maganar cikin kuka tareda rungume dan nata aadil

"Kidaina kuka Ummi insha Allahu zai samu lafiya, Ummi gara ke kinada wani dan kuma kina da yan uwa nikuwa fa? Iya jawad ne dan uwana banida wani dan uwan sai shi idan na rasashi shikenan narasa wani bangare na rayuwata" aadil ya fada yana kuka hawaye suna bin kumatunsa

"To yanzu meye amfanin wannan kukan, haba aadil kamar ba namiji ba?" Dad ya fada yana kallonsu duk kuwa da cewar shima dauriya kawai yake yi.

  Sai wurin karfe 9 na dare sannan aadil yaje gida yayi wanka anan yake sanar da Salima abunda yake faruwa, komawa asibitin yayi, daga Ummi har dad duk tausayinsa suke ji saboda sun san akwai soyayya mai tsanani tsakaninsa da dan uwansa, ko abinci ya kasa ci.

Kwanansu biyar acikin asibitin sannan jawad ya fara bude idonsa amma baya gane komai ga wata kumbura da fuskarsa tayi sai kuma ya fara tari mai wahala nan jini ya fara fita daga bakinsa da sauri aadil ya karasa gaban gadon ya rike hannunsa "sannu jawad"

Ko jinsa jawad bayayi, nan Ummi ta fara kuka sai janyeta dad yayi ya fitar da ita daga dakin, doctor ne ya shigo ya fara wasu rubuce rubuce ajikin fayil sannan ya yiwa jawad wata allura, nan yaja hannun aadil yana cewa yafi dacewa da adauki jawad akaishi kasar chairo zai fi samun lafiya fiyeda nan.

Wajensu Ummi aadil ya koma yayi musu bayani yace yanzu zaije yayi musu cuku cukun visa su hudun

"A'a aadil ban da kai, kaga yau kai saura 5 daurin aurenka, kayi mana mu uku kawai dani da mahaifiyar ka dashi jawad din"

  "To dad" ya fada ba dan yaso ba, kallon Salima yayi amma baiyi magana ba ya juya ya fita.

Cikin kankanin lokaci aka samu visa nan suka tattara duk wani abu da zasu bukata aadil ya kaisu airport suka nufi kasar chairo, daga nan kumo ya wuce gidansu pherty.

Lokacin da ta fito ta ganshi sai taji gabanta ya fadi "yayana baka da lafiya ne? Naga ka rame?"

"Pherty na jawad ne bashida lafiya, yanzun nan ma aka tafi chairo dashi, aman jini yake tayi"

"Allah yabashi lafiya" ta fada kamar zata yi kuka.


"Amin, Abba yana nan?"

"Eh" tafada a hankali

"To muje naganshi"

Rakiya tayi masa wurin abban ta fita ta basu wuri, ya dade awurin Abba sannan ya fito, ita da A'isha da Sadiya da hawy suka fito wurinsa

"Yaya aadil ango" suka fada su duka

Dan murmushi yayi

"Bakuda bukatar komai ko?"

"Muna son kudi wanda za ayiwa amarya gyaran jiki da kunshi" inji Sadiya da hawy

"Nawane?"

"20 thousand"

"To bari na bakubaku 50 thousand saboda ina son pherty na tayi kyau"

Motarsa yaje ya dauko kudin ya basu yayi musu sallama ya tafi ba tareda sun sake wata magana da pherty ba.

  Ranar juma'a da misalin karfe 2 jama'a suka taru domin shaida daurin auren pherty, bayan karfe biyu da rabi suna zazzaune agida adakin mama amarya tasha kyau saboda gyaran jikin da kunshin da akayi mata, wayar yaya aadil ce tashigo tana dauka yace tazo yana soron gidan, tashi tayi ta fita ta sameshi yasha farar shadda da jar hula wato kwankwasiyya sai kamshi yake

"Sannu yaya aadil"

"Yawwa pherty sannunki ya hidima?"

Murmushi tayi bata amsa ba,

"Pherty ayau ina mai farin cikin sanar dake cewa na cika miki burinki na aura miki wanda kike so"

Kallonsa tayi "ban ganeba yaya aadil"

"Ina nufin yau kin zama matar jawad"

Kwalalo ido tayi "haba yaya gaskiya ni bana sonsa kai nake so ni gaskiya bazan zauna dashi ba, awarware auren nan cikin gaggawa"

"Ni ina sonsa saboda dan uwana ne, pherty kenan nasan jawad kike so ni kawai kina yimin alkunya ne saboda abunda nayi miki na taimako, ina so kiyiwa jawad biyayya ki kulashi kamar yadda zaki kulani sannan ki sani jawad yana tsananin sonki fiyeda tunanin mai tunani, yanzu jirgi zanje nabi nida Salima domin gano halin da yake ciki sannan kuma nayi masa albishir da kin zama mallakinsa, pherty jawad dan uwana ne uwa daya uba daya duk duniya banida kamarsa tun Muna yara mun taso da son junanmu nasan abunda yake so nasan wanda baya so, kayan dakinki suna nan zuwa anjima nabar komai a hannun baba maigadi shine zaiyi muku jagora zuwa gidanki, sannan ina so kici gaba da kallona a matsayin yayanki ba yayan mijinki ba kamar yadda kike kallona ada, ko wani abu jawad yayi miki kar ki kunyar sanar dani, ban yarda ki kai kararsa wurin kowa ba sai wurina, ni nayi masa walinci nabada sadakinki Dubu Dari biyu da hamsin, Allah ya sanya albarka acikin aurenku, Allah ya baku zuri'a dayyaba"

Wasu hawaye ne suka fara bin kumatunta

"Nagode yaya aadil, hakika kai wani mutum ne mai mutukar muhimmanci a rayuwata nagode yaya aadil Allah ya saka maka da mafificin alkairi"

"Pherty tun farko nasan jawad kike so, kamar yadda shima ke yake so, Allah ya barku tare"

Yana fadin haka ya juya ya fita ya nufi airport inda Salima ke jiransa domin jirginsu ya kusa tashi.

Gida ta juya ta koma tana ta kuka "zaki fara sana'ar taki ne?" Sadiya ta fada tana kallonta

"Kibarta kukan farin ciki ne" hawy ta fada tana dariya

"An auri jawad ai dole ayi kukan farin ciki" inji A'isha domin dama su sun san da jawad aka daura mata aure itace bata sani ba nan suka shiga tsokanarta ita dai sai kuka take.

******

Misalin karfe 4 na yamma su aadil suka sauka akasar chairo, asibitin da su jawad suke suka nufa shida salima, lokacin da suka shiga dakin da jawad din yake yana kwance idanuwansa a rufe, inda yake aadil ya karasa ya kama hannunsa

"Jawad bude idonka kaji, ka bude idonka, pherty ta zama matarka, wlhi dama ban taba sonta ba kamar yadda itama bata sona kai take so, ni kawai taimakon da nayi mata ne yasa take girmama ni, haba dan uwana taya zan so abunda kake so, wlhi duk abinda ya faru nayi shine domin na kubutar dakai daga rasa abunda kakeso domin ba dan na rike maka pherty ba da tuni ta shiga uwa duniya kuma ba lallai ka iya gano inda take ba gashi kana fama da ciwon sonta, sannan ba don na nuna ina sonta ba da tuni yanzu wani ya gama siye zuciyarta kuma koda ka koma ba zata saurareka ba, duk taimakon da nayi mata nayi shine saboda kai dan uwana, ka saki ranka wlhi ban taba son abunda kake so ba"

Bude ido jawad yayi, idanuwansa cikeda kwalla, sake damke hannun aadil yayi,

"Meyasa baka aureta ba? Kai kafi cancanta da aurenta saboda kaine ka taimaketa a lokacin da take bukatar taimako,Kaine ka zaba gatanta a lokacin da bata da gata, nikuwa ban yi mata komai ba a rayuwarta face zalunci shiyasa Allah ya kamani"

"Kayi shiru dan uwana kar su Ummi suji, kayi hakuri ka rigada ka zama ango amma wani hanzari ba gudu ba, tanada matsala a mararta, buguwar da tayi lokacin da tasamu miscarriage dinnan taji ciwo a gefen mararta"

Daga kai jawad yayi yana hawaye "Allah ya saka maka da alkairi dan uwana, nagode nagode, banida bakin yi maka godiya"

  Cikin kankanin lokaci jawad har ya fara samun sauki, jikinsa ya danyi kyau gashi kumburin nan na fuskarsa ya sabe domin jininsa ya sauka ya koma normal, ciwon zuciyar ma tuni ya lafa sai dai har yau baiji muryar amarya ba.


******

A Gida Nigeria kuwa an gama gabatar da shagulgulan biki lafiya, anyi yini anyi walima sannan kawayen amarya sun shirya sisters night, mama kuwa ta dage ta gyara yarta tsaf ciki da waje, yau ake sa ran kaiwa amarya gidanta.

  Misalin karfe takwas na dare aka dauketa akayi cikin gombe da ita bayan iyayenta sunyi mata nasiha daidai gwargwado, wani tamfatsetsen gida aka kaita wanda indai bata manta ba to nanne gidan da jawad ya kaita, amma an sake gyara gidan an zuba masa sababbin funitures komai blue, hatta gadajen blue ne, dakuna uku da faluka biyu ga dining area da kitchen da store aciki, anan kawayen nata zasu kwana tunda ango baya nan.

"Masha Allah gida yayi kyau Allah ya kawo yan uku" inji hawy

"Yan Hudu dai ya kamata ki rokar musu" Sadiya ta fada tana dariya

"Kai duk ba wannan ba gaskiya ba zaku kwana akan gadon ma'aurata ba kuzo mu koma falo mu kwanta acan" A'isha ta fada tana kifta musu ido

Ita dai pherty tashi tayi ta shige toilet ba tare da tace musu uffan ba.




Ummi A'isha🏻
[5/12, 11:48 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

 
  Na
UMMI A'ISHA


61-63


~~~ Kwana suka yi suna hira sai tsokanarta su A'isha suke, sai da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta bacci.


   Kwanansu biyu sannan suka koma sch suka barta da iya hawy kawai, tana kuka suna kuka haka suka rabu dasu Sadiya, ranar da suka tafi da yamma suna zaune ita da hawy a falo jawad ya kirata a waya kamar ba zata dauka ba sai ta dauka

"My queen" ya fada a hankali

"Ina jinka" tafada cikin gatsali

"Kinji yadda al'amari ya sauya ko?"

"Eh naji amma ai ni dole aka yi min domin ba sonka nake ba"

Harara hawy ta wurga mata itama ta rama,

Shiru yayi ya rasa abin da zai ce mata can ya daure yace

"Ko jikin nawa ba zaki tambaya ba Queen?"

"Banida alaka da shine shiyasa kaji ban tambaya ba"

"Ok to nagode sai munyi waya"

Kashe wayar tayi sai kuma taja tsaki "mtsww"

"Mijin naki kike yiwa tsaki pherty? Wlhi kiyi ahankali tom" hawy ta fada tana hararta,

"Anki ayi ahankalin kuma anyi masa tsakin sai me?"

"Sai ya gyara miki zama idan ya dawo"

"Ya gyara din"

"Yarinya kenan, round biyu zai yi miki kwarara zaki shiga hankalinki"

"Yayi round goma ba biyu ba" ta fada tare da ficewa daga bedroom din ta nufi dayan.

  Kwanansu biyar tareda hawy agidan amma kullum sai sunyi fada akan jawad da haka har pherty ta fara shirin komawa sch aranar itama hawy ta koma gombe.

  Kayanta ta harhada cikin trolley ta nufi sch nan kawayen nata suka fara yimata oyoyo,tunda ta koma kuma ta watsar da jawad duk da cewar tasan tana sonsa amma haka take basarwa watarana ma da saninta zata kashe wayarta dan kar ya kirata ya sameta, sai dai har lokacin basu yi waya da aadil ba amma takanyi masa text ta gaida shi lokaci lokaci.

******

  Acan kasar chairo kuwa tuni jikin jawad yayi sauki garau kamar bai taba jinya ba har an bashi sallama nan suka fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria amma shi aadil da Salima zasu wuce kasar London domin hutawa to sai muce adawo lafiya.

   Ranar asabar da yamma ranar su jawad suka sauka a Nigeria yayi fresh yayi kyau saboda yanzu bashida wata damuwa gashi yana samun kulawa sosai wurin ummi sai dai har yau su Ummi basu san dalilin aadil nakin auren pherty ba sun rasa dalilinsa na aurawa jawad phertyn.

  Washe garin ranar da suka dawo Sadiya da A'isha suka matsawa pherty kan lallai dole sai ta shirya sunje duba jawad, fada sukayi sosai kafin ta yarda ta shirya cikin lace blue ta yafa mayafinta kashka shima blue,sarka ta saka silver mai kyau tasa farin takalmi flat,fita suka yi suka nufi unguwarsu jawad din domin yana gidan ummi, keke napep suka hau har unguwar.

   Kallon gidan take tayi tana tuna ranar da tazo lokacin da jawad yayi mata ciki,

  Part din ummi suka shiga suka sameta zaune tana duba wani littafi idonta sanye da medical glass, pherty tana baya Sadiya agaba, sai A'isha, sallama sukayi ta dago ta amsa musu,

"A'a pherty sannunku da zuwa" tafada cikin hausarta wadda bata fita sosai,

Zama suka yi ita kuma tafita taje da kanta ta hado musu kayan marmari ta kawo musu, pherty dai bata iya hada ido da ita ba kanta yana sunkuye suka gaisa,

"Jiya ai munje gidan naku munyi godiya, angama biki lafiya ko?"

"Lafiya lau" tafada cikeda kunya

  Zama suka yi shiru har na yan mintuna sai daga baya su sadiya suka tambayi jawad tace yana side dinsa tun dazu yafita, tashi suka yi suka nufi side din nasa.

   Lokacin da suka shiga yana cikin daki yana kwance akan gadonsa, jin sallamarsu tasa shi tashi yasa riga, shiga suka yi suka sameshi zaune,

"Sannu ango ya jikin naka?" Suka fada a tare banda pherty

"Alhamdulillah, am cued" ya fada yana kallon pherty wadda ta bata rai,

   Tashi Sadiya da A'isha suka yi suka koma falo suka basu wuri, kallonta yake tayi a hankali, sai hannunta yake bi da kallo saboda har yanzu kunshin da tayi bai gama fita ba, gashi tayi kyau fatarta tayi lukwi lukwi tayi kyau sai kyalli take saboda gyaran da tasha,

  "Ba zaki gaisheni ba?"

  Shiru tayi masa bata bashi amsa ba,

Hannu ya mika mata alamun ta matsa gareshi amma ta dauke kanta, tashi yayi ya shiga toilet sai a sannan ta fara bin dakin da kallo, ya tsaru sosai komai akan tsari, yana fitowa ya nufo inda take, cikin sauri ta mike, hannunta ya riko da niyyar janyota jikinsa, k'i tayi ta koma jikin bango binta yayi ya fara kokarin shinshina ta, "queen kinyi kyau" yafada acan cikin makoshinsa,bakinsa yakai kan fuskarta, nan ta fara kiciniyar hanashi kissing din bakinta bai damuba duk inda ya samu akan fuskar tata anan yake sakar mata kiss din,tana makure ajikin bango shi kuma ya matseta sai kai mata kiss take yana fitar da numfashi a hankali, janta yayi zai rungumeta ta kuwa kankame jikinta dole ya hakura ya saketa ya koma gefen gado ya zauna, a inda take ta zauna, har lokacin numfashi yake fitarwa, tsam ta mike ta fice bata yi masa magana ba, a falo ta tarar da sadiya da A'isha suna hirarsu,

"Sai ku tashi mu tafi ai"

Tashi sukayi suka fice sai da suka koma suka yiwa Ummi sallama sannan suka wuce makarantar tasu.

Tun akan hanya suke tsokanarta "kinsha kiss ko?"

"Oho" tafada tana zaro wayarta ajaka saboda ta jiyota tana ringing

"Hawyn mama"

"Um ya sch din?"

"Kin ganni ma a hanya nadawo daga dubiya"

"Jawad kika dubo?"

"Shi dai"

"Ya bayani, amma dai ba haka kika taho ba ko?"

"Oho miki" ta fada tareda kashe wayar.


Tun lokacin bata kara zuwa dubashi ba har ya karasa warkewa ya koma gidansu yabar gidan Ummi, ranar da daddare ya shirya yaje makarantar koda yayi mata wayama sai tace ita bacci zatayi, marairaice mata yayi yace ganinta kawai zai yi sai ta koma, daga ita sai kayan bacci ta fito amma ta zira dogon hijabi lokacin wurin karfe 9 nadare.

  Yana cikin motarsa taje ta tsaya a waje sai shine ya fito ya zagayo ta inda take tsaye,

"Queen bacci tun yanzu?"

"To me zanyi maka idan banyi bacci ba?"

"Allah ya baki hakuri abun bana fada bane"

Dauke kanta tayi hakan ya bashi damar karewa jikinta kallo, hijabin jikinta ya daga da niyyar ganin kayan dake jikinta

Kamar wacce take jira ta fara masifa,

"Meye hadinka da kayana da zaka daga min hijab? Bana son haka" tana gama fadin haka ta juya zata tafi, ta bayanta yaje ya rungumeta, yafara laluben kirjinta, ta bude baki kenan da niyyar yi masa masifa yayi saurin rufe mata bakin da hannunsa,

  Kasa kwakkwaran motsi tayi saboda yanda ya kankameta gashi ya rufe mata baki da hannunsa, kamshin turaren da yasaka ne ya fara cika mata hanci,

"Pherty na kin koyi masifa ko? Da dai Queen dina mai hakuri ce ba mai fada ba"

Hannunta tasa ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata, sakinta yayi ya tsaya ta bayanta, ko jiyowa bata yi ba tayi gaba abinta ta wuce hostel shi dinma juyawa yayi ya shiga motarsa ya tafi. Koda yaje gida yayi shirin kwanciya amma sai ya kasa baccin juyi kawai yake gashi yasan koda ya kirata ba lallai ne ta dauka ba, haka ya karaci juyinsa daga karshe ya rungume filo bacci ya daukeshi.

  Itama phertyn kasa bacci tayi sai juyi kawai take yau jawad ya baro mata aiki, juyawa ta sake yi ta kalli Sadiya da A'isha wacce ko waccensu take baccinta hankalinta kwance, dakyar ta samu baccin ya dauketa.

   Washe gari ta kama Friday su Sadiya duk sun tashi da shirin tafiya weekend kallonsu ta fara cikin jin haushi

"Wai dagaske tafiyar zakuyi? Nikuma ni kadai zaku bari?"

"Kema kina iya shiryawa ki je naki gidan ranar Sunday sai ki dawo" Sadiya ta fada lokacin da take zuge zif din Jakarta,

"Tab ai ni ko zan dawo ma wlhi sai Tuesday" A'isha ta basu amsa

"To nima Tuesdays din zan dawo ko Wednesday"  Sadiya ta sake bata amsa, nan suka shirya kayayyakinsu ganin zasu tafi su barta yasa itama tashi ta shirya suka fita gaba daya.

Keke napep ta hau har gidanta, lokacin da ta shiga taga alamar jawad yana nan saboda ga motarsa nan a ajiye agidan, gaisawa suka yi da maigadin ta wuce ciki, a falo ta sameshi kwance akan 3 sitter daga shi sai three quarter, wayoyinsa da laptop dinsa kuma ajiye akan center table, kallo tabishi dashi duk jikinsa ko ina gashine a kwance, jin tsikar jikinta ta fara tashi yasata shigewa cikin dakinta,

Kayan jikinta ta cire tasa wando iya cinya da yar riga milk colour yar karama iya cibiyarta, kitchen ta shiga ta dora abinci, tana cikin girkin sai gashi ya shigo ganin itace acikin kitchen din ya sashi yin murmushi

"Queen kece ashe?"

"Um" tafada a gajarce

Juyawa yayi ya fita ita kuma taci gaba da girkinta, indomie ta dafa da kwai ta zubo a filet tazo zata wuce daki, "queen ina nawa abincin?"

"Banyi dakaiba" tafada cikeda rashin kunya

Tashi yayi yabi bayanta, tana zama sai gashi ya shigo, abincin ta fara boyewa shikuma ya hau kan gadon nan suka fara kokawa, tsoro yaji kar ta kone yasa ya barta yatashi zai fita har yaje bakin kofa yaji tace "da saura a tukunya idan zaka ci"

Kitchen din yaje ya dibo sauran data bari ya koma falo.

  Tana gama cin abincin ta ta ture filet din ta cire rigar jikinta ta kwanta daga ita sai bra da dan gajeren wandonta, wayarta ce ta fara ringing sai kuma ta katse wayar ta mutu, ta manta ashe bata da charge gashi ta manto charger din a sch, daukar wayar tayi ta nufi falo domin neman charger,jawad yana zaune yana cin abincin sai kawai ganinta yayi ta fito a haka, baice mata komai ba yaci gaba da cin abinsa amma sai kallonta yake yana mamakin yadda ta kara cika sosai, dube dube ta fara a falon ganin bata samu abinda take nema ba ya sata nufar daya dakin wato na jawad, tashi yayi ya bita tana sunkuye tana kokarin jona wayar a charge, tana dagowa ta ganshi tsaye yana kallonta

"Wayasa ki fito a haka? Ko baki san ma'aikatan gidan nan duk maza bane?"

"Nida gidana sai anfada min yadda zan fito? Nafita duk yadda nagadama mana ina ruwan wani dani"

  Matsowa yayi kusa da ita "kin koyi rashin kunya ko?"

  Kawar da kai tayi ta kyaleshi, cikinta ya kalla "ke cikinki baya girma ne idan kinji abinci?"

Nanma shirun tayi, matsawa yayi yabata hanya alamar tazo ta wuce, tana zuwa saitinsa yasa mata kafa tafiya tayi zata kifa yayi saurin rungumeta kafin tayi wani yunkuri yayi kan gado da ita,

Jagulata ya fara yi tako ina ita kuma sai kokarin kwacewa take riko daya yayi mata takasa motsi kiss ya fara kaiwa kirjinta, ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta yi masa dabara  "ka daga ni kaga ni bana daukar abu mai nauyi saboda marata" juyawa yayi tana ganin haka ta mike "kadaina taba min jiki"

Ficewa tayi daga dakin ta koma nata ta kwanta dama bacci take son yi.

  Ta jima tana bacci kafin ta tashi tayi wanka tayi salla tana gaban mudubi daure da towel tana shiryawa ya shigo,towel dinne ya zame nan taci gaba da kwalliyarta ba tare da ta gyarashi ba, kallon kirjinta ya fara ta cikin mudubin,

"Am, um queen zan fita" ya fada muryarsa a shake,

"Umhum" tafada tana shafa powder

Juyawa yayi yana tafiya yana waiwayenta har yaci karo da bango, dawowa yayi "queen bakya bukatar komai ko?"

"Bana bukata"

  Ficewa yayi ya nufi tsakar gida,ita kuma ta tashi tasaka kaya, riga da wando masu santsi ta fesa turare mai kamshi a jikinta ta fita falo.




Ummi A'isha🏻
[5/13, 7:58 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑


  Na
UMMI A'ISHA

64-66


~~~  Motarsa ya shiga ya fita ya nufi cikin gari amma yana tafe yana tunanin pherty gaba daya yau ta sauya masa tunani nan yaji hankalinsa ya fara tashi haka ya daure ya karasa gidan ummi.

  Ita kam pherty koda ta gama shirinta falo ta fito ta nemi wuri ta zauna nan kuma zaman ya fara gundurarta saboda gidan shiru babu motsin kowa, dakin jawad ta tashi ta shiga ta zauna agefen gadonsa ta dauki laptop dinsa ta bude, password din ta fara gwadawa farko tasa sunansa yaki budewa, sunan umminsa tasa nanma bai budeba, tana saka pherty taga ta bude wani hadadden hotansa ne akan screen din yayi kyau sosai cikin jar riga da blue din wando, game ta gani kala kala dan haka ta zabi daya ta fara, ta dade adakin nasa tana game kafin ta kashe masa ta fice daga dakin.

  Dakinta ta koma tayi sallar magrib ta dawo falo hannunta rikeda cazbaha tana ja, tana nan zaune har aka kira isha, bayan ta idar da sallar ne ta shiga kitchen ta dora ruwan zafi tareda tsayawa ta fara tunanin abinda zata dafa, jalop din taliya da kifi tayi ta sauke ta koma daki ta shiga wanka tana cikin wankan jawad ya dawo, dakinta ya fara shiga bai ganta ba, kofar toilet din ya bude sai ya ganta tana wanka,

"Meye" tafada cikin masifa

"Nadawo ne ban ganki ba shiyasa ashe wanka kike"

"Malam ka fice daga bathroom dinnan"

Ciki ya shiga "ki tsaya in yi miki wankan"

"Allah ya sawwake" ta fada cikin fad'a

  Soson hannunta ya mika hannu zai karba, "kawo inyi miki"

"Nace banaso, bana so, bana so,a'a ko dole ne....!" Shiru tayi sakamakon jinta da tayi acikin kirjinshi,

Hannunshi yakai jikinta nan suka fara kokawa "bana so, nace bana so"  haka ta fara fada a hargitse,

"Yi hakuri queen, na fita"

Sakinta yayi ya juya ya fice, sauri tayi ta sawa kofar toilet din key taci gaba da wankanta yanzu ta fuskanci kamar baya son bacin ranta duk abinda ta nuna bata so hakura yake.

  Tana fitowa daga wankan ta shafa body spray tasaka wasu kayan bacci pink colour riga da wando, rigar da kadan ta rufe cibiyarta wandon kuma bai karasa gwiwa ba, fita tayi ta shiga kitchen lokacin jawad yana kwance akan doguwar kujera, abinci ta zubo ta wuce dakinta, tana gamawa sai gashi ya shigo idonsa kamar ya tashi daga bacci,

"Queen zaki zo dakina?"

Kallonsa tayi duk jikinsa a wani sanyaye idonsa kuma kamar yasha wani abu,

"Me zanzo nayi a dakinka?"

  Langabar da kai yayi

"To ni nazo?"

"Bana nemanka" tafada gamida zamewa tayi kwanciyarta,

"To shikenan sai da safe" yafada cikin kalar tausayi, bata amsa ba ganin haka ya sashi juyawa ya fita bayan ya kashe mata light din dakin.

  Dakinsa yaje ya kwanta akan gado nan yaji kwanciyar bata yi masa ba, kan doguwar kujera ya koma ya kwanta, mintuna kadan ya sake tashi ya dauki pillow ya koma kan carpet ya kwanta nan dinma bai wani dade ba ya tashi ya koma kan gadon, haka yayi ta sauye sauyen wurin kwanciya kafin asuba ya sauya wuri yafi sau goma.

  Karfe tara daidai ya fito da saurinsa ya tsaya a falo daga shi sai gajeren wando lokacin masu aikin gidan har sunzo sun fara aikinsu, tsayawa yayi yana kallonsu suna gyara falon yasan ba karamin aikinta bane ta fito a yanda ta fito jiya tunda ya fuskanci yanzu wata sangarta take ji da ita, ko minti biyar baiyi ba da tsayawa ta bude kofa ta tsaya tana mika da saurinsa ya karasa kofar dakin ya turata ciki daga ita sai dan kayan baccinta wanda basu da maraba da abin tace koko,

"Queen karki fito a haka pls kinga da mutane a falo suna aiki"

Mikar da ta fara ta karasa tareda yin wata yalwatacciyar hamma, hakan ya bashi damar ganin har cibiyarta,

"To nikuma ina ruwana da masu aiki? Ko akaina zasu yi aikin?" Tafada tana yatsina fuska,

Cikinta ya kalla ya lashi lebenshi "kiyi hakuri yanzu zasu gama, mopping suke yi sun gama sharar"

Juyawa tayi ta koma cikin dakin ta fada kan gado taja bargo tareda janyo wayarta ta kunna data, fita yayi yaja mata kofar,

Chtn tafara dasu Sadiya da A'isha da hawy dadi taji saboda ganin duk suna online "amare an shigo?" Hawy ta turo mata "um sai yanzu" ta tura mata amsa "komai ya wakana ko?" Sadiya ta turo,dariya tayi ta mayar mata da amsa "abinda ya fishi muka yi" "kun takurawa pherty fa, Ku kyaleta ma da ciwon jikin da jawad ya sa mata" A'isha ta turo harda gwalo, dariya tayi ta mayar musu da amsa "kuna wasa yara, wlhi bama daki daya muka kwana ba" ,"ehhh amma ai a takure kuke" hawy ta tura, "Allah ya shiryeku" ta tura musu tana dariya "phertyn jawad sai yaushe zaki dawo?" Sadiya ta tambayeta "sai sun gama soyewa" A'isha ta bata amsa " "sai ta samu ciki zata dawo kun san jawad bana wasa bane shi a karon farko yake bada tukwici" hawy ta tura musu amsa,"sai anjimanku zanje na dora breakfast" ta tura tana murmushi, "bawani kawai dai kice zakije dakin jawad" Aisha ta mayar mata da amsa, sauka tayi ta kashe data dinta tana murmushi, daidai lokacin jawad ya shigo,

"Ki fito sun gama sun tafi"

Bata bashi amsa ba ta taso tazo ta wuce ta gabansa ta fice, bayanta yabi yaje ya sawa kofar falon key ya rufe sannan ya koma dakinsa, kitchen ta shiga ta fara dan soye soyenta, plantain ta soya da dan dankali sannan ta soya kwai, kan dining takai kayan ta koma daki tayi wanka tayi brush ta fito, vest tasa ja da wani dan guntun wandonta wanda da kadan ya fi pant, komawa falon tayi ta zauna ta fara breakfast, tana gamawa shikuma yana fitowa, falo ta koma shikuma ya hau kan dining din, dan guntun wanda ta bari ya fara ci yana ci yana kallonta aransa yana kissima yanda zai yi da ita duk ranar da ta shiga hannunshi,


  Tv ta kunna ta fara dube duben channels, a zee aflam ta tsaya saboda ganin suna wani hadadden film mai suna kites duk da badaga farko ta fara ganin film din ba amma ya burgeta, wata irin soyayya taga jarumin film din yana nunawa yarinyar, take jikinta ya fara shock saboda yanda taga suna romancing junansu, idonta ta rufe,da sauri ta bude idonta saboda jin tafiyar tsutsa a wuyanta, jawad ta gani kusa da ita, take ta fara kokarin hade rai, hannunta ya kama ya fara mammatsa shi, shi dai a duniya yana kaunar hannun nan nata saboda yanada mutukar laushi lum lum, kiss yayi mata a goshi ta dauke kanta tareda fara kokarin fusgewa daga hannunsa, riketa yayi gam ya dauketa cancak ya dorata akan cinyarsa, kokawa sosai suka shiga yi daga karshe ya dorata akan kujerar ya matseta sosai, bakinsa ya sa a wuyanta ya fara kissing dinta,

"Jawad...!" Bai barta ta karasa ba ya hade bakinsa da nata ya fara tsotsa, hannunta ya damke yaketa mammatsawa, dagowa yayi ya kalleta

"Bakida karfi sai kuri" akule ta fara kallonsa "nafada maka bana so"  rungumeta yayi tsam tsam ajikinsa tareda cusa kansa a tsakiyar kirjinta, dakyar ta iya tureshi ta tashi, anan ya kwanta inda ta barshi, daya kujerar ta koma ta zauna amma itama tana cikeda bukatarsa,

Kofa taje ta bude ta fita ta nufi bayan dakunan da sauri ya tashi ya bita yana fita ya hangota tana tsino kananan duwatsu, tsayawa yayi tazo ta wuce ta koma falon ta zauna ta fara yar carafke, bayanta yabi ya koma ya kwanta acikin kujera, yana daga kwance yana kallonta tana ta carafke kamar wata karamar yarinya da haka bacci ya kwashe shi.

     Sai da tayi yar carafken ta tagaji sannan ta tashi taje kitchen ta dora abincin rana, macaroni da wake, tana fitowa ta ganshi tsaye yana waya da alama har ya tashi daga baccin dan gashi nan sanye da three quarter, kallo ta bishi dashi,

"Dan Allah a daure ayi aski" ta fada tana yatsina fuska, binta yayi ya janyota ya matseta ajikin bango tareda fara kokarin zame three quarter din jikinsa, runtse idonta tayi,

"Ki bude idonki kigani idan banyi askin ba"

"Bana son gani"

"Sai kin gani kuwa" kiss ya kaiwa bakinta ta goce ta shige daki da gudu.Ba ita ta fito ba sai da ta jiyo abincinta ya fara kamawa, da sauri ta fito ta shiga kitchen ta sauke abincin, dan kadan ta zubo ta zauna a falo ta fara ci, ganin jawad yana fitowa daga dakinsa ya sata kawar da kanta.



Ummi A'isha🏻
[5/14, 9:18 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

  
  Na
UMMI A'ISHA


67-68


~~~ Kusa da ita ya zo ya tsugunna ya kamo hannunta a hankali yayi mata magana cikin fillanci "sammun abincin queen"

Sam ita bata fahimtar fillanci sosai amma ta dan fahimci nufinsa,

"Menene?" Ta fada fuskarta a murtuke

"Cewa nayi ki sammin" ya fada da turanci,

"Je ka zubo naka" ta fada tana kallon wani wuri, kiss ya kaiwa kan fuskarta yayi mata akan kumatunta, tashi yayi ya wuce kitchen din ita kuma ta jiyo taci gaba da cin abincinta aranta tana tunanin ko yare nawa dansu zai ji idan yazo duniya.

   Bayan ta gama cin abincin daki ta koma ta kwanta aikin kenan daga kwanciya sai zaman falo, bacci ta dan fara yi sama sama amma sai taji alamun mutum a kusa da ita, bude idonta tayi cikin magagin bacci ganin jawad a kusa da ita ya sata saurin tashi,

"Meye haka?"

"Yi hakuri queen, dan Allah ki barni naji dumin jikinki dan Allah" ya fada cikin fuskar tausayi

"Tab wlhi bazan kwanta akusa da kai ba, idan baccin za kayi ka koma dakinka, idan kuma sai anan zaka kwanta to ka matsa can karshen gado" ta nuna masa da yatsanta,

Matsawa yayi ya koma karshen gadon ya kwanta, itama komawa tayi ta kwanta taci gaba da baccinta, kasa hakuri yayi ya sake matsawa jikinta ta bayanta ya rungume ta, tana jinsa tayi zumbur ta tashi tana kallonsa,

"Gaskiya ka tashi ka koma dakinka"

Idonsa ya lumshe sannan ya budesu sunyi dan ja

"Haba queen dan Allah ki barni, pls pls"

Komawa tayi ta kwanta ya rungumeta ta baya yana dan shafarta a hankali, baccin da bata yi ba kenan amma shi mintuna kadan taji ya fara numfashi a hankali alamar yayi bacci kenan.

  Sai misalin karfe hudu sannan ya farka lokacin ita harma ta shiga wanka, fita yayi ya nufi dakinsa yayi wanka ya shirya yayi salla ya fito, a falo ya ganta kwance tana game a wayarta tana sanye da wata bakar riga mai siririn hannu, rigar bata da nauyi domin har yana iya hango farar bra da farin pant din da ta sa ajikinta, tsayinta kuwa bazai wuce cinyarta ba dan ko gwiwarta bai karasa ba, tsayawa yayi yana kallonta yana lasar lebe kamar wani sabon maye,

"Zan fita" ya fada yana kallonta,

"Sai kadawo" ta fada cikeda rashin kulawa, juyawa yayi ya nufi kofa yana tafe yana waiwayenta har ya fice.


  Bai dawo gidan ba sai wurin karfe 8,a dakinta ya sameta kwance ta kure ac tana shan iska tasa kayan baccinta milk colour yar karamar riga da yar top dinta,

"Queen kinci abinci ne?"

"Banci ba"

"To kizo na taho miki da abinci"

"Kawo min shi nan" tafada tana yatsina fuska, fita yayi ya debo mata tarkacen da ya shigo mata dashi ya ajiye mata a gabanta ya fita, tashi tayi ta fara bude ledojin, gasasshiyar kaza da shawarma, da tarin kayan zaki su chocolate da ice cream, shawarmar taci tasha ice cream ta dauki chocolate ta fara sha, tasha chocolate sunfi goma sannan ta hakura ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dawo ta kwanta, shigowa yayi yana sanye da kayan bacci

"Lafiya?" Ta tambayeshi

"Lafiya lau, anan zan kwana saboda jiya kasa bacci nayi" ya fada yana kokarin hawa gadon,

"To karshen gado nanne wurin kwanciyar ka sannan ba za akashe light ba"

  Fuskarta ya kalla

"Ban iya bacci da light ba queen, ni komai kankantar haske hanani bacci yake"

"To sai ka koma dakinka, saboda nima ban iya bacci a duhu ba" tana gama fadin haka ta koma ta kwanta, karshen gadon ya koma ya kwanta ya juya mata baya kamar yadda itama tayi, wurin minti goma da kwanciyar su ta juya ta kalleshi sai taji ya bata tausayi saboda yadda ya takure ya cusa kansa cikin hannuwansa dan kar hasken ya dameshi, tashi tayi taje ta kashe wutar ta dawo ta kwanta.

  Asubar fari ya tashi ya fice bayan ya tasheta tayi sallah, komawa tayi ta kwanta bayan ta idar da sallar, bata fita ba sai wurin 9 lokacin masu aiki har sun gyare gidan tsaf, kazar da ya kawo mata jiya ta dumama ta dafa ruwan zafi ta ajiye akan dining, daki ta koma tayi wanka tayi kwalliya sosai ta shiryo cikin riga da wando na Pakistan kalar ruwan kwai, kan dining ta hau ta fara karyawa, shima jawad fitowar yayi ya hau kan dining din,

"Queen dan Allah ki tausaya min, kiji tausayina pherty" ya fada yana kallonta

"Me nayi maka?"

"Haba queen kullum sai tsokanoni kike yi kuma ki hanani kanki, wannan abun sam bai dace ba queen, kinki saurarata bayan kin san inada bukatarki"

"Au shiyasa ka kawo kayan zaki ashe dama saboda in baka jikina ne?" Ta fada tana tabe baki

"Ni ba saboda haka bane, amma dai kin san ina da bukatar ki ko?"

"Ni ban sani ba" tashi tayi ta shige dakinta,

  Tana nan kwance tana chtn da mutanen nata ya shigo, hayeta yayi ya fara kissing dinta,

"Jawad bana so, meye haka?"

  Bakinta ya tsotsa yaci gaba da sarrafata baji ba gani, tutture shi ta shiga yi amma ta kasa, bai barta ba sai da ya gama tara mata gajiya, duk tsikar jikinshi ta gama tashi har wani jiri yake ji, haka ya tashi zai fita ya dan kalleta,

"Dama fa kyaleki nake bana son nayi miki ta karfi ke kuma kinki ganewa"

"Malam ka fice min acikin daki sannan kar ka sake shigo min daki" ta fada cikeda masifa, fita yayi yana murmushi ya koma dakinsa ya fada akan gado ya kwanta.


  Haka ta gama weekend din nata babu wani abu da ya gudana a tsakaninsu jawad yayi nacin yayi nacin amma taki bashi hadin kai dole sai hakura yayi ya kyaleta. Kayanta ta shirya domin komawa sch, su Sadiya sun koma tun safe ita kuma tace sai da yamma zata koma, kafin yammar babu yadda jawad bai yi ba akan taji tausayinsa amma taki fur da ya matsa mata ma sai tasa kuka, hakura yayi ya kyleta.

  Wanka tayi ta shirya cikin atamfa pink ta yafa mayafi pink ta dauki jakarta ta sameshi a mota, duk baya jin dadi baya son ta tafi saboda yasan zai yi missing dinta duk da ba wani zaman arziki suka yi ba, duk da haka sun dan shaku a yan kwanaki ukun da tayi agidan, itama a tata zuciyar tunanin yanda zata yi missing dinshi take duk da bata wani jiyar dashi farin ciki ba dan ko taba jikinta zai yi sai dai ya faki idonta ya tabata ko kuma yayi mata bazata ya matseta ba tare da ta sani ba amma duk da haka sai tayi masa masifa.

  Tunda ta shiga motar babu wanda yayi magana acikinsu shi dama sam bashida yawan magana sai kuma abin ya hadu da jimamin rabuwa da pherty, radio ya kunna minti kadan ya kashe ya kunna wata wakar larabawa mai dadi, babu wanda yayi maganar har suka shiga cikin makarantar,

"Queen dan Allah karki rinka yawo da kananan kaya kamar yadda kike yi agida" ya fada yana kokarin kamo hannunta,

"To ba mata bane yan uwana, ko da maza aciki?" Tafada tana zumburo baki

"Duk da matane bana so kiyi yawo haka"

"Naji" tafada tana basarwa aranta kuwa cewa take "yaushe zanyi yawo ahaka a hostel agidan ma saboda daga ni sai kai ne shiyasa"

Hannunta ya murza "sai nazo hira"

"Um" tafada ahankali, kiss yayiwa hannun nata ya saki, fita tayi ta nufi hostel shi kuma ya juya ya koma gida.



Ummi A'isha🏻
[5/15, 8:39 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

  Na
UMMI A'ISHA

69-70


~~~ Hostel ta shiga amma tana ta jin tausayin jawad aranta na yanda ya rinka rokonta dazu amma tayi mirsisi tayi biris dashi har kuka ya kusa yi mata amma taki yarda, tana shiga dakinsu ta samu kawayen nata sunata shisshirya kayansu, kan gadonta kawai ta haye ko takalmin kafarta bata cireba,

"Malama ya haka? Idan jawad dinne baki gaji dashi ba gara tun wuri ki dauki kayanki ki koma" Sadiya ta fada cikin tsokana,

"Gaskiya kam dan na fahimci yanzu jawad ya zama rabin ranta" A'isha ta fada itama cikin zolaya

"Sai kuyi kuma" ta basu amsa, nan suka ci gaba da tsokanarta tana mayar musu da amsa amma tunanin jawad yana nan makale acikin zuciyarta.

Shima jawad hakan take dan ko gida bai koma ba gidan Ummi ya tafi can ya shantake sai bayan sallar magrib sannan ya koma gida nan dinma bai tsira ba saboda sai a lokacin yaji hankalinsa ya tashi da rashin pherty,wanka yaje yayi ya shirya cikin kananan kaya yasha turare masu kamshi ya nufi makarantar tasu, daf da zai shiga makarantar yaga sakonta ta rubuto masa text "kana ina yanzu?"

Reply ya tura mata "ina wani wuri"

"Ok kazo to" ta dawo masa da reply

"Ki fito gani nan zuwa" ya mayar mata da amsa,tana daga kwance akan gadonta sanye da kayan bacci riga da wando, mikewa tayi taje ta dauki turarruka ta feffesa daga ita sai Sadiya a dakin domin A'isha ta tafi wani dakin hira, hannun Sadiya ta kama

"Zo ki rakani" babu musu Sadiya ta dauki hijab dinta tabita, itama babban hijabi ta zira, lokacin da suka je inda yayi packing yana cikin motarsa yana waya, gaban motar ta bude ta shiga ita kuma sadiya ta shiga baya, mintuna kadan ya gama wayar,

"Queen" yafada a hankali saboda har kamshinta ya fara rudashi, hannunta ya lalubo ya rike cikin nasa daga karshe ya janyo ta cinyarsa, wutar motar ya kunna ya fara kokarin cire hijab din jikinta domin yana son ya tabbatar da ko taji maganar da yayi mata dazu ko kuma bata jiba,

"Baku gaisa da Sadiya ba" tafada tana rike hannunsa, shi sam bai ma san su biyu suka shigo ba, juyawa yayi suka gaisa da sadiya, suna gaisawa Sadiya ta fita tace tana jiranta a waje, hijabin nata ya daga kayan nata ba masu sharara bane sannan ba kanana bane dan rigar ma ba mai siririn hannu bace.

  Fuska ta bata ta hade rai "nifa bana son haka"

"Oh dama saboda Sadiya tana nanne shiyasa baki yimin gardama ba ko"

Baki ta zumbura ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata, cikinta ya shafa "kinci abinci kuwa?"

"Naci" tafada a takaice, bakinta ya kaiwa kiss ya manna mata,

"Bacci nake ji sai da safe" tafada tana kokarin tashi daga jikinsa,

"To queen sai da safe kiyi mafarkina" bata bashi amsa ba ta bude motar ta fice, tun a hanya sadiya take tsokanarta har suka shiga daki suna zuwa sadiya ta fara bawa A'isha labari nan suka hadu sukai ta tsokanarta.

  Kullum sai jawad ya kirata awaya amma taki zuwa weekend yayi yayi da ita kan tazo gida amma taki zuwa bayan kuma itama tana cikin damuwar rashinsa, wannan week din dai ta shirya zuwa gida dan haka ana idar da sallar juma'a ta yiwa A'isha da sadiya sallama ta tafi gidanta.

  Lokacin da taje gidan jawad baya nan dan haka daki ta shige tayi kwanciyarta, bata wani dade sosai da zuwa ba sai gashi ya dawo, yana ganinta ya fara murna ya karasa kusa da ita ya zauna tana kwance daga ita sai bra da pant tana shan iska,hannunta ya riko,

"Queenkin mayar dani gwauron karfi da yaji, kinga fa ko abinci sai naje gidan Ummi nake samu"

  Kallonsa tayi ta gefen ido,"to yanzu me kake son ayi kenan?"

"Queen ki hakura da zaman hostel dinnan ki dawo gida pls, nayi miki alkawari zan rinka kaiki kullum"

Zumbur ta tashi zaune,"nadawo gida fa kace, tab wlhi a'a indai kaga na bar hostel to wlhi gama karatuna nayi" ta karasa maganar tana zumbura baki, dafata yayi

"Shikenan ya isa maganar ta wuce, kinyi girki?"

"Nifa kaga hutawa nazo yi babu girkin da zan iya yi yanzu saboda gaba daya a gajiye nake"

"Ok to me zaki ci?"

"Zanci komai amma banda shinkafa"

"To bari na aiki mai gadi ya siyo mana abincin, nima yunwa nake ji" bata bashi amsa ba har ya tashi ya fice.

  Amala da miyar dage dage ya kawo mata gefe kuma sakwara da miya sai fresh milk roba biyu, tashi tayi ta fito falo daga ita sai pant ta bra, kofar yaje ya kulle gudun kar wani ya shigo sannan ya dawo ya zauna yana tambayarta wanne zata ci amala ko sakwara, amalar ta dauka dan rabonta da amala har ta manta gara gara ma sakwarar lokacin da tana gidan dada tana yawan yi.

"Bakida kunya yanzu ko queen? Ki rinka zama tsirara?" Ya fada yana kallonta

"To meya shafeka?" Ta fada tana harararsa

"Ya shafeni mana tunda property nane"

"Nice property din?" Ta fada cikeda jin haushi,

"Yes you are my property queen"

Rabuwa tayi dashi bata sake magana ba har ta gama cin abincinta ta tashi ta koma daki.

  Koda lokacin bacci yayi ya shigo dakin hanashi kwanciya tayi nan ya shiga magiya amma fafur taki dolensa yabar dakin ya koma nasa ya kwanta.

  Da safe da fushi ya tashi akan fuskarta dan gaskiya yana shiga wani hali a yan kwanakin nan kawai daurewa yake gashi abun yana neman fin karfinsa, yana kwance acikin falo yana wasa da wayarsa sai ya kamo wani tune din mage,zuruf pherty ta fito da sauri daga cikin daki,

"Jawad me nake ji a gidan nan kamar kukan mage?" Ta tambayeshi a tsorace

"Eh mage ce amma ta fita ai na dade da kawota gidan nan, bata zama ne yawo take fita sai dare take dawowa"

Idanuwanta mayalwata ta zaro "tab ai kuwa ka fitar da ita saboda ni bana shiri da kuliya tsoronta nake" kofar falon taje ta sadada ta leka amma bata hangota ba dan haka tayi gaggawar rufe kofar ta dawo ciki tana ta yi masa masifar danme zai kawo mata mage gidanta, wunin ranar tayi shine acikin daki ko falon kin fitowa tayi saboda tsoron mage, shidai yana jinta duk fadan da take amma bai cemata uffan ba.

Bayan sallar isha ta shiga wanka, sadadowa jawad yayi yazo ya tura wayar karkashin gadonta ya fice, tana gama wankan ta fito ta shirya ta shafa humra da turarruka bayan ta shafa man ambar musk, wata light blue din rigar bacci ta saka wacce da ita da babu ba bambanci ta haye gadonta ta kashe wuta ta kwanta.

  Can ta dan fara bacci ta jiyo kukan mage a karkashin gadonta, ai da gudu ta sauko daga kan gadon ta nufi kofa ta fara lalube, ita kuwa mage sai kuka take miyau miyau, dakyar ta samo kofar jikinta sai rawa yake, dakin jawad ta nufa da gudu tana shiga taga dakin duhu dim bata yi tunanin kunna haske ba ta fara neman gadonshi acikin duhun, gadon ta hau jikinta sai rawa yake tana laluben jawad amma bata jishi ba, yau nashiga uku tafada acikin zuciyarta, can tsakiyar gado ta jiyo shi yana kwance ya rungume pillow, pillow din ta zare ta shige jikinsa ta kankameshi har lokacin jikinta rawa yake,

"Queen menene?" Ya tambayeta yana sake rungumeta,

"Jawad magen nan ta dawo,tana dakina, tana karkashin gadona"

"Gobe zan fitar miki da ita tunda kinga yanzu dare yayi" kankameshi tayi saboda duk a tsorace take gani take magen na iya biyota nan dinma.

Ahaka suka yi bacci tana kankame dashi har asuba tayi, ahankali ya zare jikinshi yaje dakinta ya dauko wayarsa daga karkashin gado yazo yayi alwala ya tasheta. Sam kin komawa dakinta tayi sai da gari yayi haske sosai tare suka je ya rakata a gabanta ya dudduba ko ina amma babu mage babu dalilinta, ce mata yayi har ta fice yawonta dan haka ta saki jikinta, haka ta zauna a dakin amma har lokacin a tsorace take, shima jawad din ta hanashi fita ko ina tace sai dai su zauna tare.

Daren ranar dama ko tunanin kwanan dakinta bata yiba dakin jawad taje, yau kam yazo mata da sabon salo amma fur taki aminta, lallashin duniyar nan babu wanda bai yi mata ba amma taki, magana ya fara yi mata cikin rawar murya kamar wanda yake kuka

"Haba Xarah wannan wanne irin rashin imani ne, meyasa wai bakya tausayi nane? Yanzu idan baki kwantar min da hankali ba ina kike so naje abani kwanciyar hankalin, ki tausaya min Xarah, wlhi ina cikin wani hali ko so kike na mutu?" Ya fada muryarsa tana rawa sosai, banza tayi masa bata bashi amsa ba,

"Xarah, pherty, pherty" ya kira sunanta yana girgiza ta amma taki bude idonta, tana jinsa jikinshi har wani dan zafi yayi kamar me zazzabi, sakinta yayi ya juya mata baya ya kwanta, ta bayanshi ta rungumeshi saboda har yanzu tana tsoron mage hakan da tayi ya sake rikitashi, take ya fara hawaye amma bai bari taji ba, juyawa yayi ya kwanta ruf da ciki, hayewa bayansa tayi ta sake kwanciyarta, shikuma abin duniya yayi masa yawa gashi ya kasa bacci da haka har asuba tayi, tashi yayi yai alwala ya tasheta shi kuma ya fice daga cikin dakin.

  Tunda gari ya waye ta fara harhada shirginta saboda yau zata koma sch gobe tana da test sassafe, jawad kuwa ko magana baya yi yayi shiru yana kwance akan kujera, kitchen ta shiga ta dafa farar shinkafa ta hada salad ta yi yar sos ta fito, zama tayi taci ta koshi ta bar masa nashi a flask, tana gamawa taje tayi wanka ta shirya ta dauko dan kit dinta ta fito lokacin karfe 3 daidai, a inda ta barshi anan ta sameshi,

"Nafito" tafada tana kallonshi duk ya bata tausayi saboda bashida maraba da marar lfy, jikinshi duk ya saki idonsa ya dan yi ja, bai ce da ita komai ba ya tashi ya dauko key din motarsa ya fice tana biye dashi a baya.

Sai da suka hau titi sannan ya kalleta tasha atamfarta yellow da farin mayafi

"Ke bakida tausayi ko? Kin kwammata na mutu akan ki bani abinda nake so ko? Saboda bakya kaunata, nagode"

Kallonsa tayi duk tausayinsa ya cikata amma ba tace komai ba, shi dinma bai kara magana ba har suka je makarantar ya ajiyeta ya juya ya tafi, sukuku ta shiga hostel duk zuciyarta babu dadi.

Tunda ta koma bata da wani farin ciki ko karatun test dinma ba tayiba haka ta rubutata, tunanin halin da jawad kawai yake ciki take yi, wayarta ta dauka ta tafi gaban dakinsu ta zauna ta fara neman layin hawy, ringing biyu ana ukun ta dauka,

"Ta mama ya kike?" Fuskarta ta dan yamutsa

"Ba kalau ba, hawy jawad yana cikin wani hali amma duk laifina ne, jiya babu rokon da bai yi min ba amma nayi kememe na hanashi kaina"

Masifa hawy ta fara yi mata "ai bakida wayo, tun yaushe kukayi auren? Yaufa wurin 2 months da bakinku haba phertyn mama shifa namiji ne mai jini ajika taya ba zai bukaci mace ba, gaskiya banji dadiba, yanzu bakya tsoron ya samu wata lalurar ta dalilin wannan ko kuma bakya tsoron yaje ya nemi matan banza a waje? Gaskiya nidai kin bani mamaki, kin bani kunya, koda zaki rama abunda yayi miki a baya ai bai kamata ki rama ta hanyar hanashi kanki ba kuma ma har ya fito fili ya nuna miki yana bukatarki amma kika hanashi"

Wasu hawaye ne suka sauko akan kumatun pherty "hawy bazan sake ba in Allah ya yarda, wlhi bazan sake ba wannan dinma kuskure ne"

"Yawwa phertyn mama dan Allah kar ki sake yiwa jawad rowar kanki kinga ba dan kin hanashi ba da tuni kila kinada juna biyu yanzun"

Murmushi tayi, "yaushe zaki zo min?"

"Sai komai ya daidaita zaki ganni"

Daga nan sallama suka yi ta tashi ta shiga daki ta kwanta tafara tunanin jawad.

Tun daga nan bata sake jin jawad ba amma ta daura niyar zuwa koda shi bai zo ba. A ranar da daddare sai gashi yayi mata text wai tazo yana jiranta gashi ya shigo sch dinsu, hijabinta kawai ta dauka ta dauki phone dinta tacewa su Sadiya zata je wurin jawad, nan A'isha ta shiga tsokanarta wai yau bata neman yar rakiya, murmushi kawai tayi ta fita.

Acikin motarsa ta sameshi ya kifa kansa jikin sitayarin motar, zama tayi jikinta a sanyaye, takai minti biyu da zama amma bai dago kansa ba,

"Jawad baka da lafiya ne?" Sai a lokacin ya dago kansa idonsa a lumshe,

"Xarah koma baya gida zamuje, dan Allah Kar ki k'i zuwa, wallahi banida lafiya, ko driving dinma dakyar na iya yi nakawo kaina nan"

  Kujerar baya ta koma ta zauna shikuma ya koma dayan sit din ya zauna ya zaro wayarsa dakyar ya kira driver din dad yace yazo ya sameshi anan ya mai dashi gida saboda shi bazai iya mayar da kanshi gida ba, hannunsa ya mika baya ya kamo nata,

"Queen banida lafiya sosai, banida lafiya" ita dai bata iya cewa komai ba, mammatsa hannunta yaci gaba dayi jikinshi duk yayi kuna ya danyi zafi, da haka driver yazo ya samesu ya daukesu amma shi driver din bai ma san su biyu bane saboda bai ga phertyn ba, sai da ya kaisu gida yayi packing ya tafi sannan suka fito suka shiga ciki suna zuwa falo jawad ya yanke jiki ya fadi sharaffff!.



Ummi A'isha🏻
[5/19, 5:23 PM] Ummi A'isha🏻: [5/19, 3:38 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

  Na

UMMI A'ISHA


71-72


~~~ Da sauri pherty ta k'arasa inda yake ta tsugunna a gabanshi tareda fara jijjigashi,

"Jawad, jawad" tafada bakinta yana rawa, idonshi ya dan bude kadan wanda suka yi jajur, dakyar ya iya bude bakinsa yayi mata magana,

"Xarah bani ruwa nasha pls" ya fada yana sake lumshe idonsa, da sauri ta tashi taje ta dauko masa ruwan ta kawo masa, adaidai kanshi ta zauna ta dauki kansa ta dora akan cinyarta a hankali, robar ruwan ta saka masa akan bakinshi,

"Jawad karbi ruwan kasha kaji"

Ahankali ya bude bakinsa ta bashi ruwan yasha, bayan yasha da kamar minti uku ya fara yi mata magana a hankali,

"Queen ciro min phone dina a aljihuna ki kira min doctor"

Bata jira ya karasa ba ta fara laluben aljihunsa, wayar ta ciro ta fara kiran doctor Ansar kamar yadda taga ya rubuta ajiki.

  Mintuna kadan dr din yazo, hannunta yana makale cikin nashi jikinshi kuwa kamar wuta don kuna, yayi zafi rum, agabansu dr din ya tsugunna lokacin da ya shigo ya fara tattaba jikin jawad tareda tambayarsa abinda ke damunsa amma ita bata san me suke fada ba saboda da fulatanci suke magana ita kuma ba wani ji take yi sosai ba.

Mintuna kadan dr din ya jiyo yana kallonta, "ke ba wife dinshi bace?" Ya tambayeta

"Itace" ta bashi amsa a tsorace,

"Amma kika barshi ya shiga cikin wannan halin?"

Kwalla ce ta ciko idonta batare da tayi magana ba,

"Mijinki bashida lafiya sosai, gashinan ma yanzu may be sai na kara masa ruwa amma tunda fever ya rufeshi yanzu allura zanyi masa sai natafi, tomorrow in the morning i will be back in yaso sai naga yanda jikin nashi yayi"

Kwallar idonta ce ta gangaro kan kumatunta, dr dinne ya daga jawad ya nufi cikin bedroom dinta dashi, tashi tayi tabi bayansu, a kan gadonta ya kwantar dashi yazo ya dauki first aid box dinshi ya koma dakin lokacin tana tsaye a gaban gadon sai hawaye take, juya jawad Dr din yayi tareda zaro sirinji zaiyi masa allura, idanuwanta ta kulle har sai da ya gama sannan ta bude, juyashi ya sake yi ya rufe first aid box dinshi ya yi mata sallama ya tafi.

  Yana fita ta karasa kan gadon ta hau jikinshi ta taba taji har yanzu da akwai zafi rau, kallonsa tayi cikeda tausayawa sai kuma ta fara kuka

"Dan Allah jawad kar ka mutu, karka mutu ka barni, yanzu idan ka mutu me zan cewa su Ummi? Me zan fadawa yaya aadil idan har nayi sanadiyyar mutuwar dan uwansa?" Haka tayi ta fada acikin zuciyarta,tun tana kukan zuci har ta fara na fili, a hankali jawad ya bude idonsa, hannunsa ya mika ya jawota ya kwantar da ita a gefen jikinshi, kukan ta daina tayi shiru tana ajiyar zuciya, zuwa can taji yayi bacci, agogo ta kalla karfe 1 daidai,a hankali ta tashi taje ta rufo kofar falo ta dawo ta rufe ta dakin ta koma kan gadon ta  zauna tareda tsurawa jawad ido.

  Tana nan zaune yanda taga rana haka taga dare har asuba tayi, bayan ta idar da salla taga ya fara motsawa a hankali, da sauri ta tashi taje inda yake,

"Sannu jawad'muje kayi alwala" dakyar ya mike jiri yana daukarsa luuuuuuh, saurin rikeshi tayi ta rakashi toilet yayi alwala ya fito, daga zaune yayi sallahr yana idarwa ta taimaka masa ya koma ya kwanta akan gadon, minti kadan ya sake komawa bacci,kusa dashi taje ta kwanta tareda rungumeshi ajikinta,bacci ne itama yayi awon gaba da ita.

Wurin karfe 8 na safe ta farka, jikin jawad ta taba yanzu babu zafin da alama zazzabin ya sauka daga jikinsa, tashi tayi taje ta shiga kitchen ta hada musu breakfast ta kawo ta ajiye akan dan karamin stool din dake ajiye agaban gadon,toilet ta shiga tayi wanka ta fito daure da towel ajikinta ta zauna tayi simple make up ta tashi tasa wata farar riga yar kanti mai siririn hannu da wandonta jeans fari iya gwiwarta,jawad ta kalla wanda har yanzu yake kwance yana ta sharar bacci amma fuskarsa ta dan rame kadan, tausayinsa taji yana shigarsa, bugun da taji ana yiwa kofar falon ne ya sata daukar katon hijabi ta fita, dr ansar ta gani lokacin data bude kofar, tare da dr din suka shiga dakin har inda jawad yake kwance,

"Har yanzu bai tashi ba?" Dr din ya tambayeta

"A'a yatashi yayi salla da asubha" ta fada cikin rawar murya

Jikinsa yaje ya fara bincikawa yana tabawa, magunguna ya fito dasu ya mika mata,

"Gashi idan ya tashi yasha wadannan magungunan bayan yayi breakfast, amma karki tasheshi har sai ya tashi da kansa, idan da wani problem sai yayi calling dina" dr ya fada daidai lokacin da yake kokarin barin dakin,

"Ok dr mun gode" ta fada ahankali, yana fita taje ta zauna a gefen gadon ta kamo hannun jawad ta rike cikin nata.

Ta dade azaune tana wasa da hannunshi tana kissing dinshi ganin bai tashi ba ya sata komawa falo sai a lokacin ta tuna da wayarta, wayar ta dauka taga missed called bila adadin nasu Sadiya, Aisha da hawy, su Sadiya ta fara kira tana dauka ta fara yi mata tsiya

"Kaga phertyn jawad mai komai dozin, shine tafiya babu sallama?"

Myrmushin karfin hali tayi tace "wlhi Sadiya jawad ma kin ganshi can kwance bashida lafiya, shiyasa jiyan ban dawo ba"

Ayya to Allah ya bashi lfy, idan ya tashi ki gaisheshi"

"Zai ji, ina A'isha?"

"A'isha taje lecture amma idan tadawo zan fada mata"

"To shikenan ki gaisheta" kashe wayar tayi ta fara neman layin hawy,

"Ta mama ina kika shigane najiki shiru"

"Hmm kibari kawai yanmatan mama jawad ne bashida lfy tun daren jiya"

"Kai, meya sameshi? Hala dai kece sanadi ko?" Hawy ta jero mata wadannan tamvayoyin lokaci daya,

"Um haka dr yace wai laifinane" tafada kamar zata yi kuka,

"Hmm shima jawad ya bani haushi ai, wlhi da ace nice shi da tuni nadade da tara miki gajiya,amma shi ya wani tsaya lallaminki kamar wadda yake tsoronki"

"To muguwa sai kuma Allah yayi ba ke din bace balle kiyi mugunta"

"Ai wlhi bari ya warke sai kin dandana kudarki"

"Malama sai anjima, lokacin da kika gyara kalmominki za muyi waya amma yanzu ki barni da abinda ke damuna" tana gama fadin haka ta kashe wayar ta tashi ta nufi dakinta.


Lokacin da ta shiga dakin daidai lokacin jawad ya bude idonsa, zaune ya tashi fuskarsa a murtuke babu fara'a, kokarin saukowa daga kan gadon ya fara, da sauri pherty taje kusa da shi da niyyar rikeshi saboda tana tsoron kar ya sake faduwa irinta jiya, dakatar da ita yayi da hannunsa, cikin sauri ta kalleshi,

"Jawad menene?" Ta tambayeshi a jagule

"Babu komai, karki tabani, ai nagane bakya sona bakya kaunata tun tuni, idanma na mutu ke bakida damuwa, da raina kina neman sai kin halakani,saboda kin san koda na mutu ke bakida asara"

Manyan idanuwanta ta sauke akan fuskarsa,

"Haba jawad ya zaka rinka furta irin wadannan maganganun? "

Bai sake magana ba yayi gaba ya nufi kofar fita, dakinsa ya shiga bata yi kasa a gwiwa ba ta juya ta bishi, lokacin data shiga yana kokarin cire rigar jikinsa, toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka ta fito, baiyi mata magana ba ya shiga toilet din,

Ajiyar zuciya tayi tace "wata sabuwa,kaima ramawa zaka yi kenan" dakinta ta koma ta kinkimo kayan breakfast din data hada ta kawo dakinsa lokacin har ya fito daga wankan yana daure da towel, kayan ta ajiye ta koma ta dauko magungunansa ta kawo ta ajiye, tana zaune tana kallonsa ya tsane jikinsa da dan karamin towel ya fesa turare ya dauki kananan kaya yasa, short nicker da t shirt baka,

"Ga breakfast din, dr yace kar kasha magani sai kayi breakfast" tafada kamar wata marar gaskiya,

"Ba wani magani da zan sha, amfanin me maganin zaiyi min? Dan bansha maganin ba ai ba mutuwa zanyi ba, kuma kema ki rike abunda kike takama dashi idan kin hanani hakan ba zai zama sanadiyyar karewar rayuwata ba" ya fada yana gyara belt din wandonshi,

Kallonsa ta tsaya yi tana tunanin amsar da zata bashi saboda kalamasa sunyi mata zafi sosai ba kadan ba,

"Dama dan na hanaka kaina ai ba zaka mutu ba sai dai kawai kayi rashin lafiya tunda na fuskanci wannan din shine mahadin rayuwarka,kuma ai mutuwar ma zaka iya yi idan baka samu ba"

Kallonta yayi ya dauki cumb ya fara gyara sumar kansa,

"Kin San dai duk abinda yake agidan sarki akwai shi a kasuwa ko?"

"Ehh da akwai amma na kasuwa ai jagwalgwalo ne" tafada tana hararsa,

"Jagwalgwalo? Meye jagwalgwalon?" Ya tambayeta yana kallonta,

"Oho maka, kabari ka iya hausa tukunna kafin ka gayawa mutane magana" tana kaiwa nan ta juya ta fice daga dakin ta koma falo ta zauna.

  Tea ya hada yasha ya dauki magungunan ya tura cikin drawer gadonsa yana tsaki domin shi a duniya idan da abunda ya tsana to maganine, sam baya kaunar magani, falon shima ya fita ya sameta tana kwance a doguwar kujera ta cire rigar jikinta daga ita sai bra da dan short trouser dinta iya gwiwa,kujerar nesa da ita yaje ya zauna yana satar kallon cikinta, ita kam kanta ta dauke daga kallonsa daga karshe ma ta juya masa baya ta mayar da kanta daya barin.




Ummi A'isha🏻
[5/21, 9:30 AM] Ummi A'isha🏻: 👑👑👑MARTABA TA👑👑👑



  Na
UMMI A'ISHA


73-75


~~~  Zaman kurame suka ci gaba dayi kowa yana ta faman fushi, tashi pherty tayi taje kitchen ta hado tea empty ta dawo ta zauna ta fara juya tea din da spoon, juyowa jawad yayi ya kalleta sai kuma ya dauke kansa yayi tsaki, hararsa tayi ta fara shan tea din aranta tana cewa "kayi tsakinka ka gama ehe"
Tana gama shanyewa ta tashi ta koma kitchen ta ajiye cup din ta dawo, cikinsa taga ya rike yana kokarin saukowa daga kan kujerar da yake zaune, cikin sauri ta tashi taje wajensa,

"Jawad menene? Baka sha maganin ba ne?"

Ta tambayeshi a rude, bai iya bata amsa ba saboda aman da ya fara yunkurin yi, cikin sauri ta rungume shi a kirjinta nan ya fara sheka amai tea din da yasha duk sai da ya amayar dashi ajikinta gashi ko riga babu daga ita sai bra, dandanan zazzabi ya sake rufeshi, rungumeshi ta sake yi

"Sannu" tafada cikeda tausayawa, akan carpet ta kwantarshi ta tashi taje ta dauko karamin towel ta dawo ta fara goge masa aman jikinsa, rigar ta cire masa ta goggoge masa wuyansa sannan ta fara kokarin gyara nata jikin, bra din ta balle ta cire ta goge jikinta, bude idonsa yayi a hankali ya kalleta, suna hada ido taji kunya ta kamata saboda yanda ya kurawa kirjinta ido da sauri ta mike ta nufi dakinta ta sako riga ta ta debo ruwa acikin dan karamin kwano ta dauko wani towel din ta dawo inda jawad yake, towel din ta tsoma acikin ruwa ta fara goge masa jikinsa a hankali, fatarsa luwai luwai ga gashi kwance tako ina ajikinsa, daidai kasan cibiyarsa taga wani digon baki mai kyau nan ta tsaya kallo ganin idonsa a lumshe yasata kai bakinta wurin, harshenta tasa ta fara lasar digon bakin, shi dai jawad yana kwance yana jinta amma jikinsa sai kace wuta dan zafi.

  Hannunta ya kamo "Xarah kashe fankar nan har ac din sanyi nake ji"

  Da sauri ta tashi taje ta karkashe ta dawo wurinsa, "shine kika rufe min bayan ban gama gani ba" ya fada idonshi a lumshe, hannunsa ta matsa,

"Nakira dr ansar yazo ya dubaka?"

Kai ya daga mata alamun ehh, cikin sauri ta tashi taje dakinsa ta dauko wayarsa ta fara kiran dr din amma wayar tasa a kashe,

"Wayarsa akashe dan Allah ka daure kasha maganin"

Kamar wani karamin yaro ya yamutse fuska "bana son magani wlhi"

Kusa dashi tazo ta zauna ta kamo hannunsa ta rike, "kayi hakuri kasha kaga ai baka da lfy sosai"

Idanuwansa ya lumshe,sumar kansa ta shafa "na dauko maka kasha?" Kai ya daga mata, tashi tayi taje ta dauko maganin ta kawo masa,

"To tashi kasha"

"Ki dauko min cock" kallonsa tayi"da cock zaka sha?"

"Uhm" yafada lokacin da yake kokarin tashi, cock din ta dauko masa ta ciro magungunan ta bashi ya karba yasha, yana gama shanyewa ya koma kan doguwar kujera ya mike sai bacci.

Ajiyar zuciya tayi ta kalleshi, "jawad case ace shan magani sai da dabara?" Kujerar da yake kwance ta karasa ta tsugunna agabansa gamida hada fuskarta da tashi, ta dade tana jujjuya fuskarta akan tasa sannan ta tashi taje kitchen ta dora musu abinci, jalop din zallar wake da kifi ta dafa.

  Lokacin da ta fito ya farka, da sauri ta karasa gabansa "sannu"

Hannunta ya kamo ya tashi zaune "hada min ruwa nayi wanka zafi nakeji"

"To zo muje" hannunta ya rike yabita har cikin dakinsa ta shiga toilet ta hada masa ruwan ta fito,

"Kashiga kayi wankan"

Kai ya langabar "muje kiyi min" ido ta zaro

"Yi hakuri kayi kaji" shigewa cikin toilet din ya yi batare da yace komai ba.

  Falo ta koma ta je ta shirya masa abinci ta zauna tana jiran fitowarsa, daga shi sai farin gajeren wando da farar t shirt mahadin wandon ya fito,

"Sannu na kawo maka abincin ko?" Zama yayi yana kallonta

"Kunna min ac,kadan zaki zubo min" tashi tayi taje ta kunna ta zubo masa faten waken a filet ta kawo masa, janta jikinsa yayi "kibani a baki queen"

Batayi musu ba ta fara bashi,hannunta ya kama "nakoshi bani ruwa nasha"

"Ayya jawad dan kara kadan kaji, dan kara pls" cigaba da bashi tayi har sai da ya cinye tas, tsakiyar falon ya koma ya kwanta akan carpet,

"Queen zo kiji" ya fada yana mika mata hannu,bata yi musu ba ta tashi ta koma kusa dashi ta zauna, janta yayi jikinsa ya kwantar da ita ya fara lalubarta, bata yi masa gardama ba balle tayi kokarin hanashi yau dai ta tayi abun kai wacce rana ya tabata bata yi masa masifa ba.

  Yar guntuwar rigarta ya zame, ya kankameta ya fara wasanni ajikinta, idanuwanta kawai ta lumshe tana jin yanda yake bidirinsa a jikinta son ranshi, hannunsa ta rike,

"Kamanta abinda ka fada dazu? Dazun nan ka gama cewa na rike abinda nake takama dashi"

Dan murmushi yayi wanda ya kawata fuskarsa "ai kawai fada nayi amma ba har zuciyata ba, tayaya zan iya fushi da ke?"

  Bakinta ya tsotsa ya ja hancinta, "ni yanzu ma babu abinda zan iya yi saboda jikina ba lafiya" sai a lokacin taji hankalinta ya dan kwanta,jagulata ya fara yi ta kowanne bangare yana wasa da kirjinta wanda shine yafi komai daukar hankalinsa.

  Sun jima acikin wannan yanayi kafin ya iya hakura ya kyaleta yana maida numfashi a hankali, rungumeta yayi tsam ajikinsa ya fara sinsina gashin kanta, tana kwance akan kirjinsa a haka bacci ya dauketa, amma shi bai yi baccinba sai ma cigaba da yayi da mammatsa jikinta har lokacin salla yayi.

  Zameta yayi ya tashi ya shiga dakinsa dama jira take ya tashi dan haka yana tashi itama tayi gaggawar shigewa dakinta tasa key, toilet ta shiga tayi wanka ta fito tayi salla bayan ta idar ne ta fara kokarin shiryawa, kwalliya ta tsara a fuskarta jikinta kuma ya dauki daddadan kamshi mai tausasa zuciya, wata pink din riga tasa mai zanen lips ajiki, an rubuta KISS ME da manyan harrufa, rigar roba ce sannan bata da nauyi yar shafal take yar karama da ita, bakin wando jeans tasaka iya gwiwarta ta gyara gashin kanta ta daureshi da ribom pink colour.

  A hankali ta bude kofar dakin nata ta dan leka, jawad ta gani kwance akan kujera yana waya, fitowa tayi ta shige kitchen daga tsaye ta tsaya ta zuba faten waken dan kadan taci ta dauki juice ta fita,

"Zo kiji pherty na" ya fada yana yi mata murmushi,kusa da kujerar da yake taje ta zauna,

"Yaya aadil sun dawo dazu, yaushe za muje muyi musu sannu da zuwa?"

Dan murmushi tayi ta kurbi lemon dake hannunta,

"Sai ka samu saukin jikinka sai muje"

Gaban rigarta ya kalla, a hankali ya tashi ya matsa kusa da ita,

"Ya akayi?" Tafada tana kallonsa,

"Umarni zan cika na abinda kika nema, gashi nan rubuce jikin rigarki" ya fada yana nuna mata da dan yatsansa, ja da baya tayi

"Nidai gaskiya ba zaka bata min kwalliyata ba, tashi tayi zata gudu yayi saurin riketa ya jawota, kokawa suka fara,akan kujerar ya shimfidar da ita ya matseta,

"Gaskiya jawad nidai ka bari kar ka bata min kwalliya ta" ta fada a shagwabance,

"Idan na bata miki zan sake miki wata kinji my queen"

"A'a nidai ban yarda ba gaskiya" bai barta ta karasa ba ya hade bakinsa da nata, lips dinta na sama ya kama,

"In ciza?" Ya rada mata a kunnenta,

"Ka ciza mana nima in rama" ta fada tana lumshe idonta,dan cizar lip dinta yayi, nan suka fara kokawa ita a dole sai ta rama, kanshi ya cusa a wuyanta, gefen kunnenshi ta samu ta ciza,

"Ahh sai na rama ai ba haka nayi miki ba"

"Kaima da zafi kayi min"  a tsakiyar kirjinta ya sake cizonta, yana dagowa ta rike lip dinsa na kasa da hakoranta, kwankwasa kofar da aka fara yine ya katse musu wasannin da suke yi cikin nishadi,dagata yayi yaje ya bude kofar, Sadiya da A'isha ne suka shigo, tana nan kwance inda ya barta ganinsu ya sata daka tsalle taje ta rungumesu,

"Nayi missing dinku yan dakinmu, sannunku da zuwa" akan kujera suka zauna ta shige tsakiyarsu,

"Sai yanzu zaku zo maimakon kuzo tun safe mu wuni"

"We are sorry amarya" suka fada atare suna dariya,

"Yaya jawad ina wuni? Ya jiki?" Suka fada suna kallon jawad

"Lfy lau jiki yayi sauki" ya fada cikin hausarsa ta yan koyo,

"Kun ganshi nan har yau ya kasa iya hausa, ya iya kowanne yare hausa ne bai iyaba dan rashin kara" pherty ta fada daidai lokacin da ta tashi ta nufi kitchen,

"To ai kece baki koya min ba" ya fada tareda tashi yabi bayanta, a kitchen ya tarar da ita tana yanyanka lemo dasu abarba da sauran fruit akan filet, ta bayanta ya turata ya matseta ajikin lokokin dake jere cikin kitchen din,

"Wash jawad marata, dan Allah kabari"

Matsawa yayi,"kawayenki sunzo shiyasa zaki kyaleni ko? Wannan ranar ta yau ranace mai mutukar muhimmanci agareni, ranar da pherty ta barni ta sakar min fuska, ta kyaleni nayi wasa da ita"

Murmushi tayi ta dauki katon farantin data zuzzuba kayan zata fita, jawo rigarta yayi "bakiyi comment ba, let me go and write this moment in my diary"

Sakinta yayi ta fita yabi bayanta ya wuce dakinsa, Sadiya da A'isha suka hada ido suka kwashe da dariya,

"A'a bangane bafa, ya zaku tasani gaba kuna dariya? Yanzu zanyi muku rashin mutunci"

"Mu bake muke yiwa dariya ba" A'isha ta fada tana wata dariyar,

"Ai dama har angane yan dakinmu shiyasa mutane bazasa son zuwa saboda duk wanda yazo sai kunyi masa dariya keda Sadiya"

"Yoh mutum da bakinsa, ai dole muyi dariya" inji Sadiya

"Sai kuyi tayi ai" inji pherty

Kayan da ta hado musu ta gabar musu nan suka shiga hira suna motsa baki sai daf da mangaruba sannan suka tafi.

Dakin jawad ta shiga yana kwance akan gadonshi, a gefenshi ta kwanta, "jawad kayi salla?"

Kai ya daga mata, "to me zaka ci?"

"Fura da nono zansha"

Tashi tayi taje ta damo masa a kofi ta kawo masa, ta koma dakinta ta shiga wanka ta fito tasa sleeping dress kamar tayi kwanciyarta a dakinta sai kuma ta tuna da batun magen rannan, zuruf ta tashi ta nufi dakin jawad, tana shiga taganshi ya fito daga wanka, kan gadon taje ta haye taja blanket ta rufe jikinta ta rufe idanuwanta.



Ummi A'isha🏻
[5/22, 8:28 AM] Ummi A'isha🏻: [5/21, 9:06 PM] Ummi A'isha🏻: 👑👑MARTABA TA👑👑


Na
UMMI A'ISHA


76-78


~~~ Kwanciya tayi ta juya bayanta tana jiran hawowarsa gadon, sai da ya feshe jikinsa da turarruka masu dadin kamshi sannan yasa kayan baccinsa ya kashe wuta ya hau kan gadon, jikinsa ya matso da ita ya rungumeta yana shafa gashin kanta nan da nan bacci ya dauketa, shi dai sai da ya kwashe lokaci mai tsawo kafin yayi baccin.

  Koda safiya tayi makara suka yi basu tashi ba sai wurin 6 harda yan mintuna, pherty ce tafara bude idonta ta kalli jawad wanda ke kanannade da ita kamar za a kwace masa ita, bakinshi akan tsakiyar gashin kanta ya makalkaleta sosai, murmushi tayi, tayi kissing din kirjinsa sannan ta fara kokarin tashinsa, bayansa ta shafo ta kirashi a hankali,

"Jawad, jawad tashi"

Ahankali ya bude idonsa ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta wadda kamar ba daga bacci ta tashi ba, murmushi ya sakar mata ta mayar masa da martani, tashi yayi ba tare da yayi magana ba, ya shiga toilet kafin ya fito har ta gudu dakinta, bayan ta idar da salla ta sake kwanciya har sai wurin 9 sannan ta tashi tayi wanka taci gayunta cikin bakar t shirt da jan wando, kitchen ta shiga lokacin har masu aiki sun gama kimtsa ko ina, dankali ta dauka ta fara ferewa tareda kunna karatun alqur'ani kira'ar sudais acikin wayarta tana aikinta tana bin karatun, shigowar jawad cikin kitchen dinne ya sata kashe karatun ta jiyo ta kalleshi da alama ya warke domin yayi kyau sosai ya sha riga ja da blue din wando sai kamshin turare mai dadi yake gashi ya gyara sajensa da sumarsa sun kara fito da kyawunsa.

"Morning my queen, Xarah, my wife, my luvly one and only" ya fada yana murmushi,

"Morning" ta fada ta cigaba da aikinta,gas ta kunna ta dora mai ta zuba dankalin, lekawa jawad yaje yayi tsall mai ya fantsalo masa a hannu cikin sauri ya matsa yana yarfe hannunsa, matsowa tayi kusa dashi "mu gani, ka kone?"

  "Na kone mana, queen kalli kigani" hannun nashi ta kamo tana dubawa shi kuma yana duban rigarta wadda ta dameta kamar zata yage, kirjinta ya shafa da sauri ta matsa,

"Koma falo ka jirani"

"Queen tayaki fa zanyi kike korata"

"Nidai nace ka koma falo" juyawa yayi ya fita ya koma falon ya zauna yana jiranta, murmushi tayi taci gaba da aikinta har ta kammala ta harhado ta kawo falo ta shiryasu akan table.

  Bayan sun kammala break dinne yace ta shirya su tafi gidan yaya aadil, tashi tayi taje ta shiryo cikin wani leshi maroon ta yafo bakin mayafi da bakin takalmi ta dauki bakar jaka, tana tunanin ta yadda zata iya hada ido da yaya aadil yau,Allah sarki gashi duk kayan da take sawa kayan lefen da ya hada mata ne ashe da rabon ba shine zai ga kwalliyar ba.

A mota ta samu jawad suka tafi, yana ta yi mata hira a hanya har suka isa gidan aadil kamar wata marar gaskiya haka ta zama, jawad yana gaba tana biye dashi a baya, a babban falo suka tarar dasu Salima na zaune kusa dashi suna karanta magazine,yayi kyau yayi kiba abinsa gashi ya sake haske, caraf suka hada ido lokacin da ya dago domin amsa sallamar su, saurin sunkuyar da kanta tayi har suka karasa cikin falon kanta yana kasa, a kasan kujera ta zauna shikuma jawad ya hau kujera ya zauna,sannu da zuwa anty Salima ta fara yi musu wacce kallo daya zaka yi mata ka fahimci tana dauke da juna biyu domin alamu duk sun gama bayyana, a kunyace ta gaishe su amma bata bari sun hada ido da yaya aadil ba, sam ta kasa sakewa wata irin kunya taji tana ji.

  Basu fi minti 20 ba jawad yace ta tashi su tafi dan ya fahimci ta kasa sakewa nan suka yi musu sallama suka tafi gidan Ummi, nanma taga karamci domin ummi ta karbeta hannu bibbiyu anan ne suka dade dan har jawad ficewa yayi ya barta sai la'asar lis sannan ya dawo ya dauketa suka koma gida.

Suna shiga falo ta fada jikin jawad,

"Nagaji yimin tausa, amma bari na cire kayan nan nasha iska" riga da skirt din ta cire ta zauna daga ita sai underwear da bra, jikinta ya fara mammatsa mata tana lumshe idanu can taji ya canja salo dan haka tayi saurin rike hannunsa,

"Pls queen" ya fada idonsa a lumshe, zuruf ta tashi ta kwasa a guje tayi dakinta binta yayi tana kokarin rufo kofar ya hanata ya shiga, bathroom ta sake kwasa zata shige yayi saurin damkota ya dorata kan bed anan aka fara dambatawa har dai ta fahimci yau jawad da gaske yake dan haka ta kyaleshi ya shiga nuna mata zallar soyayya amma kuma acan kasan ranta tunani take ko zata iya bashi abinda yake so? Tunanin ta ne ya tsaya daidai lokacin da taji mararta ta yi wani irin murdawa, nan ta fara jin ciwo kamar zata mutu, kankame jawad tayi ta rirrikeshi tana numfarfashi,

"Wayyo zan mutu, wayyo Allah, jawad marata, wayyo marata" haka ta yi ta fada a gigice,

Da sauri ya katse abinda yake yi ya tallafota ya rungumeta

"Xarah menene?" Ya fada a rude,

"Marata jawad" ta fada tana cije lebenta, wata kara tasa sakamakon wani irin azababben ciwo da taji sai kuma ta fara bleeding jini guda guda ya fara fita daga jikinta, cikin tsoro gamida rudu jawad ya sake rungumeta,

"Pherty wannan jinin fa? Jinin meye wannan?" Bata iya bashi amsa ba sai hawaye data fara zubarwa, nan jawad ya sake rudewa yama rasa me zaiyi saboda har yanzu jinin ne yake fita bai daina ba, kwantarta yayi ya saka kayansa, yaje falo ya dauki wayarsa ya kira dr ansar, da sauri ya dawo wurinta ya dauko kayanta ya fara saka mata, ita kuwa pherty in banda kuka babu abinda take amma ba kukan ciwo take ba kukan kaddarar da take tare da ita take saboda tasan dole jawad ya sake aure nan gaba tunda ita ba zata iya biya mishi bukatarsa ba,yama za ace zai iya zama da ita a haka? Sai dai kawai ya kalleta amma babu wani abu da zai samu daga gareta.

Nan hankalin jawad ya sake tashi kololuwa, mintuna kadan sai ga dr ya iso nan jawad ya shiga yi masa bayanin abinda ya faru,

"To shi wannan jinin na mensuration ne ko me?" Dr ansar ya fada cikeda al'ajabi,

"No ba period bane dama ta taba samun problem ne ta bugu a mararta" jawad ya fada kamar me shirin yin kuka, nan dr ya fara kokarin bata taimakon gaggawa, bayan ya rurrubuta mata magunguna ya bawa jawad shawarar lallai suje asibiti suga likitan mata domin shi ba likitan mata bane, ita dai pherty tana kwance tana jinsu.

Bayan dr ya tafi ne jawad ya tashi da niyyar zuwa ya siyo mata magungunan, hannunsa ta riko,

"Ina zakaje? Ka zauna kar katafi" kai ya gyada mata,

"To bari na bawa mai gadi ya siyo miki maganin" hannunsa ta saki yaje ya dawo ya kwanta akusa da ita ya rungumeta shi kansa tunani yake wannan wacce irin kaddara ce? Ga mace har mace amma ace ba zata iya rayuwar aure ba, hakika wannan wata jarrabawa ce acikin rayuwar aurensu shida pherty.

  Jin ana kwankwasa kofar falon ya sashi sakinta yaje ya bude maigadin ne ya kawo maganin da aka aike shi ya siyo, karbowa yayi ya dawo ciki ya dauko mata ruwa ya tayar da ita zaune ya bata tasha maganin ya sake kwantar da ita, gumi ta fara hadawa duk da sanyin ac din dake ratsa dakin, babu shiri ya cire mata kayan dake jikinta ya barta haka, babu bata lokaci ta fara aikin bacci.




Ummi Shatu🏻
[5/23, 7:57 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑


Na
UMMI A'ISHA


79-80


~~~Ta jima tana baccin wahala kafin ta iya bude idonta lokacin har gefen marar tata ya kumbura kadan, juyi tayi ta kalli jawad wanda ke kwance a gefenta fuskarsa cikeda tausayinta gami da alhinin halin da suka tsinci kansu.

"Sannu queen, ya jikin naki" ya tambayeta cikin rada

"Da sauki, hada min ruwan zafi zanyi wanka" ta fada tana kwalla, girgiza mata kai yayi,

"Don't cry my queen,karki sawa kanki damuwa pls insha Allahu zaki samu lafiya"

  Hawayen fuskarta ta goge ta fara kokarin tashi zaune, jawad dinne ya taimaka mata ta zauna ya jawo mata towel ta daura ya shiga toilet ya hada mata ruwan zafi ya fito, dakyar ta iya tashi ta shiga toilet din saboda zugin ciwon da gefen marar ta yake yi mata.

Acikin toilet dinma ta dade tana kuka kafin tayi wankan, jin shiru shiru bata fito ba yasa jawad binta cikin toilet din nan ya sameta zaune sai faman kuka take, agabanta ya durkusa ya kamo hannuwanta ya rike ya fara yi mata magana a hankali,

"My dear menene abin kuka? Kowacce cuta tana da maganinta kar ki sawa ranki damuwa har wani ciwon ya kama min ke kinji? Oya tashi nayi miki wankan" mikar da ita yayi, shine yayi mata wankan yana yi yana yimata wasu yan wasanni da haka har yayi nasarar mantar da ita bacin ran da take ciki.

Acikin towel ya nadota tamkar yar jaririya yazo ya ajiyeta akan gado, mayuka ya debo zai shafa mata, nan ya shafeta da mai yayi mata kwalliya ita dai tana zaune tana kallonsa saboda yace ba zata kalli mudubi ba har sai ya gama, powder ya shafa mata ya shafa mata jan baki, wasu abubuwan ma bata san a inda yake shafa mata ba ko goshi ko kumatunta da haka har ya gama yi mata kwalliyar ya zabo mata kayan da zata saka, wata jar riga doguwa mai hannun shimi ya dauko mata, tun daga wurin cinya har kasa a yanke yake saboda haka ana ganin cinyarta guda daya gashi daga kirjin rigar anyi wata tattara kuma kirjin a bude yake dan haka ana iya hango albarkatun kirjinta, jan siririn mayafi ya dauko mata ya daura mata ya tsaya yana kallonta,

"Ya akayi?" Tafada tana kallonsa

"Kinyi kyau queen, taso ki gani" hannunta ya ja suka karasa gaban mirror, kallon kanta ta tsaya yi saboda yadda jawad ya rangada mata kwalliyar kai ka rantse wata shahararriyar mai kwalliyar amare ce tayi mata, abubuwan da bata taba saka su a fuskarta ba ma yau ya saka mata, rungume shi tayi tace,

"To sai muyi picx din tarihi ko dan wannan kwalliyar tayi kyau" hotuna suka shiga yi ita dashi tun suna dauka a daki har suka dawo falo suka ci gaba da dauka, kan kujera ya fada ta kuwa bishi tafada kan kirjinsa tana kallonsa kyatt ya dauka karbar wayar tayi ta kurawa hoton ido yayi kyau sosai duk cikin hotunan ma wannan na karshen yafi burgeta.

  Tana kwance a kan kirjinsa yana shafa kanta yana yi mata dadadan kalamai kasa kasa har magrib tayi sai a lokacin suka tashi dan gabatar da salla. Bayan sun idar da salla ta shiga kitchen, binta yayi ya tayata suka dafa indomie da kwai suka fito, a baki ya rinka bata har ta koshi.

  Koda lokacin bacci yayi dakinta yazo bayan yayi shirin bacci ya rungumeta tsam ajikinsa har bacci ya daukeshi amma ita pherty duniyar tunani ta shiga har bacci barawo yayi nasarar dauketa.

  Tunda wannan abun ya faru jawad bai sake kokarin kulata ba amma yana bata dukkan kulawar data dace domin kullum akoda wanne lokaci yana manne da ita yana yi mata soyayyarshi mai tsada, ko girki zata yi sai ya bita ya tayata, suna aiki suna taba soyayya. Ta dan samu sauki babu laifi sai dai kumburin da mararta keyi yanzu shine tashin hankalinsu, gefen mararta ya kumbura kamar an hura tattali amma kuma bleeding din ya tsaya.

  Tana kwance agefen gadonta daga ita sai wata yar ficiciyar riga fara mai shara shara da gajeren wando baki jawad ya shigo, a kusa da ita ya kwanta ya dauketa ya dorata a samansa ya fara yi mata cakulkuli nan ta shiga zillewa tana dariya, shima dariyar yake,

"Dan Allah ka daina" ta fada tana dariya,

"To nadaina queen, kin san wani abu? Ya kamata muje asibiti kiga Ganny doctor akan matsalar nan taki" ya kare maganar yana shafa kanta,

"Jawad ba sai munje ba saboda tun lokacin da abun ya faru doctor din yace ba zan sake daukar ciki ba kuma dakyar idan zan iya rayuwar aure" wasu hawaye suka silalo daga idonta lokacin data gama maganar,

"Kar ki sake fadin haka queen domin babu wanda yasan gobe in banda Allah"

"Kaga jawad kawai mubar maganar nan zancen zuwa asibiti ma bai taso ba ahakura kawai"

Kallonta yayi "kina nufin haka zamu zauna da wannan lalurar ba zamu nemi mafuta ba?"

Sauka tayi daga jikinsa "to wacce irin mafuta? Ai mai faruwa ta faru sai dai hakuri"

"Dole muje asibiti pherty saboda fadar likita ai ba fadar Allah bace"

"Ehh amma ai aikinsa ne dan haka abinda ya fada dole ayi aiki dashi" ta fada cikin tsiwa,

"To yanzu me kike nufi? Zamu ci gaba da zama a haka ne?" Ya fada a kule,

"Eh haka zamu zauna sai dai tunda kai ba zaka iya jurewa ba sai ka nemi solution" ta fada cikin bacin rai,

"Pherty, ke pherty wai meyasa ku mata kuke da karancin tunani ne?"

"Malam nidai inada tunani na, kawai ka fito fili ka cemin kai dai ba zaka iya zama dani ba tare da kana samun biyan bukatar ka ba, tunda yanzu ni ba mace bace shiyasa ba zaka zauna haka ba, dole ka nemo mai daukar dawainiyarka"

"Ta yaya da zan zauna ahaka? Ni dutse ne ko kuma ni ba mutum bane? Idanma kika yi tunanin zan iya zama a haka kin yaudari kanki, taya zan zauna kullum daga kiss sai hugging? Kinga ki maida hankalinki ki shirya muje muga likita"

"Eh ai sai yanzu na gano inda ka dosa, dadinta ma dai ansan ba haka nake ba tun asali kuma babu wurin likitan da zanje"

  Bai sake tanka mata ba ya tashi ya fice daga cikin dakin, yana fita ta fashe da kuka saboda dama wannan ranar take gudu ranar da jawad zai bukaci mace tunda ita ba zata iya yi masa komai ba. Tun daga wannan rana ta dauki fushi kamar yadda shima yaketa faman fushi, ganin zaman gidan yayi mata zafi ya sata tunanin komawa sch, a falo ta sameshi kwance kan kujera yasha kananan kaya kusan ita bata ma taba ganinshi da manyan kaya ba.

  "Ina son zan koma sch gobe sannan kuma provision dina ya kare" tana gama fadin haka ta juya ta koma dakinta ba tare da ta kalleshi ba, bin bayanta yayi da kallo yayi kwafa ya tashi ya fita, wani provision store yaje ya iyo mata siyayyar komai da komai na duk abinda zata bukata ya kawo ya jibge mata a falo yayi ficewarsa ya tafi gidan aadil bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha.

  Koda ta fito taga kayan barinsu tayi a wurin sai washe gari wurin karfe 11 ta shirya tasa mai gadi ya nemo mata mai keke napep ta kwashe kayan tayi tafiyarta sch lokacin ko tashi daga bacci ma jawad din bai yi ba sai tashi yayi yaga bata nan hakan ba karamin sake kular dashi yayi ba ya fuskanci yanzu yarinyar nan wata rashin kunya take ji da ita amma zai bata mamaki.

  Tunda pherty ta koma sch tayi watsi da tunanin jawad duk da cewa tasan hakan ba mai yiyuwa bane, yau ma kamar kullum tana kwance akan gadonta a dakinsu hannunta rike da waya tana kallon hotunan da suka yi ita da jawad ranar da yayi mata kwalliya suna tsaka da soyewa hotunan sukan sata nishadi duk lokacin da ta kallesu, murmushi kawai take yi ita kadai domin hotunan sun burgeta musamman ma wadanda suka dauka a falo, wani yana kissing din wuyanta, wani kuma bakinsa kan kumatunta amma wanda take kwance kan kirjinsa duk yafi burgeta,

"Baiwar Allah lafiyarki kuwa?" Sadiya ta fada tana yiwa A'isha signa,

"Tambaye ni dai" ta bata amsa tana sake kallon hoton, sai kuma ta tashi zaune ta ajiye wayar ta fita da sauri, shaf ta manta da lecture note dinta a room 1 da taje hira can dazu dan haka ta tafi daukowa da sauri.

  Tana fita sadiya ta dauki wayar ita da A'isha suka fara ganin hotunan,

"Kai wato yarinyar nan kawai sha'aninsu taje suka yi babu wata rashin lfy da jawad yayi" inji A'isha,

"Ai mu suka mayar garori amma luv dinsu kawai suka sha" Sadiya ta fada tana budo wani hoton, shigowar pherty ce ta katse musu hirar,

"Kut kuban wayata malamai, waye yasa ku kallar min sirrina nida mijina?" Hanata wayar suka yi suka gudu nan ta hakura ta kyalesu har sai da suka gama ganin picx din sannan suka dawo mata da wayar.

  Ranar tana zaune yaya aadil ya kirata yayi mata fada saboda jawad ya fada masa ya sata abu taki yi kuma sai faman fushi take yi dashi, nasiha yayi mata sosai sannan suka yi sallama aranar da daddare sai ga jawad din yazo wurinta.

"Shine zaka wani je ka hadani da yaya aadil ko?" Ta fada a shagwabance tana kallonsa,

"Eh ai naga kinfi jin maganarsa ne fiyeda tawa saboda har yanzu nasan shi zuciyarki take so"

Kallonsa tayi sai kuma tayi murmushi,

"Ni wlh ba sonsa nake ba kawai ina girmama irin halaccin da yayi min ne kamar yadda nake girmama irin son da zuciyata take yi maka"

Murmushi yayi yakai ma goshinta kiss, "to yanzu yaushe za muje asibiti? Koda yake nasamu wani likitan mata nayi masa bayanin matsalar ki to sai yake nuna min kawai gara muje kasar saudiyya sai aduba ki acan tunda abin yayi worst amma ya kika gani?"

  Cikin jikinshi ta shige domin tayi missing dinshi sosai,

"To amma abari nagama exams dina tunda kaga next week zan fara"

  "Ok to babu damuwa, i wish u all d best my queen" kwantar da kanta tayi acikin kirjinsa tana shakar daddadan kamshin da yake futarwa.

  Akwana atashi yau har pherty ta kammala exams dinta tanata shirin tafiya gida duk jinta take babu dadi saboda zasu rabu da mutanen nata sai bayan dogon hutu sannan zasu dawo sch, rungumesu tayi tana kuka suna kuka ta tafi gida. Tunda ta koma gida jawad ya fara yi musu shirin fita kasa mai tsarki, kwananta biyar da dawowa suka daga ko kumo bata je ba sai waya tayi ma su mamanta tace zasu tafi umara, haka hawy ma tayi mata wayar ta fada mata.

  Karfe 4 na yamma suka sauka a kasa mai tsarki a wani hotel mai suna ALAM TOWA acikin unguwar markaziya, aranar suka halacci asibiti suka ga likita, an dorata akan magani sannan zasu yi mata aiki, dan haka tunda suka zo kasar ta dage da ibada tana addu'ar Allah yasa ta samu lfy, cikin ikon Allah akayi aiki a sa'a kwananta biyu a asibiti aka sallameta da tulin magunguna. Daga nan yawo jawad yajata zuwa gidajen danginsu da sauran wurare, har sch din da yayi duk sai da ya kaita ta gaggani, yanayin kasar ya karbi jikin pherty nan tayi lukwikwi da ita tayi fes saboda in banda shakatawa babu abinda suke yi acikin wannan kasa duk da cewar suna ibada sosai.

  Yau satinsu biyu da zuwa kuma ahalin yanzu tana jin jikinta normal babu wani ciwo,toilet ta shiga tayi wanka da sabulu mai kamshi ta fito, bayan tagama kwalliya ne tana tsaka da fesa turare jawad ya shigo, ta bayanta yaje ya rungumeta,ya fara shafata,

"Jawad ya haka?" Ta fada a sabule,

"Queen gwaji zanyi, so nake naga ko kin samu lfy" kokarin kwacewa ta fara amma ta kasa, cak ya dauketa bai direta ako ina ba sai akan gadonsu.

  Ranar dai pherty tasha wuya a hannun jawad saboda ji tayi kamar wannan ne karon farko harma yaso yafi karon farkon, shi kuwa jawad kasa banbance waccan ranar da wannan yayi domin queen dinsa dai ta juye ta zama cikakkiyar budurwa tun anan ya gane shi dinne dai yanzun ma dama kuma baya zargin gwanar tasa.

Sai da komai ya lafa sannan ya shiga rarrashinta yana yi mata wasu kalamai wanda nidai ummi A'isha bana jin ko me yake fada, ajikinsa ya dorata ya kwantar da ita nan ta fara baccin gajiya.

Sai da tayi baccinta ta more sannan ta tashi duk jikinta ciwo yake mata amma mararta lfy lau ko alamun ciwo babu, lokacin data farka jawad baya cikin dakin dan haka ta lallaba ta shiga toilet tayi wanka da zazzafan ruwa ta fito, mai kawai ta shafa tasa turare ta zira wata yar guntuwar riga iya gwiwa tayi kwanciyarta, jawad ya shigo hannunsa dauke da wata babbar leda mai kyalkyali,

"My queen kin tashi?" Tana ganinsa ta fashe da kukan shagwaba, da sauri ya karaso inda take ya dauketa ya goyata yayi falo da ita yana jijjigata tareda yi mata albishir din kayan sawar da ya siyo mata harda sarkar gold da awarwaro da zobuna, a bayansa tayi bacci sai da ya daina jin motsinta sannan yaje ya kwantar ta. Koda ta tashi wani rikicin ta sa masa nan ya shirya itama ta shirya cikin bakar doguwar riga ta nade kanta da jan gyale suka fita yawon zaga gari, ko ina jama'a ce anata hada hadar kasuwanci kai ba zaka ce dare yayi ba, sai wurin karfe 2 nadare sannan suka koma masaukinsu.

  Hakika sunyi rayuwa mai dadi acikin wannan kasa sunsha soyayya sosai sannan sun jiyar da junansu farin ciki, satinsu biyar acan suka fara shirin dawowa Nigeria.




Ummi Shatu
[5/29, 1:56 PM] Ummi A'isha🏻: [5/27, 9:32 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

  Na
UMMI A'ISHA

81

~~~ Satinsu biyar a kasa mai tsarki sannan suka fara shirye shiryen dawowa kasar mu Nigeria bayan sun jibgo tsaraba mai tarin yawa.

  Ranar talata suka baro kasar saudiya suka nufo Nigeria, kwanciya pherty tayi ajikin jawad ta rungumeshi acikin jirgi tana tuna daddadar rayuwar da suka yi ita dashi akasar saudiyya amma samun lafiyarta yafi mata komai dadi.

  Karfe 4 na yamma suka sauka acikin garin gombe yaya aadil ne yaje dauko su sai faman fara'a da murmushi yake hakan yasa pherty tsarguwa gashi ko hada ido dashi ta kasa domin a halin yanzu kunyarsa take ji.

  Gidansu ya kaisu ya ajiyesu sannan yayi musu sallama ya tafi, gidan tsaf tsaf an gyara musu ko ina kamar suna nan, wanka suka yi sukai salla suka ci abinci jawad ya fita ya tafi gidan Ummi ita kuma pherty ta kwanta domin hutawa.

  Kwanansu biyu da dawowa suka je gidan ummi suka wuni acan da daddare suka biya ta gidan yaya aadil suka kai musu tsarabarsu kasa kasa pherty take kallon aadil da salima wadda cikinta ya dan fito yayi das ajikinta, hannunta salima ta kama zuwa cikin bedroom dinta suka zauna, ta debo mata kayayyaki na amare ta bata ita dai pherty duk kunya ta rufeta, sun dan jima sosai sannan jawad yace ta fito su tafi.

Tun a hanya yake damunta da tambayoyi wai me ta samo, kanta ta dauke taki bashi amsa,

"Queen tambayar ki fa nake, menene wannan?"

"Maganin ciwon cikine anty salima ta bani"

Juyowa yayi ya kalleta "kamar kuwa kin san nima cikina ciwo yake ,muje gida sai ki sammin nasha"

Shiru tayi bata bashi amsa ba har suka je gida, dakinta ta wuce ta zuba kayan acikin drawer din mirror dinta ta wuce bathroom tayi wanka, lokacin da ta fito ta iske jawad zaune kan dan stool din mirror da jarkar tsumin da anty salima ta bata dazu, da sauri taje ta zata kwace saboda har yasha rabi,

"Haba jawad danme zaka dauka min kasan ko meye?"

  Idanuwansa ya lumshe ya budesu a hankali, "menene? Naji da zaki kuma da kamshi"

"Kai kasani wayasa ka shamin?"

  Gaban mudubin ta karasa ta karbe robar ta rufe ta ajiye ta tsaya ta fara kokarin shiryawa, hannunta ya riko,

"Ni ki bari haka ba sai kinyi kwalliya ba haka kinfi kyau natural beauty" harararsa tayi ba tare da tayi magana ba, tashi yayi ya rungumeta ta baya, ta cikin mudubi ta kalleshi idonshi yayi dan ja kamar me jin bacci,

"Yau nashiga uku,da ya muka kare ma balle yanzu kasha wani abu" kokarin kunce towel din jikinta ya fara tayi saurin dakatar dashi,

"Meye haka" malam nifa agajiye nake ka rabuda ni in huta ka gane?"

Idanuwansa a lumshe ya sake matseta ajikinsa,

"Kiyi hakuri pherty na, kinga fa nayi hakuri sosai tunda a saudiyya ma sau daya kika barni"

  Abubuwan da ya fara yi matane suka hanata magana dolenta ta rabuda shi ta bada kai bori ya hau.

Washe gari suka shirya domin zuwa kumo wannan shine karon farko da pherty zataje gida tun bayan bikinta wurin wata hudu kenan, duk zumudi da doki ya cika mata rai saboda har ta kasa boyewa ko jawad sai da ya gane murnar da take ciki.

"Bafa kwana zakiyi ba" ya fada da niyyar zolayarta,

"Wlhi kwana biyu zanyi dan har kayana ma na debo"

"Ba kun koma sch ba?"
"Mun koma amma ni bazan koma ba sai upper week,yaushe rabona dasu mama ai dole ma na kwana"

Murmushi yayi ba tare da yace komai ba, suna shiga cikin garin kumo kasuwa jawad ya wuce dasu, a sabuwar plaza dinnan tasu ya tsaya wadda yanzu an budeta shaguna shake da kaya babu abinda ba a sayarwa,fita yayi ya barta cikin motar yaje ya debo kaya Wanda ita dai bata san ko na menene ba kawai dai taji an bude but ana zuba kayan, bayan an gama loda kayanne ya koma cikin motar suka nufi cikin gari.

  Lokacin da suka shiga unguwar su pherty pherty ji take kamar tayi tsalle ta fada gidan ai kuwa yana tsayawa ta bude kofa tayi cikin gida, tana shiga ta fara kwallawa mamanta kira,

"Mama, mama, mama kina ina?"

Da sauri maman ta fito daga cikin daki tana cewa, "wa nake ji haka? Yan tafiya har an iso mana?"

Tsalle pherty tayi ta dane jikin mamanta tana dariya daidai lokacin jawad ya shigo ya harareta, itama harararsa tayi ta saki mama ta wuce ciki. Har cikin falo mama ta shigar jawad tayi masa shimfida ya zauna ita kuwa pherty ana can cikin daki sai bincike take yiwa mama,

"Mama ina abba na?" Tafada tana daga can cikin daki,

"Yafita kasuwa sai anjima zaki ganshi ya dawo" mama ta fada lokacin da take ajiyewa jawad ruwa da lemo a kusa dashi, cikin hausarsa dai wacce bata gama isarshi ba ya samu suka gaisa da mama.

Ya dan jima agidan kafin ya yiwa mama sallama ya fita,

"Sai ki fito ki rakashi ai ja'ira kawai" mama ta fada lokacin da ta shiga dakin da pherty take ciki tana bincike,

"To mama bari naje" mayafinta ta dauka tayi hanyar kofar gida ita kuma mama tana ta fadan binciken da pherty take yi.

Lokacin data fita ya samu yara sun fara debo kayan suna kokarin shigar dasu cikin gidan, tsayawa tayi tana kallonsa kamar yadda shima ya tsaya jikin motarsa ya zuba mata manyan fararen idanuwansa, sai da yaran suka gama shigar da kayan ya sallamesu suka tafi sannan ya dubeta ta wani rike kugu tana kallonsa,

"Zaki cinyeni ne ko yaya?" Ya fada da zummar tsokanarta,

"Babu mamaki" ta fada tana dubansa,Murmushi yayi ya nufota, ciki da koma ta buya a bayan kofar zauren gidan yana shiga ya ganta, binta jikin bango yayi ya matseta yasa dan yatsansa a saman idonta,

"Yau bazan iya bacci ba, yau zan kasa bacci queen"

Bata yi magana ba taji lips dinsa kan nata, ahankali ya fara tsotar bakinta har na tsawon wani lokaci,ita kanta tasan zata yi missing din shi, hannunta yaja zuwa inda motarsa take,

Kashe mata ido yayi, sunkuyar da kanta tayi saboda duk ya saukar mata da kasala, murmushi yayi yace,

"To ni kinga tafiyata yau da daddare sai ki nemi abokin bacci" motarsa ya bude ya shiga ya fara daga mata hannu ya tafi, murmushi tayi ta koma cikin gida tana tunanin hali irin na jawad komai nashi simple ne.

  Tunda ta koma ta saka mama agaba sunata hira sai wurin la'asar sannan ta samu ta leka gidansu hawy cikin sa'a kuwa ta samu tana nan itama tazo weekend, kallonta hawy tayi cikeda tsokana,

"Kawata cikin naki wata nawa ne?"

"Ke zaki fada tunda ke kika san ina dashi" dariya hawy tayi "kema kin san kina dashi kawai fada min ne ba zaki yiba" hirarsu suka sha har lokacin sallar magrib tayi sannan suka rankaya suka koma gidansu pherty.

Suna zuwa pherty ta cicciro mata tsarabar da ta iyo mata ta takalmi da yar jaka sai atamfa mai dan karen kyau, har dare suna tare da hawy, sai lokacin da fita rakata ne sannan jawad ya kirata a waya, wata kunya taji saboda sam ta manta bata kirashi taji yaya ya sauka ba.




Ummi Shatu🏻
[6/2, 10:11 AM] Ummi A'isha🏻: [5/31, 9:07 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

Na
UMMI A'ISHA

82

~~~ Kara wayar tayi ajikin kunnenta ta soma yin magana a hankali,

"Jawad ya kaje gida?"

"Bayan kin manta dani" ya fada a shagwabance,

"Kayi hakuri yanzu nake son kiranka dama"

"Haka dai kikace, yau kin manta dani saboda kin samu su mama ko?"

Girgiza kai tayi kamar yana kallonta,

"A'a kana raina kaima ban manta da kai ba"

Sun dan taba hira kadan sannan suka yi sallama ta kashe wayar, ta karasa raka hawy,

"Um soyayya, yanzu kina sonshi kenan?" Inji Hawy,

"Da ance miki bana sonshi ne?" Pherty ta fada tana hararar hawy,

"Ato idan ke kin manta to ni ban manta ba" hawy tafada tana murmushi,

"Kinga malama sai da safe wanka nake son zuwa inyi yanzu yanzu" tana fadin haka ta juya ta nufi gida tana yiwa hawy dariya.

  Wanka tayi bayan ta koma gida, shiryawa tayi ta dawo falo wurinsu mama nan suka bude sabon babin hira har karfe 10 tayi sai a lokacin kowa ya tashi ya nufi makwancinsa, kan gadon mama taje ta dale tana fadin,

"Mama yaushe rabona da hawa gadonki? Yau akai zan kwana"

"Kema ai kin samu naki gadon ja'ira" mama ta fada daidai lokacin da take fita daga cikin dakin, murmushi pherty tayi ta lumshe idonta.

  Tunda pherty taje gida kullum suna tareda hawy suna hira, jawad kuwa kyaleta yayi har sai da tayi kwana biyar sannan yazo ya dauketa suka tafi bayan su mama sun hada musu goma ta arziki.

  Dawowarsu gida sunyi rayuwa mai dadi kuma jawad ya nuna mata yayi missing dinta over, kwananta 6 ya hado mata provision ta koma sch bayan su Sadiya sunce mata suma sun koma, tsarabarsu ta saudiyya ta fiddo musu ta basu kowaccensu riga da wando na pakistan da takalmi flat mai tsada ta siyo musu, sunyi murna mutuka tareda addu'ar Allah yasa sun kusa shan suna ai kuwa kamar sun fada a bakin "yan amin domin ko sati daya ba ayi ba pherty tafara jin wani irin yanayi a tattare da ita.

  Babu rashin lfy babu amai babu komai sai dai tana jin tashin zuciya ga yawu da yake taruwa a bakinta, tana zaune agefen gadonta da zani daurin kirji tana tsifar kai, sadiya kuma tana rubutu akan gadonta itama yayinda A'isha take kwalliya wani man shafawa A'isha ta ciro da niyyar shafawa tashi pherty tayi ta fita waje taje ta zubar da yawun bakinta ta dawo gefen gadonta ta zauna,

"A'isha man nan naki tayar min da zuciya yake wlhi" pherty tafada tana yamutsa fuska,

"Ke kuma naki cikin haka yake?" Sadiya tafada tana dariya,

"Ni ba cikine dani ba kawai son ganin man nata ne banayi" pherty ta mayar mata da amsa,

"To idanma cikin ne menene? Dama ai tunda akayi aure ai an san za ayi haihuwa" A'isha tafada tana dariya, tsaki pherty tayi,

"Ku kuka sani dai"

Tashi tayi ta dauki cumb da kibiyarta ta fice tabar dakin ta nufi wani dakin ba ita ta dawo ba sai wurin bayan awa hudu, tana shiga ta samu sun kunna risho sun dora musu abinci,ji tayi zuciyarta ta tashi sakamakon warin rishon da taji ta shaka,

"Dan Allah ku rinka kunna rishon nan awaje" kallonta suka yi,

"Saboda?" A'isha ta tambayeta,

"Saboda bana son warin risho"

Dariya sadiya tayi harda kwalla sannan tace "sai ance kinada ciki kice ke bakida ciki to meye warin risho? Ba wani wari da rishon nan keyi kece kike ji"

"Sai kiyi kuma" pherty ta fada tareda saka kayanta ta fita ta nufi captaria domin samowa cikinta abinda zata saka masa domin yanzu bata sha'awar abinci totally, abinci ta gani da kayan ciye ciye kala kala lokacin da taje captaria amma duk basu yi mata ba sai ma tashin zuciya da take ji, a wurin wata mata mai siyar da abinci ta hango awara acikin farin bokiti, awarar taje ta siyo ta dari biyu ta sai coke mai sanyi ta koma hostel.

A inda ta tafi ta barsu ta dawo ta samesu suna zaune suna cin abinci, kan gadonta taje ta zauna ta kalli abincin da suke ci, taliya da wake jallop, idonta ta dauke saboda yanzu duk abubuwan da take so da ta tsanesu,

"Zo kici abinci ga naki nan a flask" Sadiya ta fada,

"Ba zan ciba ku cinye" tafada cikin sanyin murya,

"Meyasa?" A'isha ta tambayeta,

"Awara zanci gata na siyo"

  "Ashe zamuci awara yau" inji Sadiya

"Dai dai zan san muku wlhi wannan shine abincina har dare" ta fada tareda mika musu awarar guda biyu, yaji ta dauko ta fara dandana tana cin awarar har ta ci rabi sannan ta daure sauran ta ajiye ta dauki coke ta kora ta sauka kasa ta zauna tana jiran Sadiya tayi mata kitso, koda aka zo kitson ma wai ba za asa man kitso ba bata son kamshin man haka akayi kitson suna yi suna fada da sadiya har suka gama.


Yau rabonta da jawad sati uku kenan saboda tun dawowarta sau 1 yazo mata hira shiyasa ta shirya tafiya weekend acikin wannan satin, tana zaune tayi zugum tana tunanin abin yi saboda kwadon kanzo take son ci yau domin yanzu ta tsani awarar da ta zama abincinta da, tun ranar da tayi aman awarar taji ta fita daga cikin ranta,

"Pherty me zan dafa mana?" A'isha ta tambayeta lokacin da take kokarin fitar da rishon da zatayi girkin waje,

"A'isha wallahi kanzo nake son ci, nidai jawad ya hadani da lalura" takarasa maganar acikin zuciyarta,

"Kanzo?" Sadiya ta fada cikin mamaki,

"Yanzu a ina za asamu kanzo? Indai ba son wahalar da kai ba kin san dai duk hostel dinnan ba za asamu kanzo ba"  A'isha ta bata amsa,

Kallonsu tayi daya bayan daya kawai sai ganinta suka yi ta fara hawaye,

"Yi hakuri zamu samo miki, ai dole mu samowa dan baba kanzo" Sadiya ta fada tana dariya tareda tashi ta fita, itama A'isha fitar tayi suka tafi yawon neman kanzo duk kuwa da cewar sun san abune mai wahala samun kanzo acikin hostel.

  Ita kam pherty suna fita ta shafa cikinta tana goge kwallar idonta, "yanzu jawad shi babu abinda ya dameshi yana can yana zamansa lfy ni kuma nan ya barni da laulayi" haka ta fada acikin ranta, tana nan zaune suka dawo basu samo kanzon ba nanfa taji hankalinta ya tashi wani kukan tafara kokarin yi amma shigowar Ummi Hambali yar department dinsu yasa ta hadiye kukan,

"Pherty ga wainar fulawa na kawo miki" ummin tafada tana mika mata wani flask karba tayi fuskarta dauke da murmushi,

"Nagode ummi kamar kuwa kin san yau babu abinda naci" da sauri ta dauko yaji ta fara ci ko sadiya da A'isha bata barwa ba sai da taji tayi dam sannan hankalinta ya dawo jikinta.

  Harararta Sadiya tayi "malama ki kira mijinki ya kawo miki kanzo saboda kar kizo kina tashinmu cikin dare kina cewa ke kanzo kike so"

Dariya A'isha ta saka "wlhi kar kisa yau naki kwanan dakin nan"

Murmushi pherty tayi "idan kunyi hakuri ma gobe zan tafi gidana wurin mijina"

"Dakyau dan Allah idan kinje kar ki dawo sai kin samo kanzon" Sadiya ta mayar mata da amsa, murmushi kawai tayi ta dauki wayarta ta soma kiran mamanta suna gaisawa ta fara yi mata zancen kanzo take so akawo mata,

"Kanzo kuma pherty?"

"Eh mama dan Allah ki kawo min dama kinga fa baki taba zuwa gidana ba mama, dan Allah kizo" ta fada cikin shagwaba

"To shikenan bari mahaifinki yazo zan sanar masa idan ya yarda zanzo ranar asabar idan kuma bai yarda ba to zan taso hawwa kawarki ta kawo miki"

"Mama dan Allah Ku taho tare dan Allah"

"To shikenan phertyma sai ranar asabar din"

Kashe wayar tayi tana murna nan ta tsiri shirin tafiya gida. Washe gari da yamma kuwa jawad yazo ya dauketa, sai kallonshi take cikin burgewa komanshi tsaf tsaf amma ita ya hadata da aiki bata da aiki sai tara yawu ta zubar, shi kam jawad bai ma san tana da cikin ba.

Suna zuwa gida ta fita daga motar taje ta zubar da yawun bakinta,

"Jawad murhun karfe da itace zaka siyo min kasa min acan baya dan bazan iya girki a gas ba" ta fada tana yatsina fuska, hannunta ya kama suka shiga cikin falo ya zaunar da ita akan cinyarsa, zumbur ta tashi saboda kamshin turarensa da ta shaka nan taji cikinta ya soma juyawa zuciyarta ta fara tashi.



Ummi A'isha🏻
[6/3, 7:27 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑

    Na
UMMI A'ISHA

83

~~~ Zumbur ta tashi saboda kamshin turarensa da ta shaka nan taji cikinta ya soma juyawa zuciyarta tafara tashi, yawune ya cika mata baki da sauri ta shiga dakinta nan dinma babu dadi domin kamshin da dakin yake yi shima baiyi mata ba, toilet ta shiga ta zubar da yawun bakinta ta koma falo wurin jawad,

"Queen wai meke faruwa ne?" Ya tambayeta

"A inafa?" Itama ta tambayeshi

"To naji kince na siyo miki murhu, me zai hana ki rinka girkin a electric stove tunda kince baki son yin girki a gas"

Zama tayi nesa dashi ta yatsina fuska,

"Nifa gaba daya warin girkin ma da warin rishonne bana so har warin gas din duk bana so murhu nake son ka samo min da fire wood"

"Angama ranki ya dade" mikewa yayi ya fita dan siyo mata murhun, tashi itama tayi ta shiga dakinta tana tottoshe hanci nan ta tattara kayan da zata bukata ta koma daya dakin kuma cikin sa'a sai taji nan din babu kamshin da bata so din.

Kamar yadda tace haka jawad ya siyo mata murhu guda biyu da itace ya kawo mata, acan bayan kitchen dinta ta ajiye murhun ta kunna wuta ta dora abinci, tuwon shinkafa miyar wake da busasshen kifi tayi, lokacin data gama jawad yana kishingide a falo,gabansa ta kawo abincin ta jere tashiga dakinta taje tayi wanka ko mai bata shafa ba saboda shi kansa man tayar mata da zuciya yake, yar doguwar riga ta shan iska ta zira tafito falo inda jawad yake zaune yana cin abinci.

  Dan gutsiren tuwo tasa a plate ta zuba yar miya ta fara ci, sam bata jin dadin tuwon kawai ci take domin rabonta da abinci har ta manta shiyasa duk ta dashe sai uban fari kauu da tayi, kallon jawad tayi sai zira lauma yake kamar zai hadiye kwanon, tana kallonsa ya cinye ya sake karawa ganin haka sai kawai ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya kalleta tareda matsowa kusa da ita,

"Queen menene?"

"Jawad bana jin dadin abinci gashi bakina babu dadi, komai naci bana jin dadinsa sam yanzu bakina babu taste" ta fada tana share hawayen idonta,

"Am sorry dear, tun yaushe?"

"Tunda na koma sch fa, wlhi rabona da abinci har namanta"

Hannunta ya kama ya rike cikin nasa fuskarsa cikeda tausayinta,

"Sorry queen, ko na kaiki kiga dr?"

Girgiza kai tayi

"Why?"

"Nidai basai naje asibiti ba" tafada cikin shagwaba

"Ayya sorry, to na kira miki dr ansar?" Nanma kai ta girgiza, hadata yayi da jikinsa yaci gaba da bata abincin a baki amma dakyar ta yarda ta ci rabin wanda ta zuba, "my pherty sarkin daru" yafada tareda jan hancinta.

Daren ranar kuwa bata yarda ta hada daki da jawad ba saboda wai bata son kamshin turaren da yake yi, juyin duniyar nan yayi taki yarda ya kwanar mata adaki yayi rarrashin har yagaji yayi fushi ya fita daga dakin.

Washe gari da safe kuwa kowa harkar gabansa yake ita fushi jawad fushi, shi jawad fushin da yake na ta hanashi kanta ne alhalin rabonshi da ita anfi sati uku, ita kuma pherty nata fushin na tana fama da lalura ne gashi kuma jawad bai nuna tausayinsa akanta bane,

Wanka tayi ta tsuke cikin riga blue body hug mai kyan gaske an rubuta IT'S YOUR TIME! Ajiki, da bakin wando mai laushi amma kuma tied ne, bakar hula tasa ta fita baya taje ta soya dankali da kwai tayi yar sos tana yi tana zuwa zubar da yawu da haka har ta gama ta hado kayan ta kawo masa kan dining sannan ta koma ta juyo ruwan zafin data dafa ta kawo masa, yana kallonta babu abinda taci sai aikin zuwa zubar da yawu minti kadan sai ta tashi haka ta kwanta akan doguwar kujera, ganin haka ya sashi sassauto da nashi fushin yazo ya sameta,

"Xarah me kike son ci naje na siyo miki?"

Bude idonta tayi ta kalleshi,

"Jawad babu abinda zan iya ci sai abu me k'uli k'uli"

"Zaki ci indai mai k'uli k'uli ne?"

Kai ta daga alamun ehh, key din motarshi ya dauka ya fita, wayarta ta dauka ta kira su A'isha tana fada musu to yanzu gashi nan mijinta ya tafi samo mata abinda take so tunda su basa nemo mata.

Kasuwa jawad ya shiga nan ya fara neman abinda zai siyo mata, zogale da kuli kuli ya siyo mata sannan yaga gurasa da kuli kuli nanma ya siyo daf da zai fita daga kasuwar yaga agwaluma itama ya tsaya ya siyo.

Lokacin da ya koma tana kwance inda ya barta tana bacci dan haka bai tasheta ba ya ajiye mata kayan ya fita ya nufi gidan ummi, bai dade da fita ba ta tashi, ai tana ganin kayan da ya siyo mata taji yawunta ya tsinke nan ta sauka ta zauna a kasa ta dauki zogalen da guraza ta fara zurawa, ita kuwa agwalumar da ya siyo mata koda yaushe tana tareda ita tana sha.

Ranar asabar da wurwuri ta tashi ta fara shiryawa su mama delicious, fried rice tayi musu mai dadin gaske ta soya musu kaji sannan tayi musu kunun shinkafa duk bata jin kasala yau saboda dokin zuwansu mama, bayan ta gama shirya komai ne taje ta tsalo wanka tasa wata koriyar atamfa dinkin riga da skirt mai tattara rigar ma tasha tattara, bata yi kwalliya ba saboda ko mai bata shafa ba, falo ta fito ta duba agogo lokacin karfe 11 da minti 15,

"Oh nikam mama anya zasu zo?" Ta tambayi kanta, tana nan zaune har 11:30 duk ta kosa da zaman jiran da take, kamar daga sama taji shigowar mota gidan da saurinta taje ta leka window, maman hawy ta hango da mamanta da kuma hawyn, da sauri ta nufi kofa taje ta taro su,dakinta ta kaisu bakinta yaki rufuwa sai murna take, bayan ta gabatar musu da kayan saukar da tayi musu ne suka gaggaisa sannan ta jawo hawy suka koma daya dakin.

"Phertyn mama kinyi fari gashi kin dan rame" Hawy tafada cikeda tausayi akan fuskarta,

"Um hawy ai dole na rame saboda bana cin abinci kwata kwata"

"To ai ga kanzon da kike so can an taho miki dashi"

Tashi pherty tayi taje ta dauki kanzon cikin leda viva ga kuli kuli dakakke, kitchen takai kayan ta debi wani acikin kwano ta jika tun anan taji yawunta ya guda saboda yanda kanzon yake fari tas daga gani na masara ne da shinkafa a hade, kyakkyawan hadi tayi masa tasa man gyada ta yanka kayan miya ta dauki maggi ta nufi wurin hawy,kallonta hawy tayi tana dan murmushi,

"Allah ya bada lfy amma agaskiya ki rinka cin abinci pherty"

Yamutsa fuska pherty tayi "wlh ba laifina bane, bakina ne babu taste in banda bakin shayi babu abinda nake iya sha"

"To Allah ya rabaku lfy dai"

"Amin" nan kuma suka shiga hirarsu har tsawon wani lokaci,suna nan zaune jawad ya leko bayan yaje sun gaisa dasu mama,

"Xarah kawo min abincina daki" zaraf hawy tayi tafara tsokanarsa "kaga ango" murmushi kawai yayi mata suka gaisa ya wuce,

Tiren abinci pherty ta dauka ta nufi dakin jawad kanta tsaye ta wuce cikin dakin ta dora abincin akan dan karamin stool din dake girke gefen gadonsa, ta bayanta taji yazo ya rungumeta,

"Sannu da kokari my queen"

"Yawwa sannu" tafada tana kokarin kwacewa, sakinta yayi ya bata hanya ta wuce ta koma wurin hawy, yinin ranar nan tayi shine cikin farin ciki sai yamma likis sannan su mama suka tafi nan kuma taji hankalinta ya tashi sosai, suna tafiya tasa kuka, rungumeta jawad yayi ya maida ita cikin dakinta.



Ummi Shatu🏻
[6/5, 7:43 PM] Ummi A'isha🏻: [6/2, 6:40 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑


  Na
UMMI A'ISHA

84-85

~~~ Dakyar jawad ya iya shawo kan pherty ta daina kukan tafiyar su mama, hannunta ya kama

"Oya taso ki rakani unguwa"

Babu musu ta saka after dress ta gyara fuskarta tabishi, wakar p square ya kunna musu lokacin da suka hau titi, gidan yaya aadil taga ya nufa, dan murmushi tayi mai kayatarwa ta kalleshi shima kallonta yayi yana murmushin har suka isa gidan.

  Hannunta rike cikin nashi har tsakiyar falon su yaya aadil, anty Salima na zaune tasaka katon cikinta gaba tana kallo shi kuma yaya aadil yana kitchen yana yi musu girki, pherty ji tayi sun burgeta domin dama can shi yaya aadil tasan mutumne shi mai saukin kai, zama tayi kusa da anty Salima yayinda shi kuma jawad yabi aadil kitchen.

  Dakyar yauma ta iya gaida yaya aadil amma tasaki jiki da Salima sosai suna hirarsu, har dare suka kai agidan kafin suka yi musu sallama suka tafi, ahanya saida jawad ya tsaya yayi musu siyayyar kayan makulashe gasasshen kifi dasu ice cream da chocolate sannan suka karasa gida, bayan pherty ta zauna ta tande kayan dadin da jawad ya kawo matane kuma ta mike da niyyar tafiya dakinta, kallonta jawad yayi da kalar tausayi amma ta maze tayi tafiyarta saboda ita yanzu wannan abun duk ya fita aranta.

  Washe gari ranar sunday ta shirya zata koma sch jawad dai sai cika yake yana batsewa ya murtuke fuska haka ya kaita ya dawo amma kawai kyaleta yayi saboda yasan idan ya nuna mata karfi dan karamin cikin dake jikinta yana iya zubewa, ko kallonta baiyi ba lokacin da ta fita daga motar ya figi motarsa yayi gaba.

Tun daga wannan ranar ya shareta ba waya ba zuwa haka ya rabu da ita, ita kam pherty hakan yafi mata domin yanzu tana bukatar hutu, satinta biyar cif a sch tsakaninta da jawad babu wani communicating ko ta ganshi online baya kulata itama haka, bayan sallar magrib ta fara kiran wayarsa saboda yau kwadayin kifin da ya taba siyo mata take,wayar tajima tana ringing sannan ya daga a hankali,

"Hello Xarah" ya fada kamar me yin rada,

"Jawad kana inane?"

"Naje hirane wurin kanwarki, lfy?"

Dam taji gabanta ya harba, "hira jawad? Wacce kanwar tawa? Wacece?" Ta jero masa wadannan tambayoyin ajere,

"Gata zaku gaisa"

Kafin tayi wata maganar sai jin muryar mace tayi tana yi mata sallama, tabbas wannan koma wacece tayi sa'a da samun zazzakar murya domin muryarta carkwai take nanfa kishi ya motsa pherty ko amsa sallamar da yarinyar tayi mata bata yiba balle ta tsaya amsa mata gaisuwar da take yi yanzu, kit ta kashe wayarta ta tura masa text massage kamar haka...

"Idan ka gama hira da budurwar taka ka siyo min gasasshen kifi ka kawo min"

Tura masa text din tayi duk ranta abace, lallai jawad wato ita yabarta da fama shikuma can yatafi neman aurensa ko? Haka tayi ta fada cikin zuciyarta,

Bayan sallar isha sai ga text dinsa wai ta fito ta karbi kifin gashi ya kawo mata, ranta a hade ta fice daga cikin dakin su dai su aisha da Sadiya basu san ko me ya bata mata rai ba, tana zuwa inda jawad yake ta tsaya daga waje ta rike kugu, lekowa yayi ya kalleta,

"Ki shigo mana queen"

Cikin bacin rai ta bude kofar motar ta shiga ta zauna fuskarta a daure,

"Malam bani sakon danni ba zama nazo yi ba, kuma wlhi gidanmu ni zan tafi inyaso kai sai ka zauna da amaryarka" tafada hawaye yana sauka akan kumatunta, light din cikin motar ya kunna ya tsura mata ido yanzu kam alamun masu ciki sun gama bayyana a tareda ita ta danyi kumatu fatarta tayi subul gashi cikin nata yadan fito kadan amma ba kowane zai gane ba,

"Queen koda nayi aure ke ta dabance a rayuwata, bazan taba mantawa dake ba, kece first lady"

Kallonsa tayi "dagaske auren zakayi kenan?"

Kai ya daga mata, "aure zanyi amma ba wai dan nadaina sonki ba, kuma kin san wani abu? Yarinyar da zan aura itama sunanta pherty"

Wayar hannunsa ta warce tafara kuka mai tsuma zuciya,

"Queen ba laifina bane laifinki ne saboda yanzu kin daina bani kulawa kinga kuwa dole na kara aure gudun kar nafada sabon Allah"

Ledar kifinta ta dauka tafice daga motar ta tafi tana kuka tana ji jawad na kiranta amma taki ko juyowa, kafin ta shiga hostel tayi kokarin tsayar da kukan ta shiga daki duk kifin ma jitake ta tsaneshi, agefen gado ta zauna ta bawa su Sadiya kifin ta fara binciken wayar jawad, ga text din budurwar tasa nan burjik, morning massages, good night, juma'at massages duk gasu nan amma shi bata ga nashi ba sai guda daya wanda ya tura mata shima thanks kawai ya rubuta, ta inda taji dadi number yarinyar yayi saving da pherty amma ita kuma tata ya rubuta my queen ko anan tasan yafi bata matsayi fiyeda waccan amma duk da haka dai haushinsa take ji, wayar tasa ta ajiye agefen pillow dinta ta dauki wayarta tafara chtn da hawy tana fada mata jawad yana neman aure, ido hawy ta zaro tareda fara bata hakuri, nan ta zayyanewa Hawy abubuwan da suka faffaru, shawara Hawy tabata sosai ta yanda zata sake siye zuciyar mijinta, taji dadin shawarwarin hawy kuma ta daura aniyar yin aiki dasu,

  Karar shigowar text cikin wayar jawad ne yasata yin sallama da hawy ta kashe wayarta, ta dauki wayar ta bude sakon nan taga daga budurwarsa ne ta rubuto masa "sleeping is a thing line btw life and death......" Da sauri ta goge text din ta lalubo picx din jawad tafara kallo daya bayan daya ita kanta tasan mijinta ya hadu kuma babu dama ne a fagen soyayya dan haka ya zama dole tayi duk iya iyarwata dan ganin ta mantar dashi kowacce mace acikin zuciyarsa face ita guda daya tilo.

Daren ranar sai bacci barawo ne yayi gaba da ita amma kasa bacci tayi, gari yana wayewa dama ya kama ranar friday duk su ukun basuda lectures, dan haka tace yau ranar aikinta ce,da A'isha tafara,

"A'isha yau ki kure basirarki ki tsara min jan lalle,Sadiya ke kuma kiyi min kitson da baki taba yiwa wata maceba agashinta"

Shewa suka saka su duka "tafiya zakiyi haka" A'isha ta tambayeta

"Babu inda zanje kawai zan yiwa mijina kwalliya ne"

Dariya Sadiya tasa tace "yau soyayyar jawad ta tashi kenan?"

"Kudai kawai kuzo kuyi min pls".

  Hadadden jan lalle A'isha ta tsattsarawa pherty wanda ya kama yayi dau yazama maroon, ita kuma Sadiya tayi mata kitso mai tsananin kyau wanda ni kaina ummi aisha sai da naso ace kainane, yamma tanayi ta shirya ta nufi gidanta.

  Lokacin da taje gidan jawad baya nan dan haka ta shiga tayi wanka ta sake sabuwar kwalliya cikin riga da skirt bakake marassa nauyi bata daura dankwali ba haka ta fito falo, tana zama jawad yana shigowa shima ya hade cikin kananan kaya, cikin mamaki yake kallonta kamar ba itaba tasha kwalliya cikinta ya dan fito kadan,

"Queen saukar yaushe, kai queen yau ke baturiya ce ko balarabiya" karasowa kusa da ita yayi ya fara kallon kunshin da aka rangada mata da kitson kanta,

"Queen dan Allah kar kiyi min irin na rannan, kar ki hanani kanki pls" yafada a sululuce,

Murmushi tayi ta kama hannunsa tana fara masa fararen idanuwanta tuni ya sunkuceta yayi bedroom dinsa da ita.

  Washe gari da safe bayan tasha kwalliya cikin shadda kalar shanshanbale riga da zani tafito tanata faman kamshi, kitchen ta shiga ta hada lafiyayyen breakfast ta zo ta shiryashi bisa dining table, kitchen ta koma tana duba guntun kanzonta da ta tafi tabari agidan amma bata gani ba, fitowa tayi fuskarta a turbune daidai lokacin shima jawad ya fito cikin kananan kaya wanda suka yi mutukar yi masa kyau shagwaba tafara yi masa harda buga kafafu a kasa,

"Wlhi ka nemomin kanzona duk inda ka kaimin"

"Kanzo queen" da sauri ya shiga kitchen din a cikin store ya samo ya kawo Mata yana tsokanarta.

  Bayan sun kammala breakfast yaya aadil ya iyo waya anty salima ta haihu yan biyu suna asibiti, nanfa pherty aka shiga murna suka garzaya sai asibiti, yara kyawawa masu tsananin kama da aadil farare tas dasu, nan asibiti ya cika da yan uwan salima dasu ummin jawad kafin daga bisani aka sallamesu suka rankaya suka koma gida gaba daya pherty ta dadume jariran ta rikesu bama kamar namijin har saida jawad ya tsokaneta yace itama ta kusa samun nata.

Tunda akayi haihuwar kullum suna gidan maijego har ranar suna inda yara sukaci suna jawad da phertyma, murna wurin pherty ba a magana nan sukaje supermarket suka jibgowa jarirai kaya kamar bada kudi suka siyo ba, satin anty salima biyu da haihuwa suka bar garin gombe suka nufi kasa mai tsarki.

  Irin kulawar da pherty ke bawa jawad a halin yanzu tasashi mantawa da kowacce mace sai ita kadai, cikinta ya girma ya shiga wata na takwas a lokacin bikin kawarta hawy ya taso ahaka ta kokarta taje kumo bikin, itace babbar kawar amarya haka ta zage tayi dukkanin abubuwan da babbar kawa keyi, kwanta biyar har saida takai hawy dakinta sannan ta jirgo nata ya nata ta dawo gida, damma yanzu bata zuwa sch hutu suke nan jawad yaci gaba da kulawa da ita da babynsu har ta shiga watan haihuwa nan ta haifo santalelen danta namiji lokacin yaran yaya aadil sun girma Xarah da jawad,murna wurin jawad kamar ya taka dan shege, nan aka shiga bidiri yayiwa maijego da baby kaya na garari, tun ana igobe suna Sadiya da A'isha da hawy suka zo, ranar suna yaro yaci suna aadil suna kiransa da junior, hhh nasan masu karatu har natuno muku da junior din kuluwa ko, washe garin suna su hawy da A'isha da Sadiya da Anty Salima ne suka yi mata aikin komai.

Aranar kowa ya baje aka barta da babynta sai wata yar tsohuwa da mamanta ta kawo mata mai suna iya ladi, nan suka shiga ganin gata ita da junior awurin jawad da dukkanin dangi har sukayi arba'in lokacin ansa date din bikin Sadiya da A'isha, shi kam jawad yanzu bashida damuwa dan haka ya cire kowacce mace cikin ransa sai iya queen dinsa.

  Awatan may su pherty suka sha bikin Sadiya da A'isha kwaccensu an kaita gidanta anan cikin gombe, yanzu junior har yayi wayo domin watansa 11 yana gudunsa ko ina pherty kuwa sun kammala karatunsu.

  Yau tana kwance cikin kujera tasha wani lafiyayyen leshi orange colour hannunta da kafarta kuma sunsha jan lalle ta gyara gashin kanta yayi yalo yalo ta kafa dauri tana waya da mama jawad ya shigo hannunsa rikeda junior wanda yake mutukar kama da jawad yana sanye cikin blue din riga da jan wando kafarsa sanye da combos fari yana yi mata albishir da cewar anty salima tasake haihuwa, da sauri ta ajiye wayar tana murmushi,

"Allah ya raya wancan karon sunyi min takwara nida mijina yanzu kuma kila su Ummi zasu yiwa"

"Kece zakiyiwa Ummi takwara" jawad ya fada yana kallonta rai ta bata

"A'a ni salim dina zan yiwa takwara tsohon saurayina" tafada cikeda zolaya

  Hancinta ya lakuce yace "that salim is not your true lover,i jawad am your true lover  here and for the hereafter"
Murmushi sukayi gaba dayansu shima junior da bai san abinda suke fada ba sai da ya dan dara Kadan, to nima dai Ummi Aisha murmushin nayi domin Allah ya nufeni da kammala wannan story.

   ALHAMDULILLAH!

Anan na kammala wannan labari ina fata ya fadakar, ya nishadantar kuma ya wa'azantar, inda nayi kuskure agafurceni kuma ina addu'a Allah ya yafe mana gaba dayanmu dani daku masu karatu.

Na sadaukar da wannan littafi gareku kawayena

PHERTYMA XARAH (d writer of Xarah)

SADIYA LAWAL BALA (d writer of Ballagaza)

MISS A'ISHA

HAWWA  SULAIMAN(HAWY)
Ina muku fatan alkairi akoda yaushe, Allah ya sanya albarka acikin rayuwarku.

Kin cancanci yabo babbar kawata, aminiya sahiba CWT KAUSAR LUV,mai bani shawarwari akoda yaushe, Allah ya barmu tare, ina alfahari dake kawata.

Jinjina gareki uwar dakina

HAWWA M JABO nagode da kulawarki agareni,Allah ya kara miki kaifin basira.

Kina raina
ADDA BENAXIR nagode miki much

Na yaba miki kawata KHADIJA SIDI Allah yabar zumunci.

Ban manta dakeba ta hannun damana
MIEMIE BEE

Fatan alkairi agareki
ANTY BEBEELO Allah ya raya mana iman.

Dominku ne kawayena

HUMAIRA (yarjejeniya)
A'ISHA (Maman Shakur)
FIDDAUSI SODANGI
A'ISHA (chuchun gaye)
A'ISHA DANSABO LEMU
UMMI HAMBALI

Na gaisheki
SA'ADATU DANTIYE babu shakka kinfi kowa son martabata


  Masoya nagode sosai hakika kun kaunaci martabata, ina kaunarku fiyeda yadda kuka kaunaceni, yan groups dina da sauran groups duk Allah yabar zumunci,wanda na ambaci sunansu dama wanda ban ambata ba duk kuna cikin raina idan hali yayi zaku jini cikin littafi nagaba, Allah yabar soyayya,masoyan Ummi A'isha aduk inda kuke Ummi A'isha tana sonku sosai, nagode

2 comments: