Wednesday 31 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 12,13

[5/7, 8:20 PM] Ummi Shatu: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


    _*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Gaisuwar fatan alkairi agareki Khadijat Buba, naci karo da sakonki kuma nagode, hakika nima ina yinki kamar yadda kike yina.._


   *_12_*

aishaummi.blogspot.com

   ~~~Tashin motar shaddad yayi batare da yako dubi Inda takeba, amma ta gefen idonshi yana kallonta tana dagawa alhaji bashir hannu ta cikin glass,

Sake hade fuska tayi ta bata rai saboda jin shaddad yanata aikin jan tsaki shikadai, maimakon ma ta zauna shiru sai ta dauki wayarta tafara kiran fahad abokinta,

Yana jinta ta karaci wayarta tagama lokacin da suka shiga cikin barikin, packing yayi ta bude ta fita shikuma ya shigar da motar cikin garage,

Ko cikin gidan nasu bai koma ba ya mikewarsa gidanshi domin yagama gajiya gashi ransa abace yake saboda ayanda ya fuskanta ana neman takura masa ta hanyar tirsasashi ya rinka bautawa maryama bayan kuma ita ba kintsattsiya bace, tsaki yasake ja ya bude gidan ya shiga,

Gefen katifarshi yaje ya zauna yafara rage kayan jikinshi yana yi yana tsaki har yagama cirewa,

Wani dogon tsakin yasake ja ya kwanta agefen katifar, tunani yake yi shima fa kila yanada nasa kason zunubin tunda shine ya dauketa ya kaita guest house din,

Haka yayita tunane tunane har yasamu yayi bacci. Washe gari kuwa bai fita da wuriba saboda sai misalin karfe 11:30,kansa tsaye ya shiga gidan yana sanye da jar riga da brown din wando fuskarshi babu annuri, a falon kasa ya iske maryama zaune daga ita sai rigar bacci wata Christian tana yimata kitso akanta, duk da bai san kallonta amma sai da ya dan sake dubanta domin ganin gashin kanta yayi shuri guda sai dai zuciyarshi tafi aminta da cewar na dokine ake kara mata saboda yawan gashin ya isa,

Wucewa yayi falon Dada Wanda shi tuntuni ma ya dade da fita daga gidan amma maryama tana kallonshi ta rabu dashi domin aganinta shine yafi cancanta da yafara yimata magana amma kawai tsabar isa da gadara yazo ya wani wuce kansa tsaye sai kace gidanshi,

Sai da shaddad ya shiga falon sannan ya tabbatar da cewa Dada baya nan, fitowa yayi hannayenshi acikin aljihunsa da niyyar barin gidan,

"Am kaga, kajirani na shirya yanzu zaka kaini office.."

Yajiyo muryarta cikin gadara da sigar bada umarni tana yi masa magana, batare da ya juyoba yawuce abinshi ya fita,

Tsaki taja ta mike tana karkade jikinta saboda angama yimata kitson domin manya manya ne ba kanana ba, bedroom dinta ta shiga ta shiga bathroom, wanka tayi ta fito tana daure da towel kamar wacce aka cewa ta leka window sai ta nufi wurin taje ta dauke labulen dake jiki ta leka, shaddad ta hango zaune asaman motarta sai cilla key din motar yake sama yana cafewa ba karamin kyau yayi ba gashi komai nashi yana yine cikin zafi zafi irin na jajartattun mazaje, amma shi bai ganta ba,

Sakin labulen tayi ta dawo tsakiyar dakin tafara shiryawa, wata shudiyar doguwar riga roba tasaka wacce ta kamata tayi mata das sannan ta bayyanar da shape din jikinta a fili,

Komai kalar shudi tasaka kama tun daga barimar kunnenta harta kan hancinta har zuwa takalmi da jaka,

Fuska a yatsine tafito tana kiran blessing domin ta dauko mata kayanta tabita dashi,

Shaddad yana zaune yana ganin fitowarta sai faman shan shan kamshi take tana wani bata rai,

"Banza karuwa..." Yafada acikin zuciyarsa amma afili sai yasake daure fuskarsa saboda shi yanzu ya tsani koda ganin fuskarta ne saboda duk farar fatar datake da ita to shi bakikkirin yake ganinta,

Sauka yayi daga saman motar ya bude ya shiga, itama cikeda takama tabude gaba ta zauna tana sake shan kunu,

Kiran fahad ne ya shigo wayar tata nan ta dauka cikeda yanga, tana gama waya dashi kiran dr naz ya shigo,

"Hello naz.." Tafada tana kallon fuskarta ajikin mudubin motar,

"Dr yau ko bazaki shigo bane? Gashi inata kiranki number busy dawa kike waya..?"

Sai da ta dan yi dariya kafin tabashi amsa saboda jin yanda yayi maganar sai kace wani shine gaba da ita,

"Dr naz kenan gani nan ahanya nataho nida driver na, sannan wayar da kaga inayi ba kowa bane fahad ne shikuwa kasan friend dinane ba saurayi na bane kawai mun zauna room daya dashi ne a Malaysia har muka gama karatu.."

"Iya matsayinsa kenan?" Dr naz yasake tambayarta,

"Wallahi matsayinshi kenan, lokacin da naje ban samu accommodation bane so sai yace min kawai naje muyi sikwatin so kawai sai nayarda muka zauna room daya har muka gama karatu, so yanzu yakirani ne yana fada min zai shigo Lagos gobe.."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.. Lallai yarinyar nan yar duniyace ta karshe, ko kunya bataji take fadin cewa ta zauna daki daya da namiji,namijin da mijinta ba sannan ba muharraminta ba" shaddad yafada acikin zuciyarsa, nan yasoma hango irin dukan da zaiyi mata da ace kanwarsa ce ita,

Jijjiga kai yayi yaci gaba da tukinshi baima san lokacin data gama wayarba, har sukaje asibitin bai kalli saitin datake ba saboda yaki jinin kallon fuskarta,

Bude motar tayi tafita tana takawa cikeda rangwada, yana zaune yana jiran azo a daukar mata kayanta har Joseph yazo ya kwashi kayan ya tafi,

Fisgar motar shaddad yayi ya tasamma head quarter dinsu ta sojoji yana zuwa yasamu Abbas wanda aka daukesu tare kuma tare sukayi passing out dashi,

"Abbas nifa nakusa barin garin nan, gaskiya dole nanemi canji saboda zaman garin nan bai dace daniba"

Dariya Abbas yayi ya kama hannun shaddad,

"Haba Navy, wai Kai sai yaushe idonka zai bude ne? Kai da yakamata kayi murna saboda ankawoka nan babu wanda kasani babu wanda ya sanka kaci karenka babu babbaka"

"Wallahi bazan iyaba, nidai kawai burina nasamu transfer domin rayuwar mutanen nan kwata kwata bata dace daniba"

Matsawa abbas yayi kusa dashi yafara magana ahankali,

"Naga wata sarauniyar kyawawan mata agidan oga ance yarshi ce, meyasa bazaka shigar da kanka wurinta ba kasamu ka kwashi rabonka.."

"Allah ya sawwaka wallahi, me zanyi da ita? Yarinyar da bata da maraba da karuwa.."

"Ai wayewar kenan Navy, kaine bazaka ganeba"

Shaddad bai sake magana ba yabar wurin domin yasan idan zancen yayi nisa to ranshi ne zai baci a banza.

K'arfe biyar daidai yaje dauko maryama, yanata zaune zaman jiranta ga kayanta Joseph ya kawo amma ita din kuma taki fitowa, fitowa yayi a fusace ya nufi office din nata saboda yafi minti goma sha biyar yana zaman jiranta,

Ko izini bai nemaba ya bunka kai cikin office din, tsaye yaganta tana gyara rigar jikinta gefe kuma dr naz ne yake tsaye yana gyara belt din wandonshi,

Hada ido sukayi shida ita ya sakar mata wata muguwar harara sannan yaja kofar da karfi jikake gammm ya rufe ya tafi,

Cikin halin ko in kula suka fito itada dr naz yana mai gyara necktie din dake daure a wuyanshi,

Ko a kasan takalminta babu kunya ta bude motar ta shiga kafin ta rufe kofar tuni har shaddad ya figi motar yayi gaba, sake jin kyamarta yayi saboda abinda idanuwanshi suka gane masa yanzu,

Suna zuwa gida yasake ganin wani ikon Allah domin fahad ne yazo wanda take kira da room partner dinta, hannunta cikin nashi suka shiga cikin gidan, wanka kawai tayi ta shirya cikin riga da wando tafito zasu fita club ita da fahad din,coke mai sanyi ta dauko ta ciro wasu kwayoyi guda biyu ta jefa aciki tareda ballo wasu manyan tablet guda biyu ta afa abakinta ta korasu da coke,

"Kefa yar kwayace har yanzu ashe kina sha.." Fahad yace da ita yana murmushi,

"Ai dole sai da tsaro room partner, yaushe zan daina? Ai na kariyane ko ka manta"

Dariya suka saka dukkaninsu harda tafawa taja hannunshi domin tafiya, duk wadannan maganganun a kunnen shaddad suka yisu nan yabisu da kallon takaici.......



_*Ummi Shatu*_
[5/7, 8:20 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



    *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  *_13_*

aishaummi.blogspot.com

~~~Bin bayansu da kallo shaddad yayi cikeda tsana da kyamatar hali irin nasu,

Janye jikinsa yayi yakoma ya nufi gida batare da ya shiga koda gidansu maryaman ba.

   Abangaren maryama kuwa tunda suka fita cinema suka fara zuwa itada fahad suka yi kallo na dan wani lokaci daga nan kuma suka fito suka tasamma club nan suka dade suna hirarsu sannan suna ganin abubuwan dake faruwa awurin,

Sai da misalin karfe 12 nadare harda yan mintuna sannan suka nufo gida, suna tafe suna hirarsu itada fahad wani lokacin idan hira tayi dadi har tafawa suke yi,

Gida ya kawota ya sauketa sannan yakoma domin zuwa masaukinsa wato murna hotel.

  Washe gari da safe  maryama ta sauko kasa ta shiga kitchen tana tsarawa kuku irin abubuwan da take son ya shiryawa fahad na karyawa,

Daki ta koma ta shiga wanka  tafito tasoma shiryawa, fahad ne yayi mata waya cewar ya karaso gidan dan haka tabashi izinin ya karasa dakin ya sameta,

Kayanta ta saka green din t shirt da skirt high waist ja,

Tana kokarin daura sarka a kafarta fahad ya turo kofar dakin ya shigo,

Murmushi ya aika mata dashi itama ta mayar masa da martani,

"Kinyi kyau sannan kinyi min laifi fa maryama.."

"Nagode fahad, laifin me kuma nayi maka?"

"Tunda nazo gidan nan baki hadani da dady dinki ba why?"

Murmushi tayi ta dauki dan karamin gyalenta ta yane kanta dashi ta juya tana kallonshi,

"Haba fahad kai ai ba bako bane agidan nan kazama dan gida, jiya lokacin da kazo dada baya nan yaje abuja sai asuba suka dawo, so yanzu after kayi breakfast zamuje ku gaisa.."

"Yawwa ko kefa sarauniyar mata, nagode da wannan damar da kika bani"

Murmushi ta saki na kasaita takama hannunshi suka fara saukowa daga kan matattakalar bene suna gangarowa kasa, daidai lokacin kuma shaddad shima yasako kai ya shigo cikin falon,

Dauke kai maryama tayi tasake makale hannun fahad acikin nata tana murmushi,

"Fahad kafata ciwo take wallahi.." Tafada cikin yatsina fuska,

Kan dining table suka karasa yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna kusa da ita,

"Maryama ciwon kafar nan nakifa akwai matsala, tun jimawa nafada miki"

Kallonshi tayi tana tsiyayar tea acikin wani dan karamin glass cup,

"Kai ai fahad maganarka bata da alaka da ciwon dake damuna, nafada maka dada ma haka yake fama dashi shiyasa last time nace mishi yaje saudiyya yaga dr.."

"Ayya to Allah yabashi lafiya, amma ke din dai yakamata nayi checking dinki before natafi"

Yace da ita yana dan murmushi kasancewar shima likitan matane, jin tayi shiru yasashi soko wani zancen,

"Maryama wai sai yaushe kika shirya aurata ne? Nafada miki dad dina ya matsa min da maganar aure nikuma kece macen da nake son mallaka a matsayin mata..."

Shiru tayi ta kura masa ido tana kallonshi yayinda shi dinma itan yake kallo, dan kyau fahad kyakkyawa ne sannan ga aji gashi dan masu kudi, to ita matsalar shine yayi mata yaro dayawa domin shi dinma irinsu dr naz ne yara, ita kuma a burinda take dashi tafi son auren namiji dan shekar 35 zuwa 40 aganinta kuma a ra'ayinta shine daidai da ita amma wadannan mitsi mitsin yaran ina zasu kaita?,

Pork ta dauka ta cakulo dankali takai bakinta tana kallonshi,

"Haba maryama say something please..."

Batare data zare cokalin daga bakinta ba ta langwabar da kanta gefe tana yimasa murmushi,

Ita gaba daya ma bata san auren namijin da yake yawan mu'amala da mata shiyasa duk taki auren doctors din asibitin su dake tururuwar sonta, shi kansa fahad din bata da sha'awar aurenshi saboda likitane yana mu'amula da mata sosai.

Hannunshi yakai ya rike pork din ya cireshi daga cikin bakinta,

"Nadai fahimci kawai ni dinne baki so ko maryam?"

Girgiza masa kai tayi tana murmushi,

"Ba haka bane fahad, yanzu dai kaci abinci idan kakoma gida zamuyi magana through call.."

"Hmm kullum dai haka kike cemin gaskiya nafara kosawa da wannan jan ran da kike yimin.."

"Haba fahad nace zamuyi magana, yanzu kaci abinci kawai.."

Badan yasoba haka ya hakura yaci gaba da cin abincin har suka kammala tayi masa jagora wurin dada suka gaisa lokacin shaddad yana zaune suna yin brreakfast in banda harara babu abinda ke hadashi da maryama har shi fahad dinma ji yake ya tsaneshi, fahad ne yatashi zai fita domin tafiya nan maryama tabishi ta rakashi,

Hannunta ya kama yana kallonta,

"Wancan guy din waye shi?"

Tab'e baki tayi, "driver nane.."

"Wai dagaske?"

"Dagaske mana, wani abune yafaru?"

"A,a babu komai"

"Shikenan tunda babu komai, sai munyi waya.."

Sakin hannunta yayi ya wuce ya nufi motarshi, tana tsaye awurin har saida taga fitarshi sannan ta koma cikin gida,

Takalmi tasaka tafita da wayarta a hannu ta shiga falon Dada tana yiwa shaddad kallon tara saura kwata,

"Father bari naje asibiti.."

Cikin fara'a da kulawa ya kalleta, "adawo lafiya mai sunan mama, Allah yabada sa'a"

"Amin father, thank you" tafada tareda mikewa tana kallon shaddad,

"Am muje ko"

Bai ko kalleta ba ya mike yayi gaba ta mara masa baya, so take ta kamoshi amma takasa domin kafin tayi taku daya shi yayi biyar, babu shiri ta hakura domin har tafara yin haki,

Motar ta shiga ta zauna tana dan daddanna kafafunta dake yimata ciwo,blessing nagama ajiye kayan shaddad ya fisgi motar, idanuwanta ne suka sauka akan hannuwanshi dake rike da sitiyarin motar,fatarshi luwai luwai take gwanin kyau ga gashi kwance ajiki, dauke idonta tayi daga kallonshi, har sukaje asibitin bai kalleta ba asalima lokacin da yayi packing kawar da kanshi gefe yayi har saida ta fice.

Da daddare misalin karfe 7 tace tana son zuwa stadium kallon ball, wata harara ya cilla mata sannan yayi magana,

"Ke nifa ba dan iska bane kin gane? Ki nemi mai kaiki stadium amma baniba.."

Dada tayiwa waya ta fada masa shikuma ya kira shaddad yace ya kaita, bama stadium ba duk wurinda take so ya rinka kaita,

Matsu tasha cikin jeans da t shirt da bakar hula facing cap,tasha bakin combos tafito, yana kallonta ta mirror din jikin motar lokacin da take tahowa,

"Karuwar banza karuwar wofi, Allah ya wadaran halinki" yafadi hakan acikin zuciyarshi,

Shiga tayi ta zauna tana faman taunar chewing gum, ko kallonshi ita dinma batayi ba ta dauke kanta tana kallon mirror,

Kaita stadium din yayi ya zauna acikin mota yana jiranta, sai wurin karfe 8 sannan aka gama wasan ya dauketa zasu koma gida,

"Ina son zan sai plate din wrestling" tace dashi tana tauna chewing gum din dake bakinta, bai bata amsaba amma ya nufi wurinda zasu iya samun Kaset din sai dai mamaki ya kamashi mutuka, shin ita wannan yarinyar wai duk dabi'unta irin na mazane? Itace kallon kwallo itace hawa bike itace kallon wrestling to ko shi da yake namiji ma wadannan abubuwan basu dameshi ba amma ita tana mace tana abubuwa irin na maza, da kanta tafita ta siyo Kaset din ta dawo cikin motar ya maida ita gida.

Haka rayuwar taci gaba da tafiya atsakaninsu kullum shaddad ne ke kaita office ya daukota sannan wani lokacin kuma har club yake kaita, yau ma akan hanyarsu ta dawowa daga asibiti ta yamitsa fuska tana yi masa magana,

"Anjima zaka kaini stadium da karfe 6"

Bai amsa ba dama tasan ba amsawar zaiyi ba, tana komawa gida ta shirya tana jiransa bai zoba gashi dada baya nan yatafi saudiyya ganin likita,

Cika tayi fam saboda tasan tayi missing din wannan wasan, karfe 8 shaddad din yazo ganin haka yasata fita tace yakaita club saboda bata son ta kyaleshi haka bai wahala ba duk tsiya dai sai ta fitar dashi awannan daren koda baya so,

Baiyi musuba ya dauketa suka fita zuwa club din, sanye take da wani damammen wando da riga body hug ita dinma ta kamata sosai, dan karamin gyale ta dora akanta kawai daga nan bata kara komai ba,

Lokacin da sukaje club din packing yayi tafita ta shiga ciki shikuma ya zauna acikin motar ya kunna radio yana sauraren wa'azi.

Maryama na shiga cikin club din taganshi cikeda maza da yanmata ashe wasu students ne yan university suke party awurin, tunda ta shigo samari ke kallonta domin ta hadu tayi awon gaba da imaninsu,

Can tasamu wuri ta zauna, diffff aka dauke wuta kafin tayi wani motsi tuni har an toshe mata baki anyi sama da ita, kokawa take iya karfinta domin kwatar kanta amma takasa kasancewar mazan da suka rufu akanta sunfi biyar,

Can bayan club din suka kaita suka ajiye sannan suka fara kokarin aiwatar da mummunan kudirinsu akanta....

  _Wayyo maryama maza zasuyi mata aika aika.._




*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment