Thursday 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 35,36,37

[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


     _Thanks to my masoya masu yimin fatan samun lafiya, nagode muku sosai especially masu kirana awaya da masu turo min text da duk wani wanda yadamu dani acikin mind dinsa...one love_


   *_35_*

aishaummi.blogspot.com


  ~~~Ita dai maryama shiru tayi tana sauraren bak'ak'en maganganun da shaddad ke faman fada mata, masu video da camera kuwa sai aikin haskasu suke domin ba karamin kyau suka yiba,

"And last abinda zan fada miki shine babu zuwa club agidana, babu zuwa stadium sannan babu zuwa aiki, mutukar kina son auren mu yaci gaba da numfashi to sai kinbar wannan aikin da kike yi saboda nariga da nadade da sanin duk doctors din wurin abokan mu'amularki ne more especially ma wannan karamin yaron da kike bibiya wanda baifi sa'an kaninki ba amma tsabar jaraba irin taki binshi kike.."

Maryama ji tayi kamar zata fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki domin har idanuwanta sun fara kokarin kawo ruwa, sai dai kuma ta dade da yiwa kanta alkawarin cewa  shaddad bazai taba ganin kukanta ba wannan dalilin ne yasata yin gaggawar hadiye kukan bawai dan zuciyarta ta daina kuna ba a'a kawai bata son yagano lagonta ne domin tasan muddin shaddad yagane tana jin dacin maganganun da yake fada mata to zai cigaba da fada mata sune har illa masha Allah,

Watsi tayi da al'amuransa ta mayar da hankalinta kan program din da aka fara gudanarwa,

Anty karama ce ta bude taro da addu'a sannan aka bayar da tarihin ango da amarya a gurguje, daga nan kuma aka fara chashewa, ganin su anty maijidda sun fita suna rawa yasa maryama kokarin tashi domin tana son taje tayi musu lik'i, amma kuma bazata iya tashi ba domin shaddad ya matseta sosai,

"Zan tashi.."

"Na rikeki ne..?" Ya fada yana dauke kanshi zuwa wani wuri, kokarin tashi tafara ta samu ta tashi dakyar ta nufi filin rawar tana tafiya ahankali saboda tsinin takalminta,

Liki tafara yi nan da nan wuri ya kancame, tana liki ana yi mata, shaddad yana daga can zaune yana kallonsu, tashin shima yayi ya sauko ya nufi wurinsu,

Rafar kudi ya ciro daga aljihunsa yafara zubawa jama'ar dake cikin filin, yana tsaye a bayan maryama sai kudi yake zuba mata, amma ita bata saniba saboda yanda taga yana jin kai bata zaci zai fito yayi liki ba, daga ita har shi atsaye suke cak babu wanda yake yin rawa sai liki kawai suke yi,

Kasancewar bata son hayaniya yasa taji kanta yafara juyawa, hakanne ma yasata niyyar fita daga filin, tana juyawa taci tuntube da kafarshi nan tatafi zata fadi, cikin sauri ya tareta ta fada jikinsa,

"Ka riketa ku koma sama.." Anty babba tace da shaddad da karfi tana ta faman tikar rawa,

Riketa yayi kamar yanda yayi mata lokacin da zasu shigo cikin hall din, har kan kujerar da suke zaune ya maida ta ya zaunar sannan shima ya koma ya zauna,

Dafe goshinta tayi saboda ciwon da kanta ke yimata, ita dai kawai tana zaune ne awurin amma bawai dadin zaman takeji ba,gashi duk ta takura ko yaya tayi motsi jin jikinta take acikin na shaddad,

Bayan angama cashewa ne aka kira amarya da ango domin yanka cake, tashi suka yi suka sauka zuwa inda cake din yake suka yanka ya dauka ya bata a baki itama ta dauka ta bashi bayan ta dan rissina,

Fuskarshi babu yabo babu fallasa yake gudanar da komai, haka taron yaci ya watse,

Karfe 10:30 aka gama dinner din aka fito domin tafiya,yana rikeda ita ajikinsa har wurin motar da takawosu,har zata shiga anty babba tazo tace,

"Ba a wannan motar zata koma ba, kar ta shiga tazo tare da ita zamu tafi, kai kaje kawai.."

Sakin baki yayi yana yiwa anty babba kallon mamaki ganin yanda taketa kaffa kaffa da maryama, murmushi yayi yace,

"To shikenan anty sai mun hadu agida"

Saboda yasan dalilin da yasa anty ta hanashi tafiya tareda maryaman tunani take ko zai yimata wani abu bayan itace bata saniba amma shi babu wannan acikin tsarinsa,

Gaban motar ya shiga sulaiman yaja suka tafi,

"Wallahi Navy kayi sa'ar mata, matarka masha Allah kyakkyawa babu wanda zai ganta yazaci tayi wadannan shekarun.."

Shiru shaddad yayi bai tankawa sulaiman ba saboda yasan shi sulaiman din bai san wacece maryama ba shiyasa amma shi dayake yasan wacece maryama sam kyawunta baya rudarsa.

  Abangaren maryama kuwa da ciwon kai takoma gida saboda hayaniyar wurin dinner dinnan,

Suna zuwa gida khairat ta zuba mata ruwan wanka acikin dakin hajiya, ganin babu kowa acikin dakin yasa maryama zuwa ta shiga wankan, lokacin data fito khairat na zaune da food flask agabanta tana jiran fitowarta,

"Adda maryama wai me yaya navy yake fada miki lokacin da ya rikeki acikin mota ya hanaki fitowa, nasan koma dai menene ba abu mai dadi yake fada miki ba.."

"Ba wani abu bane khairat, wai sarkar da nasa akafata yace sai nacire saboda kar mutane suyi min mummunar fahimta, nikuwa banga laifin sarka akafa ba saboda wasu kwalliya ce kawai kesasu sakawa bawai wani abuba.."

"Hakane adda maryam, ai naga kun dade ne baku fito ba shiyasa"

Murmushi maryama tayi ta zauna agefen gado tafara shafa mai marar maiko sama sama....




*_Ummi Shatu_*
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   *_36_*



  ~~~Dak'yar maryama ta iya tsakurar abincin da khairat ta kawo mata taci ta nemi wuri ta kwanta, tun daga wannan lokaci bata sake ganin shaddad ba, hajiyarshi kuwa sai nan nan take da ita cikin so da kauna domin tana tsananin son maryama,

Kwanansu biyu suka shirya aka yiwa hajiya sallama suka tafi Lagos, gidan Dada aka fara kai maryama nan suka kule a daki Dada yana yimata nasiha akan tayi kokari tayiwa mijinta biyayya sannan ta kasance mai rike sirrinta,

Kuka maryama tasha shi kamar ranta zai fita, dakyar anty maijidda ta samu ta banbareta daga jikin dada, shi kanshi dadan shima saida ya goge kwalla saboda rabuwar da zaiyi da tilon yar tashi,

Kai tsaye gidanta aka wuce da ita dama shi shaddad ya rigasu tahowa shida su anty Zainab wadanda suka yi jere suka shirya gidan wasu kayanma basu gama shiryasu ba sai gobe,

"Wallahi ban so zamu kwana agidan nan ba naso mubawa yaran nan wuri su sakata su wala suci amarcinsu" anty babba tafada tana kokarin zama agefen gadon maryama saboda bazai yiyu su tafi yanzu ba dole sai dai su kwana tunda dare yayi,

"Babu komai ai iya yaune kadai gobe iyanzu mun dade da bar musu gidansu"

Anty maijidda tabata amsa, ita dai maryama tana kwance tana jinsu amma har ga Allah har tafara jin tsoron tafiyarsu domin tasan zama zatayi irin zaman k'unci kamar yadda shaddad yayi mata albishir,

Dayake agajiye take babu bata lokaci bacci ya dauketa tabar su anty maijidda sunata faman hayaniyarsu suna hira ba ita ta tashiba sai da gari yawaye,

Wanka tayi ta shirya cikin wata dakakkiyar shadda light pink dinkin riga da skirt ne,daga rigar har skirt din sunyi mutukar amsar jikinta, lokacin da ta fito tasamu har su anty maijidda sun gyara mata gidan sun shirya sauran kayan da suka rage ba ajera ba sannan sun turare gidan da turaren wuta mai kamshin gaske ga abinci nan kuma fal cikin kuloli wanda Dada yayi order aka kawo musu daga wani hotel,

Ruwan tea kawai maryama ta iya sha daga nan bata kara iya cin komai ba har saida anty maijidda ta zo ta tisata agaba sannan ta danci faten doya dan kadan,

12 narana nayi su anty maijidda suka fara shirin tafiya ai nan da nan maryama idonta ya kada yayi jajur kafin wani lokaci har tafara kuka, ita kanta anty maijidda itama kukan take ita dasu khairat babu mai rarrashin wani ahaka suka kammala shiryawa suka tafi suka barta ita kadai sai faman kuka take, gashi wani abin karin bacin ranma unguwar barikice babu mai shigar mata,haka tayi kukanta tagama babu mai rarrashinta, mikewa tayi ta kwanta akan doguwar kujera saboda ciwon da kanta yake mata daga nan bacci ya kwasheta ba ita ta tashiba sai da misalin karfe 2 saura yan mintuna,

Bedroom dinta ta shiga tayi salla ta sake yin wanka ta shirya cikin doguwar riga ta material kalarsa purple, ta fito, dakin dake kusa da ita ta leka wanda su anty babba suka kwana aciki nan ta ganshi shima ashirye da kaya kamar nata sai dai kawai kalar kayan sun banbanta,nan tayita bin ko ina nagidan da kallo domin ba karamin kudi Dada ya kashe mata ba wurin zuba mata furnitures hadaddu,

Daya bedroom din dake can gefe daya tanufa domin dama three bedrooms ne acikin gidan, ahankali ta bude ta shiga daga ganin tsarin dakin tasan shine na shaddad saboda ga kayanshi nan aciki sannan ga uniform dinshi nan shima akan gado, karasawa tayi ta debi uniform din ta ninkesu tasaka cikin drewar ta fita,

Falo ta koma shiru ta zauna, daga karshe ta tashi ta hada kayan kallo ta kunna ta kamo tashar mbc action nan taji dadi saboda suna nuna wani american film true blood a lokacin,

Tana kwance tana kallon taji an bude kofa anshigo, kanta ta daga ta leka, shaddad tagani ya shigo yana sanye da kananan kaya,

"Sannu da zuwa.."

Tafada tareda kokarin tashi zaune saboda ita rabon da ta ganshi tun ranar dinner dinsu,

"Yawwa" shine kawai abinda yace ya wuce cikin dakinshi,

Kitchen ta shiga ta zubo masa abinci ta kai kan table ta ajiye tana jiran fitowarsa amma shiru shiru bai fitoba ganin haka yasata tashi tabishi cikin dakin, kwance ta ganshi yana bacci dan haka ta juya takoma falo taci gaba da zama,

Har karfe hudu tayi shaddad bai fitoba, tana zaune a falo akan sallaya bayan ta idar da salla sai gashi ya fito, ganin zai fice yasata dakatar dashi,

"Navy ga abincinka nan akan table.."

"Kidaina raba abincinki da ni saboda baci zanyi ba"

Wannan shine kawai amsar da ya bata yasaka kai ya fice, da kallo tabishi har yafice,

Tagumi ta rafka tafara tunanin irin zaman da zasuyi dashi....




*_Ummi Shatu_*
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    *_37_*


~~~Zaman kad'aici maryama taci gaba dayi har dare yayi, nan kuma taji zaman yafara damunta,daki takoma tayi wanka tayi shirin bacci cikin wata hadaddiyar doguwar rigar bacci ash colour, kwanciya tayi tana jin shaddad ya dawo, a falo ya yada zango ya kunna kallo,

Ahankali ta lab'ab'a ta lek'ashi nan ta ganshi zaune yana kallo komawa tayi ta kwanta saboda tasan dama babu abinda zai shigo dashi dakinta daga karshe dai har bacci ya kwasheta bata san lokacin da yabar falon ba.

   Misalin karfe 8 tafito bayan tasha kwalliya cikin dark purple din shadda dinkin riga da skirt, kitchen ta shiga nan taga buhun semovita guda daya sai ko kayan tea,mamaki ne ya kamata saboda tasan sai da mahaifinta ya cika mata store da duk wani abu wanda zata bukata, hatta chocolate da biscuits saida ya hado mata dasu saboda yasan tana yawan mu'amula dasu,

Dakin shaddad ta nufa lokacin data shiga yana zaune a bakin gado yana gyara sumar kanshi jikinshi sanye da uniform da alama fita zaiyi,

"Ina kwana?" Ta dan rissina tana gaidashi,

"Lafiya" ya amsa a takaice,

"Navy nace ko mukullin store yana hannunka?"

"Meya faru?"

"Zan dora girki ne"

"Baki ga wasu kaya awaje ba?"

"Nagani"

"To sune iya abinda zaki rinka dafawa kina ci.."

"Garin tuwo ne fa kawai sai lipton da sugar.."

"Ehh sufa, ko tuwo ba abinci bane?" Ya tambayeta yana kallonta saboda yadade da sanin babu abinda ta tsana irin tuwo dan lokacin da yana zuwa gidansu yana jinta tana yiwa kuku masifa duk ranar da taga ya dafa tuwo,

Bata kara magana ba ta fita zuwa kitchen ta shiga ta dora ruwan zafi,

"Lallai yaron nan mugune, wato nufinshi tuwo shine abincina kullum kenan? Tab"

Tafada ahankali,

Tea kawai ta hada ta fito kafin fitowarta har shaddad ya fita haka ta zauna shiru bayan tasha tea din, waya tayi ta kira blessing akan tazo, nan blessing ta tattaro kayanta ta taho, adakin kusa da na maryama ta ajiye kayanta ta fara dan shasshare gidan da goggeshi,daga nan ta shiga kitchen ta yi musu tuwo miyar kubewa, ita dai maryama da yake ta tsani tuwo baifi lauma biyar tayiba ta dauraye hannunta.

  Suna falo zaune da yamma suna hira ita maryama har ta danji sanyi saboda zuwan blessing, shaddad ne ya dawo yana shigowa ya tsaya yana kallon blessing wacce ke zaune a kasa ita kuma maryama tana kan kujera tana yin game a laptop dinta,

"Ke mekika zo yi agidan nan?"

"Anty ce ta kirani tace nazo zan rinka tayata aiki"

"To ba agidan nan ba, baki da wurin zama agidan nan, aikin gidan nan ita zata rinka yin kayanta idan kuma dole ne sai kinyi mata aikin to sai dai ta tattara ku koma gidansu sai kuje can kici gaba da yimata aikin..." Yana kaiwa nan ya wuce cikin dakinshi,

Ganin idon blessing yayi rau rau zatayi kuka yasa maryama katseta,

"Babu komai blessing ai ba rabuwa muka yiba muna tare, dauko kayanki ki koma gida, bari na dauko miki kudin okada"

Duk da abin yayiwa maryama ciwo amma haka ta danne bata nuna ba sannan tasan shaddad yayi mata hakane saboda ya kuntatawa rayuwarta domin baya son taji dadin zaman gidansa,

1000 ta daukowa blessing ta bata ta tafi tana matsar kwalla, komawa falo maryama tayi ta zauna tana tuna abinda shaddad ke shirin yimata, nafarko ya hanata aiki, ya kulle store ya boye mukullin sannan gashi yanzu ya hanata zama da yar aiki yace itace zata yi aikin gidan gaba daya.

  Tun daga ranar maryama ta shiga damuwa kafin sati har ta rame saboda bata cin abinci domin abincin tuwone ita kuma bata so gashi ya hanata siyo kayan abinci yace wallahi muddin yaga ta siyo koda indomie ne sai ya dauki mataki, dan haka ta hakura bata siyo komai ba bawai dan bata da kudiba sai dan hanawar da shaddad yayi, kullum cikin shan ruwan Lipton take ga aikin gida wanda bata saba ba jikinta ma bai sababa, ga zaman kadaici nan abu yataru yayi mata yawa, sanin idan taci gaba da damuwa zata iya kamuwa da hawan jini yasa tayiwa blessing waya ta shiga kasuwa ta kwaso mata English novels kala kala ta kawo mata, kullum aikin kenan daga kallo sai karatun novel, girki kuwa ba tayi sai ta gadama saboda shima shaddad din baci yakeba idan yana so da kansa yake shiga kitchen ya yi tuwonshi, wannan abu ba karamin damun maryama yakeba saboda tsakaninta da shaddad sai kace wasu kishiyoyi bazai ci abincinta ba bazai yimata doguwar magana ba, babu sakin fuska babu magana mai dadi, da haka suka shafe wata daya cis da aurensu.

  Yauma kamar kullum tana zaune a falo tana karanta wani novel mai suna sameer & sameera khairat ta kirata, dauka tayi tana murmushi,

"Adda Maryam ko kina wurin aiki ne?"

"Wanne aiki kuma khairat bayan yayanki ya hana, ai yace shi baya son aiki"

"Ya hana? Wai yanzu agida kike zaune?" Khairat ta fada cikin tsananin mamaki,

"To ya zanyi khairat, tunda yace bazanyi ba"

"Lallai to Allah ya rufa asiri"

"Amin khairat nagode agaida su anty"

Katse wayar tayi taci gaba da karanta novel dinta, ita kuwa khairat tana kashe wayar ta fada dakin hajiya domin dama tana Kaduna bata koma abuja ba,

"Hajiya kinji wai Yaya Navy ya hana adda Maryam zuwa aiki, kiji mugu"

"Mugun gaske kuwa autata, bani wayata in kirashi in tsigaleshi,in banda ma aure daga Allah yake shi ya isa yaje neman auren wannan yarinyar har abashi? Fitinannen yaro mai shegen taurin kan tsiya,bari na kirashi yanzu na wankeshi"

"Wallahi kam hajiya karki raga masa kiyi masa kaca kaca" khairat tafada cikin zuga tana mikawa hajiya wayarta,

Shaddad yana headquarter dinsu hajiya ta kirashi yana dauka yaji tace,

"Sannu kasaitaccen maigida,namiji mai cikakken iko, kai mazaje ka fita daga idona inrufe, meyasa ka hana matarka komawa aiki? Saboda mugunta ko me? To wallahi ban yarda ba indai na isa to gobe goben nan tafara zuwa wurin aikinta,aikin ai rufin asirinka ne idan baka saniba tunda idan tana dashi basai ta tambayeka ba, kana jina?"

"Ina jinki hajiya"

"Yawwa kaji dai nafada maka lallai lallai gobe kabarta takoma aikinta saboda dama dashi kaganta tun kafin ka aureta,idan kuma mugunta ce tasaka kake kokarin hanata aiki to wallahi baka isaba,ni nan ina mai baka umarni da kabarta taci gaba da zuwa aikinta"

"To hajiya"

Katse wayar yayi cikeda takaici, wato ma kararshi takai wurin hajiya kenan?, ko office bai komaba ya nufi gida, tana zaune a falo daga ita sai wata yar half best ta cire rigar jikinta domin bata taba zaton zai dawo yanzu ba, karatun novel take ta ajiye ta kwanta tafara bacci,k'afarshi yasa ya bugi tata,

"Ke kikayi wa hajiya waya kika fada mata cewar nahanaki zuwa aiki ko?"

Taji muryar shaddad sama sama cikin bacci, bude idonta tayi ta tashi tana kallonsa,

Sake maimaita abinda yafada da farko yayi,

Girgiza masa kai tayi "wallahi ni bamu taba yin waya da hajiya bama, sai dai idan khairat ce ta fada mata"

"To koma dai menene hajiya tace sai kinyi aiki, kuma naji nayarda zaki koma aikinki gobe amma kisani,

Wallahi wallahi duk ranar da na kamaki kina abinda bai gamsheniba da abokan aikinki wallahi abakin aurenki, daga ranar nagama aurenki,

Ke ko ganinki nayi a office din daya daga cikinsu ko kuma su naga wani a office dinki to wallahi aurenki kika yiwa saboda nadade da sanin akwai mummunar alaka tsakaninki dasu tunda kun saba shek'e ayarku acan..,

Sannan kisani shigar da kikeyi ada idan zaki fita to yanzu baki isa kinyi irinta agidan nan ba dan haka ki tanadi kayan fita unguwa.."

Wuceta yayi fuuuhhh ya nufi dakinsa, ajiyar zuciya ta saki, ita sai yanzu ma ta kula da babu riga ajikinta ta manta, duk da wadannan dokokin da ya kafa mata tasan dai idan ta fita din zata ji dan sanyi sabanin da datake zaune agida....







*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment