Thursday 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 38,39,40,41

[5/20, 8:11 PM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Special tnx to my lovely aunty (Maman meenal),tnx for your love, care, support and everything... One love cwt anty_

   _*38*_


aishaummi.blogspot.com



   ~~~ Tashi tayi bayan ta saka rigarta ta nufi cikin dakinta taje tafara bincikar akwatinanta na lefe domin tasan ansako mata hijabai masu hannu aciki, cikin Sa,a kuwa tafara zazzaro su kala kala,

Adanasu tayi acikin drewar domin tana son tabi dokar shaddad su zauna lafiya, ita burinta shine kar yasake ganin wani abu mummuna daga gareta tafi son koma fadan zasuyi to ya zamana itace mai gaskiya bashi ba,

Tsabar farin cikin da take ciki yau taji tana son dafa tuwo miyar ganye, kitchen ta shiga ta dora girkin taje cikin freezer din dake ajiye acikin kitchen din musamman domin ajiyar kayan amfani,

Alayyahu ta dauko tana daga tsaye ta gyarashi ta yanyanka ta dora miya, lokaci kankani gidan ya gauraye da kamshin girkinta hatta shaddad dake kwance adaki kamshin ya takurawa kofofin hancinsa sai dai shi ko kadan bashida ra'ayin cin abincinta,

Cikin awanni kadan ta kammala tuwon ta kwashe ta adana wanda zataci da daddare da wanda zata yi dumame gobe da safe,

Bedroom dinta takoma tayi wanka ta tsuke cikin wata blue din riga da skirt din roba marar kauri, fita tayi ta koma kitchen ta zubo tuwonta a filet ta koma falo ta zauna tana ci tana kallon wani American film mai suna _bad boys_

Tana tsaka da cin tuwon shaddad ya fito cikin kananan kaya ya wuceta daga gani masallaci zai je domin lokacin sallar la'asar yayi, ita kam maryama tafara fashin salla yau, tana nan zaune har ta koshi dan haka ta dauki wayarta ta kira Dada tace ya aiko driver ya kawo mata motarta saboda gobe zata fara zuwa office,

Tunda shaddad ya fita bai dawoba sai bayan sallar mangariba, a falo ya zauna ya kunna tv yana kallo ita kuma maryama tana can kan wata kujerar idonta sanye da medical glass tana daddanna laptop dinta,

"Mtsww jifa wai har anfani take da glass, ai ni wallahi sam ban moreba" yafada acikin zuciyarsa,

Sun dade azaune kowa yana harkar gabansa har sulaiman ya kira shaddad, dagawa yayi yana fara'a, maryama na jinsa,

"Waye angon? Zan dai zama angon sai na auri yar 18 tukunna.."

Yi tayi kamar bata san yanayi ba saboda tasan yanzu ta dade da samun matsayin da ita kanta yar 18 din da yaketa kulafaci bata samuba, duk da dai har yau wani abu bai hadasu ba amma ai dolensa ya kirata da matarsa itama dole akirashi da mijinta koda baya so,

Tana jinshi ya karaci cin fuskarshi yagama ya tashi ya fita, bata jira dawowarsa ba ta shiga bedroom dinta tayi wanka domin tana son ta kwanta da wuri tunda gobe zata fita aiki,

Tana gaban mirror tana goga lip glow akan lips dinta sai ga shaddad ya shigo rikeda key din motarta domin driver din Dada ya kawo mata motar yanzu,

"Ga mukullin motarki ankawo miki"

Ya cilla mata tareda juyawa zai fita har yakai bakin kofa yaji tace,

"Nagode"

Bai ko juyoba yasaka kai yafice,

K'arasa shiryawa tayi ta saka wata yellow din rigar bacci iya gwiwa ta kwanta, har ta dan jima da fara baccin taji kishin ruwa ta dameta dole ta fito cikin magagin bacci ta fita taje falo ta lalubi fridge acikin duhun ta dauko ruwa ta bude ta fara sha, tana gamawa ta rufe fridge din ta nufi daki cikin magagin bacci ta fada dakin shaddad ta lalubi gado ta kwanta,

Shima shaddad kasancewar yayi bacci baiji shigowarta ba, kwanciyarta tayi taci gaba da baccinta har asuba tayi, lokacin da shaddad ya tashi yaganta tsaki yaja,

"Mtswwww" ya nufi bathroom yayi alwala ya fice masallaci, sai da gari yayi haske sannan ya dawo, har lokacin tana kwance tana bacci akan gadonshi acikin dakinshi,

Tsayawa yayi akanta yana binta da kallo, maryama irin fararen matan nanne masu daukar hankali jikinta luwai luwai gwanin sha'awa,fatarta in banda kyalli babu abinda take,

"Ke..." Yafada da karfi, juyi tayi bata bude idonta ba,

"Ke kitashi haka.."

"Me zanyi idan natashi? Ta tambayeshi har lokacin idonta yana rufe,

"Ban saniba, harma wani me zakiyi? To sallah zakiyi ko ita dinma ba zakiyi ba?"

"Banayi.." Tafada tareda juyawa tana jan bargo, bargon yaje ya rike,

"To tashi kifita daga nan"

"Ina zanje? Nida dakina zakace natashi na fit.."

"Ke ki tashi ki fice min daga daki, sannan karki sake zuwar min daki ni ba nemanki nakeyiba, ko kunya bakiji ba kika janyo jiki kika biyoni.."

Jin maganganun da yakeyi yasata tashi zaune tana kallon dakin cikeda mamaki domin ita bata san ya akayi tazo ba, shikuma shaddad sai fada mata bakaken maganganu yake kamar wadda taje dakin wani gardin,

"Banda ma tsabar jaraba ai sai kibari sai na nemeki kafin kizo amma dayake kin rigada kin saba kula maza shine ba zaki iya hakuriba har sai kin kawo kanki.."

Tashi tayi ta sauka daga kan gadon tana kunkuni,

"Koma dai menene ai ba abin kunya nayiba tunda wurin mijina naje.."

Har takusa fita taji yace, "ke me kike cewa?"

"Cewa nayi ai ba abin kunya bane tunda wurin mijina naje ba wajen waniba"

Ta sake maimaita masa dakarfi yadda zaiji...



*_Ummi Shatu_*🏻
[5/20, 8:11 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    _Fatan alkairi ga k'awallita fiddausi sodangi, banida bakin yimiki godiya tawan domin kamar kinfi kowa son MS..._


   *_39_*


~~~Binta da kallo yayi harta karasa ficewa daga cikin dakin, tana fita bata zame ko inaba sai bathroom dinta, brush kawai tayi ta fito ta fara aiki, shara da goge goge sannan tayi wanke wanke, tea ta dora da dumame ta fita falo tana fesa air freshener,

Shaddad ne ya shigo jikinsa sharkaf da gumi da dukkan alamu daga motsa jiki yake, bai kulata ba itama haka yawuce zuwa cikin dakinsa,

Saida ta kammala komai sannan ta shiga wanka ta fito, powder kawai tashafa ta saka kwalli ta zira wata bakar doguwar riga mai dogon hannu sannan ta saka hijab wanda yake shidinma dogo har kasa domin ko kayan da tasaka ba iya gani,

Shaddad na zaune afalo ta fito,

"Zan tafi.." Tace dashi tana kallonsa ta gefen ido, shiru yayi mata har saida ta maimaita sannan ya juya gareta yana kallonta,

"Ai ban hanaki tafiya ba amma kisani kedai yanzu matar aurece kuma zina awurin matar aure babban laifine dan haka ki kiyaye.."

Ko tanka masa batayi ba ta kwashi kayanta ta fita tabude motarta ta zubasu sannan ta zagaya ta shiga ta finciki motarta ta tafi, lokacin da taje asibitin gaisuwa ce kawai tsakaninta da sauran abokan aikinta daga nan taje tayi report cewar ta dawo, office dinta takoma tafara ganin patients, zuwa karfe uku ta gama komai ta tattara nata inata ta nufi gida, akan hanyarta na komawa ne taga wani kilishi agefen hanya da tsire na sayarwa, tsayawa tayi ta siya sannan takarasa gida,

Wanka tayi ta zauna tabude tsiren tafara ci, tana cikin ci shaddad ya shigo, tsayawa yayi yana yi mata kallon tuhuma,

"Waye yabaki izinin shiga kasuwa har ki siyo abu, wa kika tambaya?"

"Ni ba kasuwa najeba, akan hanya Nagani na siya"

K'wafa yayi yawuce bai sake magana ba,

Tun daga ranar maryama tafara warewa yanzu har tayi kyau ta danyi kiba saboda kullum tana fita aiki zaman kuncin kadanne sai a weekend ne take wuni agida sannan koda yaushe kafin ta fita sai tayi shara ta goge ko ina tayi wanke wanke ta gyara gidanta, shikuwa shaddad takurar da yake mata bai fasaba kullum cikin maganar zai auri yar 18 yake sannan har yanzu bai taba cin abincinta ba gashi kullum tuwone abincin sai dai yanzu da yake tana fita aiki idan taje tana aiken Massinger ya siyo mata abinda takeso,

Yau kam bata tashi da wuriba saboda sunyi meeting, tana tashi kuma ta nufi gidan Dada saboda ta jima bata ganshi ba sannan tunda rana ya kirata kan cewar baya jin dadin jikinsa taje ta dubashi,

Karfe biyar da rabi ta shiga gidan Dada, fara dubashi tayi bayan sun gaisa anan ta rurrubuta maganin da zaisha drivernsa ya tafi siyo masa sai da ta jira aka kawo maganin yasha sannan tatafi gida,

Tana zuwa gidanta mangariba nayi, shaddad yana cikin falo azaune domin tunda rana yadawo ya kwanta saboda kansa ne ke ciwo,

Hade rai yayi lokacin da ta shiga ya murtuke fuska,

"Daga ina kike?" Yafada cikin tsawa,

Kafin ta bashi amsa ya sake jeho mata wata tambayar,

"Gidan ubanwa kikaje, ke nifa bazan juri wannan yawon iskar takiba, dama nasan mai hali baya fasa halinsa, to wallahi baki isa kirinka bin maza agidana ba, dama nafada miki indai zaki cigaba da munanan halayenki to aurenki yana lilo.."

Zuba masa ido kawai maryama tayi tana kallon yanda ya tsaya yana fada mata maganganu kamar wani ubanta,

Wuceshi tayi ta nufi dakinta nan yabita ya fincikota, "ina yi miki magana har zaki tafi.."

Nan dinma shirun ta sake yimasa saboda bata son tayi magana domin muddin ta bude bakinta to itama bakar zata fada masa,

Tana tsaye tana jinsa ya karaci bambaminsa yawuce yatafi masallaci, duk da maganganunsa basa damunta amma wannan ya dameta,

Cikeda bacin rai tayi shirin bacci ta kwanta, shikuwa shaddad da ya nutsu sai zuciyarsa tayita bashi laifi cewar duk abinda maryama taje ta aikata laifinsa ne tunda shi da yake matsayin mijinta bai kula ya bata hakkinta dake kansa ba,tunda tana fita waje tana ganin mazaje kala kala dan haka koma menene yafaru shine sila sannan har dakinshi taje ta kaimasa kanta amma yaki ya kulata, yanke shawarar zai fara bata hakkinta yayi amma gaskiya bazai iya tunkararta haka ba sai da condom saboda gudun daukar cuta,

Sai da yaje ya siyo condom sannan ya koma gidan, lokacin ita maryama ma har ta jima da yin bacci domin agajiye take,

Dakinshi ya zarce kai tsaye yayi wanka ya shirya yasaka kayan baccinshi sannan ya dauko condom din ya nufi dakin maryama....



*_Ummi A'isha_*🏻
[5/20, 8:11 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

 

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   _Wannan Shafin nakune ku kadai yan group dina (duniyar makaranta group 1 & 2),ina alfahari daku, Allah yabarmu tare.._


   _*40*_


  ~~~Wuta ya kunna bayan ya shiga cikin dakin, can ya hangota kudundune tana bacci, kashe wutar yayi ya karasa wurinta, cikin bacci maryma tafara jin motsinsa tun tana zaton a mafarki ne har tafahimci cewar a gaskene,

Zumbur tayi ta mike ta kunna bedside lamp, nan taga shaddad daga shi sai gajeren wando da wani abu a hannunshi dubawa tayi dakyau take ta gane cewa condom ne,

"Lafiya?" Ta tambayeshi cikin rashin fahimta,

"Lafiya lau, nazo kawo miki hakkinki ne kamar yadda kika nema rannan saboda bana son kici gaba da bibiyar mazaje awaje kina dauko min magana..."

Cikeda mamaki ta sake dubanshi, "meye wannan kuma a hannunka?"

"Condom ne, ko kina tunanin zanzo miki ne ahaka na debi cututtukan da ni kaina ban san yawansu ba?"

"Kana nufin kenan inada HIV ko?"

"HIV is a simple disease akan sauran cutukan da zan dauka wanda wanima har namutu bazan samu maganinsa ba.."

"To naji amma dan Allah ka fitar min daga daki ni nayafe basai ka bani hakkin nawa ba"

"Ai baki isa na rabuda ke kina bin maza awaje ba.."

Kokawa suka shiga yi ita dashi saboda ita ta dauki alwashin cewar wallahi bazata taba bari ya kusanceta da condom ba mutukar tana cikin hankalinta sai dai ko idan wani abu ya bata hankalinta ya gushe, kokawa sosai suke yi duk da tasan yafita karfi amma haka ta jajurce ta hanashi aiwatar da kudirinsa,

Tun farkon fara kokawarsu yayiwa rigar baccinta pieces, da taga yana neman fin karfinta tuni ta dauko bedside lamp tana huci,

"Wallahi idan baka matsaba zan kwada maka wannan.."

Tsayawa yayi yana kallonta, sai yau ya gane surar da Allah yayi mata ba kadan bace domin halittar kirjinta kadai abin kalloce sannan kamar kirjin yar shekara 18 duk da yasan dama zata gyara jikinta tunda ita likita ce amma bai tsammaci zai gansu kamar hakaba,

"Ki kwada min.. Nace ki kwada min"

Bedsheet taja ra rufe jikinta tana kallonshi, ganin ya nufota yasata sakin fitilar ta fadi kasa ta fashe, acikin duhun yaci gaba da lalubenta, ita kuwa kafarta ta zira kasa zata sauka ta gudu cikin tsautsayi ta taka kwalbar fitilar data fashe,

"Washhhh, wayyo kafata.." Tafada cikin karaji,ba shiri ya saketa ya sauka daga kan gadon yaje ya kunna fitila haske ya gauraye dakin, tuni har jini ya fara zuba kamar me, kifa kanta tayi ajikin gadon saboda azaba,

Takawa yayi yaje wurin da take yana kallon kafarta wacce jini yake zuba, zare kwalbar yayi daga jikin kafarta ya tattara sauran ya kwashe ya fita, tun daga nan bata kara jiyo motsinshi ba, tashi tayi taje tayi dressing din wurin ta dauko wata rigar baccin ta saka saboda waccan shaddad ya gama illatata, kwanciya tayi amma fur ta kasa bacci sai tunanin wulakancin da shaddad yake yi mata take, har asuba tayi bata iya yin bacci ba, gari yana wayewa bayan ta idar da salla haka ta lallaba tayi aikin gidan sannan tayi wanka ta shirya ta fita tana dingisawa, ta riga shaddad fita domin lokacin da tafito ta jiyo motsinshi acikin kitchen yana yin girki.

Tun daga wannan ranar bai sake yunkurin zuwa dakinta ba har akayi sati daya, ranar talata da safe khairat kanwar shaddad tazo, ganinta ne ma ya hana maryama fita aiki, nan ta tsaya ta karbeta sai kuma tafara tunanin abinda zata dafawa khairat din,

"Khairat me zakici inje in siyo miki?"

"Adda maryam wanne irin siya kuma? Ni da kin kyaleni ma kinyi tafiyarki office dinki kafin ki dawo na yi mana girkin"

Ita dai maryama bata son khairat tagane cewar iya tuwone abincinta amma khairat sai da ta dage maryama ta tafi tabarta agidan, kitchen ta shiga nan taga iya garin tuwo ne kadai store kuma arufe ruf,

Waya tayiwa hajiya, hajiya na dauka tafada mata abinda tagani harda su karawa da karya, suna gama wayar hajiya ta kira shaddad domin shi baima san zuwan khairat ba saboda tun asuba ya fita,

"To dan masu gida mai cikakken iko, sai kaje ka budewa yar uwarka store saboda ita tace bazata iya cin tuwo ba kamar matarka.."

Shiru shaddad yayi yakasa magana, "bakaji abinda nafada bane?"

"Hajiya naji.."

"Mazaje wato dai ni ban isa dakaiba ko? Ban isa kayi min abinda zanji dadiba ko? Yayi daidai"

K'it yaji hajiya ta kashe wayar, babu shiri ya koma gida yana zuwa yaga khairat a falo tana yin mopping, "Yaya Navy ina kwana?"

"Lafiya, ashe kece munafukar ko? Wallahi idan kina zuwa kina yimin munafurci agidana kina hadani da hajiyata sai na ballaki.."

"Oho dai nidai nafadawa hajiya yaushe zaka bar baiwar Allah da iya gayan tuwo bayan agidansu ba haka ta saba ba, kai in banda ma so me zatayi dakai, wallahi maryama kalar abuja ce senator ya kamata ta aura ko minister amma kai baka da ko sisi kama samu tana sonka shine zaka rinka wulakantata.." Khairat tafada acikin zuciyarta,

Dakinshi yaje ya dauko key din store din yaje ya bude ya sake fita, yana fita ya kira hajiya yayita bata hakuri dakyar ya samu ta saurareshi tace ta hakura,

Maryama kuwa dawuri ta dawo gida tana gama ganin patients tadawo gida lokacin ko karfe daya na rana bata yiba, lokacin data dawo tasamu har khairat ta gama shirya musu lafiyayyen girki, jalop din shinkafa da farfesun kifi, da salad,nan khairat ta kwashe yanda akayi har shaddad yazo ya bude store din ta fadawa maryama,

Gidan ba karamin dadi yayiwa maryama ba saboda zuwan khairat, sunata hirarsu gwanin dadi sai da dare sannan shaddad ya dawo, duk khairat tana lura dashi dama daukarwa hajiya rahoto tazo yi, tana ganinsa baici abincin da aka girka ba,

"Daya.." Tafada acikin zuciyarta,dama kuma tazo ta samu store a kulle, koda sukayi shirin bacci dakin maryama taje,

Suna hirarsu har tafara gyangyadi,

"Adda Maryam bari natafi na kwanta"

"Ke kiyi zamanki mu kwana anan"

"Adda Maryam ance babu kyau kwanciya akan gadon matar da mijinta yake kwana akai"

"To ai ke yayanki bai taba kwana akai ba dan haka zaki iya kwana"

"Bai taba kwana ba? Biyu" khairat tafada acikin zuciyarta, nan suka yi kwanciyarsu suka kwana tare, washe gari maryama ta tafi aiki tabarta amma da wuri take dawowa bata kaiwa yamma,

Kwanan khairat uku da zuwa gidan cikin dare ta fara jiyo maganganu, tashi zaune tayi ta duba, nan taga maryama bata nan, fita tayi taje ta tsaya a kofar dakin shaddad tana jin abinda yake faruwa,

"Wallahi baka isa ka kusanceni da condom ba sai dai mu shekara ahaka"

"Dole na kusance saboda bazan bari ki rinka bin maza awaje kina jawo min bala'i ba, kuma wallahi duk namijin da kika kula awaje Allah ya isa.."

"Naji nayarda amma nidai kam bazaka zomin da condom ba"

"To fice min adaki kar kiyi min rashin kunya"

"Zan fita saboda dama kaine kaje ka daukoni bani na kawo kaina ba"

Fuhhhh maryama ta fito daga cikin dakin, dagudu khairat taje ta kwanta saboda bata son susan cewar taji abinda yafaru domin sirrinsu ne...



*_Ummi A'isha_*
[5/20, 8:11 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  _*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Gaisuwa mai yawa ga Maryam Abdul, Maryam s Bello, Queen Mimi & Khadija candy_


  *_41_*


~~~Tana ji maryama tazo ta kwanta tana ta faman jan tsaki, yanda maryama bata iya yin bacciba haka itama bata yi bacciba saboda tsananin tausayin maryama,

Abin mamaki dasafe ko ta nunawa khairat cewar wani abu ya faru, sam bata nunaba haka ta tashi fuskarta asake ta shirya ta tafi office karfe daya ta dawo sai da ta biya ta gidan Dada ta gaidashi sannan takoma gida,

Kwanan khairat bakwai a Lagos ta shirya zata koma gida,

Wata hadaddiyar super wacce kudinta zai kai 25,000 maryama ta bata banda kayan kwalliya cikin wata leda sannan ta bada atamfa kala biyu da leshi shima guda biyu tace akaiwa hajiya,sannan ta karawa khairat da kudi dubu goma,

Murna sosai khairat ta shiga yi saboda ita harga Allah tana jin maryama kamar yayarta wacce suka fito ciki daya, karfe goma da rabi nasafe ta tafi itada shaddad wanda ya tafi rakata,

Tunda khairat taje gida ta shiga bawa hajiya labarin duk abinda tagani babu Wanda ta boye,

"Hajiya ko abincinta baya ci sannan ya rufe store ya boye key din iya tuwo kawai yake bata, sannan bai taba kwana a dakinta ba, har yau babu abinda ya hadasu da ita wai shi tsoron daukar cuta yake dan haka bazai kulata ba sai yayi amfani da condom, shine ita kuma taki, ina jinsu suna fada da daddare akan taki, gashi kullum cikin yimata gori yake yana cewa wai ta dade batayi aure ba har takai shekara talatin shi yar shekara 18 zai aura,

Banda zarginta da yakeyi babu dama yaga ta dan gota lokacin dawowarta bata dawo ba sai yace wai yawon bin maza ta tafi.."

Tunda hajiya taji wadannan maganganun ta cika tayi fam,

"Ai wannan ba maganar waya bace, zuwa ya kamata yayi ya sameni, kiduba kiga yarinya yar arziki amma kullum cikin wulakantata yake, zai zo ya hadu dani"

Waya hajiya tayi masa tace lallai lallai yazo tana son ganinsa, dayake suna cikin wasu ayyuka bai samu damar zuwaba har sai da akayi sati uku da maganar,

Maryama dai abubuwan gabanta kawai take yi bata sakawa ranta damuwa ba domin tasan idan tasa bacin ran shaddad a zuciyarta to BP dintane zaita hawa, tana office tana aiki khairat tayi mata waya tace tafadawa shaddad zatayi registration yabata kudi dubu 30 Yaya Yusuf ma zai bata rabi, ko fada masa maryama batayi ba ta turawa khairat dubu 50 tace gashi nan harda na siyan lecture notes, ai hajiya da sauran yan uwan shaddad wannan abu ba karamin dadi yayi musu ba, anty babba cewa take,

"Haka muke son surika yar arziki ba yar tsiya mai bakar rowa ba"

Acikin sati na hudu da kiran da hajiya tayi masa ya shirya ya tafi, lokacin da yafito zai tafi ya leka dakin maryama,

"Idan kin tashi daga aiki kije gidanku ki kwana ni zanje Kaduna hajiya na nemana kuma bazai yiyu indawo ayau ba sai gobe, idan kuma kika kawo min namiji gidana ko ke kikaje wurin wani kika kwana Allah ya isa.." Abinda yafada kenan yawuce ya tafi,

Shiryawa tayi ta tafi office daga can tawuce gidan Dada zata kwana, itafa gaba daya yanzu ma maganganun shaddad sun daina yimata zafi saboda inda sabo har tasaba dasu,

Tunda shaddad yaje hajiya tasashi agaba da fada, ta inda take shiga bata nan take fitaba sai da tayi masa tatas sannan tace kuma lallai lallai daga ya koma ya bawa maryama hakkinta sannan maganar condon idanma yasake yi bata yafeba,sannan idan tayi abinci baiciba nanma bata yafeba,

Kwananshi daya ya juya ya koma Lagos, kai tsaye asibitin su maryama yawuce yayi mata zuwan bazata, bai sameta a office ba dan haka ya nufi dakin yara, can ya hangota tana yiwa wani yaro wasa wanda ta duba,

Juyawa yayi ya fita yatafi gidansu maryama, yasamu Dada agida bai fita ko inaba nan suka gaggaisa Dada yake cemasa ai maryama jiya tazo agidan ma ta kwana tace yayi tafiya zuwa Kaduna,

Ajiyar zuciya ya saki saboda dama abinda yazo ji kenan, ya dan jima agidan kafin yatafi zuwa gidansu,

Maryama bata dawoba sai karfe 5 na yamma, tana dawowa ta shiga kitchen ta dora girki, jalop din taliya da macaroni tayi ta dafa kwai,

Ita bata ma san shaddad yana dakiba, akan table ta zauna taci ta shiga daki domin yin wanka, fitowa shaddad yayi ya hau table din shima ya dan zuba abincin nata yaci sai dai bai taba tunanin ta dan iya girki kamar haka ba saboda yaga agidansu bayi takeba,

Fita yayi sai bayan sallar isha ya dawo, duk ya damu saboda Allah ya isan da hajiya tayi masa idan bai bawa maryama hakkinta na aureba, shiryawa yayi ya nufi dakinta tana zaune da rigar bacci ajikinta da laptop akan cinyarta tana wani aiki,

Zama yayi agefen gadon, "kibar wannan aikin kizo muje nabaki hakkinki tunda har kin fara kai karata akai, amma kisani idan har na dauki wata cuta ajikinki to bazan taba yafe miki ba kuma sai Allah ya saka min domin ni ban taba aikata zinaba, kaddarace kawai Allah ya jarrabeni da mata mazinaciya.."

"Kabarshi hakkin nayafe"

"Idan tun farko kin san kin yafe meye naki na zuwa ki fada kice tunda muka yi aure ban baki hakkinki ba? Ki tashi ni kina bata min lokaci.."

Bai jira amsarta ba ya fincike laptop din ya je ya dorata akan bedside drewar, ya nufeta,

"Kisani kawai zan kusanceki ne dan yiwa mahaifiyata biyayya amma ba wai dan ina sonki ba, bana sonki kuma bazan taba sonki ba har abada.."

Sam yau bata son kokawa dashi saboda tasan itace zata ji jiki amma bakaken maganganun da ya yaba mata sune suka sakata kasa jurewa, nan ta shiga tureshi tana dukanshi,

Sai da suka dambatu sosai sannan yasamu nasarar rabata da komai na jikinta, saddakarwa kawai maryama tayi saboda jin irin muguntar da shaddad ke yimata,

Wahala sosai ya bata dan sam bai tausaya mata yabita ahankali ba saboda ya rigada ya gama sakawa zuciyarsa cewar tasaba bibiyar maza, amma kuma sai yaji abinda yake zargi ba haka bane,

Wahalar da maryama tasha sai da taji kamar mutuwa zatayi shikuwa shaddad baima san a duniyar da yake ba, gaba daya baya cikin hankalinsa dan haka raga raga yayi mata,

Dakyar ya iya kyaleta ya tattara ya koma dakinsa yayi kwanciyarsa, yabarta tana numfashi dakyar,

Sai da asuba tayi sannan ya tashi ya shiga bathroom ya gyara jikinsa ya fito ya tafi masallaci, lokacin da ya dawo ya dan leka dakin, har lokacin bata tashi ba tana kwance kamar yadda ya tafi yabarta, shi kansa yasan wahalar da yabata ba kadan bace sannan gajiyar da tara mata itama mai yawace, haka kuma yanzu yagane shine namiji nafarko da yafara saninta sannan komai na jikinta sabone fil kamar na budurwa yar 16,dadewar da tayi babu aure baisa ta rasa wani abu ajikinta ba,

Wucewa yayi zuwa dakinsa yana zama aka kirashi awaya daga office suzo zasu fita operation,

Wanka kawai yayi ya zira uniform ya fita, dakin maryama ya leka nan yaganta kwance cikin jini duk bedsheet din dake kan gadon yayi face face da jini, ganin har lokacin bata tashiba yasashi fita yatafi.

  Sai da misalin karfe 8 nasafe maryama ta iya tashi, da rarrafe ta shiga bathroom ta gasa jikinta tayi wanka amma yanda takejin radadi yasata fahimtar cewar shaddad yaji mata rauni ba kadanba dan haka sai anyi mata dinki,

Salla tayi ta hada tea tasha ta dauki key din motarta ta rufe gidan ta fita.

Wani asibiti mai zaman kansa tanufa asibitin wata kwararriyar likitan mata,tana zuwa ta samu ganin likitar suka shiga cikin office dinta dayake sun san juna suna haduwa awurin taron likitoci,

Bayanin matsalarta tayiwa likitar nan ta fara dubata daga karshe tace zata yimata dinki, runtse ido maryama tayi saboda dama tasan haka zata faru, kan wani dan karamin gado ta hau dr munnira tazo tafara kokarin yimata dinkin,

"Amma dai dr wannan mijin naki yarone ko?"

"Wallahi dr ba yaro bane kawai dai bai taba aureba sannan soja ne"

"Ah shiyasa, karfi kawai ya nuna miki bai san fatar wurin bata cika kwari ba"

Maryama tasha wahala sakamakon dinkin nan da akayi mata sai da tasamu gado ta kwanta domin hutawa saboda wani irin jirine yake daukarta dan haka dole saida ta huta sannan tatafi gida.

  Shaddad kuwa karfe  goma sha daya ya koma gida amma sai ya tarar maryama bata nan, fita yayi yatafi gidansu yagani ko can tatafi amma koda yaje can dinma shiru bata nan, asibiti yawuce canma bata nan, Gida ya sake komawa yana tunanin ina tatafi?

Yana zuwa gida sai gata itama ta dawo, ahankali take tafiya tana runtse idonta saboda radadin dinkin da akayi mata,

Bude gidan yayi ya shiga itama ta shiga,afalo ta tsaya ta cire hijab dinta ta kwanta akan doguwar kujera,

"Daga ina kike?"

"Asibiti naje"

"Wanne asibitin?"

"Karama clinic"

"Me kikaje yi? Dama namanta ban fada miki ba wallahi muddin kikasha kwayoyin hana daukar ciki ko kikayi allura ko duk wani abu da yake hana daukar ciki sai ranki ya baci kuma koda aboye kikayi to Allah ya isa ban yafeba"

Kallonshi tayi idonta jajur saboda ita kadai tasan irin wahalar da take sha,

"Ciwon da kaji min naje aka dinke..." Shine kawai amsar data bashi ta sake gyara kwanciyarta tana tsotsar vitamin c,

Jin abinda tace yasashi yin shiru bai kara magana ba yawuce dakinshi, wani baccine ya kwashe maryama ba ita ta tashiba sai da azahar, dakinta ta shiga domin yin wanka anan taga shaddad ya cire bedsheet din dake kan gadonta, baki ta tab'e ta shiga toilet tayi wanka tafito danma zazzabin daketa son rufeta bai rufeta ba saboda magungunan da tasha,

Zama tayi ta danyi kwalliya sama sama ta saka doguwar riga marar nauyi mai siririn hannu, sallar azahar tayi sannan ta shiga kitchen ta dafa indomie ta debi kadan taci, takoma falo ta kwanta,

Tana kwance tana kallo taji shigowar shaddad daga masallaci, indomie din data dafa ya debo ya zauna akan dining yana ci, tana jinshi yana waya da wani wanda bata san ko wayeba yana cewa wai ai yakusa ya auro karamar yarinya yar 18 years,

Yunkurawa tayi dakyar ta tashi tana kallonsa saboda yau ranace ta mayar masa da martanin gorin budurcin da yadade yana yimata,

"Dan Allah idan katashi k'ara auren tsabar kankanta ka auro yar datake cikin cikin uwarta wacce bata fito duniya ba,duk tsiya dai da yarinya yar shekara 14 wacce ta lalata rayuwarta gara tsohuwa yar shekara 35 wacce ta rike mutuncinta.."

Tana kaiwa nan takoma ta kwanta, shaddad najinta sarai yaji abinda ta fada amma yayi mata shiru bai tanka ba....



     _Fatan alkairi ga Khadija maikano,Hafsatu Alkasim, jannart & Saudat yerima.._



*_Ummi A'isha_*

2 comments:

  1. UMMI AISHA THE MOST TALENTED AND THE ICONIC OF THE WRITERS.

    ReplyDelete
  2. WHEN THE BOOK IS TO COMPLETED NOTIFI ME

    ReplyDelete