Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA..2

*_MARYAMA SARAUNIYA...!_*

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

  _Dedicated to maryam Qaumi_💕

  *2*

   Zama tayi agaban mirror tafara tsarawa jikinta da fuskarta ado, akalla saida ta shafe jikinta da mayuka fiyeda kala biyar masu kamshi da taushi gamida gyaran fata,

Pink din janbaki tashafa tayi jagira ta saka kwalli acikin idonta take ta fito a maryaman ta sak mai ji da kyau gamida takama da baiwar da Allah ya bata, wani dan karamin roba ta dauko mai kamada maganin ciwon ido ta bude ta diddisa acikin idonta lokaci daya idanuwanta suka sake zama farare tatas yayinda digon blue din dake ciki yasake zama blue sosai amaimakon bak'i,

Tashi tayi takarasa wurinda blessing ta ajiye mata kayan da zata saka, bakar skirt ce doguwa yar kanti hadeda pink t shirt mai botira da dogon hannu sai dan siririn mayafi wanda zata yane kanta shima kalarsa pink,

Anutse ta saka kayan ta koma gaban mirror ta bude drewar din dake jiki ta ciro wasu barima na gold guda hudu kasancewar kunnenta kowanne huda biyune, bayan ta kammala sakawane ta sake ciro wata siriryar barimar ta gold wadda take dauke da wani dan zare ajiki da yan kyawawan flowers ta zira acikin hudar dake kan hancinta wanda ke gefen hagu,

Yar karamar sarka siririya ta sake daukowa ita dinma dai ta gold dince, kafarta ta hagu ta dora akan stool ta daura wannan sarkar ajiki tare da wani dan karamin zobe na gold shikuma a dan yatsanta natsakiya dake kafarta ta saka,

Hatta agogon da ta daura da sauran zobunan data saka a hannunta duk na gold ne, siririn mayafinta ta dan yafa akanta wanda ana iya hango gashinta dake kwance akanta musamman ma tagaba kasancewar taja mayafin baya ta kaishi tsakiyar kanta wannan dalilin ne yasa gashin ya bayyana afili tagaba,

Turaren cute lady da sauran turaruka tabi ta feffesa ajikinta wanda suka haura kala goma nan da nan ta dauki kamshi jikinta ko ta ina kamshine ke tashi,

Blessing ce ta bude kofa ta shigo tana dan rissinawa,

"Anty kin gamane?"

Juyowa tayi kamar bazata yi magana ba ta kalleta,

"Nagama, miko min phone dina a kan bedside drewar"

"Ok anty"

Cikin sauri takarasa ta dauko mata wayar ta kawo mata,

"Kashe a.c dinnan" tafada tana touching din wayar dake hannunta, Dr Naz tafara kira tareda kara wayar ajikin kunnenta,

"Hello kana inane?" Tafada bayan taji ya daga wayar,

"Gani nazo daukarki ki fito mutafi ina waje.."

"Kamar kuwa kasan yanzu banida driver wallahi,amma dai tunda ankawo sabbin sojoji nasan dada zai bani driver acikinsu.."

"Ai laifinkine tunda kece bakya son driving ban san dalili ba koda yake may be kina jin tsoron titine"

"Hakane wallahi ban fiya son ganin motoci dayawa akan titi ba, bari nafito.." Tafada tana murmushi hadeda katse wayar,

"Blessing bani shoes din mana..."

Da sauri blessing ta debo wasu pink colour din cover shoe masu shegen tsini tazo gabanta ta tsugunna tafara saka mata,

Tana rikeda wayarta tana yin waya da Dr Sameer tafita daga cikin dakin yayinda blessing kuma taje ta dauko mata laptop dinta ta saka acikin jaka ta rufe sannan ta dauki handbag dinta yar karama pink colour tafita da sauri tabi bayanta,

Tana sauka ta iske Dada a inda ta tafi tabarshi yanata signing ajikin takardu har time din bai kammala ba, wannan guy din shima yana nan atsaye,

"Bari nayi sallama da dada, i will call you back dr.." Tace da dr sameer tacikin wayar tareda katse wayar,

"Dada nashirya.."

Dagowa dada yayi yana kallonta cikeda kaunar yar lelen yar tashi kwallo daya a duniya,

"Gashi kuma driver din naki har yanzu ba asamu ba, ko zakiyi driving da kanki?"

Girgiza kai tayi "no dada, dr naz yazo daukana.."

"To shikenan insha Allah ma ayau zan samo miki wanda zai rinka kaiki tunda gashi ankawo mana sojoji sababbi"

"Ok dada thank you, i love you, bye"

Tace dashi bayan taje tayi kissing dinshi akumatu, murmushi yayi yabi bayanta da kallo cikeda kauna, shi kuwa sojan nan yana tsaye yana kallonsu ganin irin kwalliyar da maryama taci kamar wata aljana yasashi mamaki mutuka aranshi yafara tunanin to ko gasar sarauniyar kyau zata tafi?,ga wani irin rikitaccen kamshi da ya cika falon sakamakon shigowarta ciki, sannan ko yaya ta gifta ta kusa da mutum sai kamshinta ya bugi hancinshi yayi barazanar toshe masa kofofin hanci,

Cikeda yauki take takawa acikin barikin tana tafe tana waya da mutumin nata dr sameer, sojojin dake harabar wurin kuwa ko kallo basu isheta ba, da haka ta karasa wurin da dr naz yayi packing gaban motar ta bude ta shiga yayinda ita kuma blessing ta bude bayan motar ta ajiye mata jakar laptop dinta da handbag dinta sai dan madaidaicin basket wanda ke dauke da kayan breakfast dinta aciki.

Rufe kofar tayi bayan dr naz yayi sama da glasses din motar wanda sanyin kamshi ke yawo aciki,

"Maryama sarauniyar mata..." Dr naz yafada yana kallonta, ita dinma kallonshi tayi da juyayyun idanuwanta wanda suke kamar an diga zaiba aciki, ganinshi tayi sanye cikin kananan kaya t shirt da jeans blue colour, dr naz yarone sosai bawani babba bane amma yanace adole shi ita yake so,

"Dr naz ya office din?"

Murmushi yayi tareda jan motar suka nufi gate din fita daga gidan,

"Dr maryama kenan ai kece yar gata bakya zuwa office sai lokacin da kika gadama, amma ni tun 10 nagama ganin patients dina kawai dai dan ban ganki bane shiyasa nakasa tafiya"

Yatsina fuska ta danyi sannan ta dan saki murmushi irin murmushin nan na babu yabo babu fallasa,

"So kana so kace min kenan idan kayi dropping dina tafiya zakayi?"

"Ehh akwai wurinda zanje amma idan kika tashi just call me sai nazo na mayar dake gida.."

"Ok" tafada atakaice gamida kallon screen din wayar dake hannunta kirar galaxy 444,ganin me kiranta yasata yin dan guntun tsaki tareda kai wayar jikin kunnenta tafara magana ahankali kamar me rada koda yake gaba daya ma haka maganarta take ahankali kuma asanyaye,

Shidai dr naz kida yasaki yafara sauraren wakar d banj cikin wakarsa ta no be lie,

Final care specialists hospital suka nufa,har suka shiga cikin asibitin bata kammala wayarba,jiranta dr naz yayi har tagama sannan ta juya ta dubeshi tana dan murmushi,

"My guy ya akayi?"

"Nothing, sai nadawo.."

"Ok sai kadawo ko,bye bye take care" tace dashi tareda mika hannunta ta shafi kumatinshi daya,

Murmushi yayi yabita da kallo har ta bude kofar motar tafita, tana fita Joseph Massinger ya taso da sauri yazo ya bude bayan motar ya dauko laptop bag dinta da hand bag,da lunch box dinta yabi bayanta zuwa office dinta wanda shine office na hudu acikin jerin ofisoshin kwararrun likitoci dake girke a harabar asibitin,

Dr maryama, shine sunan dake makale asaman office din nata, tana budewa ta hango dr sameer zaune akan kujerarta ta aiki yana sanye cikin bakaken suit wadanda suka yi mutukar karbarsa,

Baki ta bude tana murmushi,

"Likita ya naganka anan, i hope dai lafiya?"

Murmushi yayi yana kallonta tareda karewa shigarta kallo wacce dama a ka'ida ita haka shigarta take daga riga da skirt yan kanti sai doguwar riga gown, tunda yake da ita bai taba ganinta da atamfa ko leshi ba kai hatta material sai dai kawai ta dinkashi dogawar riga, sannan tun lokacin data fara aiki a asibitin kusan shekaru uku da suka gabata bai taba ganinta da hijab ba koda kuwa talha ne, kai ko mayafi babba bai taba ganinta dashiba kullum sai dai tasaka riga da skirt wacce take kaiwa saman ciki, sai ko dan siririn mayafi marar kauri da girma, ko kuma tasa arabian gown ta yi rolling,

"Nariga da nagama ganin patients dinki, saboda tun 7 o'clock suke jiranki baki fitoba, yanzu kawai abinda zakiyi shine kije round ki duba patients dinki.."

Murmushi tayi bayan ta zauna akujerar dake gaban table din,

"Thank you dr..."

"You are welcome, kitashi kije kar kisake yin late"

Mikewa tayi tana lallon Joseph wanda shine Massinger dinta,

"Kaje ka siyo min lemon tsami saboda yakare jiya, idan ka dawo ka ajiye min acikin fridge..."

Tana kammala fadin haka ta juya tafita, kallo dr sameer yabita dashi saboda shidai a duniya yana tsananin kaunar maryama, komai tayi burgeshi take..

   _Gaisuwa mai yawa ga masoyan maryama sarauniya..._



*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment