Saturday 7 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA..64

*RUWAN KASHE GOBARA..!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_

   _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


     _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

  *_64_*

http://aishaummi.blogspot.com
     

~~~ Daren ranar daga Lamido har ikhlas baccinsu ragagge ne domin doki,

Lamido kam juyi yake tayi ya kasa bacci har ihsan ta fahimta dan haka ta mike daga kwancen da take,

"On top wai meye haka?" Ta fadi ranta abace,

"Mefa?" Ya tambayeta yana basarwa,hakan da yayi ya sake kular da ita,

"Kazo ka kwanta sai wani juyi kake kana yin tsaki kamar dole nayi maka zuwa dakin nawa" ta fadi a kule,

"Yi hakuri my ihsan.. Na kasa yin baccinne shiyasa"

Hannunta ya kamo ya kwantar da ita akusa dashi ya fara lallashinta.

  Washe garin ranar tunda gari ya waye ikhlas tafara harhada dukkanin kayayyakinta wuri guda,

"Kidai bi ahankali kar zumudi yasa ki mance kayanki masu amfani" Farida tace da ikhlas cikin tsokana,

"Zumudin me? Kin jita" ikhlas ta mayar mata da amsa tana mai kokarin rufe akwatinta,

"Ahaf kuma dai" farida ta fada tana dariya,

Sallamar ni'ima ce ta katse musu hirar da sukeyi, nan dakin ya hargitse da hirarsu,kaya sosai ni'ima ta kawowa ikhlas ciki harda cake cikin karamin bokiti da meat pie da pepe chicken wanda tace shine gudun mowarta, wunin ranar abin gwanin ban sha'awa domin ikhlas tana cikeda farin ciki da nishadi.

Da misalin karfe 8:30 aka dunguma domin raka ikhlas dakin mijinta, mota dayace bash ya tuko yazo daukarsu kasancewar babu yan rakiyar da yawa domin daga Farida sai hajiya kakar ikhlas sai ni'ima matar barrister elmustapha,

Lokacin da suka isa gidan tsit kakeji baka jin motsin komai in banda karar na'urorin sanyaya daki wadanda suke amfani da wutar lantarki,

Suna daf da shiga falon gidanne suka yi kicibus da ihsan tareda fadila sun rako kawayensu wanda da alama tafiya zasuyi,

"Barkanku da zuwa" fadila da ihsan suka fada atare tare da yin gaba,

"Yawwa dai sannunmu" Farida ta fada tana rikeda sadiq a kafadarta wanda ke faman yin bacci,

Da addu'a a bakin ikhlas ta saka kafarta ta dama lokacin da zasu shiga falonta, har cikin dakinta suka shigar da ita ta zauna abakin gado sannan Farida ta karasa ta kwantar da sadiq agefe,

Zama sukayi sunata yaba irin kyawun da dakin nata yayi gashi komai ya tsaru iya tsaruwa,

"Ku tashi mu tafi ba dogon zama zamu yi ba" ni'ima tace dasu,

Hannun ni'ima ikhlas ta rike "haba anty ni'ima daga zuwa?"

"Kin jita kamar gaske, alla alla take yifa mu tafi" Farida tace tana dariya,

"Kuna inane? Ku fito mu tafi mana" suka jiyo muryar hajiya daga falo,

Mikewa suka yi suka fita suna cewa "to amarya Allah yabada zaman lafiya"

Shiru ikhlas tayi tafara bin dakin da kallo hakika komai yayi,tashi tayi ta leka falon wanda yasha kaya masu kyau kalar blue da baki, murmushi tayi tana jin son yan uwanta da kaunarsu yana ratsata domin sune suka yi mata wannan hidimar wacce bazata taba iya biyansu ba sai dai tayita yi musu addu'a,

Kasancewar wunin ranar bata ci abinci ba yasa taji cikinta yafara kugi hakan ya sanyata tashi taje ta bude snacks din da ni'ima ta kawo mata, meat pie ta debo da pepe chicken tazo ta zauna ta fara ci tanayi tana tunanin ina lamido ya shiga kuwa domin rabonta dashi tun kafin ta tafi yola,

Tashi tayi ta isa gaban fridge ta buda, cike ta ganshi da kayan jika makoshi kala kala,robar juice ta dauko guda daya tazo ta zauna ta bude ta fara sha,

Karar bude kofa taji hakan ya sanyata waiwaya, lamido ta gani sanye cikin yellow din t shirt mai layi layin baki ajiki da bakin wando, yayi kyau sosai yasha aski, fuskarshi dauke da murmushi amma daga gani daga bacci yatashi, bakinshi dauke da sallama ya shiga ikhlas ta amsa mashi tana murmushi.

Akusa da ita ya zauna yana murmushi,

"Bakya nemana ko? Tun rana kaina yake ciwo nasha magani na kwanta sai daf da magrib natashi na rama sallolin da ake bina nasake kwanciya sai yanzu na tashi nayi sallar isha nayi wanka na fito"

Kallonshi tayi cikeda kulawa, "ayya sannu ai ban saniba"

"Amma da kika jini shiru meyasa ba zaki nemeni kiji ba?" Ya tambayeta yana lumshe mata manyan idanunshi,

"Kayi hakuri.."

Hannu ya saka cikin filet din da take cin meat pie da pepe chicken din ya dauki daya ya fara ci,

"Nima yunwa nake ji saboda rabona da abinci tun rana"

Dagowa tayi ta kalleshi, "tsaya to na karo maka"

Daukar filet din tayi ta nufi cikin bedroom dinta binta da kallo yayi tayi kyau sosai tana sanye cikin material baki mai santsi dinkin riga da skirt gaba daya ya bayyanar da kyakkyawar surarta gashi tasha kunshi ja da baki bayada kwalliyar da fuskarta tasha irin wacce ake yiwa amare,

Bai fargaba yaji har ta dawo ta ajiye masa filet din akan dan karamin stool din dake ajiye agabanshi,

"Abban sadiq gashi" tace dashi tareda nufar wurin Adana kayan sanyi nan ta dauko masa ruwa da juice ta dawo,

"Wannan naman yayi dadi.." Ya fada yana kallonta,

"Abban sadiq banda santi dai" tace dashi tana murmushi,

"Babu wani santi dagaske yayi dadi ki ajiye min gobe dashi zanyi breakfast"

"To shikenan zan ajiye maka"

Tana nan zaune har ya kammala ya fara bin falon nata da kallo domin ba karamin tsaruwa yayiba gashi sai wani kamshine mai dadi yake tashi,

"Muje naga cikin bedroom din naki" yafada hadida kama hannunta ta mike tsaye suka tasamma cikin dakin, agefen gadonta ya zauna ya kwanta yana kallonta,

"Dakin naki yayi kyau sosai.."

"Nagode" ta amsa masa tana wasa da yan yatsun hannunta,

"Dauko sadiq mu tafi dakina" ya fada bayan ya tashi zaune, make kafada tayi alamun a'a,

"Ba zamuje dakin nawaba?" Ya tambayeta, gyada kai tayi alamun ehh,

"Anan kikeso mu kwana?" Ya sake tambayarta, daga masa kai ta sakeyi,

"Yau me ya samu bakin naki ne? Kin dai san cewar yunwa nakeji sosai ko?"

Kanta ta sunkuyar kasa tana murmushi,

"To zo naga meya samu bakin naki yau yaki magana" ya mike tsaye ya isa gareta ya kamo hannunta zuwa bakin gadon,zaunar da ita yayi a jikinshi yana shakar daddadan kamshin da jikinta yake fitarwa,

"Ikhy baby.." Ya fada ahanakali yana rikeda hannunta yana kallon zanen kunshin da aka yi mata,

"Ban san dunbin farin cikin da nake cikiba ayau sai dai kawai zaki fahimci hakan da kanki, ki tashi kiyi alwala muyi salla ko?"

Ba tare data tayi magana ba tafara shirin tashi tsaye, mikar da ita yayi ya kama hannunta zuwa cikin bathroom din wanda har ciki ya bita ya kunna fanfo yayi mata alwalar ya rikota akan kafadarshi suka dawo cikin dakin,

Sallah suka gabatar raka'a biyu tareda addu'o'in samun zaman lafiya,

Kallonta lamido yayi da murmushi akan kumatunshi "wai me kika bawa sadiq ne yaketa wannan baccin?"

"Ni babu abinda na bashi" ta fada kanta na kasa,

"Ok yaro ya gane yau babanshi angone shiyasa.."

Shiru tayi masa tana murmushi, tashi yayi yaje ya janyo dan karamin gadon sadiq ya daukeshi ya sakashi aciki ya koma gaban mirror ya tsaya yafara shafe jikinshi da dadadan turaruka masu kamshin gaske, gaban gadon ya koma ya kwanta yana kallon ikhlas, da hannu ya fara yafitota dakyar ta iya tashi ta isa gareshi saboda kunya.

Daren ranar daga shi har ita sunyi rayuwa mai dadi wanda basu taba tsintar Kansu aciki ba sai a lokacin, sai dai abinda ya daurewa ikhlas kai shine kukan da suka dade sunayi itada lamido Wanda bata san dalilin faruwar hakan ba,

Har gari ya waye lamido na dakinta duk inda ta juya yana rungume da ita wani irin zazzafan sonta ne yaji yana dada shigarsa, tare suka yi wanka suka yi salla suka koma suka kwanta.

Wani zazzabi ne ya fara rufe ikhlas nan jikinta ya fara zafi gashi sadiq ya tashi ya fara kuka, daukoshi lamido yayi yazo inda take kwance ta lulluba da bargo,

"Pretty dan daure ki bashi yasha sai na kaishi gidan innah tunda baki da lafiya" ya fadi cikin tausayawa,

Daurewa tayi ta tashi ta amsheshi ta shayar dashi har sai da ya koshi, nan kuma yafara bangalawa Lamido dariya yana son yayi masa wasa,

Hannu lamido yasa ya taba jikinta, nan yajishi zafi zau,

"Bari na kaishi nadawo"

Bata iya bashi amsaba sai daga masa kai da tayi, fita yayi da sadiq a hannunshi yaje bedroom dinshi ya dauko key din mota ya fita,

Lokacin da yaje gidan innah samunta yayi a falo tana shisshirya wasu litattafai na baffa acikin jaka,

Mika mata sadiq yayi bayan sun gaisa "innah gashi mamansa ce bata da lafiya"

Karbarshi innah tayi nan taji shima lamidon jikinshi zafi zau alamun zazzabin "lamido, kaima ai zazzabin kake yi ga jikinka nan naji da zafi..." Inna tace dashi tana sake tabashi,

"Ehh wlh innah nima zazzabin nake ji"

"To Allah ya sawwake, ka gaishe da mutanen gidan"

"Zasu ji innah"

Ko wurin baffa bai shigaba ya fice daga gidan jikinshi rau dan zafi, yayi niyyar yaje chemist ya siyo musu magani amma yaji bazai iyaba saboda zazzabin jikinshi karuwa yake wanda dakyar ma yake tukin.

A galabaice ya karasa gida yafita daga cikin motar yana rungume da hannayenshi a kirjinshi alamun yana jin sanyi, baiji motsin kowa ba da alama daga ihsan har fadila babu wacce ta fito,

Bedroom din ikhlas ya shiga nan ya sameta akundundune cikin bargo kamar yadda ya tafi ya barta, bayanta yaje ya kwanta ya rungumeta bayan ya lulluba da bargon,

Dama zazzabin kamar jira yake ya kwanta take ya rufeshi gaba daya ruf, kuka lamido ya fara da surutai saboda zafin zazzabin (hmm masu karatu kun san dai lamido da surutu marar kan gado idan yana zazzabi),

Rungume ikhlas yayi ya fara yi mata surutai "pretty wallahi ina sonki, ke kadaice macen da zuciyata take so, nafara sonki tun kina mahaukaciya lokacin dana ganki a bakin plaza, bazan iya controlling din kaina bane lokacin shiyasa har nayi miki fyade, tun daga lokacin nashiga halin damuwa har dawowa nayi adaren bayan na tafi amma ban gankiba, pretty nasha wahala akan sonki, sonki ya wahalar dani ya azabtar dani,tun daga ranar da nayi miki fyade ban sake samun farin ciki ba sai daren jiya, nasha bakin ciki da kunci kala kala adalilin rashinki musamman ma da na rasaki, kwatsam ban tashi ganinki ba sai a matsayin matar yayana wallahi pretty ji nayi kamar na mutu nabar duniya saboda tashin hankali domin rayuwata duk nagama tsarata ne tare dake" tunda yafara maganar yake kuka har kawo iyanzu.

Kumatunta ya kamo da hannuwanshi wadanda suka dau zafi ga kuma hawaye yana bin kumatunshi, "Dan Allah pretty karki sake rabuwa dani, kar ki sake guje min, idan kika gujewa rayuwata wallahi mutuwa zanyi saboda i can't do without you, you are the part and parcels of my life...".


 
    _Gaisuwa gareki yayarmu Anty Hajiya, badan kar nayi karya ba da sai nace kin fi kowa son ruwan kashe gobara.. Domin har mafarkinshi kike...!_

3 comments: