Friday 23 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 50,51

[5/25, 9:20 PM] Ommee A'esherh: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_




  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

     _Sako ga autar hajiya, in banda abinki auta ai ni ban hanaki mijina ba,matsalar kawai yace daga ni babu k'ari.._

     _*50*_


~~~Ko minti biyu batayi da kwanciya ba taji shigowarshi, tsugunnawa yayi a saitin kanta ya dafata yana bin kyakkyawar rigar baccinta da kallo,

"Bacci zakiyi?"

Kai ta daga masa saboda idanuwanta har rufewa suke yi saboda tsabar bacci, "to yi addu'a"

"Nayi" ta bashi amsa batare data bude idonta ba,yana tsugunnen har bacci yayi gaba da maryama,ya jima yana tsugunne yana kallonta yana ta faman shafa kyakkyawan sajen dake fuskarta wanda ya tafi ya lullube goshinta, ya jima ahaka kafin ya tashi ya fita, lokacin da ya fita har su anty maijidda sunyi bacci itada anty babba.

   Washe gari ya kama saura kwana biyu suna, tun sassafe maryama tayi wanka ta shirya saboda yau za ayi mata kunshi da saloon, wani leshi ta saka baki mai adon ja ajiki, kyawun da tayi ba kadan bane, gashi tako ina kamshi ne yake fita daga jikinta,

Tana rikeda jaririnta a hannu tace da anty maijidda,

"Anty bari nakai boy ya duba dadynshi yayi masa sannu bashida lafiya"

"Sai kun dawo"

Anty maijidda tafada tana kallon anty babba domin jiya da daddare sunga lokacin da taje dakin shaddad sannan shima sunga lokacin da yasake binta dakinta,

Fita tayi da jaririn akan kafadarta ta shiga dakin shaddad, yana tsaye agaban mirriro yana zira rigarshi, bakar t shirt mai dogon hannu, jaririn ta kwantar taje gaban shaddad ta tsaya tafara balle mishi botir din jikin rigar tana murmushi,

"Ya jikin?"

Hannuwanshi yasaka gaba daya ya zagayeta ya rungumeta,

"Da sauki,ina nu'aima?"

"Tana can tanata bacci bata tashi ba"

"Da ace ta tashi da ta rakani kasuwa, ina son inje in siyo muku duk abubuwan da suka kamata, gashi ma dai banida kudi wallahi.."

Jan hancinshi maryama tayi, "nima kuma ina son zaka kaini saloon anjima idan khairat ta gama yimin kunshi kuma dole zaka biya kudin kunshi da na saloon"

Fuskarshi ya hada da tata yana murmushi,tareda jan hancinta, "ai ko baki fada ba ma dole na nabiya domin matata aka gyara min tasake yin kyau"

Murmushi tayi taja shi suka karasa bakin gado ta dauki jaririn ta dorashi akan cinyarshi, "gashi dama gaisheka yazo yayi"

Tana bashi jaririn ta fita zuwa dakinta bata jima ba sai gata ta dawo rikeda ATM card dinta a hannu, zama tayi a kusa dashi ta mika mishi ATM card din,

"Naji kana cewa baka da kudi, gashi kaje ka ciri duk yanda zaiyi maka.."

Kallonta yayi sai kuma yayi murmushi ya jijjiga kansa,

"Bazan karbi kudinki ba baby, kudin wurina zai isa na siyo muku komai da komai"

Fuska ta bata ta mika masa hannu alamar ya bata jaririn, hanata jaririn yayi ya kwantar dashi agefe yana cewa,

"Muhammad kwanta anan inje in rarrashi mamanka mai daru.."

Sai lokacin tasan Muhammad zai radawa jaririn domin har yau basuyi maganar sunan da zai sakawa yaron ba.

Kusa da ita ya matsa yasa hannuwanshi guda biyu ya tallafe kumatunta,

"Baby menene nayin fushin? Kin san dai bana son bacin ranki.."

Sake daure fuska tayi, "ai dama nadade da sanin baka daukeni a matsayin abokiyar zama ba, baka daukeni a matsayin sirrinka ba, sannan ni ka daina kirana da wani baby, budurwarka da kakeso yar 18 years wacce har kabata number ta dan ta kirani tayi min rashin kunya ita ya kamata ka kira da baby"

Murmushi yayi sai kawai taji ya rungumeta,

"Allah yabaki hakuri, wallahi ke sirrina ce saboda akwai sirrin dake tsakaninmu wanda duk duniya babu wanda ya sanshi sai ubangijin da ya haliccemu, kuma ni ban bawa Amira number ki dan ta kiraki taci miki mutunci ba.."

"To ya akayi tasan shekarata 30 lokacin da ka aureni indai ba kaine ka fada mata ba.."

"Ni nafada mata amma bawai da wani abu nafada ba, haba baby tayaya zanje naci mutuncin iyalina awurin wacce ba iyalina ba? Nifa kawai cewa tayi tana so ku gaisa shine nabata number ki, anan take tambayata wai ta girmeki ko kin girmeta shine nace kin girmeta shekarunmu daya dake... Dan Allah kiyi hakuri"

Shiru tayi domin dama ta dade da hakura amma mamaki takeyi sosai wai yau itace shaddad yake bawa hakuri,

"Kin hakura? Uhm baby nah..?"

Dagowa da kanta tayi tana kallonshi shima itan yake kallo,

"Na hakura amma sai ka tafi da ATM card din nan ka ciri kudin siyayyar da zaka iyo mana"

"Baby bana son in rinka taba miki kudinki.."

"To ai ba tambayata kayiba, nice nayi niyya na baka, haba shaddad nifa kafi haka awurina wallahi duk abinda nake dashi zan iya mallaka maka, nasan abinda kake jin tsoro baka son inyi maka gori watarana, to ka kwantar da hankalinka bazan taba goranta maka ba domin mun zama daya, account dinma da babu wani kudi mai yawa aciki duk ginin asibiti ya lashe kudin..."

Sake rungumeta yayi cikeda kauna, "gashi kuma mijinki talaka ne balle ya kara miki wasu kudin ki karasa ginin.."

Dariya tayi tana shakar kamshin turaren active man dake fita daga jikinshi,

"Ina son mijina ahaka komai babunshi, da mai kudi da talaka duk daga Allah suke"

"Nagode baby Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwarki data yaranki"

Dadine ya ratsata sakamakon addu'ar da taji yayi mata, sakinshi tayi tana kallonsa,

"Zanje saloon saboda wacce take zuwa tayi min agida tatafi garinsu"

"To idan kin shirya sai ki fada min in kaiki"

"Tom, bari nakawo maka breakfast.."

Daukar jaririnta tayi ta fita shaddad yabita da kallo cikeda so da tausayawa irin na masoya,tana fita suka yi kicibus da anty maijidda,

"Nazata ai acan zaku zauna keda jaririn" anty maijidda ta fada tareda karbar jaririn tayi gaba saboda tun dazu yan barka suka zo, kitchen maryama ta wuce ta karbowa shaddad breakfast takoma takai masa,

Zama tayi tafara bashi shima yana bata har suka koshi, tare suka fito tana rikeda farantin kwanukan da suka ci abincin, a falo yasamu su hajiya ya gaisheta sannan ya dauki nu'aima wadda ke zaune tana shan tea.

Zama maryama tayi khairat ta zana mata jan lalle mai kyau, sai da yayi jajur sannan aka cire, nan ta je ta sake yin wanka tana jiran shaddad ya dawo ya kaita wurin saloon domin ya fita da motar tata,

Shaddad bai dawo gidanba sai da mangariba, siyayya ce ya iyo mai yawan gaske duk abinda za a bukata saboda shagalin suna ya siyo shi sannan ya siyo raguna biyu manya,

Shigar musu da kayayyakin da ya siyo yayi cikin kitchen ya wuce dakinsa, mintuna kadan ya fito ya shiga dakin maryama yace ta fito ya kaita saloon din,

Anty maijidda sai fada take tana cewa ahakura da wannan saloon din, ko kwana 7 da haihuwa bata yiba amma har zata fita, hajiya ce tace abarta taje ai yanzu zasu dawo, nan maryama ta dauki hijab ta fita tana tafiya ahankali saboda har lokacin bata gama warwarewa ba,

A mota ta samu shaddad ta shiga,kallonta ya tsaya yi kafin yakamo hannayenta masu taushi wadanda suka sha jan lalle yafara gani,kissing din tafin hannunta yashiga yi dakyar ya saketa ya tashi motar suka tafi cikin gari,

Wani shagon saloon ya kaita ta shiga  tabarshi acikin mota yana jiranta,

Tafi minti 40 kafin ta fito bayan angama yi mata gyaran gashin, zama tayi tana kallon shaddad,

"Allah sarki mijina yi hakuri yau sai wahalar dakai nake yi naki barinka ka huta"

Haske ya kunna acikin motar yana kallonta,

"Karki damu baby ai kinfi haka, muga gyaran kan da akayi miki"

Bude mishi tayi yagani maryama badai gashi ba, domin gashinta har kafadarta yake bakikkirin mai laushi,shafa gashin yayi,

"Nidai nayi dace duk wani abu mai kyau wanda ake bukata awurin mace matata ta mallakeshi, shiyasa babu ruwana da sha'awar na matan waje saboda nasan nima ina dashi agida na"

Murmushi maryama tayi ta mayar da dan kwalinta ta daura ta lulluba hijab dinta ajikinta,

"Banda zuga dai navy.."

"Ba zuga bace baby gaskiya ne, wallahi kina da duk wani abu wanda yake sakani farin ciki shiyasa lokacin da na tafi burtaniya idan kewarki ta dameni surarki kawai nake tunowa sai naji hankalina ya kwanta nasamu nutsuwa, gashi awurin akwai mata kala kala dayake wurin boda ne amma ni ko kadan basu taba burgeni ba saboda nasan inada wacce tafisu acan gida tana jirana ni kadai"

Murmushi maryama tayi ta shafi kumatunsa, "Allah sarki navy ashe dai kaima kayi missing dina wannan lokacin duk da baka sona sannan kana zargina da kula wasu maza awaje"

"Nifa dama najima ina sonki baby, kawai zafin kishine yake damuna idan natuno yanda naganku keda wannan yaron naziru a office dinki yana gyara belt din wandonshi, da yanda kike zuwa guest house wurin manyan mutane sai naga kamar ko akwai abinda suka taba amfana dashi daga jikinki amma ni bana zarginki ko kodan shiyasa ma da nayi tafiyar nan hankalina bai tashiba saboda nasan zaki kula min da kanki.."

"Lokacin da kaga naz yana gyara belt din wandonshi wallahi nice nayi masa fada saboda sai kaga bai daura belt ba kawai yabarta haka wandonshi yana faman sabulewa shine nayi masa magana to yana cikin gyarawa kai kuma ka leko, alh bashir kuma da nake zuwa wurinshi shine yayi min cuku cukun siyan wannan filin da nake gina asibiti na.."

Rungumeta shaddad yayi yana shinshina kanta yana shakar kamshin saloon din da akayi mata,

"Shiyasa annabi (S.A.W) acikin wani hadisi yace kabar abinda kake kokwantonsa izuwa ga wanda baka kokwantonsa, duk yanda ka kai ga ganin mutum mai laifine awurin Allah to karka kuskura ka yanke masa hukunci har sai ka ganshi ido da ido yana aikata laifin, nidai dama nadade da sanin cewar matata tawace ni daya.."

Kwace jikinta tayi tana murmushin dole amma azuciyarta tausayinshi take ji sannan dama tun jimawa ta fahimci cewar yanada tsananin kishi akanta saboda lokacin da basa shiri ya taba ganin text massage awayarta wanda dr fahad ya turo mata cewar yana nan yana jiranta bazaiyi aure ba har ranar da boko haram zasu kashe sojan mijinta sai ya aureta, masifar da shaddad yayi lokacin ba kadan bace har fahad din ya kira awaya agabanta yace masa to ko ya mutu shi bai isa ya auri matarsa ba,koda ma ya aureta to shi bai taka matsayin da ya takaba domin a bazawara ya aureta shikuwa tun tana budurwa yayi rayuwa da ita,

"Wai tunanin me kike yi?" Maganar shaddad ta dawo da ita cikin hayyacinta,

"Tunani nake nabar jaririna agida"

Murmushi yayi yafara driving, "naga alama dai kina ji da wannan jaririn"

"Yana kama da kaine shiyasa naji yafi shiga raina akan nu'aima"

"Nikuma kinga nafi son nu'aima saboda komai nata irin nakine sannan bata wahalar min dake kinyi dogon suma har ana tunanin kin mutu ba.."

Dariya maryama tayi tana kallonsa, cikeda farin ciki suka koma gida.....



*_Ummi Shatu_*
[5/25, 9:20 PM] Ommee A'esherh: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Gaisuwa ga yan haske writers association, Afra bhai,Asmy b Aliyu, Ayusher mohd,Billy galadanchi,faxy fation, Phertymah Xarah,Hajja ce,Kausar luv, Khaleesat hydar,Lilmeerah cute,miss Xoxo,miss billy,Maman Shakur,maman Khadija,Nana diso,Nuceey love, Queen Mimi, Rash kardam and rest....,Allah yakara hada kanmu ina alfahari daku..._

    _*51*_

aishaummi.blogspot.com

~~~Ahaka ranar suna tazo aka gudanar dashi cikin farin ciki da nishadi, yaro yaci suna Muhammad amma zasu kirash da nu'aim,

Aranar da akayi sunan mutane suka fara bajewa basu zauna ba kamar lokacin sunan nu'aima, iya hajiya da anty maijidda ne kawai suka zauna sai anty babba da khairat saboda yan aikace aikacen da za ayi washe garin suna amma su dinma aranar suka ce zasu tafi da zarar sun gama aikin saboda shaddad kiri kiri yanzu yake nuna musu so yake su tafi subarshi daga shi sai matarshi da yaranshi,

Hakance kuwa ta faru washe gari tunda asussuba su anty maijidda suka tashi suka gama soye soyen nama suka gyara gidan sannan suka yi girki, karfe goma na safe har sun gama dukkan abubuwan da zasuyi,

Waya shaddad yayiwa maryama yace yana kiranta, tashi tayi ta fita nan anty maijidda tabita da kallo tace,

"Idanma kunyi hakuri yanzu zamu tafi mu bar muku gidanku"

Dariya anty babba tayi, "ai yaron nan jarababbe ne wallahi daga gani baya barinta ta huta"

"Itama ai dama ta dade da sanin irin mijin data aura dan tun kafin ayi bikin na kora mata jawabi"

Dariya anty babba tasake yi, "to mudai ai yau zamu basu sarari suga filin gidansu"

Maryama na shiga dakin shaddad ta sameshi kishingide agefen gado nu'aima kuma tana jikinsa tana bacci,

"Baby kin san meye? Har baba lami karta zauna tabi su hajiya su tafi Kaduna idan da yiyuwar ta dawo zanje na dawo da ita"

"Haba mazaje har baba lamin ma tafiya zata yi? Aikin zai yimin yawa fa ga yara ga kula dakai sannan ga hidimar gida..."

Mika hannu yayi ya kamota zuwa jikinsa,

"Kema mazajen zaki kirani dashi kamar hajiya?"

Murmushi tayi,  tafara wasa da zobunan gold din dake sanye a yan yatsun hannunta,nu'aima ya gyarawa kwanciyarta ya tashi zaune yana kallon fuskarta, ba karamin kyau tayi ba sannan ga barima ta gold akan hancinta,

Hannunshi yakai kan barimar yafara juyata acikin kofar bular dake kan hancinta, ba karamin kyau hudar hancin tayi mata ba saboda komai tayi yimata kyau yake,

"Idan baba lami tatafi ai gani, zan rinka yimiki duk aikin da kika sani.."

Murmushi tayi ta kalleshii, "karfa ka sake magana daga baya"

"Bazan sakeba.."

Yafada tareda kai bakinshi kan nata,kallonshi tayi tana kokarin tashi, "ka fito fa saboda may be sun gama shiryawa"

Fita tayi ta koma wurinsu anty maijidda wadanda suka kammala shirin tafiya,

"Uhm hajiya dadyn nu'aima yace baba lami ma basai ta zauna ba.."

Kallon anty babba anty maijidda tayi suka hada ido tareda saka dariya a lokaci guda,

"Danme zata tafi, idan ta tafi waye zai rinka tayaki sauran ayyukan gidan?"

Hajiya tafada cikin fada,

"Hajiya babu komai nima zanyi ai"

Fadin haka da maryama tayi yasa hajiya fahimtar cewar itama maryaman tafi son baba lami din tatafi,

"To shikenan sai mu tafi ai inyaso duk lokacin da kuka bukaci yar aikin na samo muku wata"

Shaddad ne ya shigo cikin dakin yana kallon su hajiya, "hajiya idan kun shirya muje na kaiku tasha.."

"Ah mun shirya, ku tashi mu tafi"

Kallon maryama khairat tayi, "adda maryama sai mun sake dawowa suna next year tunda na nu'aima ma last year muka zo gashi yanzu this year mun zo na nu'aim"

Dariya anty babba tayi, "ai kuwa dai wata shekarar ma muna tafe"

Ita dai maryama bata cemusu komai ba saboda hajiya na wurin, drewar din gadonta taje ta dauko kudi sabbi yan 200 rafa guda ta bawa shaddad, "gashi idan ka kaisu kabasu susha ruwa ahanya"

"Ke babu kudin da zamu sake karba duk, wannan hidimar da kikayi mana har sai kin kara da kudi?"

Hajiya tafada bayan ta tashi  tana yafa mayafinta,

"Hajiya danma ban nuna miki kayan data baniba masu kyau wallahi har kala biyar kuma duk bata sakasu sosai ba sai munje gida zaki gani.." Khairat tafada tana murna,

"To angode Allah dai yasaka da alkairi yayi miki albarka maryama, Allah ya raya miki yaranki"

Tafiya suka yi bayan ta rakasu waje, sai da taga tafiyarsu sannan ta koma cikin gidan,wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya ta tsuke sosai cikin riga da wando English wears, rigar pink colour ce mai budadden kirji agaban rigar an rubuta, _love makes heart to beat sweeter.._,sai matsattsen bakin wando wanda ya bayyanar da hips dinta sosai,

Tana tsaye gaban mirror tana taje gashin kanta shaddad ya shigo, tsayawa yayi yana kallonta ta jikin mudubin domin indai ba sani kayiba to idan kaga maryama bazaka taba zaton ta haihu ba,

Zuwa yayi ya rungumeta ya dora kansa akan kafadarta yana kallonta ta jikin mudubin,

"Kinyi kyau sosai.."

Kiss yayi mata a kumatu ya karbi pink colour ribom din hannunta ya daure mata gashin nata yajata suka fita zuwa falo, kwanciya sukayi acikin kujera suka fara yiwa junansu hira irin ta masoya, har shi kanshi shaddad sai da yayi mamakin maryama saboda yanda ta dage tana ta yimasa labarai kala kala wanda ta sani,

Sai da suka fara jiyo kukan nu'aim sannan suka bazama sukaje kai masa agaji.

  Cikin farin ciki da kaunar juna sukayi wunin wannan ranar shaddad kuwa yana gida babu inda yaje, har 12 suka kai suna kallon wani American film a tashar MBC action,

Kashe komai shaddad yayi suka nufi dakinsa, wanka maryama ta shiga yabita cikin toilet din dole sai tare suka yi suka fito suka shirya cikin kayan bacci suka kwanta bayan sun saka nu'aim da nu'aima a tsakiya.

  Karfe 9 nasafe maryama ta tashi nan taga kan gadon babu kowa sai ita kadai, fita tayi nan ta ga ko ina na gidan agyare tsaf anshare anyi mopping dinshi ga turaren wuta yana tashi, hatta nu'aima da nu'aim shaddad yayi musu wanka ya hadawa nu'aima tea tana sha, shi kuma yana kitchen yana soya chips da kwai,

Dakinta ta fada nan dinma ashare agoge sai kamshi yake, hatta toilet din an wankeshi sannan ya tara mata ruwan da zatayi wanka dashi, wanka tayi tana cikeda farin ciki ta fito ta shirya cikin wata hadaddiyar doguwar riga ja mai dan karamin hannu, gashinta kawai ta daure ta fita saboda yunwar da take ji,

Shaddad yana shirya table ta karasa wurinsa,

"Sannu navy gaskiya kasha aiki"

Murmushi yayi, "karki damu baby ai kinfi haka agareni, ni bawanki ne saboda kasancewarki SARAUNIYA,zanyi dukkanin iyawata saboda ganin na hutar dake baki wahala ba"

Kujera ya ja mata ta zauna ya zuba mata breakfast din, tare suka ci suna ciyar da junansu har suka kammala.

  Tun daga ranar kullum kafin maryama ta tashi daga bacci shaddad ya tashi ya gyara gidan sannan ya shirya musu breakfast yayiwa su nu'aima wanka.

  Yau ma tun kafin ta tashi ya gyara gidan yayiwa su nu'aima wanka yana tsaka da shiryata yana yimata kwalliya maryama ta fito ta shiga wanka har ta fito su shaddad basu gama kwalliyar ba, kwalliya tayi ta shirya ta saka wani blue din materia riga da skirt sun kamata sosai saboda yar kibar data kara yi,

"Sweetheart kinyi kyau.." Haka shaddad yaketa fadawa nu'aima bayan ya gama yimata kwalliyar yasaka mata riga yar kanti baka doguwa,

Fushi maryama tayi ta fita tabarsu a dakin ta koma falo ta fara karyawa tana rikeda nu'aim, binta falon shaddad yayi yana murmushi yaje ya rungumeta,

"Menene abin fushin saboda nacewa daughter dina tayi kyau ke ban fada miki ba? Ai ke ba fada zanyi da bakiba nuna miki zanyi ki gani"

Kafin tayi magana ya kama lips dinta sun jima ahaka yana nuna mata yanda tayi kyau din sai da kyar tasamu ta kwace bakinta,

"Gaskiya kadaina wannan aikin gidan, ai idan wani yazo yagani sai ace na mallakewa hajiya d'a na mayar dashi mijin tace.."

Hancinta ya dan ja yafara shafa barimar dake kai, "nifa kafin kice kika mayar dani ba mijin tace ba, kafin kice na aikata duk abinda kike so.."

Kullum da safe sai shaddad yayi mata komai sannan yake tafiya office, haka suka kasance kullum, gashi idan yadawo gida sai yayi ado yasha turare ya tura nu'aima ta kirata wai yazo hira, kamar wasu saurayi da budurwa haka zata shirya ta fito falo hirar,

Yauma da misalin karfe 8 nadare hirar yazo ya tura nu'aima ta kirata,

"Kije kice bana nan.."

Dariya yayi ya kirata awaya, "yau kuma har dasu karyar ba anan?"

Kwantar da nu'aima tayi akusa da nu'aim ta fita, yana zaune yana kallo a tv sai kamshin turaren precious yake yi yana sanye da wandon sojoji da wata t shirt tasu,

Akusa dashi ta zauna ta kwantar da kanta kan kafadarshi ta rikeshi,

"Yau fa ni bacci nake ji"

Kanta ya fara shafawa daga karshe ya dawo da ita kan cinyarshi ya rungumeta,

"To muyi hirar ahaka har kiyi baccin"

Hira yake yi mata tun tana cemasa "uhm" har yaji shiru, sai da yagama kallonshi sannan ya dauketa a kafadarshi ya kaita daki, dakinshi ya koma yasaka kayan bacci ya dawo dakinta ya kwanta ajikinta ya rungumeta.

   Rayuwa mai dadi suke yi har ranar da su maryama suka cika kwana 40 cif da haihuwa, ai ranar taga hidima awurin shaddad, sallah sukayi raka'a biyu ya dauketa zuwa toilet suka yi wanka, wata kyakkyawar night gown mai zanen butterfly ajiki ya saka mata ya dauketa zuwa dakinshi wanda ya gyarashi ya shimfida wani bedsheet pink and blue colour tsakiyarshi kuma zanen wani katon butterfly ne,

Shafa hoton butterfly din tafara tana murmushi, wani farantin silver shaddad ya hawo mata dashi kan gadon wanda yake dauke da gasasshiyar kaza da fresh milk da fruits,

Tashi zaune tayi tana kallonsa tana jin soyayyarshi tana karuwa acikin zuciyarta, fresh milk din kawai ta dauka tasha sai fruit din shima ba kowanne ba apple da water milon kawai tasha ta tashi zataje wanke bakinta, riketa yayi bayan ya ajiye farantin a kasa,

"Kibarni nima nasamu sauran dake bakinki mana.." Bai barta tayi magana ba yafara tsotsar bakinta, wata soyayya mai sanyi yafara nuna mata cikin nutsuwa da so,

  Yau kam maryama ta yarda cewar shaddad yana sonta dari bisa dari kuma natane ita kadai, soyayyar da ya nuna mata bazata misaltu ba amma karshen kauna ya nuna mata tamkar zai hadiyeta dan so, wani bacci mai dadi mai cikeda nutsuwa tayi bata iya tashi ba sai 7 nasafe, tana bude idonta taga shaddad agaban mudubi yana shiryawa da alama fita zaiyi saboda umifom ne ajikinsa, ta cikin mudubi ya hangota ya sakar mata murmushi, juyawa yayi yana kallonta,

"Makararriya..."

Murmushi tayi ta tashi yayi saurin zuwa ya dauketa kamar wata jaririya, jikin maryama mai kyaune babu wanda zai kalleta ya tsammaci tafi shekara 22 shiyasa shaddad baya jin wahalar daukarta, cikin toilet ya kaita,

"Sorry baby, nine ko? Gashi zan fita yanzun nan.."

"Kaje babu komai sai kadawo"

Kissing dinta yayi agoshi ya fita, wanka maryama tayi ta fito tayi salla ta fita, yau ma babu inda bai gyaraba hatta su nu'aima ya shiryasu tana zaune a falo tana kallon carton,

  Satinsu biyu suna shan soyayya suka shirya suka tafi kaduna sukayi kwana uku daga can suka wuce abuja suka yi kwana biyu, kayan gyaran jiki anty maijidda ta tattarawa maryama ta bata tana cewa "naga wannan mijin naki bita zaizai ne"

Dariya maryama tayi, "ni anty ai wadannan kayan basu dameni ba well women kawai nakesha kuma shima har gyara mace yake shiyasa yawancin matan manya shi suke sha"

"To koma dai menene idan kana da kyau ka kara da wanka dan haka dole ki kara da wadannan".

  Kwana biyu sukayi suka koma Lagos, washe gari maryama ta koma office ta fara zuwa aiki, gidan Dada takai nu'aima da nu'aim ta ajiyesu saboda yanzu dada babu inda yake zuwa yana gida.



_*Ummi A'isha*_

No comments:

Post a Comment