[5/13, 7:16 AM] Ummi Shatu
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_💕
_Fatan alkairi agareki kawata fiddausi sodangi, nasan kema masoyiyar maryama sarauniya ce shiyasa nabaki wannan shafin kyauta keda maryama Abdul takwarar maryama sarauniya.._
*_20_*
aushaummi.blogspot.com
~~~Wani wahalallen barcine yayi gaba da ita, hatta acikin mafarkin ma in banda mafarkin shaddad babu abinda takeyi,
Mafarki take wai gashi nan ta ganshi awani gari wanda bata san kowanne bane, tana tsaye kan wani tsauni shikuma yana can nesa da ita, ahankali ahankali sai kara yimata nisa yake da haka har ta daina hangoshi,
Tashi tayi firgigit daga baccin da take duk tabi ta hada zufa kamar wacce ta kwara ruwa ajikinta,
"Me wannan mafarkin yake nufi kenan? Kodai shaddad yayi min nisan da bazan iya kamoshi ba har abada?"
Dafe kanta tayi wanda ke barazanar rabewa gida biyu,
"Ya Allah ka sassauta min, nasan hakkin shaddad ne yake bibiyata, hakkin sharrin da nayi masa ne shiyasa Allah ya jarrabeni da tsananin sonshi..."
K'walla ce ta cika mata idonta ta dauki wayarta dake ajiye agefen gado tafara trying din number dinsa amma kamar kullum yau ma wayar akashe take, cigaba da kira tayi har ba adadi daga karshe ta jefar da wayar akan gado ta kifa kanta jikin pillow tana hawayen bakin ciki masu cikeda nadama tareda dana sani,
Dakyar ta iya saita kwakwalwarta ta tashi idanuwanta jajur ta lallaba ta sauka k'asa inda Dada ke zaune akan carpet yana cin abincin dare,
Ganinta yasashi sanin ba kalau ba domin fuskarta da idanuwanta sun sanar dashi hakan,
"Daughter..." Yafada cikeda kulawa,
"Na'am Dada" ta amsa masa tana runtse idonta saboda ciwon da kanta yake yi mata,
"Bakida lafiya ne?"
Daga masa kai tayi sannan tace, "kaina ne yake ciwo.."
"To kinsha magani?"
"Ehh nasha.."
Tashi Dada yayi yabar abincin da yake ci yakoma kusa da ita ya zauna,
"Mai sunan mama kodai kinada damuwa ne kika boye min?
Idan akwai abinda yake damunki ki sanar dani domin nine mahaifinki baki da kowa sai ni, sannan bakida wanda yafini dan haka karki rufe min abinda ke damunki"
Hannuwanshi duka guda biyu ta kama ta rirrike sai ga hawaye yana bin kuncinta wanda yayi mutukar razana Dada domin sam yasan maryama ba mai saurin kuka bace sannan akwaita da dauriya tun tana yarinya karama, ita dai barta da shagwaba amma tanada dauriya akan komai,
Hankalinsa ne yaji ya tashi saboda bai saniba ko wani abune yake damunta haka wanda har yasata kuka,
"Mai sunan mama kodai mahaifiyarki kika tuno?"
K'wallar idonta ta share ta girgiza masa kai,
"To meyake damunki har yasaki kuka? Ko kina son zuwa kiga yan uwan mahaifiyarki ne?"
Nanma kai ta girgiza masa alamun a'a, take taga hankalinsa yayi kololuwar tashi nan kuma taji tsoron kar hawan jininsa ya tashi dan haka tayi gaggawar rarrashin tata zuciyar,
Murmushin dole tayi idanuwanta sun kada sunyi ja,
"Father babu fa abinda yake damuna, jikinane duk nake jinsa a daddaure amma yanzu na wartsake.."
"A,a daughter nasan abinda ke damunki, tunowa kikayi da mahaifiyarki shiyasa kikayi kuka, kiyi hakuri kiyi mata addu'a akan Allah yayi mata rahama yakai haske kabarinta,
Keda ko zama da itama bakiyi ba bare har kisan halayenta da dabi'unta da mu'amalarta,
Nida nazauna da ita ni nasan wacece ita,ni nasan wacece maryama, shiyasa bazan taba iya mantawa da maryama ba domin nagartacciyar mace ce mai hakuri mai fara,a mai son mutane sannan mai tsananin biyayya ga mijinta, sunanta kadai idan naji yakan sani farin ciki, maryama ta zauna dani a lokacin da banida arziki banida abin duniya a lokacin da ban mallaki komai ba, gashi dadin dadawa sunan mahaifiyata gareta shiyasa dan haka ko sunanta bana kira wannan dalilin ne ma yasa kema na kiraki da maryama na rada miki sunanta kuma sunan mahaifiyata,
Maryama ta nuna min dukkan soyayya ta duniya sannan ta rayu dani cikin kwanciyar hankali, lokacin bana zama agida kullum ina can jeji yawon yake yake haka zan tafi nabarta babu ko aike sai nadade zan dawo amma bata taba damuwa ba, ko mahaifiyata ce tazo ta tambayeta ko da wani abu sai tace babu.."
Shafa kan maryama yayi yana kokarin boye yar kwallar da ta taru a gefen idonsa,
"Ke kadaice yar da ta haifa a duniya kuma ta mutu wurin kawoki duniya dan haka kema kiyi koyi da ita ko kinyi aure kiyi kokarin rufe sirrin mijinki kinji mamana..."
D'aga kai maryama tayi tana murmushi, "insha Allah Dada nayi maka alkawarin zanyi irin abinda mahaifiyata tayi, bazaka taba jin na kawo maka karar mijina ba.."
"Allah yayi miki albarka mai sunan mama.."
"Amin father"
Tashi tayi taje ta hau kan exercise machine ta kunna tafara yi domin tana son ta warware ta rabu da damuwar dake damunta ko dan lafiyar Dada,
Tana daga kan exercise machine din shikuma Dada yana zaune a falo yana bata labarin kuruciyarta, murmushi tayi saboda jin yace tun tana rarrafe take kaunar butterfly shiyasa ma kusan duk kayan wasanta masu adon butterfly yake siyo mata,
Dawowa kusa dashi tayi ta zauna hannunta rikeda battle water mai sanyi,
"Father ashe na dade ina son butterfly.."
"Zan fito miki da wasu hotuna wanda aka yimiki kina karama lokacin hatta rigarki zanen butterfly ne ajiki"
Dariya tayi ta jingina ajikinsa, ko babu komai labaran da yabata yasata jin damuwarta ta ragu, sun raba dare suna hira da Dada kafin daga bisani ta shiga dakinta ta kwanta,
Kamar kowanne dare yauma kasa bacci tayi sai tsananin tunanin shaddad da yake addabar zuciyarta.
Haka taci gaba da kasancewa kullum cikin bege da kaunar shaddad amma har yau babu alamun sake ganinshi atare da ita,
Kullum cikin damuwa take sanin idan ta zauna agida damuwa ce zata yimata yawa yasata take fita aiki amma kowa yasanta da yaganta yanzu yasan akwai abinda yake damunta, akwana atashi har saida akayi shekara daya da yan watanni amma kullum son shaddad sake shiga zuciyarta yake, sam takasa cire tunaninsa aranta, wani lokacin ma idan ta zauna tana tunaninsa sai ta ringa cewa kila ma yanzu haka shi har yayi aure,
Samari bawai ta rasasu bane kawai har yanzu shaddad zuciyarta ke muradi,
Yauma kamar kullum cikin bacci shaddad yazo mata har yana cemata zata ganshi sannan zata hadu dashi amma sai taje wani gari,
"Wanne garinne shaddad?"Kafada min ko inane zanzo.."
Yabude baki kenan zai fada mata tayi firgigit ta tashi....
*_Ummi A'isha_*🏻
[5/13, 7:16 AM] Ummi Shatu🏻:
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_💕
_Anty maijidda musa your page done start...._
*_21_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Shiru tayi tana bin jikinta da kallo yanda duk tabi ta hada gumi, tagumi tayi tana son tuna inda ya dace tatafi neman shaddad ko Allah zaisa ta dace ta hadu dashi, amma zuciyarta taji ciwon rashin fada matan da baiyi ba, shekara daya kenan harda yan watanni tana fama da radadin soyayyarsa acikin ranta amma bata san inda zata sameshi ba,
Tashi tayi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito, blessing tagani tana kokarin fito mata da kayan da zata sa,
"Blessing ki fito min da kayana ki dauko babbab akwati ki shirya min su saboda gobe zanyi tafiya.."
"To anty.." Blessing ta amsa mata,
Shiryawa tayi tafito das da ita domin dama maryama badai kyau ba,komai tasa yimata kyau yake yi musamman ma bakaken kaya,
Falon Dada ta shiga ta zauna tana jiranshi yafito, bata jima da zama ba sai gashi ya fito cikin shirin fita wurin aiki,
"Father... Ina kwana"
"Lafiya lau mai sunan mama, har anfito?"
"Wallahi nafito Dada, zanje asibiti ne saboda ina son na rubuta leave with out pay..."
"Saboda me?" Yayi mata tambayar yana kallonta,
"Dada ina son zuwa wurin yan uwan mahaifiyata ne kuma zan dan jima acan.."
Ajiyar zuciya ya sauke yayi dan murmushi,
"Za kije zumunci kenan,dama ai rabonki da can tun farkon dawowarki daga Malaysia, yakamata kije kam"
"Insha Allah gobe zan tafi"
"Da wuri haka? Har kin gama shiryawa?"
Kai ta daga masa,"nagama father.."
"To Allah ya kaiki lafiya"
"Amin dada"
Tare suka fita ita ta dauki motarta ta nufi asibiti shikuma driver yajashi suka tafi office dinshi.
Tana zuwa agurguje ta dudduba marassa lafiya taje round ta fito, wasikar daukar hutun ta rubuta ta dauka da kanta ta nufi office din shugaban asibitin,
Kasancewar shima yana sonta sannan ya dade yana bibiyarta kan ta bashi dama ya aureta yasa atake awurin yayi approving yabata, babu wanda ta fadawa ta kwaso duk wasu kayanta dake cikin office din ta koma gida,
Akwatuna biyu manya manya sai da aka cika su da kayanta ahakanma dayawa barinsu zatayi bazata tafi dasu ba,
Tunda ta dawo shirya kayan suke itada blessing har magrib tayi a lokacin dada ya dawo,
Wurinshi taje ta zauna suka fara hira anan yake sanar da ita cewar yasa an yanko mata ticket din jirgi, zata bi jirgin karfe 9 nasafe,
Murnar da tayi gani take kamar ma har ta mallaki shaddad din, daren ranar tsananin murna bai barta tayi bacci ba.
Washe gari misalin karfe 8:30 tabar gida su dada suka rakata airport harda su blessing, wata kwalla ce ta siraro ta gefen idonta lokacin da suke yin sallama da dada domin idan ba dole ba bata son yin nesa dashi, sakin hannunshi tayi taje ta shiga cikin jirgin suna tsaye suna kallonta,
"Mamana kenan duk lokacin da za ayi tafiya sai anyi kuka, haka ma lokacin da tana karatu duk hutun da take zuwa idan zata koma to da kuka take komawa..."
Dada yace dasu blessing yana murmushin karfin hali domin shima zuciyar tasa a karye take.
K'arfe tara da rabi su maryama suka sauka a birnin abuja,
Taxi ta samu ta hau aka kaita har kofar gidan kanwar mahaifiyarta wanda ke cikin unguwar Yar adu'a housing estate, tana gaba mai gadi yana binta da kayanta har cikin gidan,
Tana kitchen tana hada abincin karyawa taga shigowar maryama, cikin sauri ta fito tana fadin,
"Oyoyo maryama.."
Rungume juna suka yi cikin farin ciki, har suka shiga cikin falon basu iya sakin juna ba,
"Anty maijidda yau kin ganni nasamu zuwa.."
"Naganki maryama ai gara da kikazo amma kya yi shiru ki kyalemu bakya ziyartar mu?"
Murmushi maryama tayi tana kallonta saboda bata da maraba da mahaifiyarta kamarsu daya sak,
"Anty maijidda ina yaran naji gidan shiru.."
"Maryama ai babu kowa agidan nan sai ko ke yanzu da kikazo duk sun tafi boarding school"
"Lallai anty kinyi kokari.."
"To bari na karasa shirya mana abincin nakawo dama oga baya nan bai kwana agari ba.."
Tashi tayi ta shiga kitchen ta karasa hada musu abinci ta fito dashi,
Dumamen tuwon shinkafa miyar agushi da tea sannan ga soyayyen dankali da miyar hanta,
"Kai anty duk wadannan kayan kuma a ina zamu durasu?"
Dariya anty maijidda tayi tana kallonta "maryama kenan ai dan oga baya nanne da yana nan to da sai nayi masa girkinshi daban"
"Lallai kina kokari gashi bakida yar aiki.."
"Ai shi baya son yar aiki maryama sannan nima nafi son nayi komai da kaina.."
Murmushi maryama tayi domin dama can tasan anty maijidda kwararriya ce wurin iya tarairayar miji da bashi kulawa shiyasa har yau mijinta ya kasa karo mata abokiyar zama,
"Yanzu maryama wa kika tsayar a matsayin mijin da zaki aura? Ina nufin waye proposed dinki domin yanzu ya kamata ki fara maganar aure tunda kin kammala karatu har kina yin aiki duk wata kina karbar salary, to yakamata kuma yanzu kifara shirin tunkarar shiga gidan miji domin yanzu shekarunki 30 babu watanni, dan haka ki nutsu ki zabo nagari mai kyawawan halaye wanda zakiji dadin zama dashi..."
Shiru maryama tayi sai dai maganar da anty maijidda tayi ya soso mata wurin da yake yi mata kekayi nan tafara shawara da zuciyarta kan shin ta sanar da anty maijidda abinda ya fito da ita daga gida ko kuma tayi shiru??
*_Ummi Shatu_*
No comments:
Post a Comment