Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 8

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


     *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

aishaummi.blogspot.com


    *_8_*


   _Gaisuwa mai yawa ga Salma (Ummi ja'eh),tareda Fatima Auwwal Mannir, sakonku ya riskeni nagode Allah yabar zumunci.._



    ~~~ Mayar da compliment card din yayi ya ajiye awurin da yake yana tsuke bakinsa,koma yayane dai shi bai damu da yasan amsoshin wadannan tambayoyin ba saboda ita maryaman ba damuwa yayi da itaba,

Gidansu maryama ya koma ya iske mahaifinta yana zaman jiransa domin yana son zai tafi office,

Key din motar yabawa Daniel driver wanda shine yake da alhakin kai Dada duk wani wuri da yake da bukata shima daniel din sojane asalima office ne suka bawa dada shi a matsayin driver,

"Shaddad ga key din motar maryama nan idan karfe biyar tayi sai kaje ka daukota"

Dada yafada fuskarsa kunshe da fara'a, karbar mukullin shaddad yayi cikin girmamawa ya nufi bike dinsa dake kafe anesa da wurin, hawa yayi ya tadashi ya nufi gidanshi wanda ke can gaba da nasu maryama domin nasa na sojojine masu star biyu kasancewar kowanne matsayi to da irin gidansu ba iri dayane gaba daya ba,

Gida mai lamba 25 shine gidansa wanda yake dauke da dan madaidaicin falo da bedrooms guda biyu,

Afalo ya zauna yafara kokarin cire uniform din jikinsa,kan doguwar kujera ya kwanta ya mike ya rufe idanuwansa saboda bacci yake son yi.

***

    Dr yazeed yana rike da hannun handbag dinta guda daya itama tana rike da dayan har suka karasa office dinta, hira yake danyi mata jifa jifa tana mayar masa da amsa,

Sai da yakaita har kofar office dinta sannan ya juya yawuce nasa office din,office dinta ta bude ta shiga wanda jama'a ke zaune cunkum suna jiranta,

Zama tayi akan kujerarta ta bude drewar dake jikin teburinta ta ciro wata katuwar chocolate da butter cake ta bare tafara sha,

Kararrawa ta danna Joseph ya shigo ta dubeshi kamar bazata yi maganaba sannan tace patients sufara shigowa, nan suka fara shigowa daya bayan daya,

Ta dauki tsawon lokaci tana duba yara marassa lafiya har ta kammala sannan ta tashi ta fita zuwa dakin yara wato (round) nan dinma ta dan dade domin har kusan karfe 1 saura sannan tafito ta koma office dinta,

Dr Naz tagani zaune acikin office din da laptop dinshi dore akan cinyarshi yana daddannawa,zama tayi akusa dashi tana yatsina fuska,

"Wash..." Tafada ahankali tana mai jingina kanta ajikin kujera,

"Meya faru?" Ya tambayeta yana faman kashe mata ido,

"Kafata tagaji ne" tabashi amsa, sunkuyawa yayi yafara cire mata cover shoe din dake sanye cikin kafarta, idan da sabo yasaba ganin wannan sarkar datake daurawa a kafarta da zoben da take sakawa sai dai shi sam bai taba damuwa da sai yasan dalilin da yasata take sakawa ba,

"Dole kafarki tayi ciwo irin wannan dogon takalmi haka anty maryama.." Yafada cikin tsokana yana dagowa daga sunkuyon da yayi bayan ya kammala cire mata takalman,

Murmushi tayi tana kallonsa saboda duk lokacin da yaso zolayarta to da anty yake kiranta,

"Taimaka ka danna min bell Joseph yazo" tafada tana gyara zamanta akan doguwar kujerar,

"Angama ranki ya dade"

Kan tabur dinta yaje ya danna kararrawa ko zama baiyiba Joseph ya shigo,

"Dauko min lunch box dina da flat shoe dina" tace da Joseph,

Daukowa yayi ya dora akan center table din dake gabanta ya ajiye ya fita,

Bude flask din tayi ta dauki fork tafara cin chips da kwai din da kuku ya soya mata,

"Dr ga abinci.."

Karbar spoon din hannunta dr naz yayi suka fara ci tare suna kama kama,cup ta dauka ta tsiyayo masa tea ta mika masa ya karba yafara sha ita kuma tana kurbar na cikin dan karamin tea flask din ta yar karamar kofar dake jikin murfin,

"Yau naso in turo miki wata mata ki duba min ita saboda ni taki yarda in dubata wai kunya takeji"

Dr naz yafada yana kallonta, tabe baki tayi ta mike domin dama lokaci zuwa lokaci yana turo mata patients dinsa ta duba masa su musamman ma yanmata kasancewar shi likitan mata ne,

Fridge ta nufa ta dauko coke roba daya mai sanyi ta dawo ta zauna,

Rike robar coke din dr naz yayi yana kallonta,

"Haba dr kamar baki san ba aso ahada ruwan sanyi da na zafi a lokaci guda ba? Kefa dr ce"

Yamutsa fuska tayi ta kalleshi,

"Dan Allah kabarni nasha idan bansha ba ai jina zanyi kamar marar lafiya"

"Kindai saba ne kawai"

Yace da ita tareda sakin robar yana kallonta,

Laptop dinshi ta dauka ta fara neman film din da zata kunna daga karshe ta kunna wani mai suna _behind enemies line_,tareda dr naz suka zauna suna kallon film din har yamma tayi, tanata zaune tana jiran shaddad yazo taji shiru tsaki taja ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, har karfe 5:30 bai zoba sai 6 saura sannan yazo, shikuwa shaddad yama manta da maganar wai zai dauko maryama daga office har sai da ya dawo daga headquarter dinsu sannan ya tuna,garage din gidansu maryaman yaje ya fito da motarta kirar KIA new model,kalarta ash colour,

Tana cikin office azaune ta cika tayi fam sai ga Joseph yashigo yace ta fito anzo daukarta, hada mata kayanta yayi ya fita, sai da ta gama bata lokacin ta son ranta sannan tafita ta na aikin yatsina fuska,

Yana zaune da farar riga mai gajeren hannu da wandon sojoji ya kunna radio yana sauraren wani programme na ban dariya,tafito kenan sai ga dr naz shima yana fitowa zai wuce zuwa theatre, kallonta yayi yana karasawa kusa da ita,

"Sai yanzu?" Yafada cikin tsokana,

"Wallahi tun dazu nake jiran driver amma wai bai zoba sai yanzu"

"Hakuri zakiyi maryama sarauniya.." Yafada yana kokarin gyara mata barimar gold din dake kan hancinta saboda yaga ta dan zamo kamar zata fadi, duk abinda ke faruwa akan idon shaddad ne dama tuni zuciyarsa tafara zargin cewar maryama tana bin maza ko kuma tana lesbian,wucewa tayi bayan dr naz ya gama gyara mata barimar wacce ta kasance mai kirar star sai walwali take,

Bude gaban motar tayi ta shiga ta zauna batare data kalleshi ba, shima tun kallon farko da yayi mata lokacin da zata shigo bai sake kallonta ba,

Shi Kadai yake murmushi yana driving saboda abin dariyar da yakeji, hannu maryama tasa ta kashe radion saboda har kanta yafara ciwo, sam bata son radio domin bata kaunar hayaniya a lamuranta,

Sake kunnawa yayi ta sake kashewa domin aganinta wannan ma ai rainin wayone, ita da motarta har ya tsaya yana yimata abinda yake so,

"Kai Malam bafa motarka bace tawace so baka da hujjar da zaka takura min..." Tafada akufule domin dama can ranta abace yake sai gashi kuma yasake kunnota,

"Tabbas nasan ba mota ta bace amma ya zama tilas nayi abinda nakeso da ita ahalin yanzu tunda a hannuna take.."

Tsaki taja ta juyar da kanta tana jin haushin sa saboda ya takurawa rayuwarta da yawa,

"Karki sake yimin tsaki dan ba ayimin tsaki kin gane? So respect your self..."

Rabuwa tayi dashi ta zaro iPhone dinta daga cikin hanbag dinta ta jona earpiece tasaka acikin kunnuwanta ta toshe, tana jinsa yasake kunna radion,

Sai da tabari sun kusa zuwa barikinsu sannan ta sake bata fuska tace,

"Namanta ina son shiga kasuwa zan yi siyayya.."

K'uluwa shaddad yayi saboda wannan rainin hankalin nata yayi yawa, yarinyar da batafi sa'ar kanwarshi ba itace zata rinka kokarin dole sai ta juyashi kamar wani waina acikin tanda,

"Hello father, ina son zuwa kasuwa, ka fadawa driver ya kaini"

Yajiyota tana magana da alama mahaifinta ta kira,

Tun kafin Dada ya kirashi yayi ribos ya juya ya nufi yoroba market domin itace tafi kusa dasu,kiran mahaifinta ne ya shigo cikin wayar shaddad,

Yana dauka yaji yafara rokonsa akan ya yi hakuri yakai maryama kasuwa,amsawa yayi da cewar ai sunma kusa zuwa kasuwar, katse wayar yayi ya mayar da ita cikin aljihun wandonshi,

"Bana zuwa wannan kasuwar domin abinda nake nema ba asayarwa anan.." Tafada fuskarta atamke ranta ahade,

"Ke ni ba sa'anki bane kuma ba drivern ki bane, kar ki rainamin hankali" yace da ita cikin zafin rai,

Fusgar motar yayi suka koma baya ya nufi wata kasuwar daban ransa abace,

Handbag dinta ta balle ta ciro wani chewing gum kato ta bare ta jefa cikin bakinta tafara tauna ahankali babu abinda kakeji sai k'as k'as,

Agefen titi yaja yayi packing saboda babu hanyar da mota zata shiga, bude motar tayi ta fita tana rike da handbag dinta earpiece makale a kunnenta, farin medical glass dinta ta ciro tasaka duk yana kallonta ta glass, sai taunar chewing gum take tana yin k'wai sai kuma ta fasashi tush taci gaba da taunar chewing gum din, titi ta tsallaka tana rike da high waist dinta data dage gudun kada ta kwashi datti dan haka duk k'waurinta awaje suke ga wani dogon takalmi dake kafarta amma kasancewar tasaba tafiya dashi takunta take yanda take so....


 

*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment