Wednesday 3 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 4

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Fatan alkairi ga takwarorin maryama sarauniya, duk wata mai suna maryam to tayi alfahari da wannan shafin domin ummi Aisha ta bada shi kyauta agareta...._

*_4_*


    ~~~Ahankali ta bude kofar office din nashi ta shiga bayan tayi knocking,

Yana zaune da laptop agabanshi yana daddannawa, ganin maryama yasashi dakatawa daga aikin da yake yi ya fara murmushi,

"Barka da hutawa likita.."

Tace dashi tana kokarin zama akujerar dake gaban teble dinsa,

'Barka dai ranki yadade, ya aikin?"

Kafafuwanta ta dage ta jawo kujerar dake facing dinta ta dorasu akai tana yayyatsina fuska,

"Aiki babu dadi dr.."

Murmushi yayi yace "wai danma dai kece.."

"Ko?" Tafada tana murmushi,

"Yeah..., you look muahhh this day..."

"Thank you dr"

IPhone dinta ta zubawa idanuwa bayan ta sakala earpiece acikin kunnuwanta, game din angry run tafara bugawa lokaci zuwa lokaci tana bashi amsar maganganun da yake yi mata,

Ta dade a office din dr yazeed suna hira kafin daga bisani ta yi masa sallama tafita, tare dashi suka fita ya rakata har office dinta anan dinma sake zama sukayi suna wata hirar,

Ganin karfe uku tayi yasata kiran layin dr naz domin tana son tafiya gida,

Karfe 3:30 dr naz tazo, har cikin office din yabita tana tsaye agaban table dinta tana harhada kayanta ya shiga kafadarta ya dafa yana kallonta,

"Kinzo a makare zaki tashi da wuri.."

"Ina son inje a wanke min kafata ne before nakoma gida.."

Jakarta ya karba ya rike yayinda ita kuma take rike da lunch box dinta da laptop bag dinta,

Jerawa sukayi da dr naz suka fita harabar asibitin zuwa wurinda yayi packing,

Akan hanyarsu ta zuwa gida ya tsaya awani shagon saloon wanda har wankin kafa akeyi ashagon, tare suka shiga ta zauna aka wanke mata kafar,faratanta aka kankare aka saka mata farcen roba zako zako sannan aka shafa mata farin nail paint ajiki,dr naz yana zaune yana kallon yanda faratan nata suka fito suka sake haskawa tamkar wata tauraruwa dadin dadawa kuma tafin kafarta tamkar na jarirai yake,

Shine yabada kudin wankin kafar suka tashi suka fita tare,

"Yau ina son zuwa stadium kallon ball shiyasa nake sauri naje gida.." Tace dashi tana gyara zaman mayafin dake kanta,

"Nima naso Shiga but inada uzuri gaskiya idan kin kalla kya bani labari gobe"

"Ok babu damuwa kayi sauri dai ka kaini gida"

Gudun motar ya kara mintuna kadan sai gasu acikin barikin sojoji,fita tayi daga cikin motar tana daga masa hannu,

Gidansu ta shiga tana shiga ta iske blessing tana goge mata kayanta wanda ta wanke,

"Blessing jeki ki debo min kayana a motar dr naz.."

"Ok Anty" shine kawai abinda blessing tafada ta tashi ta fice,

Upstairs ta nufa tana tafe tana kokarin cire rigar jikinta bayan ta yaye gyalen dake kanta, tana shiga bedroom ta watsar dasu akan gadonta tasoma kokarin cire agogon hannunta da sauran tarkacen data sassaka,barimar kunnenta da ta kan hancinta kawai tabari bata cireba, tana kammalawa ta nufi toilet bayan taja towel dinta dake rataye ajikin kofar toilet din,

Tana bathroom tana wanka blessing ta shigo itace ta tsittsince kayan data zubar ta ajiye kowanne a muhallinsa ta sake fito mata da wasu kayan wanda zata saka yanzu,

Bata wani bata lokaci acikin bathroom dinba tafito tana rikeda karamin towel tana goge jikinta, kwalliyar da tayi yanzu bata kai ta dazu ba domin powder kawai ta shafa sai lipstick data shafa akan lips dinta, turare tabi ta feffesa sannan ta nufi abin sallarta,sallar azahar tayi data la'asar duk a lokacin, tana idarwa ta mike ta tasamma wurin kayan da blessing ta fito mata dasu,

Rigace Jessy irin ta yan kwallo baka da wando jeans blue fela sai bakin dan karamin gyale wanda zata daura akanta,

Kayan tasaka ta daura bakin dan kwalin akanta,ta daura bakin combos ta dauki wayarta guda daya wacce take amsa call ta fita da hanzari domin tasan tuni yanzu anfara wasan saboda ganin 5 harda yan mintuna,

Tana sauka kasa tafara kiran blessing,

"Blessing ina key din bike dina?"

Da Sauri blessing taje ta dauko ta kawo mata, tana karba tafita batare da koda ta tambayi dadanta ba ta nufi garejin ajiyar motoci, tana zuwa ni ummi A'isha na hango wani lafiyayyen bike machine kalarsa pink and blue irin wanda mata suke tukawa a kasar India, shi kansa machine din abun kallo ne domin ba karamin haduwa yayiba gashi awani mulmule da fankama fankaman glass agabanshi,

Fito dashi tayi daga cikin garejin ta hau ta bashi wuta tawuce, idan da sabo to mazauna barikin sun saba ganinta akai kusan kowanne yammaci,

Express way tabi titin da babu motaci dayawa akai kusanma duk motocin dake bin wurin masu koyan motane,

Gudun da takeyi bana wasa bane baka jin komai sai shuuuuuuuu wato karar da machine din yake fitarwa yayinda ita kuma tukinta kawai take cikin annashuwa ta kure music tana ji ta cikin earpiece din dake kunnenta wanda ta jono daga cikin wayarta dake sanye cikin aljihun jeans dinta,danjojin jikin bike din ta kunna suna kawowa suna daukewa wal wal,

Cikin mintuna kalilan ta isa stadium din wanda yake katon gaske mai daukar dumbin dubban mutane,

Wurin da aka tanada domin packing din ababan hawa ta nufa ta faka bike dinta ta kulle ta zare key din ta nufi wani dan karamin shop wanda aka tanada domin sayar da kayan sanyaya makoshi da ababan makulashe,

Coke ta karba naroba da popcorn cikin wata hadaddiyar karamar container, cikin stadium din ta hara hankalinta kwance domin hatta suma ma'abota halartar wurin sun santa kusan itace mace tafarko da take zuwa wannan wurin,

Kujerun sama taje ta zauna adaya daga ciki lokacin har anfara buga wasan, tana diban popcorn dinta tana ci tana korawa da coke sannan ta zuba ido tana kallon yanda wasan yake tafiya.....



*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment