Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA..7

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

    *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

aishaummi.blogspot.com

    *_7_*


  ~~~Tunani yafara yi acikin zuciyarsa tareda zancen zuci,

"Kodai yarinyar nan 'yar lesbian ce?" Ya tambayi kansa saboda gaba daya kamannninta irin na'yan duniya ne sai dai kuma yagagara gano amsar tambayarsa,

"Dauki kayan nan ki fita dasu..." Tace da blessing cikin sanyin murya,

Daukar laptop dinta tayi taci gaba da abinda take tamkar ta manta cewar akwai wanda ke tsaye yana jiranta,

"Daughter baki kammala shiryawar bane?" Dada ya tambayeta saboda yaga tsayuwar da shaddad din keyi tayi yawa,

"Na gama dada" tafada tana yatsina fuska,

"To ki tashi ku tafi mana"

Kamar bazata yi motsiba ta samu ta mike ahankali tana mai gyara mayafin dake lullube akanta,

Wucewa tayi tana takawa ahankali saboda tsinin takalmin dake kafarta da kuma yanayin tafiyar tata ta masu jida kai,

Bin bayanta shaddad yayi yana kallon yanda take daga kafarta dakyar, kafin ta daga kafarta daya ta ajiye ta daga dayar ma aikine, abunku da soja nan da nan yaji bazai iya wannan tafiyar tata ba saboda sai tasa kafarsa tayi ciwo, yana ganin ta fita daga falon ya daga kafa yaje ya wuce ta gefenta yayi gaba, binsa tayi da kallo saboda lokacin da yake giftawa ta gefenta sai da taji wani wadataccen kuma daddadan kamshi ya doki hancinta,

Zuba masa ido tayi ta bayanshi tana kallon yanda yake tafiya da zafi da zafi kamar zai tsaga k'asa,

Dauke idonta tayi ta mayar kan screen din wayarta saboda dirinta data fara ji,ganin sunan dr naz yasata yin dan karamin tsaki,

"Dr naz ya akayi?" Tafada ahankali,

"Kin shiryane nazo mu tafi?"

"Meya faru?" Ta sake tambayarshi,

"A'a ba wani abu bane, nazo ne zan wuce ta kusa da street dinku shiyasa"

"No basai ka shigoba nima yanzu zan zo"

"Sai kin karaso ranki ya dade" yafada cikin zolaya,

Murmushi kawai tayi ta tsinke kan wayar daidai lokacin ta karasa fita daga cikin gidan ta tasamma wurin da blessing ke tsaye da kaya tana jiranta,

Fuska ta hade ta bata rai saboda ganin shaddad da tayi zaune saman wani katon bike mai kyau irin nasu na sojoji,tsayawa tayi tana kallonsa,

"Wannan guy din dan rainin wayone, nufinshi wai nice zan hau wannan bike din zuwa office?..."

Kafin ta gama zancen zucin da take taji wata muguwar kara ta hon ta cika kunnuwanta wanda har saida dodon kunnenta ya amsa,

Kallonshi tayi fuskar shi shidinma a hade take ko kallonta bayayi yasaka kansa gabas yana kallon hanya amma hon din da yayi mata yana nufin yagaji da jiranta,

"Wai meye haka? Kaje ka ciro min mota a garage saboda nagaji da wannan tsaiwar.." Tace dashi cikin jin haushinsa saboda yasoma kular da ita,

"Ban iya mota ba,so kina iya hawa idan kuma bakida ra'ayi shikenan..." Taji yabata amsa batare da ya kalleta ba, mamakine ya kamata saboda jin wulakancin da yakeda niyyar yimata,

Wayarta ta fara latsawa ta kira Dada, yana dauka ta kwabe fuska kamar zatayi kuka,

"Father kaga wai bazai kaini a mota ba sai dai akan bike..."

Shiru ta danyi sannan ta sake magana,

"Ok Dada"

Katse wayar tayi ta karasa kan wani katon dutse wanda ke kafe awurin ta zauna saboda bazata iya cigaba da wannan tsaiwar ba.

Mintuna kadan sai ga dada ya fito yana rike da wani sandanshi na karfe,

"Shaddad ya baku tafiba?"

"Yallabai gashi na dauko machine din ai itace taki hawa.."

"Ai shaddad hawan machine dinne sam bai dace da itaba, kayi hakuri ka rinka kaita a mota kaji"

"To yallabai" yafada kafin daga bisani ya buga machine din ya fisgeshi cikin kwarewa yaje ya kafeshi a gefe ya dawo wurin da suke,

"Ina key din motar?" Ya tambaya sai wani babbasarwa yake, binshi da kallo maryama tayi tana tab'e baki saboda ta fahimci so yake ya yi mata wulakanci akan tace ko ya iya mota,

"Ga na motata ka kaita inyaso idan ka dawo sai ni na fita.." Dada yace da shaddad tareda mika masa mukullin motarshi kirar croutoure black,

Rissinawa yayi ya karbi key din ya tafi dauko motar, komawa cikin gida dada yayi bai jira dawowarsa ba,

A kusa da inda take zaune yaje ya tsaya bayan ya dauko motar,

Tashi tayi dakyar tafara takawa kamar wata mai ciwon kafa tana yiwa blessing magana,

"Samin kayan agaba"

Owners corner ta bude zata shiga agadarance, sai da yabari ta shiga ta zauna blessing ta saka mata kayanta agidan gaba ta juya ta koma gida sannan ya jiyo batare da ya kalleta ba yace,

"Kifito ki kwashe kayan nan ki zauna saboda niba driver bane.."

Rabuwa tayi dashi tayi kamar batajiba ta ki tashi,

Shiru shiru taji bashida alamun tashin motar ganin haka yasata bude kofar motar ta fita ta zagaya gidan gaba ta bude, kayanta dake kan kujerar ta zuba awurin ajiye k'afa ta shiga ta zauna fuskarta babu annuri kamar yadda shima shaddad haka tashi fuskar take ahade,

Bai jira komai ba ya zuburi motar wadda har sai da maryama ta kusa buguwa da jikin motar, aguje yake tuka motar har suka yiwa barikin nisa,

"Yama sunan asibitin?" Ya tambayeta batare da ya dubeta ba,

Compliment card dinta guda daya ta dora masa akan wani dan pillow wanda ke ajiye agefenshi batare da tayi masa magana ba,

Ko kallon card din bai yiba yaci gaba da tukinshi,

Ganin sun kusa wuce hanyar da zasu bi yasata bude bakinta dakyar ta fada masa sunan asibitin, amma gaba daya ya gama kular da ita, zuciyarta har tafasa take yi dan bacin rai,

Lokacin da suka shiga cikin asibitin daidai lokacin dr sameer  shima ya shigo cikin asibitin, packing shaddad yayi yana jiran ta fita, dr sameer ne ya k'araso inda suke yana murmushi,

"Maryama sarauniya, barka da zuwa.."

Murmushi ta mayar masa tace,

"Barka dai dr.."

"Yau baki makara sosai ba tunda gashi munzo lokaci daya dake"

"Dr kenan,yanzu zan ringa zuwa da wuri tunda dada ya sama min driver.."

Wani bacin raine ya ziyarci zuciyar shaddad saboda abinda maryama ta fada,itama dama ta fadane saboda ta wulakantashi, handbag dinta ta mikawa dr sameer ta fita daga cikin motar, Joseph massinger shine ya rugo a dari yazo yana yiwa maryama sannu da zuwa hadida dauko kayanta daga gaban motar,

Ko kallon shaddad ba tayiba ta wuce itada dr sameer tana rikeda hannun handbag dinta guda daya shima ya rike guda daya,

Aguje yasake fincikar motar yafita daga cikin asibitin, compliment card dinta data ajiye ya dauka yana karantawa,

Dr maryama Faruk Bello.. Shine sunan dake rubuce dara dara ajikin card din,

"Maryama Faruk Bello..." Ya maimaita sunan nata yana sake kallon card din,

Tunani yafara yi shin ita wannan yarinyar wacece? Meyasa take zaune daga ita sai mahaifinta? Ina mahaifiyarta take yanzu? Wadannan tambayoyin sune suka kawowa kwakwalwarsa ziyara sai dai kuma bashida amsarsu, sai dai har ajikin jininsa da bargonsa yana jin wata irin tsanarta aranshi saboda gaba daya kaf dabi'unta babu wanda yayi masa saboda tarbiya bata isheta ba ayadda ya fuskanta....





*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment