Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA..9

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _*9*_

aishaummi.blogspot.com

   ~~~~D'an karamin tsaki shaddad yayi lokacin da yaga shigewarta cikin kasuwar,

"Yarinya kamar karuwa, komai nata irin na yan tasha, in banda tsabar duniyanci menene nata na shiga kasuwa tana taunar chewing gum?" Yayi wannan maganar acikin zuciyarshi,

Tunda ta shiga kasuwar bata fitoba sai da ta shafe fiyeda mintuna 20,duk yagama kosawa da jiranta sai faman tsaki yake yana bin hanyar da kallo domin ganin kota taho sai yaga shiru, yana nan zaune ya hangota ta fito tana ta faman taunar chewing gum dinta tana yin k'wai amma taunar chewing gum dinma cikin yanga da kinibibi take yi,k'ura mata ido yayi yanda take tafiya tamkar bazata taka k'asa ba saboda tsananin yanga, gashin kanta duk awaje kasancewar mayafin data yafa akanta bai gama isarshi ba,

D'auke idonshi yayi daga kanta aranshi yana jaddada tabbas mace mai kyau fitinace a duniya, yanzu kamar maryama yanda take da wannan tsananin kyau din da rashin kamun kai ai Allah ne kadai yasan yawan adadin mazan dake kwadayin kasancewa da ita,

Bude gaban motar tayi ta shiga ta zauna ta rufe tana mai cigaba da taunar chewing gum dinta, kallon ledar dake hannunta shaddad yayi saboda yana son ganin abinda ta siyo wanda har ta dade haka, sugar cane yagani acikin ledar an daddatsashi, mamakine da haushi suka kamashi saboda ganin yanda ta b'ata masa lokaci ta zaunar dashi gashi har lokaci ya kure yasan bazai samu salla a jam'i ba domin kafin su koma har an idar,

Cikin bacin rai ya yiwa motar key yahau titi, ita kuwa sarauniyar sai aikin latsa iPhone dinta take tana taunar chewing gum, chaten take da dr naz wanda har yanzu yana asibiti bai tasoba amma yace yau zai zo hira wurinta,

Har suka shiga barek din shaddad bai ko kalleta ba domin haushi take bashi tunda yazo garin nan bai taba rasa salla a jam'i ba sai yau ta dalilinta,

Bude murfin motar tayi zata fita, juyowa tayi ta kalleshi,

"Kajira blessing tazo ta daukar min kayana sai kaje kasaka motar cikin garage.."

Sake harzuka yayi ya kashe motar ya fito ya rufeta yace da ita,

"Ungo key dinki.." Bai jira amsarta ba ya wulla mata mukullin yayi gaba ranshi abace,kallo tabishi dashi ganin komai nasa yana yinsane cikin zafi zafi da zafin nama,

Bata damuba tawuce ciki tana yatsina fuska,

Blessing ce ta sauko da sauri tana rikeda duster a hannunta wacce ta kammala goge glasses din dake jikin window din dakin maryaman,

"Karbi key dinnan kije cikin motata ki dauko min kayana, akwai sugar cane idan kin kawo kisa minshi cikin fridge" abinda tafada kenan ta wuce sama, tana zuwa ta shiga wanka duk ranta abace yake saboda gadarar da shaddad yake nuna mata gamida wulakancin da yake son rinka yimata ako yaushe,

Ruwa ta sakarwa kanta tayi wanka mai kyau tafito, wasu kananan kaya ta tarar blessing tafito mata dashi,farar riga yar karama body hug da farin wando three quarter, pant kadai tasaka ta zira kayan tafesa turare ta fita bayan ta saka silifas dinta,

Fridge taje ta buda ta ciro robar coke guda daya ta nufi bedroom dinta, drewar din jikin gadonta ta bude ta ciro takardar wasu kwayoyi ta debi guda biyu ta jefa cikin coke din sannan ta sauka kasa da robar coke din a hannunta tana sha,

kan dining taje ta zauna domin ganin abinda kuku ya girka musu yau, white rice & stew tagani sai ko hadadden salad da aka hada agefe sannan ga dafaffen kwai nan agefe, shinkafar ta dan diba spoon uku tasaka miya amma ta zuba salad din da yawa sai dafaffen kwai data saka guda biyu, fara ci tayi sai dai kuma dakyar ta iya cinyewa abincin data hada,

Coke dinta ta shanye ta tashi takoma sama ta kwanta sai a lokacin ma ta tuna da cewar ashefa batayi sallar azahar ba bare la'asar kuma gashi yanzu har ankusa yin isha, kwanciyarta tayi ta mike ta lumshe idanunta.

  Tunda ta kwanta ta dan samu bacci ba ita ta tashiba sai karfe 8,dan siririn gyale ta dauka irin wanda tasaba yafawa tafita zuwa falon Dada,

Zaune ta sameshi kafarshi dore kan wani tumtum saboda ciwon kafar dake damunshi,

"Sannu dada, ciwon kafarne?" Tafada tana karasawa inda yake,

"Yawwa sannu mai sunan mama..." Dada ya amsa mata yana kallonta,

Agigice ta zauna akusa dashi tana kallonsa saboda yanada ciwon sugar sannan wannan ciwon kafar ma yadade yana fama dashi, itama kusan tayi gadon ciwon saboda tana fama dashi lokaci zuwa lokaci,

"Dada kodai sugar dinka ya hau ne?"

"A'a daughter lafiya lau fa nake"

Tashi tayi ta nufi dakinsa domin dauko na'urar gwaji wadda ta tanada musamman domin gwada mahaifin nata,

Tana fitowa taganshi zaune shida shaddad yana duba wasu takardu,

Agaban dada taje ta zauna ta ciro na'urar ta fara gwadashi, ajiyar zuciya ta sauke ganin sugar din bai hauba hakama jininsa shima bai hauba kawai dai ciwon kafarne ya tashi,

Mikewa tayi taje ta mayar da na'urar sannan ta dauko masa maganin da yake shafawa a kafarshi ta dawo falon ta zauna ta bude maganin tafara shafa masa a kafafunshi, shaddad yana kallonta ko kunyar fitowa ahaka bata ji,

Cigaba da Shafa maganin tayi tana ma mahaifinta magana ahankali,

"Father tunda kafar nan ta matsa kawai kaje saudiyya this time kar kaje chairo"

Murmushi Dada yayi yasake gyara zamansa,

"To daughter yanda kikace ai haka za ayi, insha Allah nanda 3 weeks zan nemi visa sai intafi"

Ahankali take murza masa maganin akan yan yatsunshi tana jijjiga kai cikin kulawa,

"Dada dan Allah ka rage cin tuwon semo dinnan, kaga yanzu sugar dinka normal yake Bai hau ba bai sauka ba"

"To mai sunan mama insha Allah za arage"

Mikewa tsaye tayi tana cewa, "yawwa father, ni shiyasa kullum cikin exercise nake saboda ban son nayi gadon wannan ciwon sugar din naka..."

Fita tayi daga cikin falon taje bedroom dinta ta dauko key din motar ta, falon ta koma ta mikawa shaddad key din,

"Am gashi ka saka min motar acikin garage.."

Kamar bazai karba ba sai kuma ya karba saboda nauyin idon mahaifinta da yakeji domin yajashi ajiki koda yaushe nunawa yake shi danshi ne ba bare ba,

Juyawa tayi ta fita aranta tana cewa "kai din dai kaine zaka dauke motar daga inda ka ajiyeta"

Bedroom dinta ta koma ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare saboda dr naz yazo, ayanda take dinnan ahaka ta fito zata fita wurinshi babu abinda ta kara, daga ita sai body hug din jikinta da wando three quarter iya gwiwarta sai dan siririn karamin gyalen data warware ta dora akanta sabanin da dayake adaure akanta ga wani sanyayyen kamshi dake fita daga jikinta,

Afalon kasa suka hadu da shaddad shima da alamar fitar zaiyi, batare da ya kalleta ba yawuce abinshi bin bayanshi tayi tana latsa wayarta amma kafin taje waje har ya dade awurin shi,

Ya bude kofar motar kenan yaganta ta fito ahaka ta nufi wata mota dake fake a gaba kadan da wurinda ya ajiye mata motarta, mamaki ne yaketa dawainiya dashi tun lokacin da yafara ganinta saboda dabi'unta mabanbanta ne da sauran matan da ya saba gani, in banda rashin tarbiya yaushe mace zata iya fita ahaka?

Motar ya shiga ya tadata ahankali ya nufi cikin garage din domin adanata lokacin tuni har maryama ta bude gaban motar dr naz ta shiga ta rufe ruf......


    _Gaisuwa mai tarin yawa ga baby Lilmeerahcute..!!_






*_Ummi A'isha_*

1 comment:

  1. Well gaskia aysha am a fan ov urs coz i've been reading N following ur novel,so keep it up
    We'll always follow u though with mistakeu made,ur a human N no one is above mistake .Thank u

    ReplyDelete