Tuesday 17 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA.. 70

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a Zuciya)_

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

  aishaummi.blogspot.com

   _Fatan alkairi ga yayata ta kaina mai yayina mai ji dani akoda yaushe anty Jamila Moh Ali (maman bobo),nagode sosai da kulawarki._

   *_70_*


~~~Tana jinsu sai soyayya suke zubawa har lokacin data kammala aikinta ta tsame dan wakenta ta zuba acikin flask ta fita, tsabar takaici bata iya cin abincin ba sai ajiyeshi tayi ta samu wuri ta kwanta gaba daya ranta yagama jagulewa ta kasa gane abinda ke damunta, har karfe d'ayan rana tayi bata saniba sai da ta jiyo kiran salla daga masallacin kofar gidan sannan ta farga ta tashi,

Wanka tayi tai salla ta shirya sadiq ta dauki kayan karatunta ta fita, tana fita ta samu driver din gidan baffa yazo daukarta, anan yake sanar da ita cewar lamido ne ya turoshi yakaita makaranta sannan idan ta tashi ma zai koma ya dauketa, shiga gidan baya tayi ta zauna gaba daya ji take kamar ta fashe da kuka.

  Lokacin da taje makarantar a aji biyu aka sata nan ta shiga ta zauna ta fara daukar darasi gadan gadan gashi babu laifi zamanta acikin mutane ya dan debe mata kewa, sai karfe 4 na yamma aka tashi drivern baffa yazo ya dauketa ya mayar da ita gida, lokacin da taje gidan lamido na falo a zaune shida fadila suna cin abinci bata sake kallon inda suke ba ta wuce sashenta.

Tana zaune tana cin abinci bayan ta idar da sallar la'asar lamido ya shigo ya na kallonta k'asa k'asa domin uniform din ba karamin kyau yayi mata ba kasancewar light purple ne,

"Kun dawo..?" Ya tambayeta ahankali,

Can ciki ciki tace "uhm" daga nan bata sake kallonshi ba saboda yayi mugun kyau cikin blue din t shirt da blue din wando,

Sadig ya sunkuya ya dauka ya fita, mintina kadan ya dawo ya bude drewar din kayanshi ya dauki wata bakar riga da wandonta ya fita, shirya sadiq yayi ya sauya masa kaya shima ya hade cikin suit masu kyau wadanda suka fito dashi,

Falo ya fita inda su fadila ke jiranshi suma sunsha gayu kamar ba zasu taka kasa ba,

Dunguma suka yi suka tafi bikin bud'e kamfaninshi da aka shirya, wuri ya tsaru yasha decoration ga kamfanin ya hadu wawakeken gaske,

Duk yan uwa da abokan arziki kowa ya hallara domin hatta Xahar itama tazo ita da suhaimat sunsha kwalliya sosai, su ihsan kuwa ransu ne ya b'aci saboda ganin sunan kamfanin _IKHLAS NIG COMPANY LTD_, nan suka tsiri harare harare da yatsine yatsinen fuska wanda har sai da suka nunawa Lamido tun awurin, lallab'asu yayi yace shi ba sunan ikhlas din da suka sani yasaka ba asalima bai san waye ya sauya sunan da yayi ra'ayin sawa ba domin shi sunan innarshi ya saka, kasancewar suna sonshi sai suka yarda da maganar da yayi,

Sai bayan sallar magrib sannan aka tashi daga wurin bikin bude kamfanin, dukkaninsu agajiye suka koma gida suna shiga falo lamido ya mikawa ihsan sadiq da katuwar jaka mai dauke da kayan da aka raba awurin bikin yace ta mikawa ikhlas, kamar ba zata je ba sai ta daure ta hadiye kishinta ta tafi,

Ikhlas na zaune akan doguwar kujera tana kallon wani Indian film a tashar _zee cinema_ ihsan ta shiga sai cika take tana batsewa,

Dak'yar tayi mata sallama ta mika mata sadiq, "gashi inji lamido wannan kuma yace nakine" ta mika mata paper bag din tana yamutsa fuska,

Karbarshi ikhlas tayi tace "nagode"

Ihsan bata sake magana ba ta juya ta tafi, zama ikhlas tayi cikin takaici tana kallon kayan amma indai hakane lamido ya cika dan rainin wayo wato shine zai tattara matanshi wadanda yake so ya fita dasu ita ya kyaleta agida? A lissafinta sai gobe ne ranar girkinta dan haka ya zama dole ta dauki mataki itama dole gobe sai ya bata hakkinta dake kanshi domin ba zata dauki wannan rashin adalcin ba.

  Washe gari kam sam ma bataga lamido ba domin yana can kamfaninshi sunata shirye shiryen fara gudanar da aiki dan haka bashi ya dawo gida ba sai karfe 5 na yamma, daki ya shiga yayi wanka ya kwanta, bai sake fita ko inaba har lokacin sallar isha ko su fadila ma ranar sai dakinshi suka zo suka yi hira suka tafi,

Ikhlas kam daukar sadiq tayi ta fita zuwa dakin lamido lokacin ya fito daga wanka yana zaune agefen gadonshi yana waya da xahar (Khadija Sidi kawata tace wai lamido ya girma yanzu bai kamata ya runga budurwa ba, nikuma ummi Shatu nace har yanzu lamido bai girmi yin amarya ba),bude kofar tayi ta shiga cikin dakin,

Tsaye tayi tana sauraren hirar da yake yi da xahar din,

"Sorry baby yau dinne nagaji but gobe zaki ganni i promise you...",dan dakatawa yayi kafin yaci gaba,

"Nayi tsammanin ai ko kema kinada kishi, amma tunda zaki iya zama dani ahaka tareda matana guda uku shikenan..."

"Wurinka fa nazo, kowacce mata agidan nan kana bata kulawa kana bata hakkinta amma banda ni..." Ikhlas ta fadi fuskarta dauke da tashin hankali da bacin rai,

"Hold on baby i will call you back" yace da xahar tareda zare wayar daga kunnensa,

Kallon ikhlas ya tsaya yana yi sosai batare da yayi mata magana ba amma kalamanta sunyi mutukar bashi dariya domin da dukkan alamu kishine ke damunta domin kalmomin da tayi amfani dasu sun bayyanar da hakan,

Ganin ya tsaya ya zuba mata ido yanata kallonta yasata sake magana, "ya nayi maka magana ka tsaya kana kallona?" Tace dashi a k'ufule,

"Ba bacci kika zo yiba? Ga gado nan kije ki kwanta"

Juyawa tayi ta fita batare da ta sake ceda shi komai ba, tana zuwa daki ta kwanta ta rungume sadiq ta fara kuka, takai wurin tsawon minti ishirin tana kukan kafin tayi shiru ta goge hawayenta, alamun bude kofa ta jiyo ko ba afada mata tasan lamido ne, karasowa yayi yasha kayan bacci milk colour, gadon sadiq ya tura kusa da gadon ikhlas yaje ya daukeshi ya sakashi aciki ya hau kan gadon, juya mata baya yayi kamar yadda itama yaga tayi,

Ahankali ta waiwaya ta kalleshi ganin ya juya mata baya ya sake kular da ita dan haka ta tashi ta dauki bargo ta shimfida akasa ta kwanta, zaune lamido ya tashi yana kallonta,

"Keda dakinki ya zaki kwanta akasa? Ai ni ya kamata na sauka na bar miki kan gadonki" ya fada tareda sauka daga kan gadon ya fita daga cikin dakin, tashi tayi ta bude window tana lekenshi,

Har zai wuce dakinshi sai ya hango dakin ihsan da haske dan haka ya shiga yaga abinda ya hanata bacci, azaune ya sameta da lecture notes agabanta tana karatu,

"My ihsan ashe boko ne ya hanaki bacci?"

Dagowa tayi ta kalleshi tana murmushi "test zanyi gobe da karfe takwas na safe shiyasa nake dan dubawa"

"To ayi karatu lafiya" ya fada bayan ya manna mata kiss a kumatu, juyawa yayi ya fita ya koma dakinshi.

Ikhlas kam na ganin lamido ya shiga dakin ihsan ta saki labulen windown ta koma bakin gado ta zauna,

"Gayen nan me yake nufi? Kwana na zai dauka ya kawai wata? Tab wallahi da sake, kai ni zaman gidan nan ma ya isheni wallahi nagaji da wannan wulakancin tafiya zanyi inyaso sai ya zauna da matan nashi wadanda yake so,haba wannan wulakanci  har ina" duk wadannan maganganun tayi sune acikin zuciyarta, daukar sadiq tayi daga cikin gadonshi da Lamido ya kwantar dashi ta rungumeshi ta lullubesu.

Da shirin barin gidan ta kwana dan haka da safe bayan duk sun bar gidan itama ta suri akwatin kayanta ita da sadiq ta fita sai tashar mota nan ta samu motar borno, duk jin wani kunci take yi ya rufeta tunda suka kama hanya basu suka sauka ba sai misalin karfe 6 na yamma, ammi tayi murnar ganinta amma kuma taga alamun ba kalau ba, suna nan zaune tana cin abincin da hajiya ta kawo mata yaya Hussain ya shigo shida yaya hassan hannunshi rikeda na abdallah,

"Oyoyo anty" abdalla ya fadi bayan ya tafi da gudu domin rungumeta, sai da gaban ikhlas ya fadi domin maganar abdallah irinta lamido ce banbancin kawai shi abdallah yarone,

Rungumeshi tayi tana shafa kanshi "abdallah ina karatu? Kana zuwa?"

"Kullum uncle Hussain yana kaini anty"

Murmushi tayi ta dorashi akan cinyarta "to da kyau yarona"

"Zuwan nan naki lafiya kuwa?" Hassan ya tambayeta, girgiza kai tayi alamun a'a,

"Meya faru?" Hussain ya tambaya,shiru tayi batace komai ba tana tunanin ta fada musu ko tayi shiru,

"Menene ya faru ina tambayarki" hussain ya sake tambayarta cikin fada,

"Um, um,ashe lamido,um ashe, ashe shine,shine.."

"Shine me?" Hajiya dake bakin kofar dakin ta bukata,

"Shine Baban abdallah" ikhlas tafada tareda fashewa da kuka.

Salati hajiya da ammi suka d'auka amma acikin zuciyoyinsu hakan yayi musu dad'i musamman ma sanin da suka yi cewar komai daren dadewa dole watarana idan abdallah ya girma sai ya tambayi mahaifinshi,

Shi kuwa yaya Hussain da yaya hassan mutuwar tsaye suka yi amma fa fuskokinsu babu walwala ko kadan sannan da alamar akwai abinda zai biyo baya.....!

  _Gaisuwa mai daraja gareki ummu Irfan, nagaisheki sosai._


*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment