Friday, 27 October 2017

MIJINA SIRRINA.. 71-END

[10/2, 7:47 PM] Bint Khalil: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
    _(Labarin k'auna)_


    *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*
  _Home of expert & perfect writers_


         *71*

aishaummi.blogspot.com


   *S*ake murtuke fuska tayi tana kallonshi ta cikin dan hasken da yayi saura acikin dakin,

"Baby akan wannan maganar fa ina iya batawa dake garama tun wuri ki bari.."

"Kaga ni ka kyaleni bacci nake ji.."

"Dama zan kyaleki kiyi bacci amma sai nagama yimiki kashedi da gargadi akan wancan mutumin..."

Kwace jikinta tayi ta koma ta kwanta gamida juya masa baya,

Duk da adan cikin fushi yake hakan bai hanashi rungumeta ta baya ba bayan ya kwanta,

Da asuba ta rigashi tashi bata tasheshi ba sai bayan ta iyo alwala domin ka'idane tare suke yin salla, tashinshi taje tayi,tashi yayi yana kallonta yana dan harararta alamun bai huce ba daga fushin da yayi adaren jiya,

Yi tayi kamar bata ga hararar da yake aika mata ba, sauka daga kan gadon yayi ya nufi toilet yana fitowa yaganta akwance taja bargo ta lulluba,

Bargon yaje ya yaye yana kallonta,

"Sallar fa?..."

Dan juyi tayi sannan ta waiwayo ta kalleshi,

"Kayi sallarka kai daya ni banayi.."

Wata hararar yasake jifanta da ita baice komai ba yatafi kan dadduma yatada kabbarar salla,

Bayan ya idar ne yayi addu'o'i kamar yadda yasaba sannan yatashi yakoma kan gadon,

"Gaskiya ni kin gama dani gaba daya, wai dama kin san yau zaki tashi da wannan abun shine zaki sakani agaba jiya da masifa ki hanani samun farin ciki, abu kadan ki wani hade rai kina ciccin magani dan kawai anfadi gaskiya akan wannan...."

"Yau kuma da abinda katashi kenan?? Lallai" tafada tana sake gyara kwanciyarta,

"Ehhh da abinda natashi kenan"

Shiru tayi masa ta lumshe idonta kamar mai yin bacci, tana jinshi sai faman juyi yake har gari yayi haske tun tana jin motainshi har bacci ya dauketa,

Ganin tayi bacci yasashi komawa falo ya kunna labarai yana gani anan shima baccin ya daukeshi bashi ya farka ba sai misalin karfe 8 nasafe,

Motsinta yajiyo acikin kitchen alamun tana hada abun karyawa, tashi yayi yabita zuwa cikin kitchen din ahankali ya sadada yaje ya rufe mata idanuwanta,

"Malam meye haka?"

Murmushi yayi ya matsa kusa da ita tareda kallon fuskarta, tasha kwalliya sosai sai kamshi take zubawa, tana sanye da atamfa maroon mai zanen hang bag ajiki,

"Kinyi kyau amaryata..."

Baki ta turo batare datace komai ba,

"Baby wai maganar jiyanne har yau bata wuceba, kinga fa sabuwar wayar da na siyo miki can har yanzu baki dauka ba idan bakya so ki fada min sai inkaiwa budurwata..."

Jin abinda yafada daga karshe yasata hada girar sama data kasa sannan tabashi amsa,

"Ka kai mata nima mijina zai siyo min idan nakoma gidanshi..."

Bai san lokacin da yakaiwa bakinta damka ba,

"Kinada wani miji ne bayan ni, har alahira nine mijinki bama a duniya ba..."

Ture hannunshi tayi tana kallonsa,

"Sakar min bakina,karka sake matse min baki tom.."

"Koma dai me zakice ki fada amma keda kabiru jagwal sai kallo"

Yafada yana kokarin barin cikin kitchen din, har yakai bakin kofa yasake waiwayawa,

"Kallon ma ko ahanya kuka hadu ya kalleki Allah ya isa tsakanina dashi.."

Karasa ficewa yayi daga cikin kitchen din ita kuma taci gaba da aikinta acikin zuciyarta tana cewa,

"Kaji dashi dai sarkin kishi kawai.."

K'arfe 9 daidai tagama kammala hada breakfast din dan haka ta kinkimo ta nufi kan dining,

Zaune ta sameshi akan dining din yana hada mata sabuwar wayar da yasiyo mata, daga ganin wayar mai tsada ce domin tahango tambarin kamfanin HTC ajiki,

Kalar wayar golden ne yar shafal shafal kalar ta mata amma kuma katuwa ce ba canba,

Zama tayi akujerar dake kusa dashi tana kallonshi sakamakon kamshinshi da yacika kofofin hancinta, ba karamin kyau yayi ba awannan lokaci domin pink din riga yasa ta polo da bakin trouser, sumar nan tashi tasha gyara sai kyalli take, ya daura agogon silver ahannunshi na hagu,

"Baby ga wayar zan jona miki ita a charge.."

Bai jira amsarta ba yatashi zuwa socket yajona ajiki ya dawo wurinta lokacin har tasoma kurbar tea din data hada,

Daukarta yayi cancak daga kujerar datake ya maye wurin tareda dorata asaman cinyarshi,

"Wannan fushin dai da kiketa yi dani sai kin dainashi ayau..."

"Fushi ai kai kasiya.."

"Nawa na siya? Fada min inji"

Yace da ita yana zame dan kwalin dake daure akanta,

"Ya zaka cire min dankwali na? Kasan kuwa dadewar da nayi agaban mirror kafin indaura shi?"

"Zanyi miki wanda yafi wannan.."

"Tayaya?"

"Zaki gani ai.."

Gashinta yafara sinsina,

"Serious baby yakamata ki daina fushin nan dani haka karkisa inshiga wani hali.."

Tureshi tasoma yi saboda jin yana niyyar hada bakinshi da nata,

"Ni kabari kar kasa tea dina yahuce.."

Baiyi magana ba wayarshi tafara ringing, karkacewa yayi ya cirota daga aljihunshi yana kallon screen din wayar, ganin sunan zee yasashi kallonta yana murmushi, bai dauki wayar ba ya ajiyeta akan table din dake gabansu,

"Ni ina nawa tea din? Ko tare kika hada mana.."

"A'a.." Tabashi amsa,

Wayar tashice tasake daukar kara,

"Kinga ke kin sameni sai faman wahalar dani kike amma ga wata can agefe tana son samuna domin tabani kulawa.."

Baki ta zumbura cikeda takaici ta kalli wayar tashi nan taga sunan zee baro baro,

"Ko zaki daga kuyi magana?"

Ko kallonshi batayi ba ta juyar da kanta, shi bai son yayi laifi awurin gimbiyar tasa shiyasa ma yaki daga wayar daga karshema kashewa yayi gaba daya ya ajiyeta,

Tea dinta ya dauka ya kurba, ya kula tunda yayi mata maganar zee ta sake tunzura, dan haka har suka kammala bata sake cedashi ko uffan ba,

Tana jikinshi ya dauketa zuwa falo,

Kallonshi tayi saboda jin yafara yimata ajiyar zuciya akunne,

"Lafiya..?"

"Itace ta kawo haka.." Yabata amsa, hannunshi ta buge daga kan kirjinta,

"Meye haka? Baby dan Allah kibari"

"Ni bana so.."

"Ni ai inaso.."

Harararshi tayi shima ya rama amma tashi awasance yayi,

"Bari idan andan jima zamuje kiga motar taki kinji, uhmmm baby.."

"Banjiba.."

Gwalo yayi mata,

"Duk abinki dai nine nan..."

"Bakai bane..",

"Wallahi nine kuma bari ma kiji, idan kika kara ambatar sunan wannan..."

Murtuke fuska tayi ta katseshi,

"Amma dai kasan ko babu maganar su fadeela yaya kabeer dan uwana ne najini dan haka babu mai rabani dashi..."

"Allah ya isa idan kika kara yimin maganarshi..."

Hawaye yaga tafara yi,

"Amma ai kaine kafara ko, shine sai yanzu nikuma zaka hanani.."

Rungumeta yayi yafara lashe hawayen nata dake silalowa bisa kuncinta,

"Yi hakuri baby, nine ko? Yi shiru, mubar maganar kinji..."

Rarrashinta yaci gaba dayi bai barta tasake yin magana ba har tsawon wani lokaci,

Zamewa tayi daga jikinshi ta tashi,

"Bari naje nagyara maka bedroom dinka nagyara ko ina shi kadai ne kawai ban gyara ba.."

Gyara kwanciyarshi yayi yazuba mata fararen idanuwanshi mayalwata masu dauke da bakin yalwataccen gashi,

"To sai kin dawo..."

Mikewa tayi ta nufi dakinshi mintuna kadan sai gata tafito tana kallonshi,

"Haba didi,Kaine kuma mai aikin gidan yanzu?"

Murmushi yayi ya kalleta,

"Meya faru?"

"To naje zan gyara naga already har ka gyara..."

"To kuma menene baby? Rage miki aikin nayi fa.."

Juya mishi baya tayi,

"Nidai kadaina yimin irin wannan, duk wani aiki idan kaga banyi ba kafin nafarga kayishi, ai sai inzama marar tausayi, bayan kafita ka nemomin abinda zanci kuma sannan harda su aikin gida"

Tashi yayi yakarasa inda take ya rungumeta ta baya,

"Baby wallahi ni ban dauki hakan amatsayin wani abu ba, ahar kullum ina fada miki na daukeki ne a matsayin abokiyar rayuwa bawai baiwa ba, wallahi idanma akwai abinda yafi haka zan iya yimiki saboda bazan iya kwatanta miki matsayinki agareni ba, wani irin sonki ne Allah ya jarrabeni dashi..."

Jin alamun saukar kwallarshi akan kafadarta yasata juyawa tana kallonshi kumatunshi ta fara shafawa,

"Didi na, nima ina sonka, ba son maso wani kakeyi ba, kadauka aranka cewar ban taba son wani da namijiba sai kai, bana ganin ko wanne da namiji sai kai kadai..."

Murmushinshi mai tsada taga yayi mata kafin yadagata sama yafara juyawa da ita, gaba dayansu shida ita dariya sukeyi, yau yana cikeda farin cikin da bai taba yin irinsa ba,

Sauketa yayi yana rikeda kugunta,

"To saura ni, nima adagani.."

Yafada cikin shagwaba, hannayenta tasa wai zata dagashin amma maimakon haka sai ji tayi sun fadi akan center carpet din dake shimfide afalon,

Dariya suka fara yi babu kakkautawa,

"Wai dama babyn tawa bata da karfi?"

"A'a inada shi"

"Gashi kuwa kin kasa daga mijinki.."

Hannunta yaja suka mike tsaye,

"Dauko gyalenki muje yawo amotarki.."

Fuskarta dauke da farin ciki ta shiga bedroom dinta ta ciro mayafi da takalmi kalar kayanta tafito bayan ta fesa turare,

Afalo ta sameshi yana kunna wayarshi wadda yakashe dazu,

"Baby anya kuwa fitar nan zata yiyu?" Yafada idonshi akan screen din wayarshi,

"Meya faru?"

"Wani kamshi naji Wanda yatayar min da..."

"Dan Allah kayi hakuri muje mudawo.." Tafada tana kamo hannunshi,

"Gaskiya dakyar, kar muje mutafi nutsuwata ta tafi atsakiyar titi kinga ke kuma ba driving kika iyaba"

Kallonshi tayi bayan tadago fuskarshi,

"Wai dagaske kake ne?"

"Au da dawasa kika dauka? Bari dai kawai nayi ganganci nadaukeki mutafi idan kuma ansamu matsala shikenan asan yanda za ayi"

"Bama wata matsala da za asamu.."

Jan hannunshi tayi suka fita hannayensu sarke cikin juna, saida suka fara zuwa suka gaida hajiya sannan suka wuce wurin motar tata, kusan suman tsaye tayi saboda ganin haduwar motar, ko da wasa bata taba kawowa zata mallaki irin wannan motar ba,

Motar yar karama ce ta mata kalarta blue sai sheki take, budewa yayi ya shiga itama ta shiga ta zauna kasancewar glasses din masu duhu ne yasashi janyota zuwa saman cinyarshi bayan ya kwantar da kujerar tashi,

"Infara koya miki daga yanzu?"

"Didi tsoro nakeji..."

"Babu wahala fa baby, bari kiga, taka muje ahankali.."

Tafiya suka fara yana rike da sitiyarin itama ta rike suna juyashi ahankali, ahaka suka fice daga farfajiyar gidan, saida yaga sun kusa zuwa babban titi sannan yamayar da ita kujerarta yaci gaba da driving din shi kadai,

Wuraren shakatawa kala kala suka ziyarta daga karshe yakaita gidan anty siyama, ba karamin murna anty siyama tayiba da ganinsu nan tahau tsokanar amadi,

"Anty amadi kadai zama jela duk inda nadiya take kana bibiyarta abaya.."

"Anty siyama ni ai nafi jela ma, ki kirani da kowanne suna zan amsa"

Dariya sukayi dukkaninsu, har yamma suna gidan sai daf da magrib suka tafi, ba gida yanufa dasu ba, lovers garden yakaisu,bude ido kawai nadiya tayi tana ganin yanda masoya ke guje guje wasu kuma yan tsalle tsalle,

Kallonshi tayi bata san lokacin datayi kissing dinshi a baki ba,

"Baby wannan babban tukwici haka ai sai kisa na sume.."

Dariya tayi, "wannan somun tabi ne sauran bayani sai munje gida.."

"Kice duk ranar da nashiga hannunki sunana sorry"

Dariya tayi tajashi suka fita zuwa filin wurin, babu laifi suma sun dan wataya sosai, karfe 7 suka koma gida.

   Tunda suka koma kuma yadameta da mitar fashin sallar da takeyi, juyawa tayi ta kalleshi,

"Dadina dakai rashin hakuri didi, kwana uku nefa amma duk kabi ka damu kanka.."

Shiru taji yayi mata baiyi magana ba, janshi tayi tasashi ajikinta tafara shafa sumar kanshi,dagewa tayi wurin bashi kulawa tunda tarigada tasan halin kayanta,da yan dabaru tasamu har yasamu nutsuwa yayi bacci dama haka yakamata mata su kasance bawai kawai dan kina period ba ki kauracewa miji wata ma sai ki samu mijin yana gabas ita tana yamma wannan babban kuskure ne.

A daddafe dai yasamu yahakura har kwana ukun tayi, kamar wani marar lafiya yazame mata har saida yasamu abinda yake kulafuci sannan yaware yakoma kamar da,

Lokaci zuwa lokaci yana daukarta sufita su zagaya gari amma har yanzu bata gama koyon motarba kasancewar kullum suna hanyar zuwa wudil gashi anfitar musu da time table na exam,

Yanzu bai fiya zama a part dinsu ba yafi zama a part din hajiya saboda yabata damar yin karatu sai dai abunda yake damunsa yanda yanzu duk tazama wata lazy, shi kanshi yanzu bata iya hidimta masa kamar da abu kadan sai tace masa tagaji, ana cikin haka kuma sai tafara yawan amai daga taci abinci sai amai babu abinda take jin dadinshi sai lemon zaki shikam koda yaushe cikin shansa take,

Amadi ko kadan bai san abinda yake damunta ba amma dai yaga canji atareda ita musamman ma ajikinta wanda yake sashi kasa hakuri ita kuma yanzu idan da abinda ta tsana to abinda yake shaukin ne, kusan koda wanne lokaci sai yasha aikin rarrashi kafin yasamu karbuwa,

Rigarshi yake sakawa yana kallonta tana kwance akan gadonshi,

"Dan Allah didi kayi sauri karka dade.."

"To antyn lemon zaki yanzun nan zan dawo.."

Fita yayi ganin motar anty siyama yasashi shiga part din hajiya, gaisawa sukayi kawai yajuya zai fita,

"Anty amadi ina zuwa ne?"

"Anty ina zuwa lemon zaki zanje in siyowa mutuniyar, yanzu bata iya cin komai da zarar taci sai amai narasa gane meke damunta..."

Dariya anty siyama tayi tace,

"Allah yabata lafiya"

"Amin anty"

Ya amsa mata tareda yin gaba hankalinshi akwance domin shi bai fahimci abinda anty siyama ke nufi ba....

*_Ummi Shatu_*
[10/6, 6:07 PM] Bint Khalil: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
     _(Labarin k'auna)_



    *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITER ASSO.*
   _Home of expert & perfect writers_

  _Wannan shafin sadaukarwa ne agareku masoyana, nagode Allah yabar zumunci._

        *72*

aishaummi.blogspot.com

     *A*hanzarce yake tuki bayan yadawo daga siyo mata lemon zakin kamar yadda tace, sauri yake yakoma gidan da wuri domin yakai mata,

Packing yayi yashiga cikin part din nasu amma sam baiji motsinta ba, cikin bedroom dinta yashiga nan dinma bata nan, dayan bedroom din yaleka ananma bai ganta ba dan haka yayi gaggawar nufar dakinshi koda yaje can dinma wayam,

"To ina baby ta shiga?" Yatambayi kansa, tunani yayi ko tana bathroom dan haka ahanzarce yaje ya dudduba, gaba daya kaf bata nan hakan yasashi zuwa part din hajiya ko tana can amma abin mamaki hajiya sai cemasa tayi ai yau kwata kwata ma nadiya bata shiga part dinta ba,ganin anty siyama tatafi yasashi juyawa batare da ya zauna ba,

Part dinsu yasake komawa yana shiga idanuwansa sukayi arba da wata farar takarda akan dan madaidaicin Stoll din dake gefen kujerun falon,

Da saurinsa ya karasa yadauki tskardar ya warwareta yafara karantawa,

  _Zuwa ga didi na abin alfahari na, nasan kanata nemana amma baka ganni ba to kayi hakuri kuma kayafe min duk da nasan kai dama mai hakurin ne sannan nasan kabawa rayuwata gudun mawa ta bangarori daban daban, ni nadiya ina mai bakin cikin sanar maka da cewar natafi inda bazaka sake ganina ba, na zabi inbarka saboda wasu dalilai..._

Kasa karasa karantawa yayi yazauna sharafff akan kujera idanuwanshi jajur, tunani yake aransa shin wanne laifi yayi mata da har zata yanke masa wannan mummunan hukuncin, baiyi zatoba kawai yaji kwalla na neman cika masa ido, goge kwallar yayi yasake duban wasikar tata,

_Kayi min afuwa didi na nasan hankalinka yatashi idan kadawo daga siyo min Orange din kasameni a corridor zanyi maka wani albishir, duk abinda nafada da farko ba gaskiya bane am joking..._

Cillar da takardar yayi ya nufi corridor da gudu gudu, kwance ya hangota kan doguwar kujera tana sanye cikin bakar doguwar riga ta materia taci kwalliya abinta sai kamshi ne mai dadi yake fita daga jikinta,

"Baby..." Yakira sunanta yana girgizata, bude idanuwanta tayi tana murmushi,

"Meyasa zaki yimin irin wannan wasan, kin san kuwa yanda hankalina yatashi?"

"Didi kenan nima ai haka kayi min, ramawa nayi.."

Zama yayi agefenta yakamo hannunta yarike,

"Shikenan anyi 1-1 yawuce, ki fada min albishir din da kikace zaki yimin.."

Dan yatsina fuska tayi ta muskuta,

"Ina lemon zakin yake..?"

"Yana falo.."

"To dauko min sai infada maka amma fa ka yanko min shi"

Tashi yayi mintuna kadan sai gashi yadawo rikeda filet wanda ya yanko mata lemon akai,

Tashi tayi ta dauki lemon takai bakinta tana kallon amadi wanda shima yabada attention yana kallonta,

"Kasan me? Kakusa zama dady..."

Kallonta yayi cikin rashin fahimta,

"Baby ban ganeba"

"Ina nufin nakusa inhaifa maka baby.."

Rungumeta taji yayi sosai cikin farin ciki kwalla fal acikin sexy eyes dinshi,

"Baby dagaske kike, kin gama yimin komai baby.."

Sakinta yayi yakai hannunshi yadora akan mararta yana shafawa,

"Allah yaraya min kai baby na, Allah ya fito dakai lfy.."

"Abin nema yasamu ko? Ansamu nayi.."

"Sosai kuwa domin nima nakusa nahaifi dan kaina adaina yimin gori.."

Murmushi tayi tana tsotsar lemon dake hannunta,

"Allah sarki.."

"Yes fadi ki kara, may be ma gaskiya sai dai kihakura da exam dinnan har sai kin haihu"

Kallonsa tayi afirgice,

"So kake insake maimaici? Wallahi bazai yiyu ba, kabarni kawai inyi abina ingama ni zan iya"

"Baby bana son yarona ya wahala ne"

Sakin baki tayi tana kallonshi tun daga ranar ya hanata aikin komai babu abinda takeyi abu kadan sai yace shi baya son babynshi ya wahala, ko girki yanzu tadaina yi hajiya ce ke basu sai dai kawai ita tadafa dan abinda take kwadayi,rigarta kuwa kullum cikin dageta yake yana kallon cikinta kamar wani mudubi,

Daurewa tayi sosai tayi karatun jarabawar da zatayi amma duk dare amadi cikin yimata mita yake idan yaga taki yin bacci tana karatu, ahakan dai ta samu ta kammala exam din anan kuma hutu yasamu domin babu abinda takeyi ahalin yanzu, amadi kuwa yadauki son duniya yadorashi akan wannan cikin wanda sai yanzu ne ma zai shiga wata na hudu,

Koda yaushe cikin yiwa cikin hira yake, yayi ta magana shi kadai kamar wani zautacce idan tayi magana kuma yace shida babynshi yake hira, idan zai fita aiki da safe sai yayiwa cikin sallama haka idan yadawo ma sai yace masa yadawo,

Nadiya dai kallonshi kawai take tana jin wani sabon sonshi yana ratsata saboda ko acikinta nafari bata samu irin wannan kulawar awurin kabeer ba amma shi amadi saima ya tambayeta abinda zataci, me zata sha, me take sha'awa, kullum idan zai fita tambayarshi kenan,

"Baby me zan taho miki dashi? Yau mekike sha'awar ci..?"

Ko tace babu abinda take sha'awa baya yarda sai yataho mata da kayan makulashe, ko shakka babu tasan tayi sa'ar miji mai kaunarta wanda ya share mata hawayen da suka jima suna gudana akan kumatunta, duk sanda zai tafi wudil kuwa dakyar take rarrashinsa yatafi domin baya son yayi nesa da ita,

Cikin weekend ya dauketa suka tafi rano saboda tunda tatare bataje ba, tsaraba sosai amadi yayiwa su mama su amira da twins,

Kowa agidan saida yayi murnar ganin nadiya saboda tayi bul bul takara kyau fatarta inbanda sulbi babu abinda takeyi,

Wuni cur sukayi saida yamma suka tafi wanda harda su fadeel saboda anyi hutun makaranta, nadiya jin hankalinta tayi ya kwanta saboda yanzu bata da matsalar komai,

Tana kwance acikin bedroom dinta tajiyo hayaniyar su amadi a kitchen shida su fadeel, tashi tayi tafita wurinsu daga ita sai rigar bacci iya gwiwa ash colour cikinta yadan bayyana kadan,

Kallonta amadi yayi ya hadiyi yawu,

"Baby gaskiya yau fa zanyi tawaye, gaskiya yau ina bidar wani abu.."

"Kaga ni zubo min kwan inje inci yunwa nake ji, yanda kake da ci haka babynka yake kamar gara.."

Murmushi yayi yadauki filet yana saka mata kwan da yake soyawa, rungumeta taji su fadeel sunyi suna cewa,

"Good morning momy"

"Morning fadeel, morning fadeela na.."

Karba tayi tafita falo tazauna tahada tea tafara karyawa, ita kanta mamakin yanda akayi amadi ya iya girki take saboda idan yayi maka abinci sai ka rantse itace tayi bashi ba,

Har tagama basu fitoba, tashi tayi takoma bedroom dinta ta dauki towel tashiga wanka, dama kamar jira amadi yake wuf taji yafado cikin toilet din,

"Baby kawo intayaki wankan..."

"A'a barshi basai ka tayani ba"

"Uhm uhm nidai sai natayaki.."

Babu yanda ta iya dole tabarshi yafara tayata din wanda daga karshe ya bige da abinda yafi muradi wanda dama tasan abinda yakeso kenan shine ya bullo ta haka,shiryata yayi shima ya shirya cikin kananan kaya,

Tana gani suka fita suka barta agidan shida twins yace banda ita ayawon saboda baison babynshi ya takura, jin zaman kadaici yadameta yasata shiga part din hajiya, acan suka dawo suka isketa nan ya goyeta ganin hajiya bata cikin falon ya tarkatosu suka koma part dinsu yakawo mata tsarabar kwakwa da dabino, zuba masa ido tayi tana kallonsa suna boxing shida fadeel,

"Meye ne kiketa kallona..?"

"Ina son haifar baby mai kamada kaine shiyasa"

Murmushi yayi mata,

"Ko baki kalleni ba dama na tabbatar dan da zaki haifo min mai kamada nine sak dan jinina yafi naki karfi"

Dabinon ta dauka tana ci tana kallonshi,

"Inji waye...?"

"Inji ni saboda jinin last born yafi na first born karfi"

Dariya tayi taja pillow din kujera ta kwanta taci gaba da kallon boxing din da suke yi.

"To yanzu dai fada min dalilinka na siyo min wannan kwakwar da dabino"

"Kinfi dan dako sanin tasha,Saboda tunda nabaki babyn nan kika zama wata lazy..."

Pillow tadauka ta jefeshi nan yakare dukan da hannunshi yana dariya.

***

  Al'amarin kabeer yanzu yadan samu wani aiki na wucin gadi awani companyn sarrafa auduga, amma har yanzu yana jin radadin abinda asabe mc tayi masa musamman ma rabashin datayi da abar sonshi nadiya,

Haka dai ya daure ya rungumi kaddara domin babu yanda ya iya yasan nadiya tayi masa nisan da bazai taba cimmata ba,agaba abbanshi da mama suka sashi kan dole sai yanemo aure saboda zamanshi ahaka bazai yiyuba tunda Allah yasa yasamu abinyi,

Acikin unguwarsu yasamu wata yarinya murja kawar Aisha kanwarshi suka daidaita har aka yanke ranar aure, shi dai yasan samun madadin nadiya arayuwa abune mai wahalar gaske shiyasa duk lokacin da yatuna da asabe sai yaja mata Allah ya isa.

***

Awurin nadiya su fadeela suka gama hutunsu sannan amadi yamayar dasu rano, sati daya da tafiyarsu fadeel yayi mata albishir da cewa alkawarin da yayi mata da jimawa wanda yace sai ta kammala karatu zai bata shine nanda sati biyu zasu tafi kasar Paris domin bude ido, shiru nadiya tayi dan tsananin murna tama rasa me zatayi sai kawai tafashe da kuka ta rungumeshi tana yimasa addu'ar samun babban rabo acikin rayuwarsa ta duniya da lahira,

"Nidai abu daya zaki bani tukwici" yarada mata a kunnenta,

Acikin yan kwanakin suka shirya yakaita rano da sumaila tayi sallama suka bar kasar, gaba daya amadi yasata tamanta da kowa bata iya tuna kowa sai shi sai yanzu ta gasgata maganarshi da yayi mata tun kafin aurensu lokacin tana tsaka da bashi tension cewar zai sota zai kula da ita kuma itama zata soshi tabbas kuwa hakance take faruwa domin yanzu babu wani wanda take kauna sama dashi in aka dauke mahaifanta,

Sun rabarbashi soyayya kamar babu gobe sun ziyarci wurare daban daban dan shakatawa, kasancewar cikinta yakai kimanin wata takwas yasa suka jibgo kayan babies acan,

Satinsu bakwai suka dawo nigeria, koda suka dawo dinma wata kulawar yashiga bata ta musamman har Allah ya sauketa lafiya lokacin yana wudil bai dawoba sai a standard hospital ya tarad dasu yana zuwa yasamu ta haifi yaranta maza guda biyu Ku kanku masu karatu nasan basai nafada muku irin kyawun yaranba domin kyawun amadi ne yahadu da nadiya yabada wani kyawu nadaban,

Amadi rasa inda zai cusa kanshi yayi dan tsananin murna nan yashiga kaffa kaffa da yaranshi da matarshi har aka sallamesu suka koma gida,koda wanne lokaci zaka sameshi rikeda yaran yana kissing dinsu,

Amira da husna sune suka zo domin zama awurin mai jego saiko umman sumaila wanda kunsan ita kuma dalilin zuwanta shine sabinta tsoho yakoma sabo, nan tafara bawa yartata kulawa ta musamman domin haskakata azuciyar amadi,

Abdullah da abdurrahman shine sunan da aka radawa yaran ranar suna,raguna biyu da babban Sa amadi ya yanka musu, sunan yatara dunbin mutane masu yawa domin hatta anty Dija da anty hamida yayun amadi sunzo haka Yaya yaseen shima yazo da iyalansa wannan dalilin ne yasa masaukin hajiya yacika dam dan haka tace wasu suje part din nadiya su sauka acan domin itama yan uwanta sun zazzo tunzuro baki amadi yayi kamar wani karamin yaro domin yasan takurashi za ayi shida nadiyanshi sam bazai sake ba da ita,

Ansha shagalin suna sosai sannan taro yawatse kowa yakama gabanshi sai iya umman sumaila kadai da Amira, cigaba da gyarata umman sumaila tayi har suka cika kwana 40 ranar ta hada nata yanata itada amira suka tafi bayan amadi ya hada musu sha tara ta arziki. Amadi zaucewa ne kawai bayiba saboda irin yanda nadiyan shi ta sauya,kwana yayi yana yi mata sunbatu ita kuma ta wuni tana zolayarshi da tsokanarshi, bashida bakin ramawa sai dai murmushi, ko ina tayi yana biyeda ita, sati daya yadauka agida bai fita ko inaba sai renon twins dinsu da yake tayata sai kuma fitinar da yasakota agaba da ita, itama din sam baya isarta saboda tana mutukar sonshi ahalin yanzu, wata soyaya mai wuyar fadi suke yiwa junansu.

Soyayya mai tsayawa arai amadi yashiga bata itada yaransu lokaci kankani yaran suka zama kamar basu ba saboda girma, shiryawa sukayi sukaje rano suka wuni, har gidansu kabeer nadiya taje tana rikeda abdallah shi kuma amadi yana rike da abdulrahman akan kafadarshi yasha dark blue din danyen boyel da hula ita kuma nadiya tana sanye da wani swiss les pink colour kai idan kagansu sai kaji sun burgeka, agidan kabeer ya samesu yaje gaida mamanshi ganin nadiya da iyalanta yasake tayar masa da hankali amma yasan babu yanda zaiyi tunda ta rigada ta subuce masa har abada, shi kuwa amadi ganin kabeer yasashi murtuke fuska yafara ciccin magani yana yiwa abdurrahman wasa, dakyar ya yarda suka gaisa da kabeer,cewa nadiya yayi tatashi su tafi domin yaga kamar kallonta kabeer yake yi. Har acikin mota sai faman fushi yake ta yimata duk tagane dalilinshi nayin fushin dan haka tasoma lallashinshi,

"Ayya didina kayi hakuri kadaina fushi wallahi ko bayan ranka bazan iya rayuwa da kowanne namiji ba saboda kai kadai nake so.."

Sai lokacin yaji yasamu nutsuwa, "idan kina son nahakura nidai sai kin bani abinda nafi so"

"Zan baka.." Murmushi yayi yashiga saka mata albarka.

Sosai amadi ya mayar da nadiya yar gata kuma sarauniya acikin dukkan mata, mota ya koya mata saboda baya son idan zataje wani wuri ace sai driver ne zai kaita, cikin kankanin lokaci ta kware tana iya kai kanta duk inda zataje,

Tunanin maganar da amadi yafada mata takeyi tana murmushi cewar wai next year iyanzu tasake haifa masa wasu yan biyun, dafata taji anyi tana juyawa taganshi tsaye, girarshi ya daga mata,

"Ya akayi.."

"Maganarka nake nazari da kace wai zan sake haihuwa wata shekarar.."

"Insha Allah"

"A'a gaskiya, zee tazo sai ta dora daga inda natsaya.."

Kai yagirgiza ya rungume ta,

"Ai Allah ma cewa yayi fa inkiftum fa wahidatan au mamalakat aimanikum.."

"To me kake nufi kenan? Ashe kai ba adali bane.."

"Sosai kuwa, duk matar da tashigo bayanki to bazan iya yin adalci ba domin zanyita fifitaki kinga maganin kar ayi kar asoma" yafada yana bata wani cool kiss agefen wuyanta.

Kamar kuwa yafada da bakin mala'iku shekara na zagayowa ta haifi yan biyunta mace da namiji, ranar suna aka radawa yara abdulrahim da amatullah domin dama amadi yace mata bismillahir rahamanur rahim yake son hadawa shiyasa yasawa yaran abdullah, abdurrahman da abdulrahim,

Amadi hade kan iyalanshi yayi yana basu kyakkyawar kulawa ta musamman da tafiya tai tafiya ma sai ya debo su fadeel yahada su da nashi sam baya nuna banbanci komai tare yake yi musu, shi kansa kabeer yadauki hakuri yabar musu yaran sai dai idan anyi Hutu duk term ana kaisu gidanshi hutu saboda su saba da yan uwansu,domin matarshi har ta haifi yara biyu yanzu macen sunan nadiya yasa namijin kuma Mohd.

Sam amadi baya gajiya da nadiyanshi haka kuma bai taba nuna mata cewar wai ba a budurwa ya aureta ba, koda yaushe cikin nacin son kasancewa da ita yake wannan dalilin be yasa umman sumaila sake zage dantse wurin gyara yartata domin mata saida gyara,amadi kam kullum cikin sonshi yanmata suke amma ko kusa basa gabanshi nadiyanshi ita kadai ta isheshi rayuwa.

Familyn amadi abin burgewa ne ga kowa koda yaushe cikin farin ciki suke suna ziyarta wurin bude ido, cikin yawace yawacensu sukaga asabe mc tana bara abakin titi da sanda wacce take dogarawa domin yanzu kafa daya gareta saboda ayawon barikinta taje ta dauko cuta mai karya garkuwar jiki yanzu bata da komai kawaye duk sun gujeta, mazan da take hulda dasu sun daina yayinta, dama haka duniya take yau gareka gobe ga waninka.

   ALHAMDULILLAH

Anan nakawo karshen labarin mijina sirrina, labarin yafaru agaske ba kirkirarren labari bane dafatan Allah ya amfanar damu darrusan dake cikinsa ya yafe mana kurakuran da nayi nidaku baki daya.

Littafin mijina sirrina sadaukarwa ne gareki Nasiba I uba (the writer of kannen mijina)

Tukwicine agareki Feedohm (the writer of bakonmu hasken mu)

Godiya ta musamman ga yan kungiyar haske writers Allah yasake hade kawunanmu amin.

Masu karatu sai mun hadu acikin labari nagaba idan Allah ya amince, duk wata masoyiyar ummi shatu, ko wacce taji tana kaunarta,ko son ganinta ko kuma take son jin muryarta, to ummi shatu tana mutukar kaunarta itama, gaisuwa mai yawa agareku masoyana hakika da bazarku nake rawa, ina sonku har cikin zuciyata aduk inda Luke fatana Allah yabarmu tare.

*_Ummi Shatu_*

5 comments:

  1. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  2. Thanks slot I really appreciate. I enjoyed this book.

    ReplyDelete
  3. Nice book.i really appreciate it

    ReplyDelete
  4. Kinyi kokari sosai maisunan Kanwata ,matana da Kuma "yata , Allah yakara miki basira .

    ReplyDelete
  5. https://mynovels.com.ng/aymana-hausa-romantic-novels/

    ReplyDelete