Thursday 4 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 10

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  *_10_*

aishaummi.blogspot.com


~~~Ahankali ya fito daga cikin motar ya rufeta zuciyarsa na tir da halaye irin na maryama domin tun lokacin da yafara ganinta babu wani abu guda daya da zai iya tunawa wanda ya kasance mai kyau data aikata sai dai sabanin haka,

Motar dr naz ya nufa yana zuwa yafara knocking din glass din saitin da take amma shiru sai da yayi kusan sau biyar sannan ahankali yaga glass din yana yin kasa,

Hangota yayi jingine jikin kujera tana kallonshi amma ta kasa magana, cilla mata key din yayi cikin motar ya juya ya tafi batare da yace komai ba saboda ko ba afada masa ba yasan yanayin da ta shiga wanda har yasa ta kasa yimasa magana,

Tsaki yayi ya waiwaya domin yajiyo karar tashin motar dr naz din, su dinne shida ita suka fita a mota da alama wani wurin zasuje,

Wani dogon tsaki yaja yana mai kara jin tsanarta acikin ranshi,

"To yanzu ina zasuje acikin wannan daren?" Ya tambayi kanshi,

"Yawon shedancinsu mana" wata zuciyar tasake bashi amsa,

Hannayenshi duka ya zira cikin aljihunshi ya nufi gida yanata faman tunanin irin rayuwar da maryama ta zabarwa kanta indai kuwa hakane to tayi kyan banza, tayi kyan dan maciji, da wannan tunanin yaje gida ya bude ya shiga.

***

K'arfe 11:30 daidai maryama ta sauko cikin shirinta na fita office, wata kyakkyawar hadaddiyar doguwar riga Arabian gown ce ajikinta, coffee colour mai adon stones ajiki ta dan dora dan siririn mayafinta akanta, wani cover shoe mai mutukar tsini ta saka coffee colour, babu abinda kakeji sai kamshin tuarukan data bulbulawa jikinta wanda ya gauraya yabada wani daddadan kamshi na musamman,

Tana tafe tana gyara barimar kan hancinta harta ida saukowa, shaddad yana tsaye shida kukunta wanda yake rike da lunch box dinda ya hada mata abincinta kamar yadda ya saba,

Fuska ta dan yamutsa ta dubi kuku,

"Me ka dafa min yau?"

"Tea na dafa miki sannan kuma na soya miki chips.."

Girgiza kai tayi, "yau bazan ci chips ba, plantain nake son ci dan haka kasan yanda zakayi da wannan chips din ka koma kitchen ka soya min plantain anjima driver zai dawo ya karba after yayi dropping nawa..."

Daga ido tayi ta kalli shaddad bayan kukun yabar wurin, fuskar nan tashi ko alamun murmushi babu tana nan awani murtuke ahade kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa,

"Idan kafito da motar muje ko.." Tace dashi bayan tafara tafiya,

"Idan natafi to kisani bawani dawowa da zanyi na karbar miki abinci kwara ma ki tsaya ki tafi da abinki saboda ni ba bawanki bane"

Tsayawa tayi cak saboda jin abinda shaddad yafada, juyawa tayi da niyyar ta mayar masa da martani amma sai ta kasa saboda kwarjininsa da ya cika mata ido, dole ta koma falon ta nemi kujera ta zauna ta dauki wayarta tana latsawa tana jan dan siririn tsaki,

Tana nan azaune shikuma yana can tsaye har kukun ya fito da alamu ya kammala, tashi tayi ta fara tafiya batare da ta jira abinda kukun zaice ba,

Kusa da motar taje tana jiran karasowar shaddad, tun daga nesa ya kamata ya bude mata amma baiyi hakan ba har saida ya zo gaban motar, lokacin ne ya bude ya shiga, itama shigar tayi fuskarta babu walwala ko kadan saboda wannan guy din ya gama rainata tarasa dalili,

Fisgar motar taji yayi bayan kuku yagama zuba mata kayanta abaya, babu shiri taja belt ta daura domin ta fahimci zata iya buguwa da gaban motar mutukar bata daura belt ba,

Yauma radio ya kunna yana sauraro yayinda ita kuma taji ta takura, kai alla alla ma take yaje ya sauketa yakama gabansa domin yagama takurata,

Wurin wasu sojoji suka tsaya wanda ke tsaye agefen titi suna dan yin checking, I d card dinshi ya ciro ya nuna musu ya ajiye agefenshi bai mayar aljihu ba, bude motar yayi ya fita bayan yayi packing agefen titi,

Haushine yakama ta saboda ganin sai bata mata lokaci yake yi alhalin ita kuma tanada abinyi, tsaki taja ta juyar da kanta tana tunanin to ina yaje yabarta acikin wannan zafin haka?

A.c ta kunna sai kuma idonta ya sauka akan id card dinshi, dauka tayi tafara dubawa,

SHADDAD A SADIQ shine cikakken sunansa,

Date of birth dinshi ta kalla bakinta abude saboda tsananin mamaki,

"28 years? Dama duk wannan rainin wayon nasa 28 years yake shine zai rinka yin abu kamar wani ubana, mtswwww ashema age mate dinane, to daga yanzu nadaina jin tsoronka wallahi.."

Ta mirror ta hangoshi yana tahowa dan haka tayi gaggawar ajiye I d card din tasake daure fuska taci magani ta ciro medical glass dinta ta sa tadauki phone dinta tasoma latsawa,

Bude kofar mortar yayi ya shiga ya zauna ya figeta, ko dagowa batayi ta kalleshi ba wayarta kawai take latsawa jin ya kunna radio yasata kashewa,

Bai ko bita kanta ba yaci gaba da driving dinshi har suka shiga asibitin, yana packing ta sake bata fuska,

"Ka tabbatar kadawo daukana da wuri saboda akwai inda zanje da yamma bayan natashi daga aiki"

Ko kulata ma yayi balle tasa ran samun amsa daga gareshi, hakan da yayi yasake sata jin haushi,

"Kai dakai fa nake magana",

Mamaki abin yabashi jin ta kirashi da kai sai kace wata uwarsa lallai yarinyar nan bata da kunya,

Da karfi ta rufe kofar ji kake gummm ta nufi office dinta bayan Joseph ya taho dibar mata kayanta,

"Na hadu da shu'umin driver ni maryama" tafadi hakan acikin zuciyarta,

Ranta abace fuskarta babu walwala ahaka ta kammala duba patients ta nufi round, kasancewar ma yau bata samu patients da yawaba da wuri tagama,

Tana fitowa sukayi kicibus da dr Sameer dama wurinta ya doso,

"Maryama sarauniya azo atayani aiki mana..!" Yafada tareda langabar da kansa,

Dan murmushi tayi ta kalli fuskarshi,

"Baka gama ganin patients din bane?"

"Ai maimakon raguwa karuwa ma suke yi wallahi gashi yau dinnan natashi da ciwon jiki"

"Ayya sorry, to muje"

Jerawa suka yi zuwa office dinshi suka shiga kowannensu yaja kujera ya zauna patients suka fara shigowa suna dubasu, suna yi suna hirarsu har patients din suka kare,

Agogon hannunta ta kalla karfe 1:30,mikewa tayi tana kallon dr sameer,

"Dr bari naje office saboda yau ina son komawa gida da wuri akwai wurinda zanje"

"To shikenan dr, amma ki sani idanuwana basu gaji da kallon kyakkyawar fuskar maryama sarauniya ba.."

Murmushi tayi ta juya tafita batare data sake yin magana ba,

Office dinta ta shiga ta zauna ta dauki tea dinta tafara kurba tareda kiran dada awaya,

"Father dan Allah ka turo min wannan yaron yazo ya daukeni saboda nagama abinda zanyi kuma ina son zuwa gidan gona ta idan nadawo.."

Cikeda mamaki taji Dada yace, "mai sunan mama shaddad dinne yaro? Ai yayanki ne saboda ya girmeki"

Shagwabe fuska tayi tace, "wallahi Dada yarone bai girmeni ba the same age muke dashi, yau naga date of birth dinshi 28 years yake..."

"Kina da son girma daughter, shikenan zan turo miki shi" taji Dada yafada yana murmushi,

Katse wayar tayi tana magana ahankali,

"Ai ni yanzu nadaina jin tsoronshi tunda na fahimci shi yarone ba girmata yayi ba wallahi"

Tashi tayi taje kan doguwar kujera ta kwanta tana jiran zuwan shaddad, shiru bai zoba har 3 tayi, tana nan akwance dr naz yashigo ya zauna, tana daga kwance shikuma yana zaune suna hira,

3:30 Joseph yazo ya shaida mata driver yazo, kayan tabashi ya fita dasu ita kuma ta zauna jan aji, sai da yafi minti 15 yana jiranta bata fitoba,

Motar ya rufe ya fita ya shiga masallacci domin yin sallar la'asar saboda yaji anata kokarin tada salla,

Ita da dr naz suka fito har zuwa wurin motar, ganin baya ciki yasa tasake kuluwa, wato duk lokacin data bata tana zaman jiransa shine zai rufe mortar yatafi?

"Dr muje ka ajiyeni agida" tace da dr naz,

"Ok babu damuwa dama dan baki bani wannan damar bane"

Murmushi tayi tabi bayanshi zuwa motarshi, shiga tayi yaja suka tafi, basu jima da fitaba shaddad yafito, ya dade atsaye yana jiran fitowarta yaji shiru,

Ganin karfe biyar saura amma bata fitoba yasashi niyyar binta office dinta, karo nafarko da yanufi office din domin yagane hanyar da take bi,

Dr maryama shine abinda yaga an rubuta asaman office din wannan ya tabbatar masa da cewar office dinta ne, ahankali ya buda ya shiga, wani sanyine ya ratsashi gamida daddadan kamshin turaren wuta wanda take kunnawa,

Ciki ya shiga yana bin office din da kallo wanda ya tsaru iya tsaruwa tamkar office din shugaban kasa,

Kan table dinta wani hadadden dan abune a ajiye da hoton butterfly ajiki, ga hoton wasu kyawawan yara, gefe kuma wata karamar drewar ce ta glass dauke da kayan tea su gwangwanin madara, Ovaltine, Milo, cornflakes, golden morn,da sauransu,

"Lallai yarinyar nan yar gayuce, a office dinma dadi takeji kenan" yafada acikin zuciyarsa yana girgiza kai, Joseph ne ya bude kofa ya shigo ganin shaddad yasashi mamaki,

"Ko dr tayi mantuwane?"

Kallonsa shaddad yayi, "a'a nashigo ne naduba ko tana nan"

"Ai tajima da tafiya itada dr nazir.."

Juyawa shaddad yayi ya fita bayan yayiwa Joseph sai anjima, ranshi abace yabar asibitin yana tunanin wannan ai wulakancine tasa yazo kuma shine zata tafi.

Ita kuwa maryama har taje gida tayi wanka ta shirya tasaka pink din t shirt da bakin trouser wanda ya kamata sosai, wata hula tasaka irin wacce yan fulani kesawa sai dai ita tata ta robace ba ta kaba ba, wani takalmi ta daura sau ciki pink colour tasha turare ta fito taje ta dauko bike dinta tafita saboda gidan gonarta take son zuwa wanda ke can titin zuwa kiri kiri,

Kamar kullum kure wuta tayi tana shara gudu atiti,

Shaddad shima akan hanyarsa ta dawowa gida yashawo kwana kenan ya hangota tana tahowa zata wuce.....



      _Gaisuwa marar adadi gareki ummu mukhtar nagode Allah yabarmu tare..._



*_Ummi A'isha_*

1 comment: