*_MARYAMA SARAUNIYA...!!_*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_💕
*_3_*
Tamkar wata dawisu haka take takawa tana yin tafiya mai cike da burgewa gamida ban sha'awa, duk inda tawuce sai dai kaji ana fadin,
"Welcome antyn yara..!"
Murmushi kawai take danyi dan takaitacce tawuce da haka ta samu ta isa d'akin yara domin ita kwararriyar likita ce afannin, tun tana yar karama burinta kenan nazama likitan yara domin tana mutukar kaunarsu,tana sonsu ko kadan bata gajiya da wasa dasu,
Lokacin da tasaka kafarta ta shiga cikin ward din wanda ya kasance mai mutukar girma da fasali ko ina dauke yake da hotunan ababan sha'awa na yara harda manyan tedy zube a gefe daya sannan ga katuwar tv ankunna musu cartoon domin debe musu kewa,
Mikewa nurses din dakin sukayi suna yimata sannu da zuwa,
"Antyn yara sannu da zuwa.."
Bata iya amsawa ba ta nufi wani bed inda take jiyo kukan wani yaro, ko kadan bata son taji yara suna kuka,kukansu tada mata hankali yake yi,
Da saurinta taje wurinda yaron yake shida mahaifiyarsa wacce taketa kokarin dura masa abinci amma yaki ci sai faman kuka yake, matar na ganin dr maryama tafara murna tana cewa yaron,
"To kayi shiru ga anty mai chocolate nan tazo..."
Daukar yaron maryama tayi ajikinta tana kallonsa jikinsa yayi zafi rau,
"Sorry, zaka sha chocolate??
Kai ya daga, mayarshi tayi ta ajiyeshi akan gadonshi tajuya wurin nurses din,
"Aje store afara fito da kaya"
Tun kafin ta rufe bakinta suka fita, sai da ta rarrashi wannan yaron yayi shiru sannan tafara dubashi, yaron ba karamin tausayi yake bata ba domin sikila ne,
Rubutu tayi ajikin wata doguwar takarda wacce ke manne agaban gadon, tana shirin barin gadon nurses suka shigo rikeda kwalayen chocolate manya manya, budewa tayi ta dauki guda biyu ta bawa yaron sannan tawuce zuwa next bed, duk yaron data duba indai ya isa shan chocolate to sai tabashi guda biyu haka ka'idarta take ko a office dinta idan ta duba yaro to sai tabashi chocolate kuma da kudinta take siya ta ajiye bawai asibitinne suke siya ba, hatta agida ma ta tanadi abubuwan yara ta ajiye domin tana mutukar sonsu,
Daya bayan daya ta rinka bi tana duba yaran wanda har wurin karfe daya taje bata gama ba sakamakon makarar datayi bata zo dawuri ba yau,
Agajiye tagama round din tafita iyayen yara sai sam barka suke yi mata saboda ganin yanda take kulawa da yaransu, duk wanda yakawo yaronsa asibitin nan to zaka samu dr maryama ta shiga ransa, mazan kuwa dake tururuwar sonta ata sanadiyyar kulawa da yaransu Allah ne kadai yasan adadinsu domin akwai wani senator a abuja kullum cikin yimata waya yake yana son ya aureta amma fur taki kuma bata komai suka hadu ba sai sanadiyyar yaronshi da bashi da lafiya sunzo Lagos zasu tafi Ethiopia to ta Lagos zasu tashi ganin yaron yana zazzabi sannan yakasa cin abinci sai amai yake yasashi daukar yaron zuwa asibiti, gaba daya yaron shekararshi daya, lokacin da ya kawoshi aka nuna masa office din dr maryama ya shiga dashi tana kokarin yin breakfast amma haka ta fasa cin abincin ta karbi yaron ta rikeshi ajikinta tafara checking dinsa babu zato ya kwara mata amai wanda har shi kansa uban sai da ya razana amma ita ko ajikinta, hakuri yafara bata,
"Likita kiyi hakuri dan Allah.."
Murmushi kawai tayi taja file din yaron tafara rubutu,
"Don't worry ai mun Saba da haka aikinmu ne..."
Rubutawa yaron magani tayi sannan ta dauki chocolate guda biyu dake ajiye agefen kujerarta ta sakawa yaron a hannu, to sanadiyyar wannan tasa mutumin yaji yana sonta, kusan duk bayan sati biyu sai yabiyo jirgi yazo wurinta amma ita bata jin zata iya aurensa,
Agajiye tabude office dinta ta shiga, babu kowa da alama dr sameer yafita, hand glob din hannunta tacire ta jefa cikin dustbin ta nufi toilet,
Handwash ta matsa a hannunta ta wanke sannan ta fito tawuce fridge, coke ta dauko guda daya da lemon tsami ta koma kan wata doguwar kujera wacce aka tanada saboda baki da wani madaidaicin glass table agabanta, kwandon abincinta ta jawo ta bude, wainar kwai da coke din taci ta dauki dan karamin tea flask dinta tanufi saman kujerarta ta zauna, files din dake kan table din tasoma bi tana duddubawa tana ganin yaran da dr sameer ya duba a yau, tea ta dan tsiyaya kadan ta matsa lemon tsami aciki tafara kurba, kusan ita dama abinci bai dameta ba tea take wuni tana sha kuma tea dinma ba madara empty sai dai kawai ta matsa lemon tsami aciki ta jefa tom tom,
Daga kanta tayi ta kalli kofa sakamakon budeta da taji anyi, dr sameer ne ya shigo yana rataye da jakar laptop dinshi da alama yatashi daga aikin,
Kujerar dake gaban table dinta yazauna yana kallonta,
"Likita badai har ka tashi ba?"
"Natashi mana, inada meeting ne yau shiyasa"
Jingina tayi ajikin kujerar tafara dan juyawa tana kallon hoton dake ajiye akan table dinta nawasu twins kyawawa wadanda suke yayan dr sameer dinne,
"To yau dinma dai zan fada miki kalmar da kikafi tsana wato Kalmar so....,agaskiya maryama duk namijin da yace baya sonki ko bakiyi masa ba to kawai yafada ne sakamakon yasan bazai samekiba ko kuma saboda wani personal interest nashi na kansa, ki daure kibani dama na aureki.."
Murmushi tayi ta rausayar da kanta tana juya kujerarta,
"Dr kenan, kullum dai muyita magana guda daya, nifa bawai naki aurenka bane no, kawai dai nafi son ka ajiye maganata agefe kaje ka kula da matarka da twins kids dinka..."
Murmushi yayi ya tashi yazagaya ta gefen datake zaune ya dafa table din tamkar wanda zai rungumeta,
"Tsoron matar tawa kike ko me?"
"Ba maganar tsoro bane..."
Murmushi yayi ya zuba mata ido,
"Kin san dai sai bayan da nai aure sannan nahadu dake da badan hakaba da kece zakizo first.."
Tea din dake hannunta ta dan kurba ta lumshe idanuwanta,
"Dr kenan.."
Juyawa yayi yana cewa "kin dai k'i zancen dr maryama"
Ita dinma murmushi tayi tabishi da kallo har yafita yabar office din, sauke idonta tayi akan table dinta.
Dr sameer kwararren likita ne afannin k'ashi, matarsa daya da yaranshi twins mace da namiji wanda akalla zasu kai shekaru biyu a duniya,
Fitar dr sameer keda wuya tasake nutsewa acikin kujerarta,i phone dinta ta ciro daga cikin jaka ta kunna tareda ciro laptop dinta ta ajiye akan table din, kararrawa ta matsa cikin sauri Joseph ya shigo cikin office din,
"Jona min laptop dinnan a charge..." Tace dashi tana zare cover shoe din dake kafarta,
Cikin sauri yaje ya jona mata tareda kunna plasma tv din dake manne ajikin bangon office din,
"Umm miko min wancan takalmin.." Ta nuna masa takalminta flat wanda ta ajiye musamman acikin office din domin yawo, takalmin ba awani nesa yakeba amma saboda tsabar mulki irin nata sai an dauko mata,
Dan yatsanta ta goga ajikin table din ta kalli Joseph,
"Anyi cleaning din office dinna yau..?"
"Yes dr anyi, cleaner dinma bai jima da tafiya ba"
"Ok dauko cleaner kasake gogewa dan Allah"
Takalminta tasaka ta fita da wayoyinta a hannu, office din dr yazeed ta nufa wanda bashida nisa da nata office din....
*_Ummi Shatu_*
No comments:
Post a Comment