Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 6

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Ina kike? Hawwa Jidda Aliyu marubuciyar littafin sonki ne sanadi, wannan shafin nayi shine dominki, ina ji dake tawan..._

   _*6*_

aishaummi.blogspot.com


  ~~~Kwalaben benalin guda biyu ta bude ta tuttule acikinta ta tura kwalaben kasan gadonta,

Kwanciya tayi ta mike akan gadonta idanuwanta a lumshe, mintuna kadan bacci yayi gaba da ita.....

***

  Tunda bacci ya dauketa ba ita ta tashi ba sai da misalin karfe goma nasafe, garau ta tashi tana hamma tana bin dakin nata da kallo kamar yaune tafara ganinsa,

Tashi tayi duk jikinta a mace yake kamar wacce aka yiwa duka,

Bathroom ta shiga tana rike da kanta, wanka ta silla tafito,blessing ta iske atsakar dakin tana yin mopping bayan ta kammala gyara dakin,

"Bani wuri zan shirya.." Tafada tana goggoge jikinta da karamin towel,

"To anty.. " blessing tafada tareda azamar ajiye moper din dake hannunta tafice taja mata kofar dakin dama tuni ta fito mata da kayan da zata sa,

Zama tayi ta cancada kwalliya sannan ta saka kaya, yauma kamar kullum riga da skirt high waist tasaka da dan karamin mayafi,

Sallar safe tayi sannan ta gangara falon dake kasa tana tafe tana yayyamutsa fuska,

Ganin Dada baya falo ya sanyata binshi cikin dakinsa, a kofar dakin sukayi kicibus dashi yana kokarin fitowa,

"Good morning father..." Tafada tana murmushi,

Murmushin shima yayi ya karasa fitowa yana kallonta,

"Daughter yau da wuri kika tashi...?"

Daga kai tayi tana murmushi,

"Father yau ina son nashiga office around 11 saboda may be zan shiga theatre"

Kai ya gyada ya nufi falo tana biye dashi yana cewa,

"Allah yabaki nasara mai sunan mama.."

"Thank you father" tafada tana biye dashi,

Zama tayi a falon ta dora daya akan daya tareda kwalawa blessing kira,da gudu ta garzayo tazo ta rissina agabanta,

"Miko min laptop dina acikin bedroom"

Da sauri blessing ta juya ta nufi dakinta,

"Dada yau wa zai kaini office? Ni bana son na yawaita shiga motar dr naz saboda irin hakan zai iya sawa ya rainani"

Murmushi dada yayi ya juya yana kallonta,

"Kafin kigama shiryawa dai zan samu wanda zai kaiki.."

"Ok father.."

Daidai lokacin blessing tazo wurin tana rikeda laptop din maryama a hannunta ta durkusa ta bata ta fita, suna nan zaune kuku ya kawo breakfast din da ya hada ya ajiye dada yafara ci yana kallon tv ita kuma maryama tana ta faman danne danne a laptop dinta,

Assalamu alaikum..." Suka jiyo sallama bayan an bude kofar falon,

Ahankali ta dago ta kalleshi ba kowa bane face wannan matashin sojan, yau ma yana sanye cikin uniform dinshi wanda suka karbeshi,

Cikin fara'a dada ya amsa masa,

"Shaddad ka fito?" Dada ya tambayeshi yana murmushi,

"Ehh nafito ranka ya dade" matashin sojan ya bashi amsa,

"Yawwa shaddad dan Allah abinda nake so dakai shine ga'yata nan maryama zaka rinka kaita wurin aiki kana dawo da ita da duk sauran wuararen da take so, dan Allah ka kula min da ita sosai sannan dan nayaba da nutsuwarka ne shiyasa har nasaka wannan aikin..."

Ahankali cikin sanyin jiki wanda aka kira da shaddad ya dago kansa ya dan kalleta kanta yana sunkuye tana danne danne ajikin laptop dinta,

"Blessing, dauko min medical glass dina acikin bedroom.."

Yajiyo muryarta tana yiwa blessing magana,

Dakyar ya iya buda bakinsa yayi magana saboda yana mutukar ganin girman dattijon sannan ya fahimci cewar mutum ne mai kirki mai rike d'an wani kamar nasa,

"Shikenan ranka ya dade insha Allahu baza asamu matsala ba"

"Yawwa nagode Allah yayi maka albarka"

Blessing ce ta dawo hannunta rikeda medical glass ta mikawa maryama ta karba ta saka a fuskarta,

"Daughter ga wanda zai dinga kaiki office.."

Dada yafada yana dan murmushi,

"To father.." Tafada fuskarta a cunkume,

"Blessing kira min kuku"

Dasauri blessing taje ta kira kuku suka dawo tare,

"Kuku ka dafa min tea?" Ta tambayeshi tana yatsina fuska,

"Ehh an dafa ranki ya dade"

"To soya min chips da kwai dan kadan"

"To ranki ya dade"

Kanta ta mayar taci gaba da abinda take kafin ta dago tana kallon dada,

"Father shi wannan din ya iya motane? Sannan nifa ban son driver malalaci gaskiya..."

Babu zato ya jiyota ta furta hakan cikin dakewa,

"Haba mai sunan mama ya iya mota mana, sannan in banda abinki kin taba ganin soja malalaci?"

"Ahh dada ai naganshi ne wani lange lange"

Ran shaddad ne ya fara baci saboda jin kalamanta amma sai ya share saboda yasan bata san ko shi wayeba,

Suna nan a falon har kukun yagama hado mata breakfast din nata ya kawo mata ya ajiye,

"Blessing dauko min phones dina da hand bag dina milk colour da cover shoe shima milk colour"

"To anty.."

Babu bata lokaci blessing ta kawo mata dukkan abubuwan data lissafa,

Mikawa blessing kafarta tayi bayan ta dan kwaye skirt din jikinta domin ta saka mata takalmin,

Nan take sarkar data daura a kafarta ta bayyana har idon shaddad yakai kai...



*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment