Monday 4 September 2017

MIJINA SIRRINA...21-32

[7/19, 7:50 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
      _(True life story)_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert writers_

   *21*

~~~Arude yaje inda take yafara jijjigata yana kiran sunanta,

"Nadiya, nadiya, nadiya.."

Jin bata amsaba sannan da alama bata yin numfashi yasashi cikin sauri ya mike ya fita arude domin dauko ruwan sanyi saboda abisa dukkan alamu suma tayi,

Bude idonta tayi tabishi da kallo domin dama suman karya tayi masa saboda taga alamun idan har batayi masa hakaba bazai daina wannan mummunar dabi'ar ta wayar dareba,

Tana jin alamun tahowarsa tayi saurin rufe idanuwanta tareda dauke numfashinta,yana zuwa ya kwara mata ruwan sanyi nan ta saki ajiyar zuciya da karfi ta bude idanuwanta cikin alamun galabaita,

"Nadiya ko zamu tafi asibiti..?"

Kai ta girgiza masa tana kallon duk yanda yabi ya rude domin ko kadan baya son ya sake rasa cikin dake jikinta,

"Bani abinci naci yunwa nakeji"

Cikin hanzari ya tashi yaje ya kawo mata ta karba ta fara ci, tun daga wannan lokacin tasamu yadaina yin wayar dare sannan zuwa kai shamsiyya makaranta ma da yakeyi yanzu yadaina saboda baya son asake samun matsala kamar yanda aka samu a wancan cikin,

Cikin kankanin lokaci nadiya tayi kyau tasake yin kiba saboda yanzu bata da matsalar komai kabeer yana kula da ita haka mahaifiyarsa itama tana iya bakin kokarinta wurin faranta mata rai.

  Har cikin nadiya ya shiga watan haihuwa kabeer bai sake yimata wani abu wanda zataji daci acikin ranta ba domin yana mutukar son cikin dake jikinta,

Cikin dare nakuda ta kamata nan yashiga firgici ya kinkimeta suka tafi asibiti gaba daya yakasa samun nutsuwa yayi nan yayi can har aka samu ta haifi yaranta yan tagwaye mace da namiji, murna awurin kabeer abin ba acewa komai, kasa tafiya yayi sai acikin mota ya kwana, gari yana wayewa kuwa yaje yakaiwa su mama labari kafin kace wani abu tuni har asibiti ya dinke da yan uwa yan gidansu da yan gidansu nadiya, jariran tubarkalla bul bul dasu kyawawa domin yaya kabeer shima ba baya bane awurin kyau haka nadiya,

Kwanansu biyu a asibiti aka sallamesu suka koma gida, kayan da kabeer ya hado shida mahaifiyarsa abin ba amagana domin sun jibgowa mai jego ita da jariranta kaya na kece reni,

Abban kabeer da abban nadiya tare  suka zo ganin jariran anan suke tambayar kabeer sunan da zai sawa yaran yace sunan mahaifiyarsu abban zaisa da sunan mahaifinsu wato usman da Habiba nan su abba suka yita sawa yaran albarka dasu kabeer din,

Adaki yasamu nadiya ya fada mata yanda sukayi dasu abba nan itama tabada goyon baya tace sai su rinka kiran yaran da nabeel macen kuma nabeela,

Shagali iya shagali kabeer yayishi awannan haihuwar, komai da nadiya ke bukata itada yaranta ya tanadar musu, ranar suna aka nadawa yara sunan Habiba da usman,

A washe garin suna kuma aka tafi da nadiya gida domin mamanta ta kula da ita tunda haihuwar farice sannan yara biyu,

Tunda ta koma gida ta sake samun kwanciyar hankali, yaya kabeer yana zuwa kusan kullum yana ganinsu ita da yaranta dahaka har suka yi watanni biyu agida a lokacin ne abba yace zaman ya isa haka ya kamata su koma gida nan nadiya ta hada komai nata ta shirya kabeer yazo ya dauketa suka tafi.

  Komawarta gidanta nan ma babu wani bacin rai ko tashin hankali zamansu suke yi da kabeer lafiya babu wata matsala, dan uwanta kamal kuma kullum cikin kiranta awaya yake yana tambayarta yanayin zamansu da kabeer kullum hakuri da nasiha yake yimata yana nuna mata cewar shi zaman aure ibadane dan haka dole akwai jarrabawa acikinsa.

  Kwantar da hankalinta tayi taci gaba da kulawa da yaranta har suka yi watanni a lokacinne kuma kabeer ya bijiro mata da maganar kara aure.....


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/19, 7:50 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
      _(True life story)_


    *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*

    *22*


~~~Tashin hankali sosai nadiya ta shiga lokacin da taji cewar yaya kabeer zai kara aure nan kuma tabi tafara ramewa amma mamanta da yaya kamal koda yaushe cikin kwantar mata da hankali suke suna cewa ai babu komai tadaina damuwa,

Cikin dan takaitaccen lokaci ya hada kaya ya kai gidansu yarinyar nan manya suka shiga ciki yaci gaba da zuwa wurinta suna soyayya, sunan yarinyar munnira tana zaune acan wata unguwa wai ita hammaga,

Daurewa nadiya tayi ta kwantar da hankalinta ta yakice tunanin abin aranta ta rungumi yaranta fadeel da fadeela wanda ahalin yanzu sun soma girma,

Neman aurensa yaya kabeer yasa agaba amma kuma dayake munnira ba matarsa bace sai ta kwanta rashin lafiya mai tsawo har Allah ya karbi ranta nan yabarwa gidansu kayan da ya kai mata yace bazai karba,

Daga nan kuma haka rayuwa taci gaba da juyawa har yasake haduwa da wata budurwa mai suna kareemat itama kuma da gaske yake sonta bada wasaba,

Koda ya sanar da nadiya hankalinta ba karamin tashi yayiba domin bata san wacce irin mace zai auro ba saboda tana tsoron sake shiga damuwa kamar lokacin baya,

Neman aure dagaske yaya kabeer yake yinsa domin baya son adauki dogon lokaci ba ayiba wannan dalilinne ma yasashi tura magabatansa da wuri,

Nan da nan yafara gyaran gida sannan yafara kokarin hada kayan lefe ita dai nadiya tana zaune tana ganin ikon Allah amma tayi kokarin boye masa damuwarta,

Lokacin da yagama gyara gidansa tsaf sai ya hadowa nadiya kayan fadar kishiya akwatuna uku ya iyo mata cikeda kaya ya kawo,

Sai da yafara kaiwa mamansa tagani nan taketa fada saboda ita sam bata son yayiwa nadiya kishiya saboda bataga laifin yarinyar ba yarinya mai hakuri da biyayya da ganin girman nagaba,

Haka ya debo kayan ya kawowa nadiya tana kitchen tana aiki,

"Ga kaya can nakawo miki.."

Jin abinda yafada yasata ajiye aikin da take tabi bayansa zuwa falonta nan taga akwatuna masu kyau sabbi dal guda uku, duk da cewar kayan ciki masu tsadane sannan sunada mutukar kyau hakan bai hana hankalinta tashiba,

Zama tayi ta bude kayan tafara gani tana jin wani irin bacin rai acikin ranta tamkar zata fashe da kuka amma sai ta daure ta boye damuwarta tafara yaken dole,

"Naga kaya kam kuma sunyi sosai ubangiji Allah yasaka da alkhairi yasa ayi a sa'a"

Tace dashi tana kokarin hada kayan wuri guda, "amin" yabata amsa yana dauke dasu fadeel,tun da taga kayan kuma sai ta shiga damuwa hankalinta ya tashi nan takira yaya kamal ta fada masa yayita bata hakuri, maman kabeer dinma har gida tazo ta rarrasheta tabata hakuri tace ta kwantar da hankalinta koda ace kabeer ya kara aure to bazata wulakanta ba.

Hakurin tayi ta dauki dangana ta zubawa sarautar Allah ido ta zauna tana jiran ranar da zataji yace ta shirya tazo aje akai kaya amma kuma shiru daga karshe ma sai yazo yace yafasa auren,

Duk da cewar lokacin da yace zaiyi aure hankalinta ya tashi to yanzunma da yace ya fasa hankalin nata ba kwanciya yayiba saboda tasan bazata taba fita awurin mutane ba za aga kamar itace take hanashi auren.

Amma koda ta zauna tayi tunani cewar Allah yasan gaskiya kuma yasan zuciyarta sai kawai ta share abin yadaina damunta nan ta kwantar da hankalinta babu daukar dogon lokaci tayi kiba ta murmure, haka taci gaba da zama tana mutukar kyautatawa yaya kabeer musamman ma yanzu data samu ta yaye su nabeel dan haka ta zage damtse tana kyautatawa mijinta.

Shima yaya kabeer din yanzu babu laifi ya dan sauko yana dawowa gida akan lokaci sannan yana zuwa yaci abinci da rana kuma lokaci zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji lafiyarta ita da yara kafin ya dawo gida,

Harkokinsa kuwa koda yaushe sai samuwa suke suna sake budewa domin yanzu yatara kudi wanda shi kansa bai zaci zai mallaki irinsu ba dan haka ya fada harkar business nan yafara fita kasashen waje yana shigo da kaya ko wanne iri na amfanin yau da gobe kafin wani lokacin har yaya kabeer ya zama young millionaire,

Nadiya kam koda yaushe cikin kyautata masa take musamman ma yanzu da taga ya nannemi aure amma Allah bai shirya za ayiba, ita dinma yanzu tayi fes da ita tayi kyau, duk lokacin da yafita saro kaya kasar waje yana kaiwa kamar wata daya acan koma fiyeda haka shiyasa take dauko su Amira su tayata zama kafin ya dawo.

  Haka rayuwar taci gaba da tafiya har tsawon wani lokaci, nadiya nazaune cikin kwanciyar hankali uwar mijinta da danginsa na mutukar sonta ko kadan basa son laifinta, yaranta har sun dan tasa domin yanzu shekararsu biyu da rabi.

  Acikin yawace yawacen da yaya kabeer keyi na fita kasashen waje kwatsam ya hadu da wata Mata ma'aikaciyar gidan wani radio,asalinta yar garin jos ce amma saboda tsabar bariki haka tafito daga gidan iyayenta ta gina gidanta ta tare tana duniyancinta sannan tana fita waje ta ziyarci duk kasar da takeso alokacin data gadama,

Ganin yaya kabeer yasata rudewa nan ta nufeshi tana kwarkwasa tana faman jujjuya jikinta, kamshin turaren da ta saka kuwa kamar zaiyi magana,

Farrr tayi masa da idonta ta kalleshi tana yauki,

"Sunana asabe mc..."

Dagowa yaya kabeer yayi ya kalleta.....



    _Gaisuwa da fatan alkhairi ga dunbin masoya wannan littafin ina gaisheku aduk inda kuke._


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/20, 6:36 AM] Ummi A'isha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(True life story)_

  *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert writers)_

   _Shafi na 23 tukwicine ga yan kungiyar haske writers association, Allah yakara hazak'a da basira hadida fasaha mai albarka.._


  *23*

~~~Cikin yauki da kwarkwasa gamida jan hankali asabe mc tasake magana,

"Haba handsome ya naji Kayi shiru bakace komai ba? Kodai banyi maka bane?

Gaskiya amma idan har kaki kulani bazan ji dadiba.."

Sake kallonta kabeer yayi yana mai kallon irin shigar dake jikinta,

Wani material ne mai shegen kyau gashi daga gani mai tsadane kalar light blue yasha dinkin doguwar riga wadda ta tsaru tamkar yar kanti, ta yane kanta da dan siririn mayafi fari idonta sanye cikin farin face,

"Har yanzu dai banji kace komai ba.."

Dan yake kabeer yayi domin shi ko kadan bai taba ganinta ba sai yau, yau dinma yanzu,

"Gaskiya ka hadu, duk macen data sameka tayi saaaa'a"

Yanda taja maganar daga karshe yasa kabeer zuba mata idanuwanshi yana dan miskilin murmushi,

"Kema kina da kyau ai..." Yafada yana fadada murmushinsa,

"Well.. Tunda har ka yaba dani mai zai hana muyi exchanging contacts so kaga sai mu rinka gaisawa.."

Kabeer baiyi musuba ya bata phone number dinshi ya karbi tata daga nan suka rabu kowa ya nufi wurinda zaije,

Lokacin da yagama harkokinsa zai dawo gida tsaraba ya tulowa su fadeel da nadiya kamar gaske,

Ya dawo ya iskesu lafiya nan kuma yaci gaba da kula dasu, satinshi biyu da dawowa Nigeria yana office a zaune yana aiki wayarshi tasoma ringing yana dubawa yaga asabe mc ce,

"Ranka yadade..."

Yaji muryarta bayan ya daga wayar,

"Yakike..?"

"Ranka yadade kuma haka akeyi daga ranar nan ban sake jinka ba nayi jiran nayi jiran har nagaji naji bazan jureba shine nace bari ni na kiraka na gaisheka"

"To nagode asabe.."

"No ka rinka kirana da mc shine daidai"

"To mc shikenan sai kin jini"

Katse wayar yayi yana murmushi wanda bai san dalilinsa ba,

Haka da yakoma gida ma da daddare sai da asabe mc ta kirashi sannan kuma ta turo masa da wani cool massage,

Tun daga wannan rana take kiransa akalla takan kirashi fiyeda sau biyar arana shiyasa tun baya kiranta har shima yafara kiranta yana mayar mata da reply din text massages din da take turo masa,

Tsawon watanni biyu zuwa uku suka dauka suna waya amma nadiya ko kadan bata taba saniba, wata ranar juma'a kabeer ya kira asabe mc suka gaisa anan ta kashe murya ta marerece tace,

"Gaskiya handsome ya kamata nazo har garinku naganka domin wallahi ina son sake ganin kyakkyawar fuskarka.."

"A'a ai bakece zakizo ba asabe nine yakamata nazo kuma insha Allah zanzo.."

"Yaushe? Karfa kahanani zuwa kai kuma kaki zuwar min.."

"Zanzo, kibari zan sanar dake idan natashi zuwa"

"To ina cikin garin kano dai duk lokacin da zakazo ka sanar dani.."

Sallama sukayi tun daga wannan lokacin kusan koda yaushe asabe bata da magana sai ta tambayar kabeer yaushe zaije wurinta, ganin tanata damunshi akan yaje yasashi shiryawa yayiwa nadiya sallama cewar zaije cikin kano amma bai sanar da ita abinda zaije yiba,

Sabuwar motarshi ya dauka wacce batafi 2 weeks da zuwa ba ya tafi bayan yasha kyau da kwalliya cikin wani sky blue din yadi mai tsada, sai da ya shiga cikin garin kano sannan ya kira asabe mc ya tambayeta unguwar da take nan ta sanar dashi tareda yimasa kwatancen gidan,

Cikin dan takaitaccen lokaci ya samu gidan ya karasa, gidane safe contact mai parts dayawa kusan duk kawayen asaben ne agidan kowacce da part dinta sannan idan tayi bako sai ta saukeshi anan kawai dai gidan yan barikine,

Lokacin da yashiga gidan da wata farar budurwa yafara cin karo tana brush abakin barandar part dinta daga ita sai gajeren wando da yar karamar vest, nan ya dauke idonsa yana jin kamar yakoma kada yashiga amma sai dai sam yakasa komawar haka ya kutsa kai yawuce domin dakin asabe mc shine na biyun karshe,

Wata budurwa yasake gani sun fito itada wani saurayinta suna kokarin rufe kofa nan ya kawar dakai yawuce zuwa sashen asabe,

Sai da yayi knocking sannan ya bude kofar ya shiga nan wani rantsatten kamshin turare wanda bai taba jin irinsa ba ya bugi kofofin hancinsa.....


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/20, 6:35 AM] Ummi A'isha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
      _(True life story)_


  *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.*


    *24*

~~~Bin tsarin yanda aka kawata falon ya rinka yi da idanuwansa, falone babba wanda aka kawatashi da jajayen kujeru, komai na falon ja ne in banda kamshi mai sanyaya zuciya babu abinda ke tashi daga cikin falon,

Bai kai ga karasawa cikin falon ba yajiyo muryar asabe mc tana magana ahankali,

"Barka da zuwa tauraro mai haskawa, farin wata sha kallo, yaro mai tashe dan kwalisa, kyakkyawa son kowacce kin wacce ta rasa ko tasan bazata samuba..."

Juyawa yayi nan ya hangota tana takowa ahankali tamkar wata dawisu, wata classic atamfa ce ajikinta koriya sharr wacce ta dinku sosai dinkin riga da skirt wadanda suka kamata mutuka sannan suka fallasar da asirin surar da Allah yayi mata,

Bakace doguwa mai faffadan hips da cikar kirji, tana da kyakkyawar fuska mai dauke da dogon hanci ga manyan idanuwa, iya kyau asabe mc tana dashi kusanma tana amfani da kyawun natane tana mallakar mazan da suka yi mata ko suka burgeta,

Daurin dan kwalin da tayi tamkar gwaggoro yake ya nadu sannan ya tsaru, ko mayafi bata yafaba ta nufo inda yake tana murmushin da tasan zai sace zuciyar kabeer,

"Ga wurin zama.." Ta yi masa nuni da hannunta, gaba daya kabeer ya yi la'asar kallonta kawai yake fuskarshi dauke da murmushi,

"Da fatan ka iso lafiya?"

"Lafiya lau.."

"To yagida zance ko ya iyali?"

"Iyali dai ranki ya dade.."

Dan dammm tayi alamun bata ni dadiba ko kuma bata zaci zataji haka daga gareshi ba amma da yake gogaggiyar yar barikice sai tayi wani shu'umin murmushi tayi farr da idonta wanda yasha eye shadow kalar atamfar jikinta tace,

"Masha Allah haka nake son ji, ashe dai kai dinma cikakken mutum ne kamar yanda na tsammata, gaskiya nayi mutukar farin ciki da jin haka.."

Tana maganar ne tana kokarin zama akusa dashi nan fitinannen kamshinta yakai masa ziyara,

"To yakike ya aiki ya fama da jama'a?"

Yace da ita yana kallonta domin agaskiya ba karamin kyau tayi ba sosai,

"To ya za ayi gashi nan munata fama.." Tafada cikin muryar jan hankali,

Mikewa tayi tana taku ahankali ta nufi fridge taje ta bude ta dauko masa juice na kwali da battle water ta nufoshi,

"Kar nabar bako babu ruwa babu lemo.."

Shidai kabeer baya magana murmushi dai kawai yake danyi yana binta da idanuwa duk inda ta wulga,

Ajiye ruwan da juice din tayi agabansa sannan ta juya ta nufi kitchen tana juyawa ahankali,

Yanzu kam tasan kabeer ya shiga tarkonta kamar yanda tasaba danawa sauran maza sai dai kuma ita awannan karon bata danawa kabeer tarkon da zai shiga dan kawai suyi rayuwa awajeba a'a tarkon da ta dana masa so take ta mallakeshi ta aureshi sannan kuma ta rayu dashi,

Glass cup ta dauka ta koma falon tana tafe tana yin wasa da cup din ta hanyar cillashi sama ahankali tana cafewa,

Daukar juice din tayi ta tsiyayawa kabeer ta mika masa nan ya karba yafara kurba yana kallonta,

"To ya aikin naku?" Ya tambayeta,

"Aiki muna nan munata fafatawa amma fa abun ba sauki aikin namu akwai wahala sannan gashi da hatsari.."

Ayanda take yin maganar tana yintane cikin nutsuwa da sigar dauke hankalinshi,

Nan ya tattara hankalinsa ya mayar gareta tafara shirya masa labari wanda dama tadade da tanadarsa dominshi,

Sun jima suna tattaunawa kafin ta mike tayi masa jagora zuwa dining table inda ta shirya masa hadadden faten doya da kifi wanda yasha manja da alayyahu, dama wannan shine favorite food dinshi nan ya zauna yafara kwasa batare da tunanin komai ba ita kuwa asabe mc dama ta dade dayin bincike akansa domin hatta gidansa sai da aka kaita aka nuna mata shi taganshi shiga cikine kawai batayi ba, bayada haka duk wani motsinsa saida ta bibiya dan haka tasan abubuwa masu yawan gaske atare dashi shiyasa bazai yimata wahalar samuba,

Sai da ya cinye abincin nan cikin flate yasha lemon data hada masa sannan suka bar dining table din suka koma falo nan ta dan kalleshi tana yin fari da idonta,

"Yakamata muje musha ice cream kafin ka tafi.."

"A'a yanzu tafiya zanje nayi kin gane amma nayi miki alkawari next time idan nadawo zamuje.."

"Ok to babu damuwa.." Tafada tana langabe kai tamkar wata karamar yarinya, tashi yayi tabi bayansa ayanda take babu gyale har zuwa waje wurinda motarsa take,ciki yashiga itama ta bude gefensa ta shiga ta zauna tareda shagwabe fuska,

"Sam bana son tafiyarka kabeer saboda ina girmama lokacin da duk muka kasance tare, duk lokacin da zamu kasance tare to lokacine mai tsada da muhimmanci agareni, dan Allah kar kayi nesa dani, ka daure ka amsa gayyatar zuciyata nason yin kawance tareda kasancewa da taka zuciyar.."

"Karki damu bazan ki amsa gayyatar zuciyarki ba domin tuni tawa zuciyar ta dade da aminta da taki.."

Wani farin cikine ya mamaye zuciyarta wanda yakasa boyuwa akan fuskarta,

"Yanzu to sai yaushe zaka dawo?"

"Zan dawo bada dadewa ba"

"Dan Allah kar kasa zuciyata adamuwa, wallahi idan har baka dawoba zan iya makancewa domin kaine hasken idaniyata..."

Murmushi kabeer yayi tareda janyo cheque dinshi ya dauki biro ya rubuta mata kudi sannan yayi signing ya mika mata,

Wal tayi da idonta tareda kallonsa,

"50,000 baiyi yawa ba kuwa? Anya ayi haka?"

"Babu komai is just the begining.."

"Wato next time na tsammaci fiyeda haka kenan? Tafada acikin ranta afili kuwa sai ta murmusa tace,

"To nagode Allah yabamu ikon rikewa junanmu amana, agaida iyali.."

"Zasuji"

Fita tayi ta tsaya tana daga masa hannu har ya bacewa ganinta....


*_Ummi Shatu_*
[7/20, 6:35 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
     _(True life story)_


  *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.*


  *25*

~~~Wani irin murmushi tayi wanda ita kadai tasan ma'anarshi tareda furta,

"Yaro yarone, yaro bai san wutaba sai ya taka, kabeer kenan da sannu zaka gane wacece asabe mc.."

Juyawa tayi ta nufi cikin gida cikeda takunta na k'asaita.

   Abangaren kabeer kuwa hankalinshi kwance yake driving yana sauraron music kusan kowanne bayan 15 minutes sai asabe ta kirashi taji ya hanya, nadiya kam tana gida bata san abinda ke gudana ba amma koda taga 3 na kokarin yi kabeer bai dawoba yasa ta kirashi awaya anan yake cemata yana hanya yakusa karasowa,

Tunda ya dawo yana shiga falonta taji wani irin fitinannen kamshi wanda ita dai a iya saninta yaya kabeer bashida turare mai makamancin kamshin wannan amma sai bata zargi komai aranta ba nan ta gabatar masa da abincin da tayi tuwon shinkafa miyar agushi,

Jan bakinshi yayi yai shiru bai sanar da ita komai ba agameda tafiyar da yayi haka itama bata tambayeshi ba domin tasan yana yin yawan tafiye tafiye musamman ma yanzu da yafara business.

  Tunda kabeer yaje gidan asabe sau daya yaji tayi masifar shiga ransa sam baya samun nutsuwa har sai ya kirata yaji muryarta, nan zatabi ta kalaminceshi da zancenta na yaudara mai cikeda makirci wanda tayi masa ado da birikanci,

Dolensa babu shiri yasake shiryawa ya koma cikin kano yaje yaganta nan tabi ta cikashi da kayan motsa baki sannan ga shiryayyiyar fried rice wadda taketa faman kamshi,

Sai da yagama cin abincin ya koshi sannan tayiwa kawayenta waya sukazo suka gaggaisa dashi domin dama tanata basu labarin cewa tayi babban kamu tasamu wani alhajin yaro wanda kuruciya ke daukarsa dan haka ita yanzu aure zatayi,

Bayan sun gama gaisawa da kawayen asaben ne kabeer yabasu kyautar dubu hamsin,domin shi yanzu dan yayi kyautar dubu hamsin ba wani abu bane,

Daukar asaben yayi suka fita bayan ta shiga daki ta sake sabuwar kwalliya tareda sabuwar shiga, cikin wata sabuwar shadda ta fito pink colour dinkin riga da skirt Wanda yayi mutukar kamata ta yafa wani dan yalolon gyale sai kamshi take zubawa nan suka fita, wani babban store yafara kaita taje ta lodi kayan da take bukata irinsu man shafawa, sabulun wanka, cosmetics da sauransu nan kabeer ya biya kudin daga nan kuma suka wuce wani hadadden park,

Dakyar asabe tabarshi yatafi bayan ya mayar da ita gida,

Haka yaci gaba da sintiri yana zuwa gidan asabe hira ita kuma dama ta dade dayin shiri akansa nan taci gaba da dorashi awata hanya wadda shi kansa bai saniba, lokaci kadan yaji bazai iya rayuwaba sai da ita, sonta yakeji acikin zuciyarsa kamar me,

Babu bata lokaci yafara shirin neman aurenta, abbanshi ya sanarwa cewar suje jos wurin iyayenta su nemo masa aure nan abba yace sai sunyi bincike tukunna saboda sauran auren ma da ya nannema abaya duk sai da akayi bincike,

Abba da kansa yasa aka bincika masa wacece asabe mc nan aka fede masa daga biri har wutsiya, cikeda takaici abbanshi ya shiga gida ya tarar da mamansu tana aikin girkin tuwon dare,

Akofar kitchen din ya tsaya ya dafa bango,

"Kinji kuma abinda yaron nan yake son jawo mana ko?"

Cikin rashin fahimta mama tafito tana cewa "wanne yaron kuma?"

"Kabeeru mana, wai aure yake nema auren kuma yarasa wacce zai zabo sai yar bariki, duk yan matan garin nan basuyi masaba sai yaje ya auro wadda bata da tarbiyya, wadda tabaro gidan iyayenta ta taho yawon tazubar.."

Salati mama tafara yi tana tafa hannu,

"Kabeerun ne zai janyo mana wannan abin kunyar agari?"

"Shi dai.., amma yanzu zan kirashi zan gargadeshi da babbar murya, wallahi wannan auren ban yarda dashiba, mutukar nine ubansa ni na haifeshi kuma yana ganina da wannan darajar to kuwa bazai auri asabe mc ba.."

"Yo Alhaji ai dama maganar auren wannan yarinyar ma babu ita, ga matarsa nan yar mutunci jininsa wacce tataso cikin tarbiyya, wallahi bazai yiyuba.."

Zaro waya daga cikin aljihu abbanshi yayi ya kirashi yana dagawa yaji yace,

"Kai kabeeru idan kagama abinda kake kazo gida ina son ganinka"

Cikeda murna yabar abinda yake yi zai fita nadiya dake kitchen tana girki sai sallama kawai yayi mata yace zaije abbanshi na kiranshi, adawo lafiya tayi masa saboda bata san abinda ke faruwa ba, cikin kwarin gwiwa ya nufi gidan iyayensa saboda duk a zatonshi andace akan maganar aurensa da asabe mc........

   _Sakon fatan alkhairi ga masoyan ummi shatu masu sonta masu kaunar rubutunta akoda yaushe suna bibiyarsa..._




*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 8:23 AM] Ummi A'isha🏻: [7/22, 7:43 AM] Ummi A'isha *MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(True life story)_


   _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO*


   *26*

~~~Babu b'ata lokaci yaya kabeer ya shiga motarsa ya figeta bai zame ko inaba sai gidansu duk a tunaninsa abba da mama sun amince da maganar auren da zai kara amma koda yaje sai ya tarar da sabanin haka,

Mama tana ganinsa ta zabga masa wata harara wacce rabon da yaganta tayi irinta tun yana yaro karami,

Zama yayi yagaishesu nan kowannensu ya amsa fuskarsa adaure,

"Kabeeru maganar auren wannan yarinyar da kayi ina mai baka umarni a matsayina na mahaifinka ka janyeshi sannan ka nisanceshi har abada, ko bayan raina ban yarda ban kuma laminta ba ka auri asabe mc.."

Cikeda fargaba gamida mamaki mai hadeda tashin hankali kabeer ya dago ya kalli abba saboda abinda yaji abban ya fada ba karamin sakashi acikin rudu yayiba,

"Abba saboda me?... "

"Saboda mune muka haifeka ba kaine ka haifemu ba dan haka yazama dole kayi mana biyya,

Kabeeru ai kabani mamaki ban taba sanin cewa haka kakeba sai yanzu, ashe dama baka da hankali baka da nutsuwa?

Ai kabeeru ko mutuwa mukayi bai kamata kaje ka cusa kanka acikin abinda zai dameka ba, kana zaune da matarka lafiya babu tashin hankali babu komai shine zakaje ka auro gantalalliya marar mafadi,wadda bata samu yabo ba, yarinyar da bata gaban iyayenta zaman kanta take..."

Mama ta karasa maganar tana faman numfarfashi,Kafin ta dora da cewa,

"To wallahi baka isa ba, ba zaka shigo mana da ita cikin zuriyarmu ba muddin mune muka kawoka duniya.."

Tana rufe bakinta abba ya dora daga inda ta tsaya nan suka hadu suketa yimasa fada ta inda suke shiga ba tanan suke fitaba,

In banda gumi babu abinda yake hadawa domin babu abinda yake so yanzu kamar asabe, nan su abba suka yimasa kaca kaca ya tashi ya tafi,

Hankalinsa ya tashi iya tashi, amma bai bari nadiya ta ganeba haka ya daure yabar abin acikin ransa shi kadai da niyyar idan su mama sun huce zaije ya shawo Kansu.

  Sati daya yabasu kullum yana zuwa gidan amma bai kara tada maganar ba har sai da sati daya yacika da fadan da suka yimasa aranar yaje gidan yafara lallashin mama,

"Mama dan Allah kubarni nayi auren nan, kuyi min afuwa domin kamar jihadi zanyi..."

"Kai kabeeru idan baka tashi kadaina yimin maganar nanba wallahi sai naci mutuncinka"

Abba ne yafito daga cikin dakinsa yana kallon kabeer din ransa abace,

"Kabeeru maganar nan bata wuceba? Ai mun gama magana aure nace bazaka yishiba mutukar nine na haifeka dan haka katashi kafice karka kuskusa ka sake zuwar min da magana makamanciyar wannan, kaje ka kula da matarka yar uwarka da yayanka idan kuma kaki zan sassaba maka.."

"Kayi hakuri abba.." Kabeer yafada tareda tashi ya fita,

Abubuwane suka hadu suka dagula masa lissafi domin kullum asabe damunshi take akan maganar aure sannan gashi iyayensa sunki amincewa alhalin shikuma yana mutuwar sonta,

Shiryawa yayi yaje wurin asabe ya sanar mata da halin da ake ciki nan ta rinka famfashi tana zugashi tana nuna masa cewar ko babu yardar iyayensa zai iya aurenta dafarko bai yarda ba amma koda tafiya tayi tafiya sai ya amince, nan yabata makudan kudi yace ta hadawa kanta lefe,

A Tsakaninsu suka saka date din daurin aurensu sati uku masu zuwa,

Sati ukun na cika kuwa shida abokansa suka tafi jos aka dauro masa aure da asabe mc batareda iyayensa sun saniba ita kuwa nadiya dama ko zance makamancin wannan bata taba saniba,

Aranar da aka dauro auren suka dawo shida abokansa, nadiya na cikin daki ta fito daga wanka tana shiryawa ya shigo cikin gidan nan ya iske su fadeel afalo da fadeela suna wasa akan motar wasansu,

Wasa ya danyi musu sannan ya shiga wurin nadiya, tana kokarin daura dan kwali kenan ya shiga nan ya zauna agefen gadonta yana kallonta,

"Nadiya magana nazo muyi.."

Zama taje tayi akusa dashi, "to gani"

"Nadiya dan Allah ki fahimceni, karki ga laifina, ba laifina bane haka Allah ya kadararta ki dauka cewar wannan abun kaddara ne.."

Gaban nadiyane yafara faduwa saboda sai ta zargi cewar ko rasuwa akayi ko kuma wani abu makamancin haka,

"Yaya kabeer wai menene? Dan Allah ka gaggauta fada min.."

"Nadiya na kara aure yau, an daura min aure da asabe m..."

Tsaye ta mike tana kallonsa afirgice nan hankalinta ya tashi,

Bakinta yana rawa ta furta, "yaya kabeer aure ka kara? Shine baka sanar dani zaka kara aureba..?"

Tashi yayi ya rikota zuwa jikinsa nan ta fincike tana zubarda hawaye, ko takansa bata biba ta fita tana kuka, hijab dinta ta dauka afalo ta saka su fadeel agaba suka fice nan yabiyota yana kokarin tsayar da ita amma taki,

Kafafuwansu fadeel ko takalmi babu amma haka ta tisasu agaba suka hau titi....


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 7:49 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(True life story)_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*

   *27*

~~~Ko sauraron kiran da yake yimata nadiya batayiba tayi tafiyarta tareda tare adaidaita sahu nan ta shige itada yaran, da hannu take yiwa mai adaidaita sahun kwatance saboda kuka take yi har sukaje kofar gidansu kabeer,

Mama tana daki tana salla su aisha nafalo sai ga nadiya na kuka, dukkaninsu rudewa sukayi saboda basu san abinda ke faruwaba gashi kuma sun ganta sai kuka take,

Kafin mama ta fito har abba yashigo yana cewa,

"Wacece tazo tabar dan adaidaita sahu awaje bata bashi kudinsa ba..?"

"Anty nadiya ce.." A'isha tafada tana kallon nadiya cikeda tausayawa, komawa abba yayi yaje yabiya dan adaidaita sahun sannan ya dawo cikin gida,

Fitowa mama tayi tana yin sallama daga sallar da takeyi ko addu'a bata zauna yiba,

"Nadiya menene? Meya faru? Keda kabeerun ne?" Mama tayi mata wadannan tambayoyin cikin rudewa,

Kai nadiya ta daga alamun ehh,

"To meya hadaku?"

"Wai aure ya kara shine sai bayan andauro auren yazo yana fada min.."

Salati mama ta rafka tareda rike habarta, nan abba ya shigo cikin falon cikeda mamaki,

"Kikace aure yayi? A ina?"

"Abba a jos, yanzu yazo yana fada min"

Kafin wani yasake magana sai ga kabeer din ya shigo afirgice,

Fada abba ya rufeshi dashi tun kafin ya zauna,

"Auren da muka hanaka sai da kaje kayi ko saboda baka daukemu da muhimmanci ba baka ganin mutuncinmu, to tunda ka zabi haka kaje kayi duk abinda ka gadama amma kasani yazama dole ka saki nadiya, dole ka sakar musu yarsu domin bazaka hadata da cutar hawan jiniba"

"Cutar hawan jini kuma ta nawa? Ai yadade da dora mata ciwon hawan jini sai dai aguji ciwon zuciya kuma.." Mama tafada cikin fada,

Cikeda bacin rai abba yasake magana cikin tsawa,

"Ka saketa nace, ka sakar musu yarinyarsu tun kafin bakin cikinka ya kasheta.."

Zubewa kabeer yayi akasa ya fara rokon abba,

"Dan Allah abba kayi hakuri wallahi ina son nadiya, dan Allah karku raba auren nan wallahi ina sonta.."

"Tashi ka fice daga gidan nan, ko bakaji? Katashi ka fita tun kafin ranka ya baci"

Abba ya nuna masa hanyar fita, nan kabeer yatashi yafita nadiya kuwa inbanda kuka babu abinda takeyi, fada mama da abba suka cigaba dayi abba yana cewa bazai yarda ba kuma yazama dole sai yasaki nadiya,

Kowa nagidan saida hankalinsa yatashi amma gidansu nadiya har lokacin su mama basu san abinda ke faruwa ba, cikin wannan tashin hankalin aka kwana, yanda nadiya taga rana haka taga dare sai kuka data kwana tanayi domin hankalinta yatashi sosai,

Washe gari da sassafe saiga yaya kabeer ya dawo gidan nan abba yasake fatattakarsa yatafi, A'isha da Fati abba yatura sukaje suka debowa nadiya kayanta da kayansu fadeela, daukarsu yayi zuwa gidansu nadiya,

Tunda mama tagansu tasan ba kalauba nan jikinta yabata cewar da akwai abinda yafaru, rungume mama nadiya tayi tana kuka mai ban tausayi nan itama maman tafara hawaye mai zafi,

Abbansu nadiya abban kabeer yasamu ya kwashe duk abinda yafaru yafada masa sannan kuma yace raba auren nadiya da kabeer zaiyi tunda kabeer ya nuna masa bai isaba,

Nan mama tasake jin wani tashin hankalin, iya jiya kadai har nadiya ta fita hayyacinta tayi wata iri da ita,

Saboda tsananin tashin hankali hawan jininta saida ya tashi gashi kwata kwata takasa cin abinci ko ruwa takasa sha,

Nan abban kabeer yace tatashi sutafi itada yaran, ko uffan batace ba tatashi tabishi nan ya kwashesu sai garin sumaila gidan kanwarsu hajiyan sumaila,

Can yabaro su nadiya ya juya yakoma rano, hajiya wacce su nadiya ke kira da umman sumaila saka nadiya tayi agaba tayita yimata nasiha tana bata hakuri, dakyar tasamu taci abinci dan kadan ta kwanta bayan ta kashe wayarta domin kabeer sai faman kiranta yake shiyasa takashe,

Sai da tayi sati lokacin hankalinta yafara dawowa cikin jikinta sannan ta kunna wayarta nan taga massages rututu na yaya kabeer naban hakuri, ko kulawa batayi ba bare tabada reply,

Shikuwa kabeer ya shiga damuwa mutuka domin abba da mama sun juya masa baya, hatta kannensa babu wanda yake kulashi, yaje gidansu nadiya kuwa yafi sau ishirin mama tana cemasa wallahi bata san inda abbanshi yakai nadiya ba,

Sati biyu ya dauka yana zirga zirga amma babu me kulashi, duk da yana cikin damuwa haka ya karasa gyaran part din asabe wanda yake dauke da babban falo da bedroom da toilet aciki kamar na nadiya amma kitchen dinsu awaje yake saidai kowa da nata,

Ana gama gyaran gidan akazo aka yiwa asabe jere nan aka kawota gidanta, Sam kabeer baya cikin hayyacinsa amma saida asabe tasan yanda zatayi ta kalallameshi ya kulata nan kuma suka fada duniyar soyayya koda yaushe suna tare suna shan soyayya amma kullum yana zuwa gidan iyayensa duk da babu wanda yake kulashi idan yaje.

Nadiya kam yanzu zuciyarta ta dan huce tayi sanyi saboda kullum umman sumaila cikin yimata nasiha take tana kwantar mata da hankali hakan yasata sakin ranta abu dayane yake damunta yawan tambayar dasu fadeela ke yimata kullum wai ina abbansu su suna son ganin babansu,

Duk lokacin da suka yimata wannan tambayar kuka take domin bata da amsar da zata basu.

Tunda asabe mc ta tare babu wani wanda ya leka gidan daga cikin dangin kabeer babu wanda yasanta itama babu wanda tasani acikin danginsa, sai dai koda yaushe cikin soyewa suke basa aikin komai sai soyayya, ko girki batayi sai dai suci take away,

Watansu uku da aure komai yafara sauyawa domin hankalin kabeer yafara tashi da rashin nadiya saboda yasan itace sirrinsa, gashi ko kusa bazaka taba hadata da asabe ba, domin asabe irin matan nanne masu son jiki ko kadan bata son aiki, bata girki sai dai aci take sway ko sharar dakinta bata iyawa nan gidan ya kazance idan yayi mata magana tace bazata iyaba dan haka dole yabarta tasamo yar aiki wata dattijuwa mai suna hajjo,

Fushin da su mama sukeyi dashi har yanzu basu huceba sannan kuma yanzu tunaninsa gaba daya ya raja'a akan nadiya da yaransu dan haka yafara nemarwa kansa mafita wato hanyar da zaibi yadawo da nadiya.....


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 7:54 AM] Ummi A'isha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
        _(True life story)_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*

   *28*



~~~Gaba d'aya hankalin kabeer yanzu ya koma kan nadiya domin sai mutum baya nan kake gane amfaninsa, sai yanzu yagama tabbatarwa da cewar nadiya itace jin dadin rayuwarsa, itace farin cikinsa, itace sirrinsa,

Gidansu yaje duk da cewar yasan babu mai saurararsa, abba yasamu akofar gida yana kishingide akan tabarma yana sauraren radio nan ya tsugunna agabansa yana gaidashi amma abba ko kallonsa baiyiba daga karshema sai ya tashi ya kwashe shimfidarsa ya shigewarshi gida yabarshi, cikin damuwa da tashin hankali kabeer yabi bayan abba amma ko saurararsa baiyiba,

Wurin mama yaje wacce ke cikin kitchen tana fere doya nan itama tayi watsi dashi kamar bata san yana wurinba ko kallonsa batayi ba bare ta amsa masa gaisuwarsa,

Iya tashin hankali yashiga domin yasan fushin iyaye ba abun wasa bane, rokon mama yafara cikin muryar nadama kamar zaiyi kuka abin d'a da uwa sai ita ta dan sakko ta saurareshi nan yaketa rokonta akan ta taimaka masa nadiya tadawo gareshi, cemasa tayi yaje yasamu nadiyan yabata hakuri idan taga zata dawo to idan kuma bazata dawoba shikenan,

Tashi yayi yafita da niyyar zuwa gidansu nadiya, cikin sa'a itama ranar suka zo gida itada umman sumaila dasu fadeel domin umman sumailan ta fahimci cewar nadiya tana bukatar ganin gida shiyasa tace su shirya suzo,

Koda yaje gidan nadiya banza tayi dashi amma su fadeela na ganinshi suka tafi dagudu suka fada jikinsa nan ya rungumesu yana jin sonsu har cikin ransa,

Bin nadiya yayi daki bayan sun gaisa dasu mama Allah sarki mama mace mai kirki da kawaici domin tunda abunnan yafaru bata nunawa kabeer komaiba ko canjin fuska bai gani atare da itaba,

Tana kwance akan gado Amira na zaune tana assignment ya shiga, tashi Amira tayi ta fita shikuma yakarasa bakin gadon da take kai, jinshi tayi kawai ajikinta ya rungumeta kamar zai mayar da ita cikin cikinsa, ko daga idonta ta kalleshi batayi ba nan taji yafara rokonta bayan yasake kankameta,

"Dan Allah nadiya ki kara yimin alfarma, ki sake bani second chance, kiyi hakuri ki dauki kaddara, wallahi ke ce rayuwata, nashiga damuwa na rashinki domin na tabbata babu macen da zata iya kula dani kamar ke, dan Allah kiyi hakuri ki koma dakinki.."

Har yayi ban hakurinsa yagama nadiya bata kulashi ba, duk yadda yaso ta saurareshi haka ya hakura yatafi batare da nasara ba, nan kuma tun daga wannan lokacin ya shiga kai kawo da sintiri agidan, ita nadiya yanzu haushinsa takeji sosai sannan bata jin sonsa ko digo acikin ranta dan haka ranar da umman sumaila zata tafi tace zata bita amma mama da umman suka hanata sukace tayi hakuri ta zauna nan tayi kuka kamar wadda aka yiwa mutuwa, ko hucewa daga kukan batayi ba sai gashi yazo nan ya tisata agaba da lallashi yana bata hakuri, yau dinma bata kulashi ba dai haka suka cigaba dayi kullum sai yazo amma bata yimasa magana sai yaransa ne kurum ke maraba da zuwansa,

Ahaka sai da suka dauki sati biyar yana wannan zirga zirgar daga karshe abba da mama suka kirata suka yimata nasiha akan tayi hakuri ta koma dakinta tunda mijinta nasonta, bata son tona masa asiri domin akoda yaushe ta daukeshi a matsayin sirrinta shiyasa tayi shiru bata fada musu irin rayuwar da suka yi dashi tun daga farkon aurensu ba, dayake abbanta yana son ta koma dakansa yaje ya zabo mata set din kayan daki masu kyau da kujeru, komai na daki sai da abba ya sauya mata sabo babu abinda yabari, kayan kitchen ne kawai yabata kudi yace ta siyi abinda take so,

Kannen kabeer fati da A'isha da Amira kanwarta sune sukaje suka shirya mata kayanta nan dakinta da falonta yafito tamkar na sabuwar amarya domin komai sabone, har suka gama aikin suka tafi asabe bata nan,

Adaren ranar yazo ya daukesu, ko kallansa nadiya batayi ba har sukaje gidan, dama dakinta shine na karshe na asabe na farko nanma ko kallon sashen asaben batayi ba tawuce abinta,

Har wani rawar jiki ta lura yakeyi amma ta shareshi, baiyi fushiba yabita dakinta lokacin tana kwantar dasu fadeela bayan sunyi bacci,

Zama yayi agefenta jikinshi cikin nata, jelar kitsonta yakamo yadora kansa akan kafadarta yafara bata hakuri,

"Nadiya kiyi hakuri ki yafe min kidaina wannan fushin dani dan Allah.."

Juyawa tayi ta kalleshi tareda zuba masa kyawawan idanuwanta......


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 8:01 AM] Ummi A'isha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(True life story)_


  *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.*


  *29*

~~~Ta dade tana kallonsa idonta cikin nashi batare data yi magana ba ganin haka yasashi rungumeta ajikinsa yana shakar daddadan kamshin jikinta,

"Kiyi hakuri nadiya dan Allah.."

Jin yanata bata hakuri yasata yin magana,

"Shikenan na hakura.."

Bai bari takarasa ba ya rufe mata baki da nasa, shi kansa yasan nadiya macece irin wacce kowanne namiji zaiyi burin mallaka to amma shi bai san abinda yake damunsa hakaba kawai dai ya tsinci kansa acikin wani irin yanayi.

  Da safe nadiya bata nuna masa komai ba ta tashi fuskarta asake nan ta fita ta shiga kitchen ta hada musu breakfast tafito anan taga asabe akaro nafarko tana tsaye abakin kofar dakinta ta dafa bango tasha kwalliya sosai ga wani uban dauri da tayi samfarin ture kaga tsiya tana ta faman aikin taunar cingam,

Ko kallonta nadiya batayi ba ta wuce cikin dakinta tana dauke da farantin data doro kayan karyawar akai,

Cikin bedroom dinta ta shiga inda yaya kabeer yake kwance yana bacci shida su fadeel sun sakashi atsakiya yana rungume dasu,

Tsayawa tayi tana kallon dakin nata yanda ya hadu komai light purple haka ma kayan cikin falonta suma komai kalar light purple ne,

Ruwan wanka ta shiga ta zuba tayi tafito tafara shiryawa, tana cikin yin shirin yaya kabeer ya farka nan ya zauna ya zuba mata ido domin nadiya itace rayuwarsa,

Murmushi tayi masa ta cikin mirrior, "har ka tashi?"

"Nasamu natashi dakyar..."

Tashi yayi ya sauka daga kan gadon ya nufi wurinta,

"Kin yi kyau.."

Murmushi tayi ta kalleshi, "nagode"

Wucewa yayi zuwa cikin toilet yayi wanka ya fito ya shirya suka koma falo yaci breakfast,

Tunda tadawo dai abubuwan da dan dama dama babu tashin hankali har tayi sati uku da dawowa nan kuma al'amura suka fara sauyawa domin wani iskanci asabe ta tsiro dashi, duk ranar girkin nadiya sai ta rike kabeer adaki ta hanashi fitowa,da ranar girkinta da ba ranar girkinta ba koda yaushe tana manne dashi,

Sannan idanma ta barshi yatafi wurin nadiyan to kwana zatayi tana yimusu hayaniya ta hanasu bacci ko kuma ta kunna kida ta cika gidan da kara,

Ko kadan nadiya bata taba tankawa asabe ba domin shima kabeer din bashida yanda zaiyi kullum cikin bawa nadiya hakuri yake yana cewa ta rufa masa asiri karta tafi ta barshi domin idan har ta rabu dashi baisan yanda rayuwarsa zata kasance ba,

Tun nadiya tana hakuri har abin yasoma isarta domin asabe ta iya duk wani salo na bariki, sai ta daidaici kabeer zai shigo gida idan girkin nadiyane sai tafito half niket tazo ta tsaya akofar daki tana taunar cingum yana shigowa zata janyeshi zuwa dakinta,

Wannan abun yana mutukar kona ran nadiya amma duk lokacin da suka kebe dashi bata hakuri yake yi, dole take zaune dashi kawai dan babu yanda zatayi amma yana mutukar kyautatawa yaransa yana sonsu sosai haka itama asaben tana masifar son fadeela da fadeel uwarsu ce kawai bata so,

Yau kam tunda yamma nadiya ta tafka tagumi tana jin ihu ihun dake tashi daga cikin dakin asabe ita sam bata san abinda yafaru ba sai kawai ihu takeji gamida sautin kida daketa faman tashi,

Jin abin ya isheta yasata komawa cikin bedroom dinta ta dauki alqur'aninta tafara karantawa anan taji zuciyarta tayi sanyi,

Kabeer ne yashigo yana rikeda su fadeel yazauna akusa da ita ya riko hannunta,

"Nadiya kiyi hakuri nasan mun dameki.."

"Dame?..." Ta tambaya domin ta nuna masa abinsu bai dameta ba,

"Da ihun da mukeyi na birthday din asabe..."

Shiru tayi masa taci gaba da karatun alqur'aninta nan ya tashi yafice, haka suka raba dare suna bikin birthday dinnan har nadiya tayi bacci wurin 12 basu gamaba daga karshema bata san lokacin da suka tashiba.

Haka taci gaba da zama da asabe zaman hakuri da kunci domin kusan kullum sai kawayen asaben sunzo sun kafa daba suna zagin nadiya tareda aikamata da habaici ita kuwa bata taba tanka musuba idanma a kitchen take taji abin ya isheta sai ta kashe wutar data kunna tayi komawarta daki ta kwanta inyaso idan sun gama sun tafi sai tadawo ta karasa,

Ita aduk iskancin da asabe keyi babu wanda yake kona mata rai kamar rike yaya kabeer datake har sai tagadama zata barshi yazo wurinta koda kuwa ranar girkinta ne,

Wannan abu ba karamin yiwa nadiya ciwo yakeba, yauma kamar koda yaushe dakinta yake amma sam asabe ta hanashi fitowa sai hirarsu da shewarsu take jiyowa nan ta tashi tafita ranta abace ta nufi dakin asaben wanda bata taba shiga ba sai yau, su fadeel da fadeela ne ke zuwa subi babansu saboda yaga tana sonsu amma shi fadeel idan akwai wanda ya tsana aduniya to asabe ce idan sunje ya rinka kuka kenan har sai sun baro dakin,

Afusace ta bude kofar dakin ta shiga nan taga asaben daga ita sai wando three quarter da wata yar bingilar riga tana kwance akan cinyar kabeer sai dariya take kyalkyalawa can kuma gefe mai aikinta ce keta faman goge goge,

Ai asabe tana ganin nadiya ta shigo ta daure fuska,

"Yaya kabeer kaifa naketa jira.."

Zuruf asabe ta mike ta nufi nadiya tareda bude fefen bala'i,

"To mahaukaciya, jahila wacce bata san hakkin aureba mai son shiga tsakanin masoya, idan bakida hankali ni zan koya miki, uban waye yabaki izinin shigo min daki..."

Iya wuya nadiya tazo domin zagin da asabe ta tisata agaba tana yimata ba kadan bane dan haka itama ta rama,

"Gaki nan babbar jahila, ai idan ana maganar mai raba masoya to bazaki saka bakiba domin da mijina kika ganni amma kike burin ganin kin rabamu, banza yar bariki marar tarbiyya wadda tabaro gaban iyayenta tafito yawon karuwanci.."

Wani mari asabe ta zabgawa nadiya tana kokarin kai mata na biyu kabeer yatashi ya riketa,

"Ka sakeni in koya mata hankali, wallahi da sai na yimiki shegen duka acikin gidan nan.."

Mai aikin asaben ce ta taso tazo tana basu hakuri tareda rike nadiya, "hajiya kiyi hakuri kinji, dan Allah kuyi hakuri.."

Wata ashar asabe ta mulmulo ta jefawa hajjo mai aiki nan jikin hajjon ya dauki rawa tabar wurin da Sauri, fita nadiya tayi tana kuka ta nufi dakinta.....



*_Ummi Shatu_*🏻
[7/22, 8:20 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(True life story)_


   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.*


    *30*

~~~Nadiya nafita asabe taci gaba dure duren ashar tana zage zage shidai kabeer yarasa me ma zaice yayi shiru yana jinta,

Nadiya tana daki tana kuka ta dauki waya ta kira abbansa ai kuwa lokaci kadan sai ga abba agidan nan yazo kabeer din yafito abba ya ringa surfa fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba dama asabe bata fitoba domin abba yace shi ba wurinta yazo ba wurin yayansa yazo,

Saida abba yayiwa kabeer wankin babban bargo sannan yatafi da sharadin indai aka sake batawa nadiya to zaizo yatafi da ita kuma bazata dawoba sai dai yasaketa,nan ita kuma nadiyan abban ya bata hakuri yatafi,

Abba na tafiya kabeer yabi nadiya daki shima ya bata hakuri dama kuma yaji dadin zagin da tayiwa asabe domin shima ta isheshi saboda kazantarta da rashin bashi girma ga wulakanci da rashin mutunci,

Iya kuluwa asabe ta kulu dan haka ta shirya tanata masifa ta fice bayan ta kira kawayenta awaya tanata dure duren ashar tana sanar musu da abinda yafaru,

Tana fita hajjo mai aikinta tazo kofar dakin nadiya ta kwankwasa nan nadiya tazo ta bude mata, hakuri tafara bawa nadiya gamida karfin gwiwa domin ita hajjo kirkin nadiya take gani sannan gata da hakuri sabanin uwar dakinta, nunawa hajjo cewar babu komai nadiya tayi domin dama lokuta da dama idan asabe bata nan hajjo nazuwa wurin nadiya suyi hira,

Tunda haka tafaru asabe tasake shirin rashin mutunci agidan koda yaushe kawayenta da wasu yara guda biyu yanmata wadanda take ikirarin cewar kannenta ne sai suzo gidan suyita shewa da zage zage kadan suke jira nadiya ta tanka musu suyi mata duka amma nadiya bata taba kulasu ba haka zasu karaci abinsu su tafi, domin ita yanzu abinsu bai dameta ba saboda yan uwan mijinta na tsananin sonta, kowa wurinta yake zuwa babu wanda ya taba zuwa wurin asabe sannan har yanzu mamansu kabeer tana yimata hidima kamar da kuma tana ji da ita,

Haka suka cigaba da zama asabe koda yaushe tana kule acikin daki itada kabeer koda kuwa ranar girkin nadiya ne, nadiya kam ta zubawa sarautar Allah ido kallonsu kawai take, mamanta kuwa koda yaushe cikin bata hakuri take tana nuna mata cewar komai mai wucewa ne haka shima yaya kamal dan uwanta koda yaushe hakuri yake bata yana nuna mata cewa ko wanne mutum da irin kaddararsa,

Yau dai bata san abinda yahada asabe da kabeer fada ba amma tanata jiyo hayaniyarsu domin hayaniyar tasuce ma ta tasheta daga bacci nan kuma tafara jiyo karar alamun duka kabeer yana dukan asabe sai da yayi mata lilis sannan ya kyaleta yafice daga gidan gaba daya, yana fita babu jimawa itama asaben ta hada kayanta ta fita,

"Auren bariki kenan.." Nadiya tafada acikin ranta domin ita tunda take da kabeer bai taba yunkurin dukanta ba sai dai fada kawai amma ita asabe ji yadda ya nada mata duka kuma tasan yadaki banza,

Tunda asabe tatafi gidan yayiwa nadiya dadi suka dawo rayuwarsu ta da babu takurar kowa nan zama yayi dadi har kabeer yana cewa zata koma makaranta tunda bata sake samun wani cikinba nan yaje ya siyo mata form din jami'a ya cike yayi submitting, bikin cousin dinta kamal ya tashi a kura nan kabeer yakaita gidansu mama saboda tare zasu tafi sannan yabata 30,000 yace takaiwa kamal gudun mawa,

Bayan dawowar nadiya daga bikin kamal da sati uku sai ga asabe mc ta dawo amma wannan dawowar kamar da lumana tadawo saboda ko fita zatayi sai ta yiwa nadiya sallama cewar tafita haka idan tadawo ma zata leko tace mata tadawo sai dai kuma wannan bai hanasu kulewa acikin daki ita da kabeer ba wannan abu shi yafi komai yiwa nadiya ciwo, gashi ko abu zai siyo agidan to bai isa ya siyowa nadiya ba sai asabe tayita tijara tana zage zage gamida dure duren ashar,

Makarantar ma da yace nadiya zata koma lokacin da admission din ya fito nan asabe ta tada rikici dolensa yahakura itama nadiya tace bazata yarda ba nan tatafi taje ta fadawa su abban kabeer din fada abba da mama suka fara sukace dole sai tayi karatu ko bayaso, abu dai ya zama rigima da tashin hankali ganin yana neman yayi yawa abban nadiya yakirata yabata hakuri yace ta hakura da karatun tunda shima kabeer din yanzu baya so, nan nadiya tayita kuka itafa gaba daya yanzu tagaji da zamanta da yaya kabeer, zaman gidansa yagama isarta,

Ahaka ta hakura ta dawo gidan amma kullum cikin bacin rai take domin ada kome kabeer zaiyi yana fada mata kuma yana neman shawararta amma banda yanzu, yanzu duk abinda zaiyi sai dai kawai taganshi da abinsa sun gama magana da asabe,

Kudin kunshi da na gyaran kai ya bata yau ta fita tatafi gidansu mamanshi domin a unguwar takeyi, can tawuni agidan mama tareda su A'isha sai yamma suka dawo itada yaranta suna shigowa gidan suka iske asabe mc ta dora daya akan daya akan farar kujera akofar dakinta tana taunar cingum tayi daurin nata kamar yadda ta saba na ture kaga tsiya,

Kallon nadiya tayi tana farfara ido, "Ashe bakya nan?"

"Ehhh" nadiya ta amsa mata,

"To sannu da zuwa"

"Yawwa" nadiya ta amsa a takaice tawuc,

Tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira kabeer tana tambayarsa yana ina, nan yace mata mota yaje daukowa amma yakusa dawowa,

Tana daki tana shiryawa tafito daga wanka taji knocking nan taje ta bude, asabe ce ta shigo har cikin falonta yau tana kallon falon cikin mamaki domin bata taba zaton haka falon nadiya yahadu ba bata san nadiya tanada gata hakaba,

"Lafiya?" Inji nadiya,

"Ehh lafiya kiranki nazo kije kiga sabuwar motar da muka sake.."

Asabe nagama fadin haka ta juya tafita, hijab nadiya tasa ta nufi packing space nan taga sabuwar mota dal hadaddiya mai tsada, tsayawa kawai tayi tana kallon kabeer cikeda takaici domin lokacin da yake neman shawararta tasha fada masa cewar ya runka adana kudinsa yana alkintawa domin yanada yara sannan nan gaba zai sake haifar wasu kuma ya rinka yiwa gidansu da yan uwansa abin arziki ba albazzaranci ba,

"Kizo muje dani.."

Asabe tace da nadiya tana murmushin naci gari,

"A'a sai kun dawo"

Nadiya tafadi tareda juyawa tayi tafiyarta, nan asabe da kabeer suka fita asabuwar motar, ahanya asabe take ta tambayar kabeer wai dama nadiya iyayenta suna da kudine ko shine yayi Mata wadannan kayan falon shi kuma yabata amsa da cewa ai baban nadiya yafishi kudima domin tun duniya tana kwance yake da arzikinsa,

Al'amura sun sake kwabewa abubuwan babu sauki nadiya kawai tana zaune agidan kabeer ne amma asabe ita ke juya gidan domin duk lokacin data raya mata zata biyawa kabeer kudin jirgi da ita kanta suyi tafiya sai sun dade sannan su dawo, duk lokacin da sukayi tafiyar sai dai nadiya tatafi gida idan yadawo sai ta dawo nan zaita bata hakuri,

Haka take zaune zaman hakuri tun tana ganin saukin abin har abu yazama babba domin yanzu sunkai matsayin da kabeer ko abincinta baya ci, baya zuwa dakinta, baya kulata koda yaushe Allah take kaiwa kukanta tunda ada duk da masifar asabe kabeer yana kwana adakinta sannan yana cin abincinta domin nadiya mace ce mai tsafta amma yanzu gaba daya ya sauya,

Ita kanta nadiya jin zaman gidan take ya isheta kamar tana kan kaya, burinta kawai shine tabar gidan nan takira mama take fada mata, kamar koda yaushe nasiha mama tayi mata ta bata hakuri tace taci gaba da addu'a, haka ta hakura ta zauna amma rayuwar babu dadi atattare da ita,

Fada kuwa tsakaninta da asabe kullum ne sai dai idan bazata fito wajeba, yauma daga fitowarta zata kitchen asabe tafara zaginta akan wai kawai dan jiya yaya kabeer ya siyo musu lemo da ruwa dukkaninsu wai akanme zai siyowa nadiya, zagi sosai asabe keyiwa nadiya, dama nadiya tagama gajiya nan tafara ramawa asabe tazo ta kamata da kokawa wai zata daketa itama tarama tuni suka kaure da fada nadiya ta jefarta tahau ruwan cikinta tana duka ahaka kabeer yazo ya iskesu nan ya janye nadiya, dakinta ta koma ita kuma asabe taci gaba da zage zage, daga karshe takoma daki ita da kabeer nadiya bata san me asabe ta fadawa kabeer ba kawai tana zaune adaki sai ganinsa tayi ya shigo nan ya juya mata baya ya mika mata takarda,

"Nadiya na sakeki saki biyu.."

Wata mummunar faduwar gabace ta dirarwa nadiya duk da tagama gajiya da zaman gidansa sannan yanzu ta tsaneshi bata sonshi amma saida hankalinta yatashi, juyawa yayi ya fita ita kuma ta hada kayanta tana kuka taja yaranta suka bar gidan suka nufi gidan mahaifinta........


*_Ummi Shatu_*🏻
[7/23, 7:40 AM] Ummi A'isha🏻: [7/23, 7:37 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(True life story)_


*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert writers)_


   *31*

aishaummi.blogspot.com

     *D*a kuka nadiya taje gidansu mama na ganinta ta tashi agigice domin tasan ba lafiya ce ta kawota ba,

Cikin kuka mai ban tausayi nadiya ta mikawa mama takardar sakin da kabeer yayi mata, mama na karantawa tafara hawaye, daga mama har nadiya kuka suke babu mai rarrashin wani,

Sai da sukayi kuka mai isarsu sannan mama ta goge hawayenta tace,

"Babu komai nadiya kiyi hakuri kinji ki dauka duk abinda yafaru dake kaddara ce sannan jarrabawace daga Allah kuma insha Allah zakiyi farin ciki agaba, insha Allah zaki samu ribar hakurin da kikayi, kiyi hakuri kidaina kuka kinji.."

Tashi mama tayi taje ta damawa nadiya kunun gyada mai zafi ta kawo mata amma ko kadan nadiya takasa sha,

Ahaka abba yadawo ya iskesu, shi kansa yayi mamakin sakin da kabeer yayiwa nadiya lokaci guda dan kawai sunyi fada da asabe,

Waya abba yayiwa abban kabeer ya sanar dashi abinda ya faru nan ran abban ya baci iya baci babu shiri yataho zuwa gidansu nadiya fada yake yi sosai daga karshe yace koda kabeer yadawo bikon nadiya to kar akuskura asaurareshi sannan tunda kabeer yayi haka to babu ruwanshi da shi ya fita sabgarsa,

Haka suka gama jajantawa juna abban kabeer yatafi yaje ya sanarwa da mama abinda yafaru, iya tashin hankali itama mama ta shiga ranta duk ya baci akan wannan maganar, ita kuwa asabe danma kar kabeer yace zai dawo da nadiya sai ta biya musu kudin jirgi suka bar kasar.

Tsabar damuwar da nadiya tashiga sai da tayi kwana 7 bata bacci, mama koda yaushe cikin yimata nasiha take haka ma kamal cousin dinta lokacin data fada masa cewar yaya kabeer ya saketa takanas yazo har gida yayi mata nasiha akan ta dauki kaddara sannan ta manta da batun kabeer,

Da taimakon Allah da taimakon addu'ar iyayenta tasamu tafara rabuwa da damuwa da bacin ran dake damunta, dangana tafara yi ta dauki kaddara domin tasan komai yasamu bawa daga ubangijine,

Cikin yan satittika ta fara mantawa da kabeer babu laifi tafara murmurewa, nan ta danyi kyau tayi fari domin yanzu ta rage yawan tunani,

Kabeer kuwa shida asabe sai da sukayi sati biyar akasar Holland sannan suka dawo Nigeria lokacin da suka dawo yaje gidansu mama yi tayi kamar zata dakeshi saboda tsananin bacin ran abinda yayi, nan yayita bata hakuri amma bata saurareshi ba bare kuma abba wanda dama shi yadade da zare hannunsa daga al'amuran kabeer,

Cikin lokacin bikin fati kanwar kabeer ya taso nan su nadiya sukaje itada mama akayi komai dasu basu nuna komai ba nan kabeer ya rinka bin nadiya da kallo domin ba karamin kyau tayiba,

Hankalin asabe ne yatashi da taji yana ta ambaton nadiya nan tasan yanda tayi ta zugeshi ya rubutawa nadiya cikon saki ukun domin bata son yadawo da ita,

Yaro ya tura ya kira masa nadiya nan tafito ganin shine yasata niyyar komawa amma sai ta daure taje envelope ya miko mata ta karba yaja motarsa yayi tafiyarsa, duk a tunaninta wani abune ko kuma takardar bada hakurice amma koda ta buda sai taga cikon saki dayanne da ya rage a tsakaninsu nan ta fashe da kuka,

Bata nunawa kowa ba hatta mama sai da suka koma gida sannan ta bata takardar tagani, itama mama da abba yadawo takai masa,

Nasiha sosai mama da abba suka hadu suka yimata cewar tayi hakuri ta dauki kaddara insha Allah bazata shiga halin kaka nakayi ba,

Kiran abban kabeer abban nadiya yayi yafada masa yanzu babu aure tsakanin kabeer da nadiya, bakin ciki iya bakin ciki abban kabeer ya shiga amma babu yanda ya iya tunda dan yanzu ka haifeshi ne amma baka haifi halinsa ba.

   Nadiya ta shiga damuwa sosai duk wanda yaganta sai ya tausaya mata amma kuma da yake tana yin addu'a sai ta samu nutsuwa nan ta tattara kabeer da duk wani bacin ran da ya kunsa mata da tunaninsa tayi watsi dasu, tunda ta cire damuwa aranta tayi kyau tayi kiba tayi fari ta rungumi yaranta,

Koda yaushe tana cikin kannenta suna hirarsu domin yanzu kowa yagirma amir har yayi candy zai shiga jami'a ita kuma Amira tana SS 3 yayinda waleeda da husna sukuma suke SS 1,

Rayuwar gidansu dama tun fil'azal rayuwa ce mai tsari da dadi kuma har yanzun ma ahaka take shiyasa nadiya ta kwantar da hankalinta daga ita har yaranta sunyi kyau sosai,

Wata bakwai da mutuwar aurenta tana zaune agida da yamma amir yashigo yake cemata tayi bako, fuskarta ta gyara tafita nan taga musty abokin kabeer,

Gaisawa sukayi yayi mata jajanton abinda yafaru sannan yace shi idan zata bashi dama har yanzu yana sonta zai aureta duk da bawani jimawa yayi da aureba, nan ita kuma nadiya tace yayi hakuri ita wallahi ba yanzu zatayi aureba zata dade bata sake aureba, haka musty ya hakura yatafi, nadiya na shiga gida tabawa mama labarin yanda sukayi da musty sannan ta kara da cewa,

"Ni yanzu duk aure ya fita akaina karatu ma zan koma wallahi, zan dade banyi aureba"

"To Allah ya zabi abinda yafi alkhairi" inji mama domin ita yanzu ta yiwa zuciyarta alkawarin bazata sake takura nadiya ta shiga rayuwar kunci ba,

Ko sati daya ba ayi da zuwan musty ba sai ga yaya kamal yazo cousin din nadiya shima kuma wai yana sonta zai aureta, shima hakuri tabashi tace ita yanzu ba aure zatayi ba karatu zata koma, ita nadiya yanzu duk ta cire maza acikin lissafinta saboda gani take tunda yaya kabeer yayi mata butulci ya juya mata baya babu wanda bazai yimata butulci ba,

Kasancewar yaya kamal yasan irin halin data tsinci kanta yasa bai matsanta mataba gashi kuma tace ita yanzu ita da auren zumunci har abada, ko yaranta bazata yimusu auren zumunci ba,

Haka dai abubuwa suka cigaba da tafiya koda yaushe zawarawa suna yimata sallama amma taki amincewa da ko daya acikinsu, ahaka har ta kwashe watanni 10 agida ganin zawarawa suna yawan damunta yasata yiwa abba magana akan tana son zata koma makaranta, abba bai hanata ba asalima da kanshi yasamo mata form din KUT tayi filling akayi submitting nan ta zauna zaman jiran admission, su fadeel kuwa da fadeela har abba yasasu awata nursery school batare da ya fadawa abban kabeer ba domin acewarsa shi mai kula da yaran kabeer ne koda kuwa ba nadiya ce ta haifesu ba tunda kabeer dansa ne.

Cikin ikon Allah lokacin da aka fitar da admission sai ga sunan nadiya sun bata zata karanci biology kuma dama ita yar science class ce a secondary school nan abba yabata kudi ta shirya ita da amir yakaita tayi registration tagama suka dawo, sai kuma tafara jinjina tafiyar da zatayi zuwa wudil tabar gida domin dole sai dai ta zauna a hostel amma taso ace amir ma a kut yasamu admission da sun tafi tare amma ina shi a north west university ya nema kuma yasamu inda zai karanci law,

Tunda taji ance anfara lectures ta fara shirin tafiya, kudi mai yawa abba yabata yace taje ta hado provision nan ta shiga kasuwa taje ta sissiyo abubuwan da suka kamata sauran kuma tace sai taje wudil din ta siya saboda kar abubuwan suyi mata yawa....



    _Gaisuwa marar adadi ga masoya na masu bibiyar labarin,no one be like you my fans..._



*_Ummi Shatu_*🏻
[7/23, 7:37 AM] Ummi A'isha🏻: _HASKE WRITERS ASSO._ (Home of expert writers)

    *MIJINA SIRRINA...!*🌹
          _(Labarin k'auna)_

_Writing by_

  *_UMMI A'ISHA_*

    *32*


   *B*abu b'ata lokaci nadiya tagama duk wani shirye shiryen tafiya da zatayi komai wanda tasan zatayi amfani dashi ta tanadi abinta, ranar lahadi tayi sallama dagida bayan su mama da abba sun zaunarta sunyi mata nasiha akan ta tsare mutuncinta sannan tasan da irin mutanen da zatayi mu'amula,

Ji tayi kuma kamar tafasa tafiya makarantar saboda irin yanda taji zuciyarta ta karye lokacin da su abba nayi mata nasiha,

Saida ta hadesu fadeel ta rungumesu tana jin kwalla acikin idonta sannan tafita duk da cewa tasan yaranta zasu samu kulawa awurin mama amma dole zasuyi missing dinta musamman ma da yaya kabeer ba zuwa ganinsu yakeba domin tunda suka rabu dashi bai kara zuwa ganin yaranba,

Misalin karfe 3 na yamma ta isa makarantar nan ta shigar da kayanta taje ta shirya kayanta ta fita cikin gari ta iyo provision, saboda halin data tsinci kanta abaya yanzu ta sakawa ranta cewar ba zatayi aureba har sai tasan wanda zata aura domin auren da tayi abaya aurene na kaddara wadda ta riga fata ko kadan bata ji dadinsa ba saboda tayi auren batare da tasan waye wanda zata aura ba,

Wannan dalilinne yasa nadiya ta ajiye maza agefe tayi facing din karatunta tayanda zatayi shi tagama successfully batare da wata damuwa ba musamman ma dataga mama da abba sun mara mata baya,

Tunda nadiya tazo makarantar bata da kawa ko guda daya ita kadai take al'amuranta wannan dalilinne yasa dayawa suke yimata kallon mai girman kai,

Zuwanta jami'a yasata tasake gogewa ta waye saboda tana ganin hadaddun yanmata yan gayu masu class shiyasa itama yanzu tazama mai class sosai dama bata da matsalar kudi ko nawa take so da zarar ta tambayi abba zai turo mata haka shima yaya kamal koda yaushe cikin yimata hidima yake, lokacin data yi wata daya da tafiya  sai gashi yaje mata yakai mata hadaddun mayuka da sabulai da turaruka masu tsada, ita dai harga Allah tasan yaya kamal bashida makusa to amma ita kawai yanzunne bata jin zata sake son wani da namiji bare harta aureshi ya wahalar da rayuwarta,

Nan suka sha hirarsu taje ta iyo masa girki ta kawo masa yaci sai kallonta yake domin nadiya sam jikinta bai nuna ta taba aureba bare har ace tanada yara guda biyu, duk wanda yaganta kallon budurwa zaiyi mata,

Sai da yamma tayi sannan yaya kamal yatafi, acikin satin itama nadiyan ta shirya taje gida weekend, wannan shine karo na farko da taje Gida tun bayan tafiyarta,

Lokacin da amira taganta dariya ta shiga yi saboda sai taga nadiyan tayi kiba tayi kyau abinta kamar ba daliba ba, waya tayiwa amir tace tazo weekend shima yazo ranar friday kuwa sai gashi ita dai mama duk murna ta cikata saboda ganin nadiya ta kwantar da hankalinta tayi kyau tayi bul bul,

"Anty nadiya ya anayin rama a school ke kuma kina yin kiba..?" Inji amir,

"Wallahi yaya nima haka nace Anty nadiya kamar ba student ba mu da muke gidama tafimu kiba.." Amira ta cafke zancen tana dariya,

"Yara kwayi kwa gama dai" nadiya tafada tana dora fadeela akan cinyarta wadda tunda taganta taje ta kankameta taki matsawa ko ina,

Haka nadiya tagama hutunta takoma makaranta ranar monday da sassafe, tunda takoma kuma ta sake maida hankalinta akan abinda tajeyi wato karatu nan tayita raba dare tana karatu tun kafin exam tazo,

Lokacin da suka fara jarabawa kuwa daina bacci tayi saboda karatu, bata wuni a hostel koda yaushe tana library domin bata son damar data samu yanzu ta wuceta,

A ranar da suka gama exam aranar ta tafi gida bayan ta jibgawa su mama tsaraba ta kifi,

Ba karamin dadin hutunta tajiba domin tsakanin dawowarta da dawowar amir kwana biyune, cikin wannan hutun har gidansu kabeer taje babu wanda yayi mata maganar kabeer haka itama bata yiwa kowa maganarsa ba,

Sumaila ta tafi wurin umman sumaila canma tayi kwana biyu sannan tadawo gida tafara shirin komawa school wato zangon karatu na biyu wanda bature ke kira da second semester.

****

  "Yaya amadi yaushe zaka fara zuwa university dinne ko har yanzu baka shirya ba..?"

Wata farar mata tas tafadi hakan lokacin da taga shigowar wani matashin saurayi kyakkyawa wanda ke sanye da green din t shirt da three quarter din wando iya gwiwarsa,

Zama yayi akusa da wata yar dattijuwar mata fara wacce ke sanye da farin glass tana shirya beat gefenta kuma wannan matashiyar matarce wadda tayi magana da farko hannunta rikeda fork tana daukar kankana tana jefawa abaki, kallo daya zakayi musu kagane cewar suna cikin jin dadi da hutu domin tsarin falon kadai ya isa ya tabbatar maka da gidan na masu abinne,

"Washh wallahi Anty kina takura min da yawa.." Matashin saurayin yafada yana kokarin janye flate din kankanar dake gabanta,

"Kai wannan yaron dadina dakai iya sharri yanzu da badan agaban tsohuwarka akayi ba da sai ka kunna min wuta ta dauka gaskene..."

"Hajiya kina jin anty siyama ko..?" Yafada cikin shagwaba,

"Autana kyaleta kayi harkar gabanka kaji" yar dattijuwar ta fada tana cigaba da shirya beat din da takeyi.

"Allah hajiya ke kike kara ahagwaba yaron nan abu kadan sai ki goya masa baya.."

"Ke kuma hakanne bakya so?" Hajiya ta tambayeta tana gyara glass din dake sanye akan fuskarta,

"To hajiya amma dai yaron nan yariga da ya girma fa ai ya kamata ki rage shagwabashi haka.."

"Nak'i na rage din.."

Juyawa gun amadi hajiya tayi wanda ya dauki remote yana canja channel,

"Auta na me zakaci da daddare tuwo ko me?"

"Hajiya tuwo zanci.."

"Tuwon me? Na semo ko na alkama ko na shinkafa?"

"Tuwon shinkafa.." Yabada amsa yana kallon yayarshi anty siyama wadda tayi shiru tana faman kallonsu shida hajiya domin idan akwai abinda hajiya keso a duniya to bayan amadi ne autanta, duk a yayanta tafi sonshi sannan tafi ji dashi ko kadan bata son laifinsa,

Tashi yayi yana yin mika ya nufi dakinshi wanda ke jikin na hajiya,ba karamin tsaruwa dakin yayiba kamar dakin mace komai fes fes ga hadaddun furnitures,

Akan tangamemen gadonshi ya zube ya jawo laptop dinshi wadda ke jikin charge ya bude, kwanciya yayi ya tallafe kumatunsa da hannunshi yana latsa laptop din,

Acan falo kuwa lokacin da yaya amadi ya tashi ya shiga dakinshi kallon hajiya anty siyama tayi tace,

"Hajiya to yanzu dan Allah idan yaya amadi ya tashi aure yaya zakiyi tunda naga yagama karatu kuma gashi yasamu lecturing.."

Murmushi hajiya tayi, "ga dakinsa nan akusa da nawa sai su zauna da matar anan.."

"Haba hajiya ai yayi musu kadan.."

"To basai kiyi tayiba yar nema.."

Tashi anty siyama tayi ta nufi dakin amadi domin ta tsokanoshi da abinda baya so wanda tasan tana fada masa zasuyi fada dashi take awurin,tura kofar dakin tayi ta shiga fuskarta kunshe da murmushin tsokana.....


*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment