Wednesday 31 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 16,17,18,19

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   
_Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  *_Gaisuwa mai tarin yawa ga Maryam s Bello da Aysha garkuwa, tabbas ku masoyana ne na hak'ik'a dan haka wannan shafin na badashi tukwici agareku daku da duk wani wanda yake jin yana son ummi Shatu_*

aishaummi.blogspot.com

     _*16*_

~~~Tagaban gidansu maryama yawuce yana jin wani bacin rai yana ziyartar zuciyarshi,ko daga ido bai yi y kalli gidanba har yayi nisa dashi amma acikin zuciyarsa damuwace kwance saboda yasan mahaifin maryama ya kullace shi acikin ransa domin yana tsananin son yar tashi sannan ya daukeshi kamar dan cikinsa yabashi dukkan yarda sai dai kuma daga karshe yaci amana,

Tamkar marar jini ajiki haka yake takawa har ya karasa fita daga cikin barikin, taxi ya tara ya shiga ya tasamma tashar mota.

***

  Tsalle ta doka ta fad'a kan gado ta kwanta tana shakar daddadar iskar air condition din dake ratsata, yanzu kam ranta yayi mata fari kuma hankalinta ya kwanta sakamakon mayarwa da shaddad martanin abinda yayi mata da tayi,

Bargo ta jawo ta rufe jikinta ta lumshe idanuwanta tana jin wani irin farin ciki yana ziyartar zuciyarta,

Rungume daya daga cikin manyan teddy din dake kan gadon nata tayi tana murmushi,

"Wai har ni wannan yaron zai daga hannu ya mara sannan ya kirani da karuwa..., sannan kuma har ya tsammaci zama lafiya, wallahi bazai yiyuba, yanzu nasan na tabbatar masa da cewa ni karuwar ce kamar yadda yace.."

Duk wadannan maganganun tana yinsu ne acikin zuciyarta fuskarta kunshe da fara'a, ranta fari tas bacci ya kwasheta.

  Washe gari kamar kullum haka ta tashi tana zuba mulki tayi wanka ta shirya kuku ya hada mata abincinta kamar yadda ya saba, wata red din gown tasaka mai adon duwatsu ta yafa dan siririn mayafin rigar tana ta faman zuba kamshi,ga yar siririyar barimar gold tasaka acikin hudar hancinta domin tana tsananin son kwalliyar hanci,

Falon Dada ta nufa tana tafe tana taunar chewing gum, zaune ta iskeshi ya kammala breakfast yana jiran driver yazo ya kaishi office, zama tayi agefenshi tana dan murmushi,

"Good morning father.."

"Morning daughter, har anfito?"

"Nafito Dada.."

"Gashi kuma babu mai kaiki office, koda yake kibari idan driver na yazo sai mu fita tare muyi dropping dinki"

"Babu komai dada kabarshi ma zanyi driving da kaina yau..."

"To shikenan dama ina son kifara driving din saboda bana son nasake baki wani drivern asamu wata matsalar"

"To Dada, insha Allah ma daga yau ni zan rinka kai kaina office ina dawowa.."

"Idan kikayi hakan nima hankalina zai fi kwanciya"

Murmushi tayi ta mike tsaye, "Dada bari naje natafi.."

"To mai sunan mama sai kin dawo sannan daga yanzu zuwa yamma zan turo miki kudin da kika nema harda kari.."

"Dada rencen kabani?" Ta tambaya tana dariya wanda har saida kyawawan fararen hakoranta suka fito waje,

"Kyauta nabaki daughter saboda ina son ki samu ki kammala ginin asibitin naki.."

"Ai dada akwai saura sosai yau idan natashi daga office zan biya nadubo ginin, nagode sosai dada Allah ya kara girma da lafiya.."

"Amin mai sunan mama"

Fita tayi fuskarta kunshe da murmushi, har cikin motarta blessing ta rakata tana dauke da hang bag dinta da sauran kayan tarkacenta nazuwa office,

Bakin glass tasaka ta daura belt ta tashi motar, sosai motar tayi mata kyau kuma ta karbeta, ahankali tafara driving tabar harabar wurin ta nufi asibiti.

  Tunda shaddad yabar Lagos bai ko je gidaba ya tafi Benin domin abubuwan dasu gudanar awurin masu muhimmanci ne, dadin dadawa kuma za abasu training na sati biyu shiyasa ma baiyi yunkurin zuwa gidaba, kullum da haushin abinda maryama tayi masa yake kwana yake tashi gaba daya yakasa mantawa da ita balle ya manta da abinda tayi masa, zuciyarsa duk lokacin da ta tuno masa da abin sai yaji kamar zata hudo kirjinsa tafito waje, ahaka ya daure ya kammala wannan training din ya nemi izinin zuwa gida kuma cikin sa'a ya samu, shiryawa yayi ya hari gida saboda yanada abu mai muhimmnanci da yake son aiwatarwa.

   K'arfe Biyar daidai maryama ta fito daga cikin office dinta ta nufi packing space domin daukar motarta, dr sameer ne ya biyota a baya yana tsayar da ita,

"Ranki ya dade har zaki fita..?"

Murmushi tayi ta bude motarta ta dafa murfin kofar motar ta dage glass dinta dake sanye afuskarta ta mayar dashi kan goshinta,

"Wallahi har zan fita dr, ina sone nafara zuwa wurin ginin hospital dina da akeyi acan agege"

"To Allah yabada nasara, dama kawai zuwa nayi nace miki wani abu idan kin bani dama sai na fada.."

"Nabaka dama dr kafadi ko menene.."

Sai da ya danyi murmushi sannan yace, "kinyi kyau yau, sannan da ace zaki bani dama to da na aureki na kasance dake har abada.."

Murmushi tayi ta shiga cikin motar ta zauna, tana kokarin daura belt ta kalleshi,

"Dr kenan zandai baka damar nan in gani.."

"Amma kuwa da kin gama yimin komai"

Rufe kofar tayi tana murmushi ta tashi motarta ta fita tana yi masa bye bye, can agege ta nufa wani katon daji inda ake gina mata asibitin yara wanda yake mai girman gaske, kasancewar ginin katone yasa ko rabi ba ayiba, fita tayi ta dan dudduba takoma cikin mota ta nufi gida, tana zuwa gida ta sake yin wanka ta tsuke tafito domin zuwa stadium,

Kullum haka take bata da lokacin hutu sai week end sai dai tunda samari suka yi yunkurin keta mata mutuncinta har yau bata sake komawa club ba.

  Lamurranta kawai take aiwatarwa hankali kwance kuma yanzu tafara ji a zuciyarta cewar zata zabi daya daga cikin samarinta dr sameer ko da yazeed ta aura saboda shi dr naz da fahad duk yara ne amma har yanzu  zuciyarta ta gaza tantance mata wanda ya dace ta aura, batun shaddad kuwa tuni har ta mance dashi saboda yanzu a kalla za ayi kimanin watanni biyu da tafiyarsa daga gidansu.

   Fitowarta kenan daga wanka ta danyi abubuwan da zatayi ta fesa turare ta saka rigar bacci pink colour light, rigar bata da nauyi sannan iyakacinta gwiwarta,

Kwanciya tayi ta kunna air condition ta kashe wuta, babu bata lokaci bacci yace muje zuwa, can cikin dare tana tsaka da bacci taji kamar motsin ana daure mata hannu ta baya, sake gyara kwanciyarta tayi, abu sai kara gaba yake sai jin kafafunta tayi suma a daure, kafin ta iya saita tunaninta har andaure mata baki, a lokacin tsoro da razani suka dirar mata, ihu take son yi amma babu hali, tana ji aka dauketa aka dorata akafada akayi waje da ita cikin sand'a,

Hankalinta idan yayi dubu to duk yagama tashi sannan gashi garin bakikkirin yake da duhu kasancewar anyi ruwan sama gashi babu wuta kuma ankashe injin da aka kunna tun karfe 1,

Wani lallausan hannune ke rikeda ita sannan ga wani kamshi mai dadi da sanyi da take shaka, zuciyarta sai harbawa take a tamanin musamman ma dataga an nufi dajin kare kukanka da ita wanda ke cikin barikin daga can karshe gashi yayi nisa da gidajen cikin barikin ko kashe mutum za a iya yi batare da an saniba,

Kan wani yayi taji an jefata tareda take kafafuwanta, idanuwanta ta runtse dan tsananin azaba, ahankali taji an matso saitin fuskarta, fitila ya kunna ya haska mata fuskarsa take taji tana shirin sakin fitsari a wando saboda ganinshi, idanuwanta ta zazzaro saboda tsananin firgici,

Daurin da yayiwa hannunta da kafarta ya kunce yasake saka kafarshi ya take kafarta, kyallen da ya daure bakinta yakunce mata ya kura mata ido,

Ita dinma kallonshi take fuskarta cikeda tsoro tana kokarin ja da baya sai dai amma takasa saboda ya take mata kafafu wanda take ji kamar ya karya mata su, cikin rawar jiki take kallonshi tana rufe bakinta, ba kowa bane illa shaddad, yana sanye da bakin wando da bakar riga ajiki an rubuta Nigerian Navy,

"Kinyi min sharrin fyade ko? To yau zanyi miki na gaske in yaso sai mahaifinki yasa aharbeni, yau zanyi miki abinda baki taba ji ba ko acikin tarihi so kishirya..."

D'aga mata kafarta yayi daga takewar da yayi take tafara jada baya tana girgiza masa kai cikin rawar murya mai hadeda tsoro tareda firgici tafara magana,

"Dan Allah dan annabi kayi hakuri, dan Allah karka keta min alfarmata...."

"Shhhhhh...." Yadora hannunshi akan bakinsa,

"Karki kuskura ki hadani da Allah saboda yau sai na nuna miki cewar ke karamar karuwa ce, zan nuna miki ke ba kowa bace.."

Ganin yafara kokarin kunce belt din wandonshi yasata cigaba da matsawa baya tana runtse idonta gashi duk tabi ta kukkuje jikinta sai jini ne yake fita, yana fara dosota ta sake yin baya tana shirin yin kuka....

*_Ummi Shatu_*🏻
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



     *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Kuna raina akoda yaushe, Basma er lele, Nasma mai Kano, Umma yahaya musa (marubuciyar goyon kaka), tareda Baby Rasheed...nagode muku Allah yabar zumunci._

aishaummi.blogspot.com

   *_17_*


~~~Ja da baya take yana binta tana sake jada baya yana sake matsowa da haka har taje ta tokaru da wani katon ice,

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba..." Tafada idanuwanta sunyi jajur suna shirin fitar da hawaye,

K'afarsa yasa ya take kafarta guda daya nan taji wani radadi ya shigeta, babu shiri ta bude baki da niyyar kwalla ihu,

Cikin sauri ya katseta,

"Shhhhh, idan kika sake kika yimin ihu wallahi sai na lahira yafiki jin dadi,kin yimin karya kince zanyi raping dinki to yanzu zanyi raping din naki dagaske...."

Hannu tasa ta toshe bakinta tafara jijjiga masa kai alamun yayi hakuri kar ya aikata abinda yake shirin aikatawa,

Kafarta ya kama yajawota gabanshi ya direta, rufe idanuwanta tayi saboda ganin abinda ke shirin faruwa gashi ita ba wani iya addu'o'i tayiba balle ta karanto,

Shi kuwa shaddad zuciyarshi sai angazashi take tana zugashi akan ya aikata hakan amma kuma wani bangaren na daya zuciyar tashi sai hanashi take tana cewa,

"Haba shaddad kai da baka taba aikata zinaba koda wasa meyasa yanzu zaka aikata baka tsoron haduwarka da ubangiji? Ko baka tsoron daukar cuta ajikinta tunda dai ba kamilalliya bace ita..."

Shawarar zuciyarsa yabi na kawai ya kyaleta saboda ko yanzu yasan ta gane kuskurenta sannan ta fahimci shi ba sa'anta bane tunda gashi nan har hakuri take bashi,

Mayar da belt dinshi yayi ya daura yana kallonta, jikinta inbanda rawa kamar mazari babu abinda yake yi ta runtse idanuwanta ta gagara budesu,

"Mtsssss Allah ya sawwake na hada jiki da karuwa irinki wacce take bibiyar maza kala- kala,na tabbata idan na kusanceki sai na dauki cututtuka barkatai...."

Shureta yayi da kafarsa nan ta fadi sharaffff, ko kallonta bai sake yiba ya juya yayi tafiyarsa mintuna kadan ta daina hangoshi, duk irin radadi da ciwon da jikinta yake yi mata hakan bai hanata tashi da rugawa aguje ba, gudu take iya fin karfinta kamar zata kifa,tana ji tana tattaka abubuwa masu tsini suna shige mata cikin kafarta amma hakan baisa tafasa gudun ba,

Ko alamar shaddad bata gani bare ta saka ran zai sake biyota, kafin ta karasa gida tagama jigata,

Kamar yadda shaddad yabar gidan haka ta sameshi a bude nan ta lallaba ta shige tayi gaggawar hawa sama ta fada dakinta, kan gado tafada ta kankame jikinta wuri guda tana kakkarwa,

Gaba daya jinta take ta kasa tuna koda abu guda daya saboda tsananin tsoro da razani hadida fargaba da suka dabaibayeta,

Ta dade sosai kafin tasamu tadawo cikin nutsuwarta, ganin abinda yafaru take yi kamar acikin mafarki aka yishi,

Sai alokacin ciwon da jikinta yake yi yadawo sabo nan kafafunta wanda shaddad ya tattaka suka dauki ciwo gashi ko ina na jikinta radadi yake yi mata musamman ma tafin kafarta wanda bai saba jin wahala ba gashi yau ta tattaka k'aya da sauran abubuwa masu shiga k'afa,

Tana nan akwance tana tuna yanda abubuwan suka faru har ta jiyo an shiga masallaci sallar asuba,

"Shin yakamata na sanarwa da father wannan abun da yafaru kuwa..?" Ta tambayi kanta, juyawa tayi ta sake gyara kwanciyarta,

"Idan har nafadawa Dada wannan abun to nasan bazai taba hakura ba har sai ya dauki mummunan mataki akan shaddad gara kawai nayi shiru nayi hakuri sannan nabar abin acikin zuciyata ni kadai.."

Wuta ta kunna saboda taji alamun ankawo, kallon jikinta tayi duk yanda rigar baccinta tayi kaca kaca da kasa da tab'o,

"Ohhhh yaron nan gaskiya yanada karfi... Kalli fa rik'o daya yayi min nakasa k'wacewa.."

Haka tayita maganganu ita kadai amma ta rigada ta yankewa kanta hukunci cewar bazata sanar da kowa abinda shaddad yayi mata ba har mahaifinta tunda dai Allah ya taimaketa bai yi mata komai ba.

   Bandaki ta shiga ta tari ruwan zafi cikin baho ta surka da na sanyi tashiga tayi wanka ta gasa jikinta sosai saboda ko ina ciwo yake yimata,

Alwala tayi ta fito tayi salla sannan ta dauko first aid box dinta ta duba magungunan da ya dace da ita a yanzu wanda ya kamata tasha,

Zab'a tayi ta dauki ruwa dake ajiye agefen gadonta tasha taja bargo ta lulluba lokaci kadan zazzabi ya hau jikinta ga wani irin ciwo da kanta yake yi...


*_Ummi A'isha_*
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



    _*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

    _Gaisuwa mai yawa ga masoyiyar ummi A'isha, wato Meenah 4eva tareda Khadija Magaji bk,da duk masoyana gaba daya.._

    *_18_*

aishaummi.blogspot.com

~~~Kwana tayi da zazzabi ajikinta ga matsanannacin ciwon kai dake addabarta,

Misalin karfe 10 nasafe Dada ya shigo dakin nata saboda har ya kammala shirin tafiya office rashin jin motsinta yasashi zuwa dubawa yagani ko lafiya,

Ido ta bude tasake rufe jikinta sosai da bargo domin bata son dada ya ga ciwukan dake jikinta,

"Daughter lafiya kuwa?" Dada yafada yana karasawa gaban gadon,

"Dada bana jin dadine yau dinnan da zazzabi natashi ga wani irin ciwon kai.."

Kanta dada ya dafa yana yimata sannu, kuku ya kira yace ya dan hado mata wani abun taci sai tasha magani, kasancewar akwai wurinda zaije shiyasa yatafi batare da ya tsaya yaga taci abincin ba,

Dakyar tasamu ta tashi ta zauna saboda radadin da jikinta keyi mata musamman ma tafin kafarta da kafofinta,

Blessing ce ta kawo mata indomie wacce aka dafa da naman kaza da kwai,

"Sorry anty, meya samu jikinki haka?"

Harara ta wullawa blessing sannan ta nuna mata hanyar fita da hannunta,

"Zo ki fice min adaki, kar ki sake ki dawo har sai idan nice na nemeki..."

Sum sum blessing ta fice daga cikin dakin tabarta tana cin indomie din data kawo mata,

Abincin take ci tana ganin shaddad yana yi mata gizo, wani irin masifaffen tsoronshi ne yake shigarta wanda ta kasa sanin dalili gefe daya kuma tunanin ta yadda akayi har ya shigo gidan yafita da ita take yi,

"Koda yake babu mamaki tunda shi ba bak'on gidan bane" ta fadi hakan acikin zuciyarta,

Abincin ta ture gefe ta dauki robar ruwa ta fara sha kafin daga baya ta debi magunguna ta sha.

  Kwananta biyu akwance tana zazzabi kafin ta Samu ta warware, office ta koma taci gaba da zuwa aikinta saboda yanzu ta dawo normal sai dai amma duk wanda yasanta ada idan yaganta ayanzu zai fahimci canjin dake tare da ita, domin yanzu bata doguwar magana gashi jikinta yayi sanyi komai asanyaye take aiwatar dashi duk da cewar dama can haka take da rashin son hayaniya to yanzu har gara da,

Tun ranar da shaddad yaso yayi mata wannan cin mutuncin tun aranar taso ta yakice tunaninshi amma hakan ya faskara,

A kowanne lokaci cikin ganin kyakkyawar fuskarshi take acikin zuciyarta, da farko tayi zaton abin na wasane sai daga baya ta fahimci ba haka bane,

Gaba daya yanzu tunanin shaddad yagama zame mata dimin da'iman daga baya dakanta ta fahimci cewar tashiga tarkon so da kauna, ganin zata yiwa kanta illa yasata nemanshi a waya amma abin haushi koda ta kira bata sameshi ba saboda wayar akashe take.

"Yanzu ya zanyi ni maryama...?"

Ta tambayi kanta tana tallafe da kumatunta acikin office dinta bayan ta kammala duba marassa lafiyar dake ziyartar office din nata,

"Guy dinnan nasan bazan taba samunsa ba domin ba zai iya aurena ba saboda haushina yake ji, kawai abinda yafi shine nabawa dr sameer ko dr yazeed dama na auri daya daga cikinsu,

Kai sai dai kuma gaskiya ni basuda wasu qualities din da nake son mijina ya mallaka,

Shaddad dai shi kadai shine namijin da nake ganin zai iya dani sannan zanji dadin zama dashi duk da nasan baya sona baya kaunata, asalima babu macen da yafi tsana irina...

Waima duk ba wannan ba yanzu a ina zan ganshi har na mallakeshi....?"

Wadannan sune tarin maganganun da take tayi acikin zuciyarta ita kadai sai kace zautacciya...

Sake gyara zamanta tayi ta dafe kanta ta zubawa teburinta idanu,

"Nifa ko sanin garinsu ma banyi ba yanzu wa zan tunkura da tambayar inda yake?"

Dabarace ta fado mata, "koda yake nasan ada shi mutumin dada ne babu mamaki watikil ya taba sanar da dada sunan garinsu, bari idan nakoma gida zan tambayi dada"

Mikewa tayi jikinta babu kwari tamkar marar lafiya ta nufi dakin yara, round tayi ta dudduba marassa lafiyar ta kammala ta fito domin yau bata jin zata iya kaiwa yamma acikin asibitin, gida kawai take son tafiya domin ta samu dada ta tambayeshi labarin shaddad......

*_Ummi Shatu_*
[5/12, 10:18 AM] Ummi Shat🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



    *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*19*_

aishaummi.blogspot.com

   ~~~Jikinta a sabule ta tashi ta fita tana rikeda key din motarta tana faman karkadashi sai dai kuma duk jikinta a sanyaye yake, babu wanda tayiwa sallama ta bude motarta ta shiga domin bata son damuwa,

Driving take hankalinta kwance idanuwanta na bisa titi, wayarta ta dauka ta kira dada ta tambayeshi ko yana gida, cikin sa'a yace mata yana gida tun rana ya dawo,

Katse wayar tayi ta sake bawa motar wuta ta nufi gida cikeda kwarin gwiwar abinda take son aikatawa,

Lokacin da ta shiga gida falon dada ta shiga direct ta iskeshi zaune yana rikeda jaridar daily trust yana karantawa, zama tayi ta yaye gyalen dake kanta ta kalli Dada,

"Barka da hutawa dada.."

"Yawwa barka da dawowa mai sunan mama, ya aikin?"

"Lafiya lau dada..."

Shiru tayi tafara nazarin ta inda ya kamata ta fara, can dai ta daure tayi magana,

"Uhm Dada nace nikuwa wannan sojan wanda da ya yake kaini asibiti da d'an wanne garine...?"

Dago da idonshi yayi daga kan magazine din da yake karantawa ya kalleta,

"Daughter meya faru? Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau Dada dama musu muke yi da dr naz shine nace zan tambayeka.."

"Shi nazirun ina yace garinsu?"

Dan jim tayi kafin tabada amsa,

"Cewa yayi wai dan katsina ne.."

Jijjiga kai Dada yayi,

"Bana jin wannan yaron dan katsina ne sai dai ko wajen kano ko Kaduna amma ni gaskiya ban taba tambayarshi sunan garinsu ba.."

Murmushin yake maryama tayi ta mike tana kallon dada,

"Dada bari na shiga ciki nayi wanka..."

Dakinta ta shiga ta zauna ta rafka uban tagumi,tunani take shin yanzu awurin wa zata iya samo labarin shaddad da garin da yake?

Ganin bata samu mafita ba yasata tashi ta cire kayan jikinta ta shiga wanka, ko acikin bathroom dinma ganin shaddad tayi yana yimata gizo, dakyar ta samu ta kammala wankan ta fito ta zauna domin shiryawa,

Komai nata cikin sanyi takeyi domin damuwar dake kwance cikin zuciyarta tafi gaban wasa,

Doguwar riga brown colour tasa ta yafa mayafi ta dauki key din mota ta fita, headquarter din sojoji take son zuwa domin bincikawa ko Allah zaisa ta dace tasamu wanda ya sanshi,

Koda taje cikin rashin sa'a babu wani bayani ko kwaya daya data samu saboda sojojin da ake turowa nan Allah ne kadai yasan adadinsu,

Cikeda takaici da bacin rai hadeda kunar zuci ta fito ta koma gida, wani irin jiri taji yana daukarta sama sama wanda har yana barazanar kayar da ita, dakyar ta fara dafa bango ta samu ta haura zuwa dakinta,

Har wani kai kawo take ji numfashinta yake yi kamar zai fita daga jikinta babu shiri ta kwanta akan gado ta dafe goshinta tana kallon sama nan da nan taga dakin ya fara juya mata,

Runtse idanuwanta tayi wadanda suka kada suka yi jajur duk da tsananin farin da suke dashi,

Gaba daya ta gagara samun nutsuwarta balle tasan abinda ya kamata tayi, blessing ce ta turo kofa ta shigo tana dauke da kayan sawar maryama wanda aka wanke aka goge, drewar taje tafara jerasu daya bayan daya amma kuma sai take jin kamar nishi nishi,da sauri ta waiwaya ga maryama,

Ganinta tayi dafe da goshinta idanuwanta arufe tana yin numfashi sama sama,

Matsawa tayi kusa da ita, "sannu anty..."

Kai kawai maryama ta daga mata ta yi mata nuni da ta dauko mata first aid box dinta,

Cikin gaggawa blessing taje ta kinkimo mata shi ta kawo mata, dakyar ta iya yunkurawa ta tashi zaune ta bude box din ta dauki magani, da gudu blessing taje ta dauko mata ruwa roba daya ta kawo mata, maganin tasha ta zame ta sake kwanciya tana jin zuciyarta tana bugawa da sauri saboda tsananin soyayyar shaddad dake azalzalarta, jitake kamar ba zata iya rayuwa ba mutukar bata mallakeshi ba mallaki na har abada.......








*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment