Thursday 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 32,33,34

[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Kuna ina? Aminiyata ta k'warai cwt Kausar luv, and my besty Pherty Xarah, idan kuna kusa to ga shafinku ummi shatunku ta baku domin jin dadinku..._



   *_32_*

aishaummi.blogspot.com


   ~~~Haka Shaddad ya shirya ya tafi cikin bacin rai, aranar da yaje aranar yagama komai yawuce masaukinsa, yana kwanciya ko gama hutawa baiyi ba hajiya ta kirashi awaya,

Yana dauka yaji tafara fadin,

"Lallai lallai kaje wajen amaryarka ku gaisa kafin kadawo, kajini ko mazaje?"

"Ehhh hajiya naji.." Yafada yana jin wani irin kunci yana shiga zuciyarsa,

"Yawwa idan kaje kace ina gaisheta"

"To zataji"

Daga haka ya kashe wayar cikeda bacin rai saboda shi sam baya son wannan auren na maryama domin yana ganin kamar wata wahala ce zai tsunduma kansa aciki,

"Nidai kawai sangartacciya zan aura, yarinyar da babu abinda ta iya sai shan cyrup da zuwa club da bibiyar maza wai kuma yanzu azo ace itace matata, kai gaskiya nidai wallahi ba akyauta min ba,yarinyar nan babu abinda ta iya, ko shara bata iyaba bare girki"

Yafada afili yana cizon leb'e amma yasawa ransa cewar shi babu wani gidansu maryama dai zaije kawai dama ya amsawa hajiya da to ne saboda gudun bacin ranta.

   Abangaren maryama kuwa tana can sun fara tunkurar shirin biki itada Dada domin har Dada yayi order akawo furnitures din da za akaiwa maryama gidanta daga kasar Italy,

Ranar alhamis da safe su anty maijidda da anty zainab suka zo gidan dauke da kaya niki niki wanda sai sojoji ne ma suke binsu da akwatunan,

Maryama tana zaune afalo da filet a hannunta tana cin soyeyyen plantain ga waya makale a kunnenta suna hira da dr fahad sai ga su anty maijidda sun shigo, ajiye wayar tayi ko tsayawa kashewa batayi ba ta tafi da gudu ta rungumesu,

"Yata kayanki muka zo kawo miki"

Anty zainab tace tana ajiye kit din dake hannunta,

"To anty zainab kuma baku barinshi anan idan nazo sai nagani"

"To uwar yan hankali ai akawowa dadan naki yagani ko?"

Anty maijidda tafada tana yaye mayafin dake kanta saboda zafi,

"To anty ai mantawa nayi"

Tafada tana bin akwatinan da kallo saboda sunyi mutukar daukar hankalinta gashi best colour dinta aka samu wato pink and blue,

Gaban akwatin ta karasa tana shafashi saboda ganin hoton butterfly ajikin mirfin daga sama,

"Wowwww,anty wadannan akwatinan sun yimin kyau"

"To ai dama nakine" inji anty zainab,

"Yata albishirinki"

Anty maijidda tafada tana murmushi,

"Goro anty.."

"Me zaki bani tukwici"

"Idan labarin mai dadine anty zan baki salaryna na 1 month"

"Nawa kike karba per month?"

"Anty dubu dari bakwai da hamsin ne kacal"

"Ke yar nan ashe kudi kika tara bamu saniba, wannan uban kudin ya kike yi dashi?"

Anty zainab tafada tana zazzare ido dan tsananin mamaki,

"Wallahi anty ginin asibiti ake yimin, so nake nagina asibitin yara nawa na kaina, kuma inada gidan gona.."

"Ato kinyi dabara ai hakan yayi kyau"

Anty zainab tafada tana murmushi,

"Albashinki na wata yayi min yawa maryama amma dai dole kibani tukwici tunda har nakawo miki kayan lefen shaddad gidan nan.."

Mikewa tsaye maryama tayi, "anty wanne shaddad kuma?"

"Wanda dai kika sani, shaddad dinki, Navy.."

"Wayyo anty maijidda tsokanar har takai haka"

"Ke idan zaki ware ki ware babu wani tsokana wallahi dagaske ne shaddad shi zaki aura shine ya kawo miki wannan kayan"

"Alhamdulillah.." Shine kawai abinda maryama tafada ta fadi tayi sujjada tana murmushi, kallon kayan jikinta anty maijidda tayi daga ita sai farar body hug da jeans ta tattare kafar wandon sai kace wata yar kokawa,

"To yanzu dai ciwo ya kare, ankusa aje gidan shaddad ayita tsukewa da kananan kaya tunda kedai bakya kaunar kayan hausawa"

"Ai anty ni wallahi bana jin dadin kaya indai ba doguwar rigane ko riga da wando ba, ni kwata kwata ma bana son wasu kaya inba english wears ba.."

"Zaki saka da kyau ai" anty zainab tace da ita,

Blessing ce tafito hannunta rikeda faranti takawo gabansu ta dire,

"Woww anty kayan aurenki ne? Ni inama in samu quarter din wannan da naji dadi.."

"Kayanta ne blessing zauna kigani"

Anty maijidda tafada tana tsiyayar juice acikin cup,

"Kema kije kiga kayan lefenki yarinya"

Anty zainab tace da maryama.

Matsawa gaban kayan maryama tayi suka fara kallo itada blessing,duk abinda blessing ta daga sai kaji tana cewa,

"Woww anty wannan zai yi miki kyau.."

"Kema za akawo miki irinshi wata rana blessing ai tunda zanyi aure to kowa ma zaiyi.." Maryama tafada tana murmushi,

Da haka suka gama kallon uban tulin kayan wanda sai hakura ma sukayi basu iya kallo gaba daya ba, ko tashi daga wurin basuyi ba Dada ya shigo yana rikeda sandar da yake dan dogarawa da ita duk lokacin da ciwon kafarshi ya tashi,

"A'a kayan maman nawane suka sauka.."

Dada yace yana murmushi,

"Ga kaya nan kam mun kawo" inji anty maijidda,

Zama shima dadan yayi blessing tafara daga masa kayan yana gani sai sanya albarka yake,ita dai maryama tashi tayi ta shiga kitchen ta dorawa su anty maijidda abinci, zuciyarta tana cikeda tarin farin ciki wanda ba zata iya kwatantashi ba sai dai kuma tana jimamin irin zaman da zatayi da shaddad kafin ta samu hankalinsa ya dawo gareta ya fara kaunarta...

*_Ummi A'isha_*
[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Gaisuwa mai yawa ga antyn amarya, antyn ummi Shatu wato anty maijidda musa.._


    *_33_*

~~~Kwanan shaddad 5 a Lagos bai tafi Kaduna ba har sai da yagama dukkan abubuwan da suka kamata sannan ya nemi hutun sati biyu saboda bikinsa,hatta mukullin gidan da zai zauna sai da ya karba, wasu sabbin gidajene masu dakunan bacci guda uku da babban falo guda daya sai kitchen da store, a unguwar Victoria island yake shima na sojoji ne aka gina musu musamman,

Aranar da yagama komai yayi tafiyarsa Kaduna bai ko nemi ganin maryama ba balle yaje inda take,

Lokacin da yaje gida tisashi da tambaya hajiya tayi kan ya yabaro maryama, shikuwa kawai amsawa yake da tana nan lafiya, saboda yasan idan tagane baijeba zai sha fada.

  Maryama kuwa daren ranar da su anty maijidda suka zo kasa bacci tayi dan tsananin murna nan ta kira khairat tana yi mata godiyar ceton rayuwarta da tayi,

Kusan kwanan zaune suka yi dasu anty maijidda suna hira,kwanansu biyar agidan suka tattara har maryaman suka nufi abuja saboda suna son suje su gyarata, za ayi mata gyaran jiki da sauran abubuwan da suka kamata, sallama tayiwa dada da sauran mutanen dake gidan domin idan tatafi bazata sake dawowa gidanba sai ranar da za akaita gidan mijinta aranar ne za akawota dan tayiwa dada sallama,

Tattarawa sukayi suka tafi ita dasu anty maijidda zuwa abuja, suna zuwa kuma ta shiga busy domin bikin saura kwana biyar kacal, shagunan dinki sukaje takai dunkunanta sannan suka shiga kasuwa suka dan iyo siyayyar da baza arasa domin ashe gaba daya anty maijidda tagama siya mata kayan kitchen da sauran kayan kwalliyar falo zuwa bedroom da sauransu,

Suna komawa gida anty maijidda ta kira hajiya fiddausi Sodangi kwararriya wurin gyara amare tazo takanas tun daga garin borno domin gyara maryama,tana zuwa tafara tsumata da kayan gyara sahihi dan borno,

Nan aka fara dirjar fatarta ana shafeta da kayan hadin gyaran fata, cikin kwana biyu kacal maryama ta juye ta zama balarabiya,sai dai tulin abubuwan dasu anty maijidda da hajiya sodangi suke dura mata amai yake sata, daga tasha sai amai gashi sam bata iya cin abinci kwata kwata,

Kallon anty maijidda tayi sannan ta kalli cup din dake hannunta cikeda wani abu mai kamada madara,take tafara jin zuciyarta tana tashi,

"Anty dan Allah kiyi hakuri kibar abin nan wallahi amai karninsa yake sani.."

"Sai fa kinsha garama ki daina hadani da Allah, ko kin amayar ai dole wani zai zauna acikinki.."

Anty maijidda tafada tana mika mata cup din,

"Anty zainab,anty zainab.."  Maryama tafara kwalawa anty zee kira wai ko zatazo ta ceceta, amma koda anty zainab din ta shigo itama rike take da farfesun yan shila acikin plate ta kawo mata, haka suka tisata agaba sai da ta cinye sannan ta shanye wannan abun, kullum haka suke yimata tun tana yin amai har ta daina.

A bangaren shaddad kuwa shi babu wani shiri da yake yi, su hajiya ne kawai ke yin shirinsu sai sauran jama'ar gidan amma shi sam babu abinda ya d'ad'a shi da k'asa da wannan bikin,

Ita kuwa hajiya tsabar soyayya cewa tayi bayan an daura aure akawo mata maryama tayi kwana biyu sannan su tafi Lagos itada shaddad din.

   Tun ranar laraba gidan anty maijidda ya dinke da dangi da yan uwa harda abokan arziki, maryama tasha kunshi da gyaran gashi tafito tayi kyau sosai,fatar nan tata kamar ta jarirai domin ta yan hutuce gashi kuma ta had'u da gyara na musamman,

Aranar sulaiman abokin shaddad yazo kawo mata kudaden da zata yi hidima dasu kamar yadda ake bawa kowacce amarya da kawayenta, to ita bata da kawayen ma, bata da wata kawa ko daya komai nata ita kadai take yi,

Lokacin data fita sulaiman yaganta sakin baki yayi ya tsaya yana kallonta, shi mamaki yake da ganin wautar shaddad da yaketa ikirarin baya sonta, shikuwa sulaiman sam baiga laifinta ba asalima babu wanda zai ganta yace takai wadannan shekarun gata kyakkyawar gaske,

Gaisawa suka yi yabata kudin ya tafi, itama cikin gida ta koma tana cike da murnar ashe dai shaddad yana sane da ita.

  Ranar alhamis da yamma aka yi kamun maryama awani babban hall dake cikin Real Hotel, kamun yayi kyau sosai kuma ya kayatar, karfe shida aka gama aka watse kowa ya koma gidansa, anty babba yayar shaddad suma sun halarci wurin itada sauran dangi,

Washe gari ranar juma'a aka daura auren SHADDAD A SADIQ da DR  MARYAMA FARUQ BELLO akan sadaki naira dubu hamsin agarin jimeta, kuma aranar su anty maijidda suka shirya suka tafi Kaduna tareda amarya,

Suna zuwa aka karbesu cikin mutunci da girmamawa, hajiya kuwa kamar zata karawa maryama numfashi dan tsananin so, jin anty maijidda ma tace bata ci abinci ba haka ta zauna ta bata abincin tanayi tana lallabata da haka har sai da ta koshi,

Sosai itama maryaman taji tana kaunar mahaifiyar shaddad domin itama tana tsananin sonta gashi dadin dadawa ma ashe sunansu daya itama hajiyan sunanta hajiya maryam,

Dare yanayi misalin karfe 8 aka fara shirin tafiya dinner wacce sisters din shaddad suka shirya, nan aka rangadawa amarya kwalliya aka shiryata tafito cikin doguwar wedding gown pink and blue colour, tasha head shima pink, komai dai pink,

Gabanta ne ya fadi lokacin da anty babba ta kaita gaban motar da shaddad ke ciki yana zaune agidan baya saboda rabonta dashi tun ranar da yaje abuja, shikuwa shaddad ta cikin glass din window din motar ya zuba mata ido yana kallonta dan kyau kam tayi kyau shi kawai matsalar baya sonta ne bata cikin irin tsarin matan da yake son aura,

Bude mata kofar motar anty babba tayi ta shiga ta zauna, yana zaune yasha farar shadda sai kyalli da maiko take daga gani an kashe naira wurin siyanta...

*_Ummi Shatu_*🏻
[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   *_34_*

aishaummi.blogspot.com


~~~Shima shaddad din kallonta yake yi ta gefen idonshi yana ganin irin dukiyar da aka kashe ajikinta domin bayaga tsadadden materia din da tasa wasu gwala gwalai ne aka zuba mata ajikinta tun daga kan sarkar da ke wuyanta wanda Allah ne kadai yasan adadin kudinta zuwa kan abubuwan hannunta da agogo da zobbuna sannan ga wata yar karamar barima akan hancinta barimar tayi mata mutukar kyau kamar indiya haka ta fito, ko yaya ta juya kyalli da walwali take yi wal wal,

"Ina yini..." Yaji ta gaisheshi mamaikon ya amsa sai ya matsa kusa da ita nan kamshin turaren da yake addabarshi ya sake karuwa,

Bakinshi yakai saitin kunnenta saboda baya son sulaiman ya jiyo abinda zai fada,

"Congratulations, ina tayaki murnar zama matata tafarko da kiyi, sannan kinyi namijin kokari wajen shiga da fita har kika mallakeni, to ina son nasanar dake abu guda daya,

Kisani kamar yadda kika yi kokarin auren yaro sa'anki to da fatan zaki yi hakurin zama da shi, zama da yaro sa'anki sai kin jure sannan sai kin daure, saboda zanyi mutukar kuntatawa rayuwarki ,zan tsananta miki ko kadan ba zakiji dadin zama daniba saboda dama sai da nafada miki bana sonki bana kaunar zama dake, ke ba irin matan da nakeso bace amma sai da kika nace kika mayance har nakai ga aurenki,

To kinyi nasara kuma kinyi sa'a sannan zakara yabaki sa'a kin aureni sai dai kuma ina mai shawartarki da ki shirya zama dani zama na raba raini, ki shirya zama da sa'anki a matsayin mijinki..."

Shiru yayi sakamakon jin motar ta tsaya har sunzo wurin da za a gudanar da shagalin,

Ita kam maryama duk murnar da take ciki yau sai da gabanta ya fadi hankalinta ya tashi saboda jin kalaman shaddad, banda cin fuskar da yayi mata harda bakaken maganganu ya fada mata,

Bude kofar barin da take akayi domin ta fito har ta zira kafarta daya zata fita idonshi ya hango masa sarkar gold din dake daure akafarta ta hagu,

Rikota yayi ya dawo da ita cikin motar ya janyo kofa ya rufe,

"Cire wannan sarkar ta kafarki, ko baki daura ba dama nasan kina hulda da mata kamar yadda kike yi da maza, basai kin nunawa nawaje koke wacece ba.."

Sunkuyawa kawai maryama tayi batace dashi ko uffan ba ta fara kokarin cire sarkar da take daure a kafarta, tajima a sunkuye amma ta kasa cirewa,

"Kaga taki ciruwa, nakasa.."

Ta dago tana yimishi magana cikin maganarta mai sanyi hadeda shagwaba shagwaba saboda ita tsabar gayu da gatan da ta taso aciki maganarta ma gaba daya ta shagwababbu ce,

A zuciye ya kwaye rigar tata wanda ba kwaurinta kadai ba hatta cinyarta sai da ta bayyana jan kafar yayi wacce ke sanye cikin wani dogon high hill pink colour,yafara kokarin kunce sarkar amma shi dinma dakyar ya iya kuncewa dan sai da sarkar ta wahalar dashi, nan ya dago da sarkar a hannunshi yana dubawa,

Inbanda kyalli babu abinda takeyi domin ta gold ce, akan cinyarta ya cilla mata, nan ta dauka ta saka acikin jakar hannun dake rike a hannunta,

Anty babba ce ta bude kofar motar suka firfito nan tabi shaddad da kallon tuhuma,kasancewar su sun rigasu tahowa sannan tun dazu itama ta karaso tana jiran su fito amma taga shiru har sai yanzu da tayi kundunbala ta bude su,

"Kai shaddad meye hakan? Idan kayi hakurima gobe za akawo maka ita amma nan wurin mutane kazo ka makaleta ka hanata fitowa bayan ga mutane nan sunata faman jiranku"

Shiru shaddad yayi cikeda bacin rai wato ita anty ta zargi ko wani abu ya rike maryama yake yimata kenan, dan karamin tsaki yaja,

"Inma yanzu daga nan can zaku wuce ku kaita ni babu abinda ya dameni" yafadi acikin zuciyarsa,

Ganin maryama nagaba yana baya yasa anty babba dakatar dasu,

"Haba haba ai ba haka akeyi ba"

Janyo shaddad tayi zuwa wurin maryama ta sakala hannunta cikin nashi ta rab'ata da gefen kirjinshi,

"Yawwa kunga yanda akeyi,ai haka ya kamata kuyi tunda an rigada an daura muku aure da ba adaura bane shine, kai shaddad ka ruketa fa sosai saboda wannan dogon takalmin nata wahalar tafiyane dashi idanma tazo da tsautsayi zata iya faduwa.."

Shi dai bai tsaya jiran jin karshen zancen anty ba ya, ya rike maryama ba wai dan yasoba, tana rab'e a kirjinshi ya ziro daya hannunshi ta bayanta ya rike kugunta, karshen kyau ma'auran sunyi kuma sun hadu duk wanda ya kallesu bazai iya hakuri ba sai yaji ya sake maimaitawa gwaurayen wurin kuwa take suka fara burin suma kasancewa a irin wannan rana,

Suna shiga cikin hall din kowa da kowa ya mike tsaye, su anty maijidda da anty babba na biye dasu har suka hau kan dining table,

Sai da shaddad yaje ya zaunar da maryama akan kujera sannan shima ya zagaya ya zauna a kusa da ita domin wata kujerace ta alfarma aka ajiye musu wadda tasha decoration,

Yanayin kujerar yasa dole sai da suka matsi juna domin bata da fadi sosai girmanta bai kai na two sitter ba dan haka dole manne suke da juna,

"Ina son kisani na aureki ne kawai domin yin biyayya ga mahaifiyata bawai dan so ba saboda ko sau daya ban taba jin sonki acikin zuciyata ba kuma nasan bazan sokin ba har abada domin inada wacce nake so yarinya mai hankali,

Mai nutsuwa mai addini, mai kamun kai, sannan gata yarinya karama danya shakaf yar shekara goma sha takwas ba irinki ba wacce ta tara shekaru ba aure..."

Duk da taji zafin maganganunsa sai bata ko tanka masa ba saboda nasihar da anty maijidda tayi mata tun dadewa ita take tunawa inda anty maijidda take cemata,

"Maryama zaki samu shaddad kuma zaki aureshi amma sai kinyi hakuri sai kin jure, ko bayan aurenku dashi dole sai kinyi hakurin zama dashi har zuwa lokacin da Allah zai karkato miki da hankalinsa gareki.."

To duk lokacin data tuna wannan maganar ta anty maijidda sai taji sanyi taji cewar zata iya jure duk wasu miyagun maganganun da zai jefeta dasu,

"Kuma ina so ki sani, wallahi zaman gidana zaman ukuba ne agareki.."

Ta jiyo muryarsa a saitin kunnenta, kai idan ba jin abinda yake fada kayiba zaka zaci wasu kalaman soyayya yake fada mata ko wasu kalamai masu sanyaya zuciyar masoya saboda irin yanda sukayi zaman, hatta cinyarta guda daya akan tashi take, gaba daya acikin jikinsa take shikuma yasa hannushi guda daya ya zagayeta, gashi sai saitin kunnenta yake kai kanshi, dan kamshi kam yashaki kamshi har ya cika masa ciki domin tako ina kamshi ne yake ambaliya daga jikin maryama to amma shi shaddad sam ba kamshin ne sababin kai kanshi jikinta ba asalima yana yin hakane domin ya kuntata mata.....



   _Fans ku taya Ummi shatunku da addu'a mura nakeyi duk hancina atoshe, muryata adashe.. Luvs you all._



*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment