Friday 14 April 2017

RAMUWAR GAYYA.. 46

Ramuwar gayya.. 46
*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_


*_Ummi A'isha_*
_with_
*_Phertymerh Xarah_*

46

K'arfe biyar da rabi sawwam yafarka,
ummulkhair ya kalla wacce ke kwance gefenshi
ta cure jikinta wuri guda,

Hannunshi yakai kan goshinta ya taba, duk zufa
ta tsatssafo mata kamar wacce take zaune
atsakiyar rana,

Tashi yayi ya shiga toilet ya tsaftace jikinsa
yafito, zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi
kamar kankara sai zallar farin ciki dake
wanzuwa acikinta marar yankewa,
Idonshi akan khairi ya dauko kayanshi yasaka,
gaban gadon yaje ya dagata ahankali ya gyara
mata kwanciyarta, fuskarta yabi da kallo yana
murmushi saboda baccinta take hani'an kamar
ta shekara batayi ba,

Sai da yabata wani zazzafan kiss a kumatunta
sannan yaja bargo ya lullubeta yafita masallaci.

Karfe shida da yan mintuna yadawo cikin dakin
amma har lokacin ummulkhair bata tashiba
asalima ko juyi bata yiba tana nan a yarda
yatafi yabarta,
Gefenta yaje ya kwanta ya dagota zuwa
jikinshi ya rungumeta,

"My lonely yau kin tabbatar da abinda nadade
ina fada miki cewar zan baki daddadar rayuwa
duk ranar da muka kasance tare,

Gashi yau Allah cikin jin kansa ya nuna mana
wannan lokacin, Allah yayi miki albarka
khairi,Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya
albarkacemu da 'yaya masu albarka,
Ina tsananin sonki ummulkhair and bazan taba
daina sonki ba har karshen rayuwata, babu
abinda zai rabani dake...."

Sharrr hawaye suka fara bin kumatunsa, ita dai
khairi kamar a mafarki take jin maganganunsa
kasancewar bacci take yi sosai,

Rungumeta yayi sosai ajikinshi har bacci ya
sake tafiya dashi bashi ya tashi ba sai da
misalin karfe tara saura,

Mamakine ya kamashi ganin har lokacin
ummulkhair bata tashiba, tashinta yafara yi
ahankali,
"My lonely..., my lonely rana tayi bakiyi salla
ba.."

Sake gyara kwanciyarta tayi ta juya baya, bai
hakura ba yasake komawa gefen datake yana
shafar fuskarta,

"Tashi mana yanmata na..."
"Um, um ka kyaleni"
"Sai yaushe zaki tashi to?"
"Yanzu..." Tabashi amsa har lokacin bata bude
idanuwanta ba,

Ganin bata da niyyar tashi yasashi kyaleta
yafita, motarshi ya dauka ya nufi gidansu,
lokacin da yashiga ko dakinsa bai shigaba ya
nufi falon Mami, tana cikin kitchen ita da mai
aikinta suna hada breakfast,

Daga bakin kofa ya tsaya yafara gaida mami,
kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka fahimci irin
tsananin farin cikin da yake ciki,
"Sawwam har ka tashi?" Mami tace dashi tana
fara'a,

"Ehh wallahi Mami" yabata amsa yana sosa
keyarshi saboda yasan mami ta rigada ta
fahimci komai,
"Mami kawo natayaki..."
"To zo ka debi wannan flasks din ka kai kan
dining ka jera"

Da murmushi akan fuskarshi yakarasa cikin
kitchen din yafara diban flasks din yana kaiwa
kan dining, mami sai kallonshi take in banda
murmushi babu abinda yake yi shi kadai,
Girgiza kai Mami tayi ita dinma wani farin
cikine yake ratsata domin farin cikin sawwam
shine farin cikinta,

Tare suka kammala shirya breakfast din har dad
ya shigo cikin shirinsa na zuwa office,
Fuska dauke da fara'a da walwala sawwam ya
gaidashi, shi kansa dad din sai da yayi mamaki
saboda yajima baiga fara'ar sawwam haka ba,

Cikin farin ciki sukayi karin kumallon suka
kammala, lokacin da dad zai fita har farfajiyar
gida sawwam ya rakashi,
Yana ganin dad yafita yakoma wurin mami,
"Mami zanje natafi, nabar ummulkhair ita kadai"

Murmushi mami tayi tana harhada masa food
flasks acikin wani dan madaidaicin kwando,
"Lafiyarta dai kalau ko?"
"Mami lafiya lau take"
"To ka gaisheta dakyau, ga abincin"
Karba yayi yajuya ya fita yana fadin, "zata ji
mami".

Sawwam bai jima da fitaba ummulkhair ta
tashi, zama tayi tana kallon ko ina nacikin dakin
da kallo, take kuma abubuwan da suka faru
suka rinka dawo mata daya bayan daya,

Mikewa tayi ta lallaba ta shiga bathroom ta yi
wanka bayan ta gasa jikinta da ruwa mai zafi,

Fitowa tayi daure da towel ta nufi dakinta, kaya
tasaka riga da skirt na shadda kalar ruwan kwai,

Salla tayi sannan tayi musu addu'ar samun
zaman lafiya itada mijinta, tana idarwa ta mike
ta dan gyara fuskarta tafita falo,

Abincin da sawwam ya kawo mata jiya shi ta
ciro daga cikin fridge, ko dumamawa batayi ba
ta zauna taci ahaka saboda yunwa takeji,
Kan doguwar kujera takoma ta kwanta bayan ta
kammala cin abincin, bata jima da kwanciyar ba
sawwam ya shigo hannuwansa dauke da kaya,
Kayan ya ajiye akan center table yana kallonta,

"Ba zakizo kiyi min sannu da zuwa ba?"
Zaune ta tashi tana murmushi sai dai takasa
hada ido dashi,

"Sannu da zuwa..."
Kafada ya makale alamun bai yarda ba,
"Nidai sai kinzo kinyi min sannu da zuwa
sannan zan amsa"

Murmushi tayi idonta yana kallon kasa gashi
takasa tashi taje inda yake,karasawa yayi ya
zauna akusa da ita tareda kamo hannuwanta
yarike cikin nasa,
"Kin tashi?"kai ta daga masa,
"Kinsha bacci.."

Kallonsa tayi sai kuma tayi saurin kawar da
kwayar idonta kafin su hada ido dashi,
"Ga abinci mami ta bayar akawo miki, taso
muje nabaki"
Girgiza masa kai tayi, "na koshi"
"Me kikaci?"
"Abincin jiya"

Murmushi yayi ya tsaida idonshi akan fuskarta
ya lura duk maganar da take masa tana yine
idonta akasa batare data kalleshi ba yasan
kunyarsa takeji yanzu, niyyar tsokanarta yayi
yakai hannunshi kan zif din rigarta, cikin sauri ta
rike hannunsa tana kallonsa,

"Meya faru?" Yace da ita yana murmushi kasa
kasa,

"Babu komai"

"To zomuje ki kwanta ki huta"
Kai ta girgiza masa alamun a'a, murmushi yayi
ya shafi gefen fuskarta,

"My lonely matsoraciyace duk kinbi kin tsorata
daga jiya kadai, sannan wannan kunyar babu
inda zata kaiki garama ki cireta"

Bai barta tayi magana ba ya mikar da ita tsaye
yakamata zuwa bedroom dinta, kwantar da ita
yayi ya zauna agefenta yana yi mata tausa har
bacci ya dauketa yana ganin haka shima ya
kwanta akusa da ita.

Ranar dai tare suka wuni agida baije ko inaba
dama ko office bashida niyyar zuwa, sai da dare
yayi sannan suka fita tare, gari suka dan
kewaya sannan yadawo da ita gida ya koma
gidan mami, sai da yajira suka ci abincin dare
tareda dad,har sai da yaga dad din yashiga part
dinsa sannan yayiwa mami sallama zai tafi,

"Ka gaisheta, sannan dan Allah sawwam ka
kula da ita sosai kaji, kaga dai irin halaccin da
tayi maka"

"Insha Allah mami zan kiyaye"

Lokacin da yaje gidan yasamu har ummulkhair
ta yi shirin bacci ta kwanta adakinta,

"Badai har kinyi bacciba?" Yafada yana shafar
kumatunta,
"Nadai fara, kadawo?"

"Ehh nadawo, tunda kin kwanta bari naje nayi
wanka"

"To sai da safe" tafada tareda gyara
kwanciyarta,

"Wanne irin sai da safe? Ai zan dawo, ko yau
korata kike?"
Shiru tayi tana jinsa bata amsa ba, hannunta ya
kamo,

"Zo mutafi dakina"
Kafada ta makale,

"a'a"

"Wai yau abin tsoro nazama ne? Dakin nawa ma
tsoronshi kike?"
Sake kwanciya tayi tana turo baki,

"Zo mutafi maza my lonely dina..., Allah muna
zuwa baccinki zakiyi"

Da lallami da komai yasamu ta tashi tabishi
zuwa dakin nashi, wanka ya shiga ita kuma ta
hau kan gadonshi ta kwanta, kafin yafito daga
wankan har tayi bacci,murmushi yayi ya shirya
ya matsa kusa da ita ya rungumeta,

"Shine kikayi bacci kika barni baki jirani nazo
munyi hiraba"

"Indai wannan hirarce nayafe" yaji tabashi
amsa, murmushi yayi ya sake kankameta
tamkar zai mayar da ita cikin kirjinsa.

Ahaka har sukayi sati daya, kullum mami ce
take basu abinci shi dad ma sam bai san
sawwam baya kwana agidan ba saboda yana
ganinshi kamar da, sai dai wani lokacin idan ya
nemeshi cikin dare sai mami tace yayi bacci
saboda yasha maganin mura, sam dad bai taba
ganewa ba shiyasa hankalinsa ya kwanta
musamman ma da yaga shi kansa sawwam din
shima hankinsa ya kwanta.

Tunda ummulkhair tazo gidan yau kwana goma
kenan sai yau sawwam zai fita office amma da
kullum agida yake wuni suna soyayyarsu shida
khairi idan dare yayi kuma sufita su zagaya gari,

Yana kwance yana bacci ta shigo taci kwalliya
sosai, daga shi har ita har sunyi kiba a yan
kwanakin da suka dauka tare,
Bakinshi ta tsotsa da nata tana dariya,

"sahibi
kafasa fita aikin ne?"
Kamota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta, "ban
gama baccin bane"

"To katashi kayi wanka ko ka makara"
Jin zata zame ta gudu yasashi bude idonshi,
"ina zakije?"

"To bakaine kaki tashiba"
Tashi yayi yana kallonta, "natashi, shikenan?"

Kai ta daga masa taja hannunshi, wanka ya
shiga ya fito ta shiryashi yafito fes dashi,
breakfast ta gabatar musu sukaci sai da ya
sammata soyayyarsa mai tsayawa arai sannan
ya mike domin fita, babu zato yaganta tafara
zubar da hawaye,
Rungumeta yayi yafara lallashinta,

"My lonely nima ba ason raina zan tafi nabarki
ba amma sai dai zanyi miki albishir guda daya,
kema acikin week dinnan zaki koma makaranta"
Tsalle tayi ta rungumeshi ta fara kissing dinshi
a wuyanshi,

"Nagode sahibina, Allah ya kiyaye hanya.."

"Shikenan kuka yakare..?" Yafada cikin tsokana,
murmushi tayi ta daga masa kai, bayanshi ta
dale, ahaka yafita tana goye abayanshi har sai
da yaje wurin motarshi sannan ta sauka tana
dariya, shima dariyar yake ya bude motar ya
shiga,

"Zan iya tafiya?" Ya tambayeta, kiss tayi masa a
baki tana dariya,

"Zaka iya tafiya Allah ya tsare min kai har ka
dawo"

"Amin my lonely, sai nadawo"

Tana tsaye tana kallonsa har yafice daga gidan,
ciki takoma duk sai taji gidan babu dadi saboda
sawwam baya nan ita sai yanzune ma tasan ta
shaku dashi ashe da shakuwar da sukayi a
makaranta ba shakuwa bace shirme ne,
yanzune suka shaku shakuwa irin ta zuciya da
zuciya, yanzune take sonshi soyayyar da Allah
ne kadai yasan adadinta,

Tana zaune tanata missing dinshi har yamma
tayi, ta idar da salla kenan taji sallamarshi,
fitowa tayi ta rungumeshi sosai tana
murna,kallonta yayi tayi kwalliya tayi kyau sosai
abinta,
Kugunta ya rike yana hada fuskarshi da tata,

"Kinyi bakuwa"
Saurin sakinshi tayi ta kalli bayanshi, alawiyya
tagani tsaye tana murmushi, da gudu ta tafi ta
rungumeta,

"Ashe tare kuke? Wallahi ban ganki ba"

"Dama taya zaki ganni" alawiyya tafada tana
dariya, zaunar da ita ummulkhairi tayi ta kawo
mata abinci, sannan taje ta gabatarwa da
sawwam shima nasa abincin,hannunta yaja ya
hadata da jikinsa,

"Nifa ke kadai nake bukata ba wani abincin ba"
ido ta kwalalo,

"Haba sawwam bakaga munyi bakuwa bane,
kabari mana tatafi"
Dariya abin yabashi saboda yanda yaga ta zaro
ido,

"To naji..." Cakulkul yafara yi mata tayi saurin
kwacewa tagudu tana dariya,
Wurin alawiyya takoma suka fara hirar yaushe
gamo,

"Khairi kinyi kyau wallahi kuma gashi kinyi kiba
abinki"

Dariya ummulkhair tayi,

"nikuma wallahi bana
ganin kibar, shima sawwam kullum sai ya
tsokaneni wai nayi kiba"

"Gaskiya kinyi kiba, shima sawwam din naga
yayi kiba, da alama kuna kulawa da junanku"

Dariya ummulkhair tayi suka cigaba da hirarsu
da alawiyya,har dare suna tare sai da akayi
sallar isha sannan sukaje itada sawwam suka
mayar da ita gida.

Acikin satin ummulkhair takoma makaranta
tafara zuwa lectures, kullum tare suke fita da
sawwam yasauketa sannan yawuce office,

Gidan mami kuwa tunda ta tare bata jeba
saboda suna tsoron kar dad yaganta, ganin haka
yasa ita mamin ta shiryo tazo, basu jima da
dawowa gidan ba suna kitchen tana girki
sawwam yana tayata saiga mami tazo, ko
sallamarta basuji ba saboda hira suke yi, tana
bashi labarin wasu yanmata da sukayi fada akan
saurayi a makaranta yau,

"Kema fa kin taba fada akaina" yafada cikeda
tsokana,

"Ai ko yanzu da kake mijina bazanyi fada
akanka ba balle da a matsayinka na saurayi"

Dariya yasaka

"wallahi karya kike, yanzu idan
nakawo miki budurwata da dambe zaki kamata"

"Haba dai sai kace wata gara.."

"Allah kina kishina sosai nasani, duk daren
duniya fa sai kin fada min kalmar so sannan
kike yin bacci, au ashefa wani lokacin bakya
sanin kina fada, jiyama dan bakiji abinda kika
fada bane ko kina son ji in fada miki?

"Banda sharri dai" tafada tana murmushi,

"Babu wani sharri, kedai kam nasan idan baniba
sai rijiya"

Kafin tabashi amsa ya lallabo ta bayanta ya
rungumeta yana yi mata rada,

"nima idan bake
ba sai rijiya, ki gama girkin nan muje kibani
tukwici.."

"Haka dai.." Tafada tana tureshi,

"Idan kika hanani wurin yanmata na zan tafi,
ohh Allah sarki khairina rannan da kika yimin
rowa nace zan je wurin yanmatana fa rudewa
kikayi harda kukanki kina cewa dan Allah
sawwam karkaje wallahi zina babu kyau, dan
Allah kar kaje su bata min kai..."

Ya karashe
maganar yana dariya,
Dariya itama tayi ta debi ruwan da take fere
dankali ta watsa masa,

"Kuna inane?" Suka jiyo muryar mami,

"Lahh mamice tazo, dan Allah dauko min
hijabina"

Kafada ya makale yana dariya, "sai dai kifito
haka"

Rikeshi taje yi ya goce ya gudu yana mata
dariya domin wata yar rigace kamar shimi iya
cinyarta kalarta pink,

"Mami sannu da zuwa"

sawwam yafada bayan
ya zauna akusa da mamin, kallonsa mami tayi
dagashi sai short nicker da riga mai gajeren
hannu,

"Yawwa sannu ina ummulkhairin?"

"Mami taki fitowa wai kunya take ji"

Zaninta dake kan kujera ya dauka ya mika mata
cikin kitchen din ya fito, dole haka ta daure
tafito, kallo daya mami tayi mata ta fahimci
tana dauke da juna biyu amma su dayake
yarane duk cikinsu babu wanda yasani,

"Mami sannu da zuwa" ummulkhair tafada
cikeda kunya,

"Yawwa sannu, aiki ake tayine?"

"Ehh mami"

Mikewa tayi ta shiga daki ta sako hijab tafito ta
kawowa mami kayan motsa baki,
Cike da kunya ta gaisar da mami, cikin fara'a
da kauna Mami ta amsa mata tana tambayar ta
babu wani abu ko,

"Babu komai mami" ta amsa cikin jin kunya,
shikuma sawwam dake kusa da ita sai
mintsininta yake tayadda Mami ba zata
ganiba,hannunshi ta buge ta mike ta canja wuri
tana harararsa,

Mami bata wani dadeba sosai tace tafiya zatayi
saboda dama ganinsu kawai tazo yi, tare suka
fito suka rakota, kallon sawwam tayi tace,

"Ina fata dai baka matsa mata ko? Kaga juna
biyu gareta idan kafiya matsa mata dayawa to
cikin zai iya zubewa..."

Dukkaninsu mamakine ya kamasu, ga kunya mai
nauyi data rufe khairi,

"Mami ciki kuma?" Yafada cikeda mamaki,

"Kai baka saniba ba ko saboda kana shirme,
juna biyu gareta mana, Allah dai yaraba lafiya"

"Wallahi mami bata gaya minba boye min tayi
sai yanzu nasani da kika fada"

"To Allah yaraba lafiya, kuma ku kula sosai
banda shiririta"

"To mami..."

Ita dai ummulkhair takasa magana sai sawwam
ne kadai ke amsawa, har mami tatafi bata bari
sun kara hada idoba,

Yana ganin fitar motar mami yaja hannunta
suka koma ciki,

"Shine kika boye min?"

"Wallahi nima fa ban san dashiba nidai kawai
nasan tunda nazo gidan nan banyi period ba"

Rungumeta yayi yana murmushi, nan kuma
yashiga tsokanarta....

"Maman yan biyu ce ko?"

"Yan uku" tafada tana turo baki,

"Idan ma hudu kika Haifa min wallahi ina so,
gaskiya ke hadamammiya ce har kinyi ciki, koda yake nagane
bakya son wata tazo tafiki samuna ko?"

Tureshi tashiga yi,

"ni kyaleni naje nakarasa
girkina"

Tashi yayi yabita yana murmushi, "mu karasa
tare dai tunda dama tare muka fara"

Tana jinshi ta rabu dashi sai murmushi da
takeyi aranta tana ta mamakin wai har sun kusa
samun baby ita da sawwam lallai abin babu
wuya awurin Allah...

***

"Yau zanje nagano yarinyar nan" mahaifin
khairi yafada yana gyara babbar rigarsa,
Mama dake tsaye kamar zata saka kuka tace

"Allah ya kiyaye hanya, kagaisheta"

"Zataji" shine kawai abinda yafada yasa
takalminsa yafice,binsa mama tayi da ido amma
duk zuciyarta babu dadi saboda rabata da yarta
da akayi,

Karfe 12 suka shiga garin gombe, kai tsaye
gidan dan uwansa suka wuce sunci Sa,a sun
sameshi agida bai fita ko inaba,
Saida suka gaisa aka dan jima sannan abban
khairi yadubi yayansa,

"Ina ita wannan yarinyar take?
Kallonsa yayansa yayi,

"wafa?"

"Ummulkhairi mana" yafada yana fara,a,

"Ai bata zoba"
"Haba yaya, nifa nakawo yarinyar da hannuna"

"To ai tun wannan turowar da kayi aka tafi da
ita shikenan rabonmu da ita"

"Ni? Da yaushe?" Baban ummulkhair yafada
cikin tashin hankali,

"Banfa gane abinda kake son fada min ba, kaine
fa ka aiko aka tafi da ita.."

"Yaya wallahi ban san wannan maganar ba..."

Tashi yayansa yayi ya leka cikin gida yana
kwallawa umma kira, tana zuwa yafara magana,

"Zoki jiye min wani abin al'ajabi, kinji wai
bashine yaturo aka tafi da khairi ba"

Shiga rudani umma tayi jikinta yana rawa,

"Alhaji ka gafarceni wallahi banyi haka dan in
bata maka ba, dan Allah kayi hakuri"

"Me kuma yafaru?" Alhaji mukhtar yafada
hankali tashe,

"Alhaji wallahi ba shine ya turo atafi da itaba
mijinta ne..."

Zunbur abba ya mike arazane,

"wai kuna nufin
khairi bata gidan nan? Tana ina?"

"Tana kano gidan mijinta tun kimanin watanni
uku baya da suka wuce"

Mamakine karara ya bayyana a fuskokinsu
amma shi abban khairi bayan mamakin ma
harda tashin hankali, ko takansu bai sake biba
ya saba babbar rigarsa yafita yana cewa,

"Wallahi yau ko ani ko a mahaifin wannan yaron,
bazan yarda ba sai sun sakar min yata, yata
bazata zauna dashi ba".....

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment