Wednesday 31 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 14,15

[5/9, 9:42 AM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


       *_14_*

aishaummi.blogspot.com

   ~~~Rufuwa samarin suka yi akanta suna kokarin rabata da sutturar dake jikinta, jin idan batayi dagaske ba zasu cimma manufarsu akanta yasata dagewa ta ciji hannun wanda ya toshe mata bakin babu shiri yayi azamar sakinta, wata kara mai karfi ta k'walla tareda kiran sunan shaddad akaro nafarko acikin rayuwarta,

"Shaddad...." Tafada cikin karaji,

Shaddad yana cikin mota zaune sai kunnensa yajiyo karar da maryama ta kwalla, bai gasgata cewar itace ba har sai da yaji ta ambaci sunanshi, cikin azama ya fito daga motar ko kulleta bai tsaya yiba ya nufi inda yake jiyo sautin muryarta, gashi ko ina na club din duhune dim babu haske ko kadan sai ko na farin wata,

Bayan club din ya nufa jikinsa har wani rawa yake saboda tsananin gigita, yana zuwa ya iske samari fal sunyi mata runfa har sun kusa rabata da sutturar dake jikinta, bindigarsa ya ciro ya harbi sama ji kake, tauuuu...!!

Babu bata lokaci samarin suka baje kowa yayi ta kansa, maryama dake kwance sai faman kankame jikinta take yi ta samu ta mike da kyar sai layi take tana tangadi kamar wacce tasha kayan maye,

Ko kallonta baiyiba ya juya yafara tafiya, da saurinta tabi bayanshi batare data tsaya daukar gyalenta ba wanda yafadi awurin,

Jikake garammm lokacin da ya shiga motar ya rufeta,

"Washhhh...!" Tafada tana runtse idonta bayan ta danna kafafunta domin dama can ciwo suke yimata kuma gashi yanzu an tattaka mata su,

Kallonta yayi zuciyarsa na radadi da tafarfasa wanda bai san dalili ba,

"Sunyi miki wani abune?" Ya tambayeta yana kallonta cikeda tsana,

Kai ta girgiza masa alamun a'a, bai sake magana ba ya kunna motar suka bar wurin,

Tsaki yaja mai karfin gaske sannan yafara magana cikin zafin rai,

"Ni ban taba ganin mahaukaciya, marar tunani, jahila, marar kamun kai irinki ba, kowacce mace tana adana halittar da Allah yayi mata, tana kare mutuncinta amma banda ke, ke kullum burinki shine ki bayyanar da surar da Allah yayi miki..."

Dauke kanta tayi alamun maganganun nashi basu shigeta ba, nan yaci gaba,

"In banda iskanci da rashin ilmi da rashin sanin yakamata ina macen kirki da zuwa club, mace indai ta arziki ce babu abinda ya danganta ta da club, idan kina ganin hakan kamar wayewa ne ko kuma wata burgewa ce to wallahi kinyi kuskure domin ba hali ne mai kyau ba, duk macen dake zuwa wannan wurin karuwa ce..."

Cikin razani ta juyo tana kallonsa lokaci guda fuskarta ta sauya,

"Wacece karuwan??"

Ta fada cikin bacin rai da masifa,

"Ke mana, keda mecece idan ba karuwa ba, bakida maraba da karuwai..."

Nunashi tayi da yatsa, "karka kara kirana da karuwa.."

Packing din motar yayi agefen titi ya juya yana kallonta cikin bacin rai,

"Idan ankiraki da karuwan me kika isa kiyi? Kinada wani sunan ne bayada wannan? Ke karuwace cikakkiya..."

"Naji ni karuwace amma da kanwarka ko yayarka muke karuwancin tare..."

Tun kafin ta karasa rufe bakinta ya dauketa da wani gigitaccen mari wanda yayi barazanar makantar da ita domin lokaci guda ta nemi ganinta ta rasa sannan taji kanta ya dauki ciwo yana barazanar barin jikinta ga wani jiri da yafara daukarta,

Nunata yayi da dan yatsa,

"Ki iya bakinki, ni duk dangina babu yan iska sannan babu karuwai aciki..."

Dakyar ta iya bude idonta ta kalleshi tana mai jin wani bakin ciki yana shigarta sanadiyyar marin da yayi mata domin tunda take a duniya babu namijin da yataba gigin kai hannunsa fuskarta da sunan mari amma yau wannan yaron da baifi Sa,anta ba wai shine ya mareta,

"Ka mareni..?"

"An mareki din ko zaki ramane?" Yabata amsa yana huci,

"Wallahi sai na rama, bazaka taba marina kuma ka zauna lafiya ba, kamar yadda kace ni karuwace to zan nuna maka cewar ni din karuwarce cikakkiya kamar yadda kafada, wallahi bazan yarda ba..."

Tafada idanuwanta sun kada sunyi jajur, fuskarta kuwa har ta kumbura musamman barin da ya mareta, hatta hakorinta dake barin sun kumbura sun fara yimata ciwo,

"Karki fasa ki rama idan baki ramaba ke ba yar halak bace.." Yafada yana huci,

Murmushin takaici tayi ta gyara zamanta tana shafa kuncinta da ya Mara,

"Sai na nuna maka kai yarone karami, wallahi sai na koyar dakai babban darasi.."

"Karki fasa.."

Bata kara magana ba shima bai sake koda kallonta ba ya figi motar, suna zuwa gida yayi packing ya cilla mata key din motar kan cinyarta ya fita yayi gaba ransa yana wani irin zafi,

Har lokacin maryama na dafe da kuncinta tana kallonsa zuciyarta tana yimata wani irin kuna sakamakon marin da shaddad yayi mata gashi wai ita ya kalla ya kira da karuwa,

Fita tayi ta rufe motar tabarta anan ta shiga cikin gida, bedroom dinta ta shiga ta kunna wuta ta karasa gaban mudubi tana bin fuskarta da kallo....


*_Ummi A'isha_*🏻
[5/9, 9:42 AM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   *_15_*

~~~ Ji take kamar ta fashe da kuka sai dai kuma ta dauki alwashin bazata taba yiwa wannan yaron kuka ba kome zaiyi mata,

Kallon fuskarta taci gaba dayi wanda take a kumbure sannan ga shatin yan yatsun shaddad nan sun fito rado rado ajiki,

Girgiza kai tayi ta Shiga bathroom tayi wanka tafito, rigar baccinta ta zira ta fiddo kwalabin benalin guda hudu ta shanye saboda jin ranta take yana sake dagule mata,

Babu bata lokaci bacci yayi gaba da ita, da safe kuwa da wani irin zazzabi ta tashi ajikinta wanda tasan marin da shaddad yayi matane sanadinshi,

Ko tashi kasawa tayi har saida blessing ta shigo ta taimaka mata ta rakata toilet tayi wanka tafito, har lokacin fuskarta tana nan a kumbure,

Komawa tayi ta sake lwanciya ta lulluba tana mai jin tsanar shaddad acikin ranta,

Wuni guda tana kwance bata ci komai ba dakyar ta iya tashi tasha ruwan tea ta kwanta, koda shaddad yazo kaita office blessing cemasa tayi bata da lafiya, kafada kawai ya daga alamun ko oho yayi tafiyarsa.

Da yamma misalin karfe 5 dr naz yazo gidan duba maryaman, har dakinta ya shiga shida blessing domin ganin jikin nata, blessing ya tambaya ko tasha magani tace a'a nan yafara yimata magana,

"Haba dr ya za ace bakida lafiya amma bakisha maganiba? Meyasa?"

Dakyar ta bude idonta wadanda suke jajur ta kalleshi,

"Zansha dr so nake sai natashi lokacin naji karfin jikina.."

"To bari nayi miki allura inyaso idan kika tashi sai kisha magani.."

Dakyar ta yarda dr naz yayi mata allurar a hannu saboda tana tsananin tsoron allura ko kadan bata sonta,

Murmushi dr naz yayi yana kallonta bayan ya zare allurar daga jikinta,

"Ke baki son allura amma kuma kinfi kowa yiwa mutane allura,koda yake ashe fa ance doctors sunfi tsoron allura.."

Kwanciya tayi tasake lulluba, "nagode likita"

Sallama yayi mata yatafi, ahaka tasake kwana da zazzabin gashi jini har yataru a idonta guda daya wanda shaddad ya mareta, washe gari ma sai da dr naz yasake dawowa yayi mata allurar.

Sai da ta kwana uku tana zazzabi kafin ta dan warware,akwana na hudune ta shirya fita office, koda shaddad yazo kaita bata musaba ta shiga suka tafi yakaita ya sauketa sai dai amma ko k'ala bata shiga tsakaninsu ba, lokacin da ta tashi ma haka ya koma ya daukota,

Kullum haka yake kaita ya daukota sai dai babu kalmar dake hadasu,shi dai yanzu yagama sanin wacece maryama, kaf halayenta babu wanda bai saniba hatta shaye shayen datake yasani

Ranar juma'a da daddare mahaifinta yadawo daga tafiyar da yayi zuwa saudiyya, shaddad yayi mutukar mamaki jin bata sanar da Dada cewar ya mareta ba, harkarta kawai taci gaba dayi,

Tana zaune afalon dada da medical glass a idonta gabanta kuma laptop dintace ajiye tana kallon wani american film _iron man_,sanye take da pink colour din doguwar riga mai hannun shimi kanta babu dan kwali, gefenta kuma Dada ne zaune yana cin tuwon alkama miyar kubewa danya, hira suke yi ita tana kallon film din data kunna shikuma Dada yana kallon tv,

"Father zan samu rancen kudi.."

Kafin yabata amsa shaddad yaturo kofa ya shigo hannunsa rikeda envelope babba,

Zama yayi suka gaisa da dada ya mika masa envelope din,

"Mai sunan mama me zakiyi da kudi idan nabaki rence?" Dada yafada yana bude envelope din da shaddad yabashi,

"Dada ginin asibitina da aka fara yifa ya tsaya gashi ko rabi ba ayiba kuma wallahi banida kudi, shine nake son ka ara min 3 millions adan kara tsayin ginin.."

Dariya dada ya danyi yaciro zungureriyar takardar dake nade cikin envelope din yafara dubawa,

"Daughter dama shi gini ai sai da kudi, shiyasa nace miki kibari sai kin tara kudi sosai sai kiyi ginin amma haka kawai kika tsiri gini ba kadanba bayan baki tara kudiba.."

Juyawa yayi ga shaddad ya kalleshi,

"Masu tafiya Niger delta dinnan aka turo, jiyama munyi meeting kan cewa za atura sojoji ta ruwa zuwa Benin to amma bana jin za atura dakai.."

"Ah ranka yadade ai da antura ni nima ina son zuwa kawai dai matsalar banida lafiya ne dan zazzabi ne ke damuna"

Shaddad yafada yana murmushi,

"Allah yabada lafiya, ga maryama nan ai sai tayi maka allura ko?"

Girgiza kai yayi "nasha magani ai Yallabai"

Tashi Dada yayi ya shiga cikin bedroom dinshi,

"Nima dama ba yimaka allurar zanyi ba, maza nawa nagani irinka atube..?" Yajiyo muryar maryama tana yimasa gatsali,

Ko saurarenta baiyiba yamaida hankalinsa kan tv,amma aranshi cewa yake,

"Dama nasan ai kin ga maza irina dayawa tsirara koda baki fada ba.."

Bai sake kallon inda take ba har dada yafito suka gama abinda zasuyi yayi masa sallama yatafi.

Yau kimanin sati uku kenan da marin maryama da shaddad yayi,

Yana kwance adakinsa yana bacci yaji karar wayarshi, hannu ya mika ya katse kiran, nan aka sake kira, sai da aka kira wurin sau biyar sannan yatashi yana dubawa, bakuwar number yagani nan ya kalli agogo,karfe 2 nadare,

Kara wayar yayi a kunnenshi nan yaji muryar mace tana kuka,

"Shaddad ka taimaka min Dada babu lafiya kazo mu kaishi asibiti, dan Allah kayi sauri ko motsi bayayi gashi acikin dakina, wayyo nashiga uku..."

Ko ba afada masa ba yasan maryama ce saboda ya gane muryarta,dagashi sai dogon wando da singileti ta maza ko neman riga bai tsaya yiba ya fita da sauri, tsabar gaggawa ma agida yabar wayar tashi,

Yana zuwa gidan ana dauke wuta, acikin duhun yasamu ya kutsa ya tasamma dakin maryama, yana shiga yafara jiyo shesshekar kukanta,

"Maryam, kunna fitila mana, ina Yallabai din yake, maryam kunna haske.."

Yana wadannan maganganun yana tafiya domin karasawa gadonta, caraf yaji an makaleshi tareda jefashi kan gadon, nan ta haye jikinsa ta kwalla kara mai mutukar karfi,

Kansa ne ya daure gaba daya yana tunanin to meye yake shirin faruwa, makalkaleshi yaji ta sakeyi tana ihu, kafin yayi wani yunkuri har dada ya shigo cikin dakin kuma daidai lokacin NEPA suka dawo da wuta mai karfin gaske, mirginawa tayi karkashinsa ya zama shine asamanta,

Duk gashin kanta ya tarwatse, rigarta anfara yagata,tana rungume dashi sai ihu take kwallawa,

Tsayawa dada yayi yana kallon shaddad fuskarsa a daure, kafin wani lokaci har gidan yacika da mazauna barikin wadanda suka shigo domin bayar da taimako saboda sun jiyo karar maryama,

Tashi tayi dagudu taje ta tsaya a bayan dada tana kuka,

"Wayyo dada nashiga uku.."

Shikam shaddad yama kasa motsi yana zaune akan gadon kansa a daure,

Wata tsawa dada ya daka masa mai sa firgici,

"Kai shaddad ashe bakada mutunci ban saniba? Yar tawa kwaya daya zaka lalatawa rayuwa kayi mata fyade? Na daukeka kamar dan da nahaifa acikina shine zaka yimin mummunar sakayya? To daga yau sai yau karka sake shigo min cikin gidana sannan babu kai babu yata, kuma sai kabar garin nan agobe ba jibiba, sannan sai na dauki mummunan mataki akanka..., get out!"

Tashi shaddad yayi batare da yayi magana ba sai dai idanuwansa sun kada sunyi jajur, ko musu baiyiba domin yasan zaiyi wahala a yarda dashi kasancewar ankamashi red handed, wato dumu dumu,

Daga idanuwansa yayi ya kalli maryama wadda ke tsaye tana yimasa murmushin mugunta sai yanzu yagane ashe makirci ta shirya masa,

Fita yayi daga gidan cikeda kunya da takaici domin yasan yanzu duk jama'ar wurin zasu daina ganin kimarshi sannan sun gama yadda cewar kwadayine yakaishi dakin maryama har yaso yimata fyade,

Gida yakoma yanemi wuri ya zauna yana kukan zuci, ji yake kamar ya kira mahaifiyarshi ya sanar da ita halin da ya shiga sai dai kuma baya son ya daga mata hankali, wayarshi ce tadauki ruri yadaga batare da yayi magana ba,

"Hello, yanzu nasan kagama tabbatar da cewa maryama cikakkiyar karuwace kamar yadda ka fada....."

Kit ya katse wayar yana rike da kanshi, har gari yawaye idonshi biyu, shiryawa yayi ya tattara kayansa domin yasan yau zai bar garin Lagos koda baya so saboda zai bi sahun wadanda za atura Benin,

Fita yayi zuwa headquarter amma duk inda ya gifta maganarshi akeyi cewar yaje yiwa maryama fyade, abokinshi Abbas ne kawai ya tareshi da maganar yace yasan bazai aikata hakaba, nan ya kwashe duk abinda yafaru ya fadawa Abbas,

Posting letter dinshi yaje ya karba saboda dama an rigada an buga sai dai kawai arubuta sunan mutum abashi yayi signing,

Barikin yakoma ya tattara komai nasa ya fito yana mai yiwa barikin kallon karshe saboda yasan shida sake dawowa ciki har abada...


*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment