Wednesday 31 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA..22,23

[5/14, 4:31 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Wannan Shafin nakine yar uwa rabin jiki Khairat Dandawakee keda duk k'awayenki.._

    *_22_*


   ~~~Ganin tayi shiru ta shiga duniyar tunani yasa anty maijidda fahimtar cewa akwai wani abu dake damunta,

"Maryama meyake damunki ne? Ki fada min mana, nifa mamanki ce haifarki ne kawai banyi ba, wallahi dake da dan da nahaifa acikina duk daya nake ganinku babu banbanci..."

"Anty maijidda wallahi nima ina son nayi auren to amma wanda nake son aurar ne shikuma bani yake soba asalima ya tsaneni, rabona dashi anfi shekara daya da rabi..." Nan ta kwashe labarin komai ta sanar da anty maijidda,

Zuba mata ido anty maijidda tayi tana kallonta cikin tausayawa amma sai ta dake domin tana son karfafa mata gwiwa har ta samu wanda take so ta aura,

Dan haka cikin sigar lallashi anty maijidda tace,

"Haba maryama to kuma menene na daga hankali? Ki kalli fa irin baiwar kyau da Allah yayi miki, wallahi babu wani d'a namiji da zai ce bakiyi masa ba sai dai idan har yasan bazai sameki ba,

Kina da baiwar da kowanne namiji zai so ya mallakeki dan haka ko kaffara bazanyi ba idan na rantse miki kan shima shaddad din yana sonki, yatafi da tabon sonki acikin zuciyarsa, son da yake miki ma koke bakya yi masa, kuma koda bai fito ya furta miki ba afili to azuciyarsa hakane,

Dan haka ki kwantar da hankalinki ki nutsu Ki saurareni domin zan doraki akan hanya wacce zata kaiki ga muradinki har burinki ya cika,

Nafarko dai sai kin zama mai hakuri da juriya domin hakuri shine matakin da yake kai bawa ga kowanne irin nasara, idan kika kasance mai hakuri da juriya to wallahi zaki kai ga nasara, ba yanzu ba ko bayan aurenku da shaddad to sai kin zama mai hakuri da juriya, bari nabaki misali, zakiga akwai matan da suke zaune lafiya agidan mazajensu ko kansu ba aji amma idan zama ya hadaku dasu zaka fahimci tsananin hakurinsu ne yakaisu ga wannan matsayin wanda har ake yimusu kallon marassa matsala agidan aure, dan haka samun nasararki yanada alaka ga hakurinki da kuma juriyarki,

Abu nagaba kuma shine ki zama mai zurfin ciki marar tona sirrinta ko kuma matsalarta, dayawa daga cikin mata zaki samu bamuda sirri idan abu yana damun mu to sai kowa yaji bama iya rike abin acikin ranmu, to ki zama mai rike sirrinki duk abinda ya dameki Allah zaki fadawa sannan awurinsa zaki nemi sauki,

Wadannan abubuwan guda biyu sune masomin samuwar nasararki, sannan insha Allah a wannan zaman da zamuyi dake zan koyar dake abubuwa da dama kama tun daga kan girki, kula da maigida,gyaran jiki da sauransu, sai abu na karshe shine ilmin addini, ya zama dole maryama ki shiga makarantar islamiyya har yanzu baki makaraba,idan kika shiga makaranta zaki karu da abubuwa da dama kafin kibar garinnan, kin san kowanne namiji baya son jahilar mace domin tarbiyar yaransa zata samu nakasu,ita mace duk kyanta duk arzikinta duk kyawun nasabarta to mutukar bata da ilmin addini to wallahi ansamu matsala..."

Ajiyar zuciya maryama tayi sannan ta bude bakinta dakyar tayi magana,

"Nagode anty maijidda sannan insha Allah zanyi yadda kikace.."

"Yawwa 'yata, insha Allah sai kin mallaki abinda kike so"

Murmushi maryama tayi acikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya amsa,

"Yawwa tunda kinzo sai ki rubuta min maganin ciwon baya wallahi bayana ciwo yake, baby likita.."

Murmushi maryama tayi saboda jin yanda anty maijidda tayi maganar cikin barkwanci.

  Tunda maryama tazo gidan anty maijidda tare suke shiga kitchen kullum su shirya abinci banda drinks kala kala da take koya mata gashi babu kunya ko wani abun ta hadawa mijinta da ita kanta sai tafito ta fada mata amfaninsa da kuma dalilin yinsa,

Satinta biyu da zuwa suka fara fita ganin gari, sune wurin shakatawa da super market da duk wani wuri wanda masu son bude ido suke ziyarta,gashi duk lokacin da suka fita to maryama bata dawowa sai da sabon saurayi,

Yauma kamar kullum agajiye suka dawo daf da sallar magrib, hannun maryama dauke suke da ledojin ice cream da cake ga wata ledar kuma mai dauke da dambun nama dan gaske,

Tunda suka fito daga exclusive supermarket wani guy yake faman binta ganin taki kulashi yasashi shiga motarshi kirar Lexus ya biyosu, har gida ya bisu amma ita sam bai burgeta ba, dakyar anty maijidda ta lallabata taje ta saurareshi nan dinma duk fuskarta babu walwala,

Bayanin kanshi yayi mata yace sunanshi mufid kallonshi kawai take kyakkyawa ne kuma daga gani dan manyan mutane ne amma bata jin zata iya amincewa ta aureshi, nan yabata phone number dinshi ta karba tana yatsina fuska, ganin kamar atakure take yasashi yi mata sallama ya tafi,

Tafiya take tana tsaki har ta shiga falon inda anty maijidda ke zaune tana cin dambun naman da suka shigo dashi,

"Yata mai farin jini wannan kuma waye? Ni ai da shi dinma kika aura.."

"Tab haba anty maijidda ni wallahi sai navy.."

Dariya anty maijidda tayi ta bugeta akafada cikin wasa,

"To shima ai naga dan gayune kakkarfa.."

"Kinga anty ni idan kina da pad kibani kawai uzuri gareni.."

"Kashhh ai kuwa saura kwaya daya kuma ina jin guda bakwai ne aciki da kamar tun dazu muka yi maganar ai da mun siyo wani, koda yake dayanma ai zai isheki.."

"Anty wallahi yayi min kadan"

"Kai maryama har kwana nawa kikeyi?"

"Kwana takwas anty"

Ido anty maijidda ta zaro tana kallonta,

"Kwana takwas? Amma idan kinyi aure zaki rinka shan maganin da zai rage miki kwanakin ko? Ai wannan kwanakin yayi yawa maryama gashi maza basa so saboda takura suke.."

Sunkuyar da kanta tayi saboda kunya ita kuma anty maijidda sam babu boye boye komai fada take yi afili baro baro....



*_Ummi Shatu_*
[5/14, 4:31 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

   _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*23*_

aishaummi.blogspot.com

  ~~~Jin tayi shiru yasa anty maijidda taci gaba da fadin,

"Kidaina wani kunya da nuku nuku maryama, ba abin kunya bane dan kin san wadannan abubuwan,

Ni kinganni nan tun kafin nayi aure lokacin ina budurwa nasan abubuwa da yawa wadanda suka shafi al'amuran aure wallahi, ba laifi bane dan budurwa ta samu ilmi na rayuwar aure amma sai kiji wasu suna cewa wai yan matan yanzu menene basu saniba ai practical ne kawai basu yiba amma sun san komai, to wannan din shine daidai domin yanada kyau budurwa tasan hakan tun kafin tayi aure ba wai sai lokacin da tayi auren sannan zata fara tunanin tayaya zan zauna da mijina ko kuma me mijina ya kamata inyi masa ba,

Wallahi maryama nasan abubuwa da dama ina budurwa wanda wasu matan auren da yawa basu saniba kuma zurfi acikin karatun addini shine yakaini ga wannan matakin, saboda alokacin nakasance ma'abociyar karance karancen littattafan addini da sauraren wa'azozi wadanda malaman addini sukayi akan rayuwar aure, amma mu yanzu sai muke ganin abin banbarakwai idan budurwa tasan abubuwan da suka shafi, sai mu rinka yi mata kallon yar duniya ko kuma ai yar iskace, to wallahi ba iskanci bane kuma ba mummunar wayewa bace asalima wannan itace wayewa irin wacce musulunci ya tanada mutukar ba ta mummunar hanya tasan hakanba, shiyasa nake cewa zaki shiga islamiyya domin ina son ki kara samun gogewa da wasu tarin ilmin wanda ya shafi lamarin aure duk da nasan kin san dayawa daga cikinsu tunda ke likita ce amma wannan wanda zaki samu a makaranta daban yake,

Kuma nasan zakiyi alfahari dani koba yanzu ba saboda zaki gane cewar nayi miki babban gata wurin doraki akan turba mai kyau, sannan ko bayan kinyi aure zaki ji dadin zama da mijinki batare da matsala ba,

Shiyasa kika ga tunda nake babu wurin wacce nake zuwa neman shawarar wai ya zan yi inbawa mijina kulawa, domin nadade da sanin abubuwan da maza keso da wanda bakya so, shiyasa nazama star mai haskawa awurin mijina"

Dafa kafadar maryama anty maijidda tayi sannan taci gaba,

"Yanda nasamu fada awurin mijina kema haka nake miki fata yata, amma sai kin nutsu sannan kuma kin jajurce, akwai wa'azi dayawa da malamai suka yi akan yammata da masu shirin shiga dakin miji musamman dan abasu wani ilimi na yanda zasu kula da mazajensu ya kamata ki nemesu ki adana kuma ki rinka saurara sannan kinga idan har hakan ba abune mai kyau ba to da malamai basu bata lokacin su sun zauna sun rubuta ba, kamar yadda nafada miki ba iskanci bane kuma ba abin kunya bane saboda acikin magabata ma ansamu matar da tayiwa yarta nasiha tabata shawarwari lokacin da zata kaita dakin miji, hatta yanda yadace ta kula da mijinta da irin yanda zata faranta ran mijinta da abinda zata yimasa lokacin rayuwar auratayyarsu duk sai da wannan matar ta koyar da yarta,kuma hakanne ya kamata ko wacce uwa ta zama, mu rashin zurfafa awurin karance karancen addini da sauraren malamai duk shine ya mayar damu baya har muke aibanta abinda yake mai kyau,wallahi indai yarinya mai addini ce hadisin zadiz zaujaini kadai ya isa ya sanar da ita ilmin aure dan haka yana da kyau mu tashi mu nemi ilmi,

Wadannan kwanakin kamar yanda nafada miki sunyi yawa maryama musamman ma awurinki keda kike saka ran cewar zaki auri soja, kin san karfin sha'awar sojoji tafi ta sauran maza saboda su yanayin motsa jikinsu da shan wahalarsu, idan normal namiji zai bukaceki adare sau biyu to soja sai dai sau uku ko hudu, kinga kuwa indai hakane bazaku shirya dashi ba mutukar kina yin period har tsawon kwanaki takwas, wani namijin ma ko kwana hudu kikeyi sai kinga ya shiga damuwa, yanzu dai nasan bakya gane abinda nake sanar dake sai dai idan lokacin yayi zaki fahimta"

Mikewa maryama tayi cikeda jin kunyar anty maijidda ta nufi bedroom taje ta dauko pad din ta shiga dakinta,

Wanka tayi ta shirya cikin wasu pink din riga da wando masu laushi ta koma falo inda anty maijidda ke zaune tana kallon _Dhoom_ a tashar mbc Bollywood,

Zama tayi ta dauki robar dambun nama ta bude tafara tsakura tana ci,

"Maryama mai zaki dan dafa mana muci?"

"Duk abinda kikace anty"

"To dafa mana taliya sai ki danyi mana sos da kifi.."

"To anty.."

Tashi tayi ta ajiye dambun naman da take ci ta nufi cikin kitchen, tana ji wayarta na kara amma ko ta kula saboda tasan samarin dake damunta kullum ne,

Binta da kallo anty maijidda tayi fuskarta dauke da murmushi saboda da saninta take saka maryama aiki kamar su girki da sauransu saboda tana son kiwar dake tattare da ita ta ragu sannan idan tana yawan yin girki akai akai to hakan zai sata ta goge ta kware afannin girkin shiyasa yanzu yawancin girkin ita take barwa tayi musu kuma alhamdulillah tun ba ayi nisa ba har maryaman tafara kwarewa sabanin da wanda babu abinda ta iya ko dafa ruwan zafi ma wahala yake mata saboda ita tunda ta taso agidansu kuku ne yake dafa musu duk abinda zasu ci,

Jin karar wayar maryama yayi yawa ya cikawa anty maijidda kunne yasata dauka ta kaimata kitchen din,

"Ungo phone dinki samarinki sai cika min kunne suke da kira.."

Hannunta ta tsame daga robar da take wanke kifi sukumbiya da ruwan kal saboda magance karninsa,

Daga wayar tayi tana murmushi saboda ganin dr fahad ne wanda ke kiranta,

Makale wayar tayi akafadarta tafara amsawa yayinda anty maijidda ta juya ta fita daga cikin kitchen din,

"Hello fahad...." Tafada tareda jan sunan,

"Hy maryama ta, yakike?"

Murmushi tayi "lafiya lau fahad ya aiki?"

"Alhamdulillah maryama, ya lagos"

"Lfy, ni ina abuja ma nazo hutu"

"Ahh daidai kenan, zanzo miki mu gaisa sai mu gama maganar bikinmu ko, saboda nidai na kosa.."

Tana jin haka ta bata fuska kamar yana ganinta saboda ita ta tsani taji anyi mata zancen aure mutukar ba za a danganta maganar auren da shaddad ba,

"Ok, to kabari zan kiraka yanzu ina kitchen ne"

"Me ake dafa mana sarauniya?"

"Cikin kosawa da maganar ta amsa masa, "ina wanke kifine so we will talk later.."

"Ok queen bye"

Ajiye wayar tayi tana tsaki, "yara kanana basu taka kara sun karya ba suce wai kaine Sa,an aurensu saboda tsabar rashin kunya, ko idan sun aureni ina zasu kaini oho.."

Da haka ta samu ta kammala girkin tana yi tana ta korafi ita kadai,

A babban farantin tangaran ta zuba musu abincin itada anty maijidda ta fita,

A inda ta tafi tabar ta anan ta sameta tana rikeda remote tana rage volume din tv,

Ajiye abincin tayi wanda yaketa faman kamshi domin sos din tasha curry kala kala,

Fara cin abincin sukayi, girkin ya danyi sai dai kuma akwai yan kura kurai wanda ba arasa ba nan anty maijidda ta danyi mata gyaran da yadace saboda gaba....


*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment