Wednesday 31 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 11

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


    *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕



    *_11_*

aishaummi.blogspot.com


  ~~~Wuta ya k'ara bawa motar ya nufi kanta gadan gadan amma cikin kwarewa ta kauce masa tawuce babu alamun razana ko tsoro atare da ita, mamakine ya kamashi saboda ganin yanda take yin abubuwa kamar wata namiji komai nata cikin rashin tsoro take aiwatar dashi,

Ita kuwa maryama dama ta rigada tasan cewar shaddad ne domin tunda motar tace ai dole ta gane, murmushi tayi ta jijjiga kai tana cewa,

"Yaron nan dan rainin hankaline wato da so yake ya razanani in fadi ko? Neva wallahi" tafada tana kokarin shiga kwanar da zata sadata da gidan gonarta,

Wani katon kangone wanda aka zagayeshi da waya ga wani tsoho zaune yana daddasa wasu tsirrai acikin kaskon kasa yan madaidaita, yana ganinta ya washe baki yana murmushi,

"Sannu da zuwa ranki ya dade.."

"Yawwa baba dan azumi, bude min nashiga"

Cikin azama ya tashi yaje ya bude mata kofar shiga ta shige tana bisa kan bike dinta,

Daga gate din zuwa cikin wurin tafiyace mai dan karen nisa domin kangon yanada mutukar girma in banda sanyi babu abinda wurin yake yi domin harda dan kwarya kwaryar rafi aciki, sannan ga wani karamin lambu agefe wanda ke dauke da kayan itatuwa shuke acikinsa,

Sauka tayi daga kan bike din ta nufi wani wuri dake kewaye da waya wanda ke dauke da kaji lukuta lukuta aciki da alama wurin kiwon kajine, bi tayi tana duddubawa, wasu sunyiyyi kwai yayinda wasu kuma sai a lokacin suke yi,

Wurin da ake kiwata kifi ta karasa nanma ta dudduba ta fito ta shiga lambu wanda abubuwan dake cikinsa sai Wanda yagani kawai domin abubuwane masu tarin yawa shuke acikinsa ga kuma tsuntsaye abisa bishiyoyin dake wurin sunata faman rera kuka mai dadi,

Duk lokacin da ta shiga lambun nan bata son fitowa domin yana sanyata nishadi mutuka, yauna kamar kullum kan wani rishen bishiyar goba tasamu ta zauna wanda ya dan sauko sosai sannan ya kanannade kamar kujera,

Zama tayi tana faman bin wurin da kallo musamman ma wurinda aka dasa flowers masu kyau kalar pink da yellow da kuma blue sannan ga mutumin nata butterfly sai sauka yake yana tashi akan flowers din,

Har duhun mangariba yafara bayyana bata iya tashi tabar wurin ba sai da baba dan azumi yazo yace mata dare yafara yi sannan tayi masa salla ta fita bayan ya cika mata leda da kayan marmarin dake shuke awurin.

K'arfe 8 saura ta isa gida, a falo tasamu Dada shida shaddad suna hira, yanzu ta kula cikin kwana biyun nan har shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin shaddad da Dada kuma dadan yana jin shaddad kamar d'an da ya haifa shiyasa ma yajashi ajiki ya sake dashi kamar dama can yasanshi tun asali,

A kujera ta zauna yaraff tareda cire hular kanta tana kallon Dada fuskarta cikeda alamun gajiya,

"Mai sunan mama kin dawo?" Dada yace da ita cikin kulawa,

"Ehh father nadawo amma nagaji sosai"

"To kullum dai idan kikaje wannan gidan gonar taki agajiye kike dawowa ban saniba ko aiki kikeyi idan kinje..." Dada yafada yana murmushi,

"Yau dai banyi aikin komai ba father, kallo kawai nayi bakaga kifaye na ba da kaji na sun girma sosai nakusa nakawo maka irinsu ayi maka miya kaci kaji..."

Dariya dada yayi cikeda farin ciki domin a duniya hirarshi da maryama kan sakashi annashuwa,

"To daughter Allah ya kara arziki ashe mun kusa muci kiwonki.."

Takalmin kafarta ta ciccire tana kallon dada,

"Insha Allah dada, yanzu ma ga fruits nataho maka dashi bari nasa blessing ta wanke sai ta kawo maka"

Tashi tayi ta hau sama tana kiran blessing,

Wanka ta shiga tayi tafito daure da towel, kullum haka take bata gajiya da wanka dan akalla arana tana yin wanka fiyeda sau biyar sai kace kifi,

Tana tsaka da goge jikinta da towel taji wayarta tana k'ara, ahankali ta taka taje gaban mirror ta dauki wayar,

Sunan Alhaji Bashir shine abinda tagani, cikeda jan aji da yanga ta daga wayar,

"Ranka yadade.."

"Sarauniyar mata ina gaisuwa, dama nashigo garine amma gobe da asubha zan tafi shine nace yakamata na karaso mu dan gana.."

Jijjiga kai tayi fuskarta dauke da murmushi, "kana ina yanzu?"

"Ina guest house dina dake Ikeja road"

"To ka jirani zanzo.."

Tana gama fadin haka ta tsinke kan wayar ta ajiyeta agefe ta shiga shiryawa, kwalliya taci sosai kamar wacce zata je zaben sarauniyar kyau,

Doguwar riga baka tasa da dan mayafinta wanda ta yane kanta dashi, tasa flat din takalmi baki sannan tabi ko ina najikinta ta fesa turaren beautiful lady,

Wani kwalin tablet ta dauka ta balli guda daya ta fita, fridge ta mike kai tsaye ta dauko robar ruwa tajefa maganin a bakinta ta kurbi ruwa ta kora sannan ta bude jakarta ta dauki chewing gum mai kamshin strawberry ta jefa a bakinta ta nufi falon dada,

Ahankali ta shiga ta zauna tana kallon dada wanda shikuma ke kallon tv,

"Am dada zanje Ikeja road nadawo, Alhaji bashir ne yazo so kuma ina son ganinshi before ya tafi"

"Adawo lafiya, idan kinje ki gaisheshi" dada yafada cikin rashin damuwa,

Shaddad ta kalla, ta tashi tsaye,

"Um kaga ga key kazo ka fito min da motata ka kaini"

Sarai yasan dashi take amma sai yayi fuska ya maze kamar bai san dashi take ba,har sai da tasake maimaitawa,

"Haba mai sunan mama ai girma zaki rinka bashi sai yana jin dadin kaiki duk wurinda kikeso amma ba da irin wannan sigar ba nafada miki yayanki ne"

Baki ta turo tayi wani katon kwai ta fasa ta kalli dada,

"Waye yayan nawa? Haba father ni wallahi kana rage min shekaru na, baifa girmeni ba wallahi age mate dinane nida da naganshi ma nayi zaton na girmeshi saboda naganshi yaro irinsu dr naz.."

"To ya isa kiyi hanzari dai ki tafi"

Juyawa dada yayi ga shaddad wanda yagama cika fam yace,

"Shaddad yi hakuri ka taimaka ka kaita.."

Mikewa yayi baice komai ba yayi gaba yana kallon agogon dake hannunshi a daure karfe tara saura minti biyar, inbanda iskanci ina zataje a wannan daren? Koda yake yawon karuwanci zata, Haka zuciyarshi keta raya masa,

Azuciye yake tafiya tana binshi a baya har sukaje waje,

Hannu kawai ya mika mata alamar tabashi key din, mika masa tayi tana binshi da kallo tana mamakin zafin zuciya da kwarjini gamida cikar kamala irin tashi,

Garage ya shiga ya fito da motar ya tsaya, cikin takunta na isa da kasaita ta bude gaban motar ta shiga ta zauna nan da nan kofofin hancinsa suka soma aikawa kwakwalwarsa kamshinta dake faman tashi daga jikinta,

"Ikeja road zamuje.." Tafadi tana taunar chewing gum yana kara kas kas, banza yayi da ita saboda ya fahimci sam bata da kunya da mutunci gashi wani abu da yafi bashi bakin ciki wai shi zata kalla tace ta girmeshi wai kuma shi age mate dinta ne,

"Wai yanzu wannan yarinyar tana nufin shekarunta 28? Tab Allah ya sawwake, to amma a ina taga date of birth dina har tasan shekarunmu daya da ita?" Wadannan sune tambayoyin da yaketa yiwa kansa har suka je inda tace, ita kuwa gogar tana zaune sai faman waya take, tayi da wannan tayi da wannan,

Wani dankareren katoton guest house ta nuna masa, awaje yayi packing tace ya shigar da ita ciki,

Harara ya watsa mata sannan yace "wannan ne kuma baki isaba, kawowa ce dai nakawo ki amma shiga ciki kuma sai dai kafarki ta kaiki.."

"Mtswwww" taja tsaki tareda bude kofar tafita ta nufi cikin guest house din,

Tsakin shima yaja yadafe kansa shiyasa fa sam baiso aka yi posting dinshi Lagos ba yaso ace agida aka barshi saboda dama ya dade yana jin labarin garin awurin mutane ana cewa idan mutum yaje wannan garin mutukar baiyi da gaskeba to yana iya rasa imaninsa saboda garine wanda babu mai sawa babu mai hanawa kowa son ranshi yake aikatawa babu ruwan wani dashi, amma ai ita maryama tanada mahaifi asalima agabanshi take gudanar da wadannan abubuwan,

Tsaki yasake ja ya kifa kanshi ajikin sitiyarin motar yana jin tsanar maryama da duk wata mai irin halinta,

"Allah kabani mata tagari kar kabani yar tasha irin wannan yarinyar, koda yake ita wannan ma waye zai aureta yarinyar data gama rabarwa maza mutuncinta tagama karar da kuruciyarta a titi, yarinyar da yanzu haka ya kamata ace tana dakin mijinta harda yara amma ita gata a titi sai sheke ayarta take yi"

Haka yayita zantuka shi kadai yana tsaki, har karfe goma tayi bata fitoba sai wurin goma da rabi sannan ta fito ita da alhaji bashir Wanda ya iyo mata rakiya,

Kurawa Alhaji bashir ido shaddad yayi yana son tuna a inda yasanshi, gyara zamanshi yayi yana jijjiga kai domin ya tunoshi senator ne a abuja,

Bude kofar motar tayi ta shiga ta zauna tana gyara mayafin dake kanta....


*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment