Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA..5

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*5*_


   ~~~Cikin kankanin lokaci samari matasa suka cika kujerun dake kusa da ita kowa yana son kulata amma yana tsoron karta wulakanta shi ita kuwa maryama shan coke din dake hannunta kawai takeyi tamkar bata san abinda suke yiba,

Har karfe 8 tayi ana buga wasan kasancewar wurin tal yake kamar hasken rana yasa mutane da dama basu san cewar dare yafara yiba domin hasken wurin ko allurar kace tafadi to zaka ganta, sai misalin karfe takwas da rabi sannan aka tashi daga wasan,haushi aran maryama kamar zatayi kuka kasancewar wadanda take supporting basune suka yi nasara ba,

"Mtswww...." Taja wani dogon tsaki tareda mikewa tsaye cikeda takaici domin ji take inama bata zo ta kalli wannan abin haushin ba, key din bike dinta ta ciro daga aljihun jeans dinta fuskarta babu walwala,

Wurin da tayi packing taje ta hau bike dinta tabashi wuta ta Lula...,gudun datake yanzu yafi na dazu saboda yanzu titin shiru yake sai  yan ababan hawan dake wucewa tsilla tsilla, har tayi kwanar zuwa barikinsu sai kuma tafasa ta juya ta tasamma club domin tana son taje ta rage wannan haushin da ya cika mata zuciya,

Wani kayataccen club ta je wanda ya amsa sunansa domin abubuwan dake gudana acikinsa sai wanda yagani, ko ina na wurin samarine da yanmata wadanda idonsu ya bude suna shagulgulansu wasu kuma disco aka kunna musu suna rawa gefe daya kuma akwai wurin sai da drinks kala kala domin jika makoshi,

Hannuwanta duka biyu ta saka cikin aljihun wandon jeans dinta kunnenta makale da earpiece tana takawa ahankali,

"Abbas kazo mu bar wurinnan dan Allah saboda kasan nifa ban saba zuwa irin wadannan wuraren ba..." Kunnenta ya jiyo mata wata daddadar murya tana magana, zuciyarta ce ta tilasta mata son ganin fuskar mai maganar, juyawa tayi ta koma da baya wurinda taji muryar tana tashi,

"Kai Navy kacika matsala, ban san ko sai yaushe zaka waye ka fito gariba.."

"Babu wata wayewa da zan sake yi bayan wacce nake da ita ayanzu..."

Full light aka bawa wurin daga duhun hasken dake dan kawowa yana daukewa cikin kaloli red,blue,green, yellow da sauransu,

Ido ta zuba masa, shi dinma kallonta yayi cikeda tsanarta domin yagane kowacece,

Kallonta ta dauke daga gareshi tana kokarin barin wurin, ko shakka babu shine wannan guy din data gani agidansu awurin dada dazu da safe sai dai yanzu ba acikin uniform yake ba, kananan kaya yasaka wadanda suka yi daidai da siffarshi,

Ji tayi gaba daya club dinma ya isheta dan haka tafice da niyyar tafiya gida, daidai lokacin suma suka fito zasu tafi, yana kallonta taje ta hau bike dinta ta fita, ba karamin mamaki abin yabashi ba ganin yanda take tuka machine din tamkar wata namiji babu alamun tsoro atattare da ita dadin dadawa kuma ganinta da yayi a club din yasake tabbatar masa da ko ita wacece atake yaji ya tsani duk wata yarinya wacce ta kasance rainon bariki,

"Navy muje mana" muryar abbas ta katse masa tunanin da yakeyi,

Baiyi magana ba yawuce suka tafi, kasancewar shine yake driving din yasashi kurewa motar gudu domin ya iske maryama ahanya, cikin kankanin lokaci ya fara hangota, full light ya kunna ya hasketa, gudun da takeyi ta dan rage tana jin haushin koma waye mai wannan motar sai tayi masa rashin mutunci, ganin mai motar baizo yawuce ba kuma bai barta tawuce ba yasata kara wuta kamar wacce zata tashi sama mintina kadan ta bacewa ganinsa,

Asukwane ta shiga cikin barek din ta nufi garejin gidansu taje ta ajiye bike dinta tafito tawuce ciki,

Dada ne zaune shi kadai yana kallon labarai wanda ake gabatarwa a nta (news @ 9),

Kusa dashi taje ta zube acikin kujera,

"Dada...!"

Murmushi yayi ya kalleta,

"Mai sunan mama daga ina haka?"

"Dada daga stadium nake daga nan kuma nabiya ta club amma ban jimaba nafito.."

"Ai nadawo ina tambayarki awurin blessing tace kin fita, tunda naji haka nasan kallon kwallo kika tafi"

Murmushi tayi tana kunce zaren jikin combos din dake kafarta,

"Dada ina katafi da?"

"Nima naje headquarter dinmu ne saboda naman approval din new staffs dinmu wanda aka turo, sune da safe kikaga inata cuku cukun yimusu signing"

"Yawwa dada ka samar min driver?"

"Kiyi hakuri mana mai sunan mama, ai zuwa gobe insha Allah zan baki driver acikinsu, ina sone nasamu yaro nutsattse, kamilalle mai hankali wanda zai rinka kulawa dake koda bana nan kamar yadda malam isa yayi,nasan kinji mutukar dadin zama dashi ko ba haka bane?"

"Hakane dada" tabashi amsa bayan ta kammala cire combos din dake kafarta,

Kan dining ta kalla "dada me kuku yadafa yau?"

"Mai sunan mama tuwon semovita yayi mana miyar kuka.."

Yayyatsina fuska tafara ta tashi tana kunkumbura baki domin idan akwai abinda ta tsana a duniya to tuwone ko sunanshi ma bata sonji,

Bedroom dinta ta shiga ta rage kayan dake jikinta tanayi tana tsaki saboda ta tsani ayi tuwo agidan nan gashi kuma shi dada yana son tuwo sosai,

Toilet ta shiga ta watso ruwa tafito tazira wata coffee colour din doguwar riga mai santsi, kanta babu dankwali ta sauka kasa ta shiga kitchen,

Tea tadafa ta zubo a cikin wani dan mitsitsin tea flask na silver ta koma falo wurin dada ta zauna,

Tayashi kallo take suna yar hira har 10 tayi,

Dakinta ta koma tayi sallar mangariba da isha ta hau kan gadonta wanda yake cike da tedy manya manya,

Laptop dinta ta jawo ta kunna tafara kallon wani american film mai suna _Revolution_,tana kallo tana hamma saboda baccin da yafara cika idonta,

Dr yazeed taga yana kiranta takan screen din dake wayarta, mikewa tayi ta kwanta taja teddy guda daya ta rungume,

"Likita bakayi bacci ba?"

"Kira nayi naji ko kinyi bacci ko kuma kina zaune kina kallo sai gobe kizo mana aiki a makare.." Tajiyoshi yafada yana murmushi,

"Likita kenan zan dai baka mamaki idan nafara zuwa office karfe 7"

"Idan hakan tafaru nikuma ina mai tabbatar miki da cewar zan baki gagarumar kyauta"

"Likita kenan.." Tace dashi tana murmushi,

"Maryama kenan kidai daure ki fitar da gwani acikinmu saboda kowa sonki yake, ko kina sone kiga mun fara fad'a?"

Shiru tayi tana dan murmushi kasa kasa,

"Kodai har kin fara baccine kin kyaleni inata surutu ni daya"

"Wallahi baccin dai nake son nayi"

"To bari na kyaleki karna cikaki da surutu"

"Thank you dr" tace dashi tareda katse wayar, laptop dinta ta rufe ta jawo drewar din gadonta wacce take cike da wasu kwalabe ta debo kwalayen magunguna guda biyu ta bude.....


  _Gaisuwa mai yawa gareki maman Sultan, nagode Allah yabar zumunci._


*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment