Monday 4 September 2017

MIJINA SIRRINA..33-43

*MIJINA SIRRINA...!*🌹
        _(Labarin k'auna)_


  *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.*  _Home of expert writers_


    *33*

aishaummi.blogspot.com


      *J*in alamun bude kofa yasa amadi dagowa ya maida idanuwansa kan kofa nan yaga anty siyama ta shigo fuskarta dauke da murmushi,

Zama tayi agefen gadon tana kallonsa, earpiece din dake kunnensa ya cire ya kalleta,

"Yaron nan kana hutawarka, koda yaushe baka fita ko ina daga gida sai gida.."

"To anty siyama ina kike son na rinka zuwa? Club ko hotel..?"

Murmushi tayi takai masa duka yagoce,

"Idan ka kuskura muka ganoka a club ko hotel basai mun karyaka ba.."

"To tunda bakya son na rinka zuwa wadannan wuraren basai nayi zamana agida kusa da hajiyata ba.."

"To naji yanzu dai maganar zee nazo yimaka.."

Shiru yayi mata saboda baya son wannan maganar ta yarinyar nan zee ita kuma anty siyama ta dage koda yaushe sai tayi masa maganarta,

"Wai anty ni waya fada miki zanyi aure yanzune? Kin san hajiya ma dai bazata bari nayi aure yanzuba sai nanda wasu shekaru.."

"Ai dama yaya amadi ba yanzu ba sai lokacin yayi, kawai dai yanzu daurewa zakayi karinka kulata kana nuna mata kana sonta har kasamu ka kamu da sonta.. Wallahi zee tana sonka sosai"

"To anty naji amma akyaleni nayi tunani tukunna"

Mikewa anty tayi saboda ganin yanda ya hade rai dama tasan baya son maganar zainab ko kadan amma ita zainab din ta dage cewar shi take so,

"To kasaki fuskar taka mana.."

Murmushi yayi wanda ya bayyanar da kyawunsa har kumatunsa sai da ya lotsa sosai, jan lips dinsa ya lasa,

"Anty dan Allah kije mayi maganar wani lokacin"

Juyawa anty siyama tayi tafita tana cewa "ai kai koda yaushe ahaka kake indai akan maganar zee ne narasa meyasa baka son yarinyar nan.."

Komawa yayi ya kishingida bayan fitar anty siyama yaci gaba da tsara lecture note din da yake son fara gabatarwa a gobe litinin,

Ajiye laptop din yayi yafita falo wurin hajiya nan ya tarar anty siyama bata nan tatafi gidanta, zama yayi akusa da hajiya yana cewa,

"Anty siyama shine harda tafiya babu ko sallama.."

"To ai autana kai dinne taga kanata kwallo da kanwarta shiyasa baza ku na shiri da itaba.."

"Hajiya yarinyar ce sam ni bata yimin ba wallahi.."

Murmushi hajiya tayi takawar da zancen domin zee kanwar mijin anty siyama ce tadade tana fama da radadin ciwon son amadi amma shikuma baya sonta ko kadan saboda batayi masaba,

"Yawwa miyar me kakeso ayi maka ne..?"

"Hajiya ai ni kin san miyata bata wuce miyar kuka musamman ma idan taji man shanu.. "

Murmushi hajiya tayi "Allah yabar autana, magajiya... Magajiya"

Hajiya tafara kwallawa yar aikinta kira domin taje ta dorawa Amadi tuwo.

***

Alhaji Nasiru musa hamshakine kuma sananne wanda yayi suna ta fuskoki daban daban a Nigeria, ya rike mukamai daban daban ciki harda babban minister na harkokin kasashen waje, daga baya kuma ya koma ambassador na Nigeria akasar Japan,

Matarsa daya hajiya Farida sai yaransu guda biyar biyu maza uku mata,

Yaseen shine babba sai anty Dija dake binsa sai anty siyama sai anty hameeda daga nan sai dan autansu Ahmad wato yaya amadi wanda haka suke kiransa tun yana dan karami, dalilin da yasa suke kiran amadi da yaya amadi shine tun lokacin da yana dan karami sai yayita kuka wai shima sai ance masa yaya saboda yaji kowa agidan yaya ake cemasa ko anty, da dafarko anty amadi suke cemasa hajiya ta hana saboda tace baza a bata mata sunan dan autanta ba,

Gaba daya gidan a kasar japan suka taso kusan acan ma duk suka yi karatunsu, sai da mahaifinsu ya rasu shekaru hudu da suka wuce sannan suka dawo Nigeria amma anty Dija ita har yanzu tana can zaune da mijinta da yaranta guda biyu,haka itama hameeda tana can akasar Turkish itada mijinta,

Ayanzu suna zaune ne acikin garin kano a unguwar sabuwar gandu, ginin gidan kadai abin kallone domin ginine na zamani kuma na masu hannu da shuni.

  Amadi bai jima da dawowa daga Oxford university dake birnin London ba inda yayi degree dinshi da masters amma yayunshi sunce zai sake komawa yakaro karatu domin gidansu yan boko ne na karshe  hatta yayunshi mata basa aure sai sunyi masters bare kuma namiji shi kansa babban yayansu yaseen matarsa sai da tagama Masters sannan ya aureta shiyasa shima amadi sukace yanzu ya dan huta kafin yakoma, shi dama kwata kwata ma babu wanda yake yimasa maganar aure yanzu saboda aganinsu har yanzu shi yarone tunda gaba daya shekarunsa 28 yanzu aduniya, anty siyama ce kadai ke tsokanarsa da maganar aure saboda akwai wata kanwar mijinta zee datake masifar sonshi duk da anty siyama ta fada mata cewar amadi bazaiyi aure yanzu ba domin ita kanta anty siyaman sai da takai shekaru 30 sannan tayi aure haka babbar yayarsu ma anty dija, haka itama hameeda sai da takai 31 domin su yan bokone kuma dayake sun dade a turai yasa rayuwar turawa sukeyi gaba daya kuma dama gasu farare sosol kyawawa kamar larabawa. K'arshen gata amadi yana ganinsa sosai amma kuma duk da gatan da yake samu hakan baisa ya iskance ba domin tarbiyar gidansu tarbiyace mai kyau sannan kuma iyayensu sun tsaya kai da fata sun kula da rayuwarsu, har yayi Oxford university yagama bashida aboki ko daya bare kawa mace domin yayansu yace duk ranar da yaganshi da mace sai ya targadashi tun yana shekararsa tafarko a jami'a yaseen yayi masa wannan gargadin shiyasa babu ruwanshi da mata asalima ko kulasu bayayi duk da yana ganinsu a school fal dasu da yawa yanmata suna cewa suna sonshi saboda yanada kyau amma baya shiga harkarsu kwata kwata ma shi bai taba yin budurwa ba domin yayansa yace masa bazaiyi masa aure yanzu ba sai ya mallaki hankalinsa da abin hannunsa yanda zai iya kula da kansa da iyalinsa sannan idan ya tsaya kula yanmata kaishi zasuyi su baroshi, wannan dalilinne yasa amadi baya kula kawaye da abokai sai ko cousins dinsa domin mahaifinsu dan asalin kano ne nasarawa local government, hajiya kuma yar borno ce.

***

  Ranar Monday amadi ya shirya yasaka manyan kaya blue din yadi mai tsada da takalmi baki yafito,

"Autana ina hular kuma? Ai yakamata kasaka hula saboda kar daliban naka su rainaka.."

Hajiya tafada tana zuba masa breakfast, kanshi ya shafa ya shafo sumarsa sannan ya kalli hajiya,

"Wallahi hajiya ni banson saka hula gaba daya.."

"Daurewa zakayi autana, kasani ma ko kasamo matar acan..."

Dariya yayi yaja flate din farfesun kayan ciki yafara ci, yana cin abincin suna hira da hajiya har yagama yaje ya dauko blue din hula kalar yadin dake jikinsa yasa yayiwa hajiya salla yafita yana rikeda laptop dinshi da iPhone dinshi,

Wata rantsattsiyar mota sabuwa fil kirar BMW 7 new series yabude ya shiga kalarta black nan yafita daga gidan ya tasamma KUT wudil wato university of wudil, kasancewar ya iya gudu a mota yasashi zuwa da wuri domin a ka'idar time table din daliban da zaiyiwa lecture karfe 10 ne daidai, 9:55 ya shiga cikin makarantar yaje admin block ya ajiye motarsa ya fito yana rikeda iPhone dinshi,

Daidai lokacin nadiya tafito daga admin din tana sanye da bakar riga doguwa mai stones ajiki tayi rolling da jan gyale,

Karaf idanuwansu suka hadu da juna, b'ata rai nadiya tayi yayinda shikuma amadi ya tsaya ya zuba mata manyan sexy eyes dinshi.......



  _Sakon fatan alkhairi ga dunbin masoyan ummi A'isha aduk inda suke.._


*_Ummi Shatu_*
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
         _(Labarin k'auna)_


   *BY*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*  _(Home of expert & perfect writers)_


     _Every day begins with new hopes and dreams, but not all of them make it to the most memorable days of my life list, The day we met, is one of them, It will always be one of my most favourite days. Have a very happy birthday and may God bless you with everything_

  *HBD DAUGHTER MEENAL*



   *34*

aishaummi.blogspot.com

   *T*sawon yan sakanni masu yawa idanuwansu sarke cikin juna, nadiya ce tayi gaggawar dauke idonta daga cikin nasa bayan ta sake tamke fuskarta,

Binta da kallo Amadi yasake yi bayan ta wuceshi tana mai yin dan siririn tsaki domin ta tsani taga namiji yana kallonta yanzu,

Wucewa tayi ta nufi ajinsu dama time table taje ta gano,

Rufe kofar motarshi yayi ya dauko wayarshi ya kira class rep din wadanda zai yiwa lecture din,

Cikin makarantar ya nufa ya tasamma ajin da daliban ke zaman jiransa, nadiya tana zaune ta dukufa tana neman bironta acikin jakarta amadi ya shigo, jin ajin yayi shiru kowa ya nutsu yasa nadiya dagowa nan suka sake yin ido hudu dashi gabansu ne ya fadi atare a lokaci guda,

Mamakine yakama nadiya saboda jin gabanta yanata faduwa saboda kawai sun hada ido da wannan malamin, dauke idonsa yayi ya nutsu saboda duk dalibai sun zuba masa ido shi kadai kawai suke kallo,

Cikin nutsuwa yayi musu sallama abinda yayi mutukar burge daliban, nan yafara bayani a nutse dangane da course din da zai daukesu sannan yace kafin yafara zai so kowa da kowa ya gabatar da kansa, ciki kuwa har dashi dan haka yafara da kansa cikin kwarewa da wayewa ta masu ilmi,

"Am Ahmad Nasir..." Sannan ya nuna wani dake zaune agefensa na dama sit din gaba alamun shima ya gabatar da kansa, nan daya bayan daya kowa yafara mikewa yana fadar sunanshi,

Duk amadi ya kosa azo kan nadiya domin yana son yaji sunanta,iPhone dinshi ya kunna ya dora akan stand din da yake tsaye yafara kokarin lalubo lecture note din da ya shirya, yana dagowa sai ganin nadiya yayi kawai ta zauna nakusa da ita zai tashi nan ya dakatar dashi ya nunata da yatsa, yace,

"Sorry, ke meye sunanki?"

Sai da ta hade rai sannan tayi magana, "Nadiya mu'az.."

Yanda tayi maganar ahankali yasa baijiba kawai dai yaga lebenta ya motsa,

"Sorry.." Yasake fada yana kallonta,

"Nadiya mu'az" yan ajin suka maimaita da karfi nan ya jijjiga kai, haka daya bayan daya suka gama gabatar da kansu,

Course outline ya zayyano musu sannan ya dauki topic guda daya yafara yimusu bayani akai, komai nashi yana yine cikin nutsuwa babu hayaniya, dama kana ganinsa kaga mai cikar kamala domin yanada suffa ta mutanen kirki,

Kowa a ajin sai da amadi ya burgeshi domin turancin shi kadai abun burgewa ne irin yanda yake fitar da kalmomi,

Tsawon awa daya da rabi ya dauka acikin ajin sannan ya fita bayan ya amsa tambayoyin daliban,

Tunda yafita zuciyarsa take nuno masa hoton nadiya, har ga Allah shidai bai taba ganin wata halitta wadda ta dauki hankalinsa lokaci daya kamar nadiya ba, gaba daya ta tafi da tunaninsa wanda har yanzu bai gane abinda hakan yake nufiba,

Har yaje admin block ita kawai yake gani acikin idanuwansa, office din shugaban makarantar yaje sannan ya shiga wurin sauran lecturers din wadanda yakeda alaka dasu yan department din da yake suka gaggaisa ya fito,

Jikin motarshi ya tsaya ko zai sake ganin nadiya amma hakan bai faruba ganin babu alamunta gashi yanata tsaye a rana yasashi bude motarshi ya shiga, hakura yayi ya tafi amma kuma zuciyarsa cike take da hotunan nadiya wanda taketa tunato masa dasu, tun a lokacin yasan lallai maganar hajiya ta tabbata da tace masa kila acan zai samo matar...

  Nadiya kuwa duk haushin amadi takeji saboda ya cika kallo gaba daya ya hanata sakewa ya takura mata da kallo dan haka take ganin dakyar idan zasu daidaita dashi,

Lokacin da yagama lecture ya fita ba karamin dadi tajiba saboda ita yanzu duk wani namiji mai kallonta baya burgeta saboda ta dawo daga rakiyar maza yaya kabeer ya shafawa sauran maza kashin kaji awurinta,

Sannan har yanzu yaya kamal cousin dinta bai hakura da itaba domin kusan koda yaushe yana yawan yimata waya ga turo katin waya da kudi da yake yimata,Wannan ya tabbatar mata da cewa yana nan akan bakansa har yanzu,

Tun daga ranar ita nadiya ta manta da batun wani amadi amma shi amadi fa? Wai..! Ai ranar da tunaninta yakoma Gida sannan shi duk a tuninsa budurwa ce bata taba aureba bare harda yara 2,kasa bacci yayi tunaninta ne kawai ke addabar zuciyarsa,

Kwana biyu da ganinta duk tunaninshi ya sauya, zuciyarsa ta kamu da kaunarta babu abinda idanuwansa keson gani sai ita, shi bai san ai haka so yakeba, daga ganinta sau daya sai kawai tunaninta ya hanashi sukuni?.

   Yammacine mai cikeda dadi domin wata sanyayyiyar iskace kawai ke kadawa yayinda tsuntsaye keta faman shawagi a sararin samaniya, amadi yana kwance akan three sitter a falo sanye yakeda jar t shirt da bakin boxer ya kunna tv yana kallon kwallon kafa amma kuma sai tunanin nadiya yafara kwankwasa masa kofa dole tunaninsa ya rinjayi zuciyarsa yafada kogin tunanin nadiya, har hajiya ta shigo bai saniba domin yatafi duniyar tunani,

"Auta kosai za ayi maka ko alale?" Shiru taji yayi bai amsa,

"Autana.., autanah.."

Sai a lokacin yaji kiran da hajiya keyi masa,

"Autanah lafiya kuwa? Kodai yunwar ce.." Hajiya tafada tana murmushi domin azumi yakeyi duk litinin da alhamis baya wuceshi,

"Haba hajiya yunwa sai kace wani yaro.."

"Ato nasani, ai nazata yunwace ince ko bazaka iya kaiwa ba ka karya.."

Dariya yayi ya tashi zaune yana dafe da kansa, "cewa nayi alale za ayi maka ko kosai?"

"Hajiya ayi kosan kawai.." Juyawa hajiya tayi zuwa kitchen inda magajiya mai aiki take tana ta kiciniyar hadawa amadi kayan shan ruwa,

Bin hajiya yayi da kallo aransa yana jin cewa anya kuwa zai jure har kwana hudu batare da yaga wannan yarinyar nadiya ba saboda yau alhamis shikuma sai Monday sukeda lecture dinshi....

*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
       _(Labarin k'auna)_


   *_BY_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*  _Home of expert and perfect writers_

      _Ina kuke? Momcyn Anas, Boddo Alka, Hafsat mai sheriff, kunfi kowa son mijina sirrina shiyasa nabaku page 35 tukwici kyauta, Allah yabar zumunci.._

    *35*

aishaummi.blogspot.com


   *J*ingina yayi da jikin kujerar da yake zaune azuciyarsa kuma yana tunanin cewa gaskiya ya zama dole gobe yaje makarantarsu nadiya yaganta ko yasamu sassauci daga radadin da zuciyarsa keyi masa saboda ita.

  Washe gari da safe yayiwa hajiya sallama yatafi bayan ya cab'a kyau cikin wata coffee colour din t shirt da bakin jeans, ba karamin kyau yayiba domin ya fito akamarsa sak,

Yana fita anty siyama na zuwa gidan itada zee kanwar mijinta, jin baya nan yasa Anty siyama kiranshi a waya lokacin har yakusa fita daga cikin Kano,

Yana tuki yaga Kiran anty siyama ya shigo, dagawa yayi yana murmushi,

"Anty amadi ya muka tafka sabani?"

Yaji anty siyama tafada cikin tsokana,

"Anty siyama natafi wudil neman aure.."

Dariya yaji tayi saboda duk azatonta wasa yake yi,

"Kaji yaro da rainin wayo,to dama zee nakawo maka kuyi sallama saboda gobe zata koma Malaysia hutunta ya kare.."

"Allah ya kiyaye hanya anty.."

"Ba Allah ya kiyaye hanya zakace ba zuwa zakayi idan ka dawo kuyi sallama kaji..?"

"To anty naji.."

"Dan Allah yaya amadi karka shanyamu kaki zuwa fa.."

"To anty sai nazo"

Katse wayar yayi yana dariya saboda yasan idan bai amsawa anty da to ba yau wuni zatayi tana aikin yimasa waya.

  A b'angaren nadiya kuwa tun ranar laraba ta tafi gida saboda su fadeel basuda lafiya nan hankalinta ya tashi duk da mama tace mata sunji sauki dama zazzabi ne amma hankalin nadiya kasa kwanciya yayi sanin idan ta zauna a makarantar ma ba iya karatun zatayi ba yasa ta shirya kawai tatafi gida,tana zuwa ta samesu suna wasansu Amira tana yi musu wainar fulawa,

Da gudu suka zo suka dale jikinta ajiye jakar hannunta tayi tana kallon su gaba dayansu huciyar zazzabi ta fito musu a kan lebensu,

"Fadeelan momy kawo bakin mu gani.."

"Momy nima kinga.." Fadeel ya matsa jikinta yana nuna mata,

Tsalle suka fara suna murna saboda ganin nadiya suna kiran "momyn mu tadawo, momyn mu tadawo.."

Jin ihunsu yasa mama fitowa daga dakinta nan kuwa taga nadiya,

"Ashe dagaske suke, ni ai nazaci wasa ne.." Mama tafada tana kokarin karasa fitowa daga cikin dakinta,

"Wallahi dagaske ne mama gani nayi kawai gara nataho..."

"Kai anty nadiya dama dai kina son zuwa inbanda haka ai sun samu sauki.." Amira dake zaune acan gefen kitchen tana suyar wainar fulawa ta fada tana dariya,

"Yarinya dan dai ke agida kike ne baki san zafin barin gidaba.."

Tunda nadiya tazo gida tace bazata koma school ba sai ranar Sunday, dan haka koda amadi yaje makarantar sai bai samu ganinta ba haka ya dawo gida yana cikeda damuwa,

Gaba daya amadi yana cikin damuwa dan haka alla alla yakeyi litinin tayi yaje yaga nadiya, kwanakin ma ganinsu yakeyi sam basa gudu sunki yin sauri,

Ranar lahadi da yamma nadiya tayi sallama da gida takoma makaranta, ranar litinin ta fita lecture, wata maroon din atamfa tasaka ta yafa bakin mayafi mai stones ajiki, ba karamin kyau tayiba tayi makeup dinta daidai misali,

Tana shiga class ko minti biyu batayi ba amadi ya shigo,farin yadine ajikinsa da hula ko kadan yau bata yarda ta kalleshiba bare su hada ido amma kuma tana jin gabanta yanata faduwa,

Lokacin da yagama lecture yace ayi question kowa sai yayi shiru jin haka yasashi rubuta musu snap test,

Nan kowa ya dauki paper ya rubutu test din wadda yace 10 minutes test ce kawai,

Lokacin da nadiya tazo yin submitting ta mika masa kin karba yayi yabarta atsaye har saida yagama karbar ta kowa sannan ya juya ya kalleta nan yaga ta wani hade rai ta tamke fuska kamar zatayi kuka,

"Lafiya?" Ya tambayeta tareda karbar paper dinta,

"Lafiya lau.." Tabashi amsa tareda saurin barin wurin,

Cije lip dinshi yayi nakasa yabita da kallo, bai san meke faruwa ba amma ya lura kamar bata son yin koda maganane dashi domin ranar farko da yafara ganinta haka yaga ta bata rai ta hade fuska,

Tattara takardun yayi ya dauki iPhone dinsa yafita aransa yana son sanin wacece nadiya.

Kasancewar anbashi office yasashi nufar office din nasa bashi ya bar school dinba sai yamma, saboda bai tafi da wuri ba ahanya ma yasha ruwa.

  Daga nan bai sake dawowa makarantar ba sai da wani satin yayi bayan yayi marking din test din su nadiya, sosai yaji tasake burgeshi domin yaga tana da kokari sosai, boye test dinta yayi acikin motarsa yabarta anan dan haka koda yaraba test din nadiya bataga tataba dan haka ta daura niyyar binshi tayi complain bayan yafita,

Shi kuwa dama amadi da saninshi yayi haka yasan dolenta zatayi magana mutukar bataga test dinta ba, komai rashin son maganarta sai tayi,

Yana fita daga class din tafita tabishi, yana sanye cikin wata shadda light brown, ita kuma nadiya doguwar riga ta atamfa tasa kalar atamfar farace sai ko digon kaloli ajiki ta yafa jan mayafi,

"Excuse me sir.."

Yi yayi tamkar bai jitaba har saida ta sake maimaitawa anan ya jiyo caraf suka hada ido take gabanta ya fadi,

"Ya akayi..?" Ya tambayeta yana tafiya batareda ya tsayaba saboda office yake son kaita,

"Sir banga test dinaba.."

"Bakiga test dinki ba?" Yayi mata wata tambayar maimakon yabata amsar tambayarta,

"Yes Sir.."

"Ok biyoni office.."

Jin abinda yace yasata yin dan turus kamar bazata bishiba, nan tafara tunanin to tabishi kodai tayi tafiyarta, shikuwa tuni har yayi gaba bai jira tagama shawarar ba....


*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
          _(Labarin k'auna)_



   *_BY_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*   _Home of expert and perfect writers_


      _Gaisuwa mai kima ga k'awata takaina kuma aminiyata Maryam Qaumi ina yimiki fatan alkhairi aduk inda kike.._

   *36*

aishaummi.blogspot.com

     *G*anin har yayi mata dan nisa yasata daga kafarta tabishi zuciyarta nacemata,

"Tunda kece akasa ya zakiyi, ai durkusawa wada ba gajiyawa bane.."

Da sake sake cikin ranta har ta isa office din nashi wanda shi tuni har yabude ya shiga ya zauna,

Ahankali itama ta bude ta shiga, idonsa fes akanta domin dama k'ofa yake facing kuma nan ya ajiye idanuwanshi,

Ji tayi kamar ta koma saboda irin yanda taga ya kura mata ido,sannan office din nashi ba karamin haduwa yayiba,

"Sir gani.."

"To zauna mana.." Yafada yana mai yimata nuni da hannunshi izuwa wata kujera dake gaban tabur dinshi, zama tayi batare data kalleshi ba,

"Mema kikace..?"

Jin tambayar rainin hankalin da yayi mata yasata saurin kallonshi amma babu shiri ta dauke idonta saboda ganinshi tayi dafe da kumatunsa yana kallonta,

"Sir cewa nayi ni banga test dinaba.."

"Kuma kinyi test din?"

Kallonshi tayi tace "ehhh nayi.."

"Kinyi?"

"Ehhh"

"Waye shaidarki idan har dagaske kinyi..?"

"Sir kaima shaida ne cewar nayi.."

"Tayaya?"

"Saboda ranar sai da ka gama collecting din ta kowa before ka karbi tawa,

Hular kanshi ya cire ya shafa sumarsa,

"Ohhh anyi haka.."

"Ok let me check.."

Nan yafara bincike binciken karya dan haka ya Karaci bincikensa yagama batare da yagani ba, kallonta yayi yanda tasha kunu sai abin yanemi bashi dariya,shi yarasa bata ran me takeyi,

"Nadiya... Kinyi satar amsa ko?"

Cikin sauri ta kalleshi, "wallahi Malam a'a"

"To ya akayi taki ta bata amma ta sauran bata bata ba..?"

"Shine ai nima abinda yabani mamaki"

"To kodai kina da aljanun sata ne?"

Ba karamin bata mata rai maganarshi tayiba dan haka ta sake daure fuska tana deciding cewar gara kawai ta hakura ta tashi tatafi tabar masa test din,

"Bari nasake yimiki wata yanzu saboda gaskiya i think bazan kara yimuku second test ba.."

"To Malam bari naje na dauko biro da paper.."

Drawer dinshi ya jawo yaciro biro da plane sheet ya ajiye mata,

"Basai kinsha wahalar komawa ba inada su anan.."

"Wannan wanne irin rainin wayone?" Ta tambayi zuciyarta, "yama rainani.."

"Sir gaskiya am not ready yanzu..."

"Ok duk ranar da kika zama ready sai kizo inyi miki.."

"Ok" tashi tayi ta nufi hanyar fita nan yaji tamkar ya tsaidata ya sanar mata da sirrin dake cikin zuciyarsa amma kuma yagagara yin hakan haka yanaji yana gani ta bude kofar office din tafita.

Naushin iska yayi cikeda takaici,

"Meyasa nakasa fada mata irin son da nake mata?"

Zuciyarshi ce tabashi amsa,

"Ai yanzu idan ka fada mata yayi wuri kabari kabata lokaci tukunna.."

Shawarar zuciyarsa ya dauka na zai cigaba da bibiyarta inyaso sannu ahankali sai ya amayar mata da sirrin zuciyarsa.

  Tun daga lokacin babu abinda yasake hadasu sai dai idan yaje yimusu lecture yaganta, ita kuma nadiya duk yabi ya takura mata saboda ko question ya tashi yi a class to ita zai fara jefawa wannan abu ba karamin bata mata rai yakeba gashi koda yaushe idan taganshi gabanta ya rinka faduwa kenan,

Wannan dalilin ne yasata niyyar fara saka nikab a fuskarta domin amadi yana mutukar takura mata,

Amadi kam yanata son yasamu kofar da zai yimata magana amma yarasa sannan kuma haduwarsu a iya class ne ba ganinta yake awaje ba nan yafara tunanin yanda zaiyi yaganta,

Dabarace tafado masa nan ya kira class rep din su nadiya yace masa wacece nadiya mu'az, nan class rep din yace watace itama a ajin take,

"Ok kace ta kirani yanzu.."

Nadiya tana zaune tagama hada kayanta ajaka tana shirin fita class rep yazo ya fada mata sakon amadi,

Karbar number din amadi din tayi tai saving sannan ta mike ta fita,

Gabanta ne yafara faduwa lokacin da zata kira number, tana shiga taji gabanta ya tsananta faduwa,

"Hello.."

Tana jin muryar ta tabbatar da cewar shi dinne nan taji tana neman rikicewa,

"Sir nadiya mu'az ce class rep ne yace wai kace na kiraka yanzu.."

Shiru yayi yana jinta har sai da yaji tayi shiru sannan yasaki ajiyar zuciya mai nauyi tareda yin mika daga kwancen da yake akan gadonshi,

"Nadiya bakiyi test ba sannan nace kizo kiyi kin k'i zuwa ko kina son kiyi carryover din course dinne next year kidawo ki gyara?"

"No sir"

"To meyasa da kikace zaki dawo baki dawoba.."

"Am sorry Sir.."

"Ok to next week ki tabbatar kin zo kinyi.."

"Ok sir nagode.."

Katse wayar yayi tareda yin saving din number dama dabararshi ya samu contact dinta to kuma gashi ya samu yanzu saura stage nagaba.

   Kamar yadda tafada masa ranar monday bayan yagama yimusu lecture ta dan zauna ta dudduba lecture note dinta sannan tatashi tabishi office dinshi,

Zaune ta sameshi ya kishingida yana waya cikeda barkwanci, katse wayar yayi ya kalleta,

"Are you ready..?"

"Yes Sir.."

Murmushi yayi tareda jan drewar dinsa yaciro test dinta da ya boye ya mika mata,

"Ga test dinki.."

Mamakine ya bayyana a fuskarta bayan ta karbi takardar,

"How comes..?" Ta furta har afili batare data saniba,

"Uhm nadiya ina son zanyi miki wasu yan tambayoyi..?"

Kallonshi tayi, "To Allah yasa nasani"

"Nadiya ke yar wanne garice?"

"Rano.."

"Anyi miki miji?"

Tambayar tasa jinta tayi tayi mata zuwan bazata hakan yasata kallonshi da sauri tareda girgiza kanta,

"A'a"

Wani farin cikine ya ziyarceshi,

"Nadiya ina sonki kuma so na aure bana wasa ba, bana yaudara ba...."

"Kana sona?" Ta maimaita hakan tana kallonsa,

"Ehh ina sonki.."

Ya maimaita hakan with full confidence.....



*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
         _(Labarin k'auna)_



    *_BY_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_

    _This page is for you Nana Hafsat (miss xoxo), & your fighting partner Hafsat Rano,nice to meet you.... One love_

  *37*

aishaummi.blogspot.com


   *K*allonsa nadiya tayi cikeda takaici gamida jin haushinsa,

"To kayi hakuri kadaina sona saboda bazan taba sonka ba, kuma bazan iya aurenka ba.."

"Ko menene dalili?" Ya tambayeta yana yimata kallon mamaki,

"Babu ruwanka da dalilina kawai dai kabawa zuciyarka hakuri tadaina sona.."

"Bazan iyaba nadiya, bani nasakawa zuciyata sonki ba dan haka banida ikon hanata ko kuma cireshi daga cikinta.."

"To nidai bana sonka kuma bazan soka ba"

Tana kaiwa nan ta mike tabarshi da mamaki,shi mamakinta yakeyi yanda take fada masa kiri kiri cewar wai bata sonshi kuma bazata soshi ba,

Ganin tana kokarin fita daga office din yasashi hanzarin mikewa yaje yasha gabanta,

Nan ta kankace ido ta sake bata rai tana kallonshi,

"Nadiya meyasa bakya sona? Banyi miki bane kokuma da akwai wani abu atare dani wanda kike ganin baiyi miki ba?"

Kallonsa tayi babu annuri akan fuskarta ko kadan,

"Ni kawai sonka ne banayi"

"Naji bakya sona amma menene dalili?" Yana maganar ne zuciyarshi na radadi saboda yanda take fadar cewar wai bata sonshi kanta tsaye ko dan sayawa batayi,

"Nafada maka haka kawai nidai baka yimin ba kuma bana sonka.."

"Kenan bakida dalilin tsanata kamar yadda bakida dalilin kin karbar soyayyata..?"

Zuba mata ido yayi yana kallonta yana son yagane menene asalin damuwarta da har bata sonsa domin ayanda take yin maganar tana yinta ne cikin fushi da damuwa hadeda bacin rai,

"Nadiya.." Yakira sunanta tareda matsawa kusa da ita,

"Kisani wallahi ban taba soyayya ba, ban san ya ake yinta ba sannan bansan yanda takeba, kwatsam sai idanuwana suka ganki zuciyata tayi na'am dake har ta kamu da sonki"

Wani bakin cikine ya sake turnuke zuciyar nadiya domin yaya kabeer ma da irin wadannan dadadan kalaman yayi amfani ya gurbata rayuwarta, ya wahalar da zuciyarta, ya sanya damuwa acikin ranta, ya rabata da farin cikinta ya maye gurbinsa da bacin rai tareda damuwa dan haka take ganin anyi nafarko kuma na karshe, yanda yaya kabeer ya lahanta mata rayuwa akaro nafarko to bazata sake bawa wani dama yazo ya dora daga inda yaya kabeer ya tsaya ba,

Shiyasa duk wadannan kalaman na amadi take ganin na yaudara ne wanda babu komai acikinsu face karya da yaudara,

"Ai nafada maka kayi kokari ka bawa zuciyarka hakuri domin ni bana sonka sannan bazan taba sonka ba"

Runtse idonsa yayi cikeda takaici ya budesu sun danyi ja saboda dacin da maganarta keyi masa,

"Naji bakya sona kuma nayarda amma kiyi min alfarma guda daya, kiyi hakuri kibarni na aureki nikuma nayi miki alkawarin zan koyar dake yanda zaki soni, zan mantar dake kiyayyata.."

"Ni bazanyi aure ba har abada kaga kuwa idan hakane to babu amfanin naci gaba da saurarenka.."

Bata sake jiran abinda zaice ba tayi gaba abinta zuciyarta na zugi,

Kamar yadda zuciyar nadiya ke zugi da radadi haka ta amadi shima ke zugin tana yimasa radadi,

Kan kujerarshi yakoma ya zauna yana tunanin abinda ke damun nadiya,

"To Kodai yarinyar nan tanada aljanu ne?" Ya tambayi kansa domin aganinshi idan ba mai aljanu ba wacece zatace bazata yi aureba har abada,

Ya dade zaune a office dinsa abun yanata damunsa sannan yatashi ya tattare kayansa ya rufe office din yafita.

  Ita kuwa nadiya abubuwan da ta fadawa amadi tsakaninta da Allah tafada domin har cikin zuciyarta abinda tafada gaskiyane, sam yanzu bata da burin sake aure kwana kusa sannan ta cire soyayya aranta bata tunanin zata sake son wani da namiji domin tunda dan uwanta jininta yaci amanarta ya ha'inceta gani take babu kuma wanda bazai yimata haka ba,

Yanzu ta dade da sakawa ranta cewar ba ita babu soyayya sannan ai ba a saran mumuni sau biyu a rami guda daya.

  Amadi cikeda damuwa yabar makarantar yafita yana tuki yana tunanin nadiya amma ko da wasa kalaman da ta farfada masa basusa yaji sonta ya ragu daga cikin ransa ba shi yanzu ne ma yake jin cewar yafara sonta,

Koda ya samu ya karasa gida, da lokacin kwanciya baccinshi yayi wayarta yayita kira amma taki dagawa,daga taga shine sai taki dauka daga karshe sai ya tura mata da text massage,

  _pls peak my call, just to hear your voice please.._

Sai da yasake kira fiyeda sau biyar sannan ta daga,shiru tayi lokacin da ta daga wayarma taki magana,

"Nadiya, dan Allah kiyi min magana.."

Kememe tayi taki amsawa, shiru shi dinma yayi kamar yadda tayi suka bar kstinshi yanata konewa,

Sunfi minti 20 ahaka taki tayi magana shikuma yaki kashe wayar yana jiran yaji tayi magana yaji muryarta ko zai ji sanyi acikin ransa,

"Nadiya.." Yakira sunanta ahankali wanda kanaji kasan damuwace aranshi domin muryarshi har tayi wani irin sanyi kalau,

Jin yana neman matsa mata yasata amsawa saboda so take yayi ya kashe wayarsa domin tanada uzuri amma ita ko kadan bata jin zatayi nadama ko dana sanin wannan abun da tayiwa amadi domin itama abaya bataji da dadiba shiyasa yanzu dole ta dauki matakin hana sake komawa gidan jiya.....


*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
          _(Labarin k'auna)_




   *_BY_*

_*UMMI A'ISHA*_


® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & Perfect writers)_

     *38*

aishaummi.blogspot.com


    *S*ai da yayi fiyeda mintu biyu da kiran sunanta sannan ta amsa,

"Ina ji.."

"Nasan kina ji ai.."

Shiru tayi sanin bazata sake magana ba yasashi cigaba,

"Yaushe kike free inzo in ganki?"

"Babu rana"

"Meyasa?"

"Saboda ni karatu nazo yi ba soyayya ba"

Dan shiru yayi na tsawon wasu sakanni,

"Nasani, nima bance soyayya kika zo yiba.."

Daga nan shiru ta sake yi masa taki magana, agogon dake kafe a bangon dakinsa ya kalla, karfe 12 saura yan mintuna kuma tun 10:40 ya kirata,

"Shikenan saida safe.."

Tun kafin yakarasa ta katse wayar kittt, ko kadan baiji ciwon abinda tayi masa ba bare har ransa ya baci, asalima shi dadi yaji da yasamu zarafin jin muryarta a wannan dare.

  Washe gari da safe ma bai iya hakura ba haka ya kirata amma bata dauka ba, ganin yayi mata 2 miss called bata dauka ba yashi hakura saboda yayi tunanin ko ta shiga lecture ne tunda lokacin 10:30 nasafe,

Barinta yayi tayi lectures tagama sai wurin karfe 5 nayamma sannan yasake kiranta, yanzun ma dai dakyar ta dauka tayi shiru,

"Kin fito daga lectures din..?"

"Uhm..." Tabashi amsa wanda kanaji kasan ta dolece,

"To sannu"

Shiru tayi masa nan suka cigaba da zaman kurame, ko tari babu wanda yayi acikinsu fiyeda mintina 20,sai can tayi magana,

"Ina son zanje nayi uzuri"

"Adawo lafiya" shine kawai abinda yace tayi hanzarin katse wayar, ko kadan bata son taci gaba da kulashi balle har takamu da sonshi yazo ya wulakantata kamar yadda yaya kabeer yayi mata,shiyasa bata jin zata sake yin soyaya acikin rayuwarta domin tayi tun tana yar karama daga karshe bata ci ribaba kuma bata samu alfanu ba to me zaisa yanzu ta sakeyi alhalin ta mallaki hankalin kanta,

Ko kusa abinda tayiwa amadi da yamma bai dameshi ba bare ya hanashi kiranta da daddare, sake kiranta yayi bayan ya kwanta yayi shirin bacci,

"Bakiyi bacci ba baby..?"

Yafada ahankali, shiru tayi bata amsa ba dama shi dinma yasan ba amsawar zatayi ba dan haka ya kyaleta bai matsa dole sai tayi magana ba maimakon hakama sai kawai yajawo iPhone dinshi ya kunna ya hau Facebook ga wayar kuma makale a kunnenshi yasa earpiece,

"Ko kina jin bacci?"

"Eh inaji" tafada cikin kaguwa domin alla alla take yace sai anjima,

"To kwanta kiyi baccinki basai kin kashe wayar ba saboda ina son naji ko kina yin minshari..."

Jin yafadi haka yasata cewa, "banida charge sai anjima"

Tun kafin ya amsa ta katse wayar ta kasheta gaba daya ta tura karkashin pillow, wannan dalilinne ma yasa washe gari taki kunna wayar gaba daya saboda kar amadi ya dameta dama kuma tafara tunanin sake layi saboda shi.

Tun safe yake kiran wayarta akashe har wurin 1, kawai sai yaji hankalinsa yatashi bazai iya hakura ba har sai yaje wudil ya gano lafiyarta,

Hajiya tana falo idonta sanye cikin glass tana karanta littafi mai tsarki sai gashi yafito cikin bakar t shirt mai gajeren hannu da blue din wando,

"Hajiya zanje wudil yanzu nadawo.."

Dagowa hajiya tayi ta kalleshi,

"Autana lafiya? Inji dai kalau?"

"Hajiya lafiya lau, ba jimawa zanyiba"

"To ai bakaci abinci ba ka zauna magajiya ta karasa abinci kaci sai ka tafi"

Girgiza kai yayi, "a'a hajiya barshi kawai sai nadawo.."

Tashi hajiya tayi takama hannunsa, "to kaga tunda bazaka jiraba zo ka cinye guntun farfesun nan maza.."

Babu yadda ya iya haka yabita zuwa kan table, nan ta mika masa bread da farfesun hanta guntun wanda sukaci da safe, tana tsaye akansa har saida ya cinye sannan ta mika masa tissue da ruwa tana fadin,

"Yawwa kaga ai yanzu sai nafi yarda da cewar sai kadawo sannan zaka ci abincin.."

Murmushi yayi acikin ransa yace "no body will be like mother.."

Afili kuma yace "to hajiya sai nadawo,bye.."

Fita yayi ya tasamma wudil cikin lokaci kankani sai gashi acikin makarantar,class rep din su nadiya yakira domin har lokacin ita wayarta akashe take,

Cewa yayi yaturo masa nadiya, office dinsa yaje ya bude yashiga,

Yayi kamar minti 10 da zama sai gata ta shigo bayan tayi knocking,

Fes ya sauke idanuwansa akanta, tana sanye cikin pink din doguwar riga tayi rolling da farin mayafi dan madaidaici,

Ahankali ta bude bakinta tayi sallama takarasa ta zauna akujerar dake gaban tebur din amadi,

Kallonta yayi kafin yayi magana,

"Meyasa kika kashe wayarki?"

"Saboda ina da lectures kuma banson adameni.."

Murmushi yayi ya lashi pink lips dinshi,

"To kidaina kashe waya, is better kisata a silent akan ki kasheta gaba daya,

Saboda idan ankira anji akashe sai ayi tunanin ko ba lafiyaba, kinga ni yanzu ina zaman zamana agida kika saka nataso nataho saboda tun safe nake kiranki amma wayar akashe shiyasa nazo naga meya faru.."

Cikeda mamaki ta kalleshi nan suka hada ido, ita abin nasa kamar almara take ganinsa, yanzu kenan yana nufin purposely itace dalilinsa na zuwa wudil yau?

"Tunda naganki kina lafiya shikenan yanzu kinga sai nasamu damar gudanar da duk abubuwan da zanyi.."

Ita dai nadiya shiru tayi tana tunanin wannan kaddara, wannan wanne irin sone Allah ya jarrabi amadi dashi akanta bayan ita kuma ba sonshi zatayi ba,

Kallonta kawai yake yi batare da yasake yin magana ba kamar yadda ita dinma batayi magana ba,sai hade rai da tayi ta bata fuska taci magani,

Sun dade ahaka kafin yace shikenan taje tatafi shima tafiya zaiyi, batayi magana ba ta tashi ta fita,

Murmushi yayi sannan yatashi yafita ya rufe office dinsa,

Kafin yamma har yakoma gida, yana kan dining yana cin abinci bayan hajiya tatashi ya kira nadiya,

Ajiyar zuciya yayi saboda jin ta bude wayar tata amma har yakaraci kiranshi yagama bata dauka ba, sai text ya tura mata cewar yaje gida lafiya.

  Haka al'amarin nasu ya kasance koda yaushe yana kiranta awaya amma idan ta dauka sai dai tayi masa shiru kudinsa yayita tafiya abanza amma wannan bazai hanashi sake kiranta idan anjima ba,

Yau kam ranar lecture dinshi ce, lokacin da ya shiga class yi yayi kamar bai san tana ajinba yayi lecture dinshi yagama, yana tsaye agaban stand ya dauki wayarshi yafara latsawa bayan ya gama lecture din yana jiran questions daga daliban,

"Kizo office ina son ganinki.."

Shine abinda ya tura mata, din din, taji shigowar text nan taga shine tana budewa taga abinda ya rubuta, bata yi reply ba saboda dama batayi illa dai kawai kallonsa da tayi taga ya maida hankali wurin yiwa wani dalibi da yayi masa tambaya bayani,

Bata fuska tayi saboda tasan duk kyawun yaya kabeer amadi yafishi, sannan yafi kabeer wayewa yafishi komai na rayuwa, to kabeer ma da bai kai amadi kyau ba yayi wannan tururuwar yan matan bareshi, sannan yaya kabeer da bai kaishi ajiba yayi mata wannan kwarya kwaryar wulakancin to inaga amadi?

Lokacin da taga ya kammala ya fita itama tashi tayi tafita tana tsakin matsantawa rayuwarta da amadi yake yi....

   _Fatan alkhairi gareku masoya masu bibiyar labarin.._

*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
          _(Labarin k'auna)_



    *_BY_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_



   _Sak'on fatan alkhairi ga yayata mai sona, (Maman meenal), Allah ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki gaba daya, I dey over love you my aunty.._



     *39-40*


aishsummi.blogspot.com


     *B*in bayanshi tayi yana tafiya ahankali kamar wani marar lafiya,

Kusan atare suka karasa office din nan yabude ya shiga tareda bar mata kofar a bude saboda yaganta tana binshi a baya,

Barin kofar a bude itama tayi taje ta zauna ganin haka yasashi tashi da kansa yaje ya rufe kofar ya dawo ya zauna,

"Nadiya, wai har yanzu baki sauya ra'ayinki akaina ba? Har yanzu baki ji aranki cewar ni masoyinki ne na hakika ba?"

Kamar bazata yi magana ba sai kuma ta bude bakinta,

"Gaskiya banjiba, shiyasa nafada maka tun farko cewar ka hakura dani saboda bana jin zan soka.."

"Har yanzu bakya sona kenan..?"

"Bana sonka gaskiya"

Murmushi yayi,

"Nadiya kenan, nikuwa kina bani mamaki irin yadda kike fada min wai bakya sona kanki tsaye, ke ko yar karantawa ma babu, bakya tsoron nayi miki halinmu na lecturers in kadake?"

Shiru tayi bata amsaba,

"Shikenan you can go, sai munyi waya.."

Mamaki ne yakamata saboda ita duk tunaninta yayi fushi bazai sake bi takanta ba amma sai taji sabanin haka,

Tashi tayi tafita yabita da kallo ya tattara inasa inasa ya tafi,

Tun daga nan yaci gaba da yimata waya, text da sauransu, dai dai da rana daya basu taba yin hira ta minti dayaba sai dai kawai ta dauki wayar tayi shiru idan yagaji yace mata sai anjima ya kashe,

Text massage kuwa ko ya aiko mata bata yimasa reply, gashi da zarar ya kirata yaji bai sameta ba hankalinsa zai tashi nan zai bar duk abinda yakeyi yatafi ganinta, har sai yaganta lafiya lau sannan zai koma yaci gaba da harkokinsa,

Ita abin nashi mamaki yake bata saboda lokuta da yawa sai taganshi yazo makaranta idan tazo sai yace kawai ita yazo gani bawai wani uzurinne ya kawoshi ba, wannan abu yana mutukar daure mata kai amma koda ta tuna yaudara irinta maza sai take ganin ai wannan ba komai bane domin zasu iya yin fiyeda haka ma,

Ganin abin nashi bamai karewa bane yasata shirya yanda zatayi masa wanda tasan cikin ruwan sanyi zai rabu da ita, dakansa ma zai ce mata ya hakura,

Ranar da zai zo yayi musu lecture ya kirata da safe,

"Yawwa dama Ina son zamuyi magana dakai.."

"Inajinki, ai gani"

"Dan Allah dan annabi ka rabu dani.."

"Saboda me?" Ya tambayeta,

"Saboda ni ba sa'ar aurenka bace"

"Kamar ya kenan?" Ya bukata,

"Ni bazawara ce harda yara biyu, yarana har sun fara zuwa school, kai kuma kaga saurayine dan haka aurenmu bazai yiyu ba.."

Shiru taji yayi dan haka tafara tunanin daga yau zasuyi bankwana dashi, bankwana na har abada,

"To kibari idan Nazo makaranta bayan mun gama lecture sai inganki ko 10 minutes ne"

"Ok" shine kawai abinda ta fada ta kashe wayar,

Kamar yadda yafada bayan yagama yimusu lecture tabishi zuwa office dinshi, kallonta ya jima yanayi sama da kasa yana son yagano banbancinta da budurwa amma yakasa, shi har yanzu kallon budurwa yake yimata,

"Kikace kin taba aure?"

"Ehh har inada yara ma guda biyu.."

Murmushi taga yayi ya kalleta,

"To ina babansu? Rasuwa yayi?"

"A'a rabuwa muka yi"

"May be saboda in sameki ne shiyasa Allah ya rabaku,rabona ne ya danne nashi..."

Mamaki maganarshi tabata nan takasa koda kwakkwaran motsi tayi shiru tarasa abinda zatace.

Zuba mata ido yayi yana kallonta shidai yasan bawai son nashine bata yiba akwai dai dalili mai karfi wanda bazai barta ta amshi soyayyarshi ba bawai dan baiyi mata ba, shida mata ke binsa suna cewa suna sonshi to tayaya ita da yace yana sonta da bakinsa zata ce bata sonshi,

"Indai akan cewa kin taba aurene sannan kinada yara yasa bakya sona ko kuma kike son kin amsar soyayyata to kisa aranki cewar yanzu ne ma nasake jin ina sonki fiye da yanda nake sonki ada, zan aure ki ahaka sannan zanci gaba da sonki ahaka..."

Dafe goshinta tayi tana al'ajabin wannan abu na amadi sai kace abin asiri, ga yan mata nan a makarantar kyawawa hadaddu masu aji amma duk yarasa wacce zai so sai ita?

"Kayi hakuri fa, ni sonka ne kawai banayi.."

Tashi tayi ta dauki jakarta har taje bakin kofa taji yace,

"Nikuma ina sonki sannan insha Allah sai na aureki.."

Bude kofar tayi tafita tana jin haushinsa saboda ita tagama dawowa daga rakiyar maza tasan mafi yawansu abinda yake bakinsu bashine acikin zuciyarsu ba, abinda yaya kabeer yayi mata kadai ya isheta example a rayuwa domin yasota awaje ya kaunaceta kamar zaiyi hauka amma daga ranar da aka kaita gidanshi tayi sallama da farin ciki ta shiga damuwa, rashin mutuncin da yayi mata ko wacce taje gidan miji babu budurci sai haka,

Shiyasa shima amadin zuciyarta takasa aminta dashi, takasa yarda da cewar son gaskiya yake yimata, dan haka tasaka aranta cewar bazata taba sonshi ba sai dai yayi yagama inyaso idan yaga babu riba sai ya hakura.

  Shi kuwa amadi koda wasa baiyi fushiba sannan wai dan tace ta taba aure harda yara bai sauya komai na daga son da yake yimata acikin zuciyarshi ba, sai dai kawai yana jin kishin koma waye wanda ya rigashi auren nadiya sannan kuma yana yimishi kallon soko wawa marar tunani da har ya iya rabuwa da mace kamar nadiya,

Koda yatafi tun yana hanya bai karasa cikin kano ba yake kiranta yace mata yatafi amma bata dauka ba, packing yayi agefen titi yatura mata text,

  _Baby natafi, ki dauki wayar kiji abinda zan fada miki please.._

Bayan yatura mata text din da yan mintuna yasake kiranta anan ta dauka tayi shiru kamar yadda ta saba,

"Baby.. Kina jina?"

"Uhm.." Shine amsar data bashi,

"Wai ko sayar min da muryar za ayine? Ko sai na siya sannan za arinka yimin magana.."

Tana jinsa amma tayi shiru bata yimasa magana ba,

"Shikenan dama kira nayi nafada miki natafi, yanzu ma haka ina hanya nakusa shiga cikin kano..."

Idan wayar da take hannunta tayi magana to itama tayi,

"Sai kinji ni anjima ko?"

"Uhm" dama amsar kenan koda yaushe uhm bata yimasa magana wadda tawuce wannan,

"To sai anjima" yafada tareda katse wayar yana murmushi.

  Kamar yadda yafada mata cewar babu abinda zai sauya soyayyarta acikin zuciyarshi hakance kuwa ta faru domin kullum cikin yimata waya yake ko text amma sai ta gadama zata dauki wayar, idan text ne kuwa iyakaci ta karanta ta ajiye wayar babu amsa, a ka'ida sau daya zaije wudil a sati amma saboda ita sai yaje sau biyu ko sau uku saboda kawai yana son yaganta,

Rashin yimasa magana a waya kuwa idan ya kirata harma yasaba domin yanzu idan ya kirata sha'anin gabansa yake yi yana rike da wayar saboda yasan ba magana zatayi ba haka zasu bar credit din yayita tafiya a banza har zuwa lokacin da zai cemata sai anjima, ita kanta tana mamaki tarasa gane ko amadi wanne irin mutum ne wanda baya fushi, duk abubuwan nan da take yimasa rana daya bai taba nuna mata cewar yayi fushi ba gashi wani lokacin da gayya zata kashe wayarta ai yana jin wayar akashe zata ganshi a wudil,

Akwai wata rana da takashe wayar da daddare saboda tasan yasaba kiranta da daddare dan haka tun 8 takashe, 9 ya kirata yaji waya akashe, yasake kira yaji akashe adaren yafito zai tafi wudil nan hajiya ta hanashi tace koma menene yabari sai da safe saboda ita bata sonshi da tafiyar dare haka ya hakura yakasa bacci,

Ita kuma karfe 2 ta kunna wayar saboda babu wuta gashi tana son tayi karatu, ai tana kunnawa sai ga kiranshi,

"Dan naci.." Tafada aranta, daukar wayar tayi badan tasoba,

"Meyasa nakira wayarki naji akashe..?"

"Na kashe ne saboda ina son yin bacci da wuri.."

"Kin kashe kinyi bacci nikuma kin hanani bacci ko?"

"Kamar ya?" Ta tambayeshi cikin rashin fahimta,

"Saboda banji muryarki ba shiyasa nakasa bacci da tuni ma sai dai ki ganni a wannan daren hajiyace ta hanani tace dare yayi..."

"Ohhh" shine kawai abinda tace,

"Yanzun me zakiyi?"

"Karatu" tafada atakaice,

"To shikenan nikuma tunda naji muryarki yanzu bacci zanyi sai da safe"

"Uhm" tafada tareda katse wayar.

Haka amadi keta fama da nadiya akan tasoshi amma taki, har semester ta kare babu wata gamsasshiyar magana da tayi masa, ana igobe zata tafi gida sai da yaje makarantar yayi yayi da ita tafada masa dalilinta na rashin sonsa da batayi amma tayi shiru, address din gidansu ya tambaya nanma taki fada, tamkar kurma haka take zame masa dama duk lokacin da yazo,

Murmushi yayi ya saka hannunshi a aljihu ya dauko rafar yan dari bibbiyu ya dauki jakarta ya bude yasaka mata aciki,

"To ga kudin mota Allah ya kiyaye hanya saboda nasan idan nace zanzo nakaiki ba yarda zakiyi ba, amma ki shirya ganina agidanku akoda wanne lokaci.."

Ko kadan maganarsa bata dauketa da gaske ba domin tayaya zai san gidan har yaje? Sallama yayi mata yatafi ita kuma ta koma hostel takarasa shirya kayanta tafita cikin gari taje ta siyo kayan tsaraba tayiwa twins dinta siyayya sosai washe gari tatafi gida inda zatasha dogon hutu domin hutun nasu da yawa.

  Komawarta gida yasa ta mance da wani amadi saboda hatta wayarta ma sai ta gadama take kunnawa saboda kar ya takura mata, ita yanzu bata da wani bazawari ma domin hatta yaya kamal ma ya hakura saboda yaga ba aurensa zatayi ba, yanzu iya amadi ne kawai ke yimata naci,

Satinta uku da dawowa gida tana zaune da yamma a tsakar gida tana yiwa fadeela kitso ita kuma ameera tana yimata tsifa mama tana kitchen tana aiki, fadeel da husna da walida da amir suna yin ball,

Wayarta ce tafara kukan neman agaji, kamar bazata dauka ba saboda ganin amadi ne amma sai ta dauka,

"Ki fito gani a kofar gidanku.."

Jin abinda yafada yayi mutukar sata mamaki,

"Wanne kofar gidan namu?"

"Kunada wani kofar gidanne bayan wanda kuke ciki? Ke da wai kin dauka bazan biyoki ba?"

"Ni bana gida"

Murmushi yayi,

"Hmm nidai nace miki ina kofar gida ina jiranki".



*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
         _(Labarin k'auna)_



   *_BY_*

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_

  _Fatan Alkhairi ga yan k'ungiyar haske writers, this page is for you...!_


    *41*

aishaummi.blogspot.com


   *A*jiyar zuciya ta ajiye sannan ta sake hade rai kamar yana ganinta,

"Nace maka bana gida naje unguwa.."

"To ina nan ina jiranki, sai kin dawo.."

Kasancewar duk abinda take fada mama tana jinta yasa mama fitowa daga cikin kitchen,

"Nadiya keda waye ne?"

"Mama wallahi wani nacaccen mutum ne.."

"Haba nadiya, kefa yanzu ba karamar yarinya bace akan me zaki rinka yin abu irin na kananan yara, ko Amira ce tayi haka ai zakiyi mata fada bare ke da kanki, ina ga mai sonka wanda yatako yazo har inda kake? Ki tashi maza ki shirya kije"

Jin abinda mama tafada yasata sakin kitson da take yiwa fadeela ta tashi tawuce daki,

Kallon amir mama tayi tace masa,

"Amir maza fita kofar gida kacewa bakon nadiya yayi hakuri tana zuwa, kabashi hakuri kaji, ai ba ayin haka.."

Fita Amir yayi yana fita yaga wani handsome jingine jikin motarsa baka sai sheki take, gayen yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda kalar ruwan toka, da hula akansa itama ash colour amma ya zameta ya turata baya can keyarsa, hannunshi daure da agogon azurfa fari,

Gaba daya kamshin turarensa na one man yagama cika ilahirin wurin, amir ji yayi gayen ya shiga ransa lokaci guda sannan gashi dan gayu dashi,

Sallama amir yayi masa, dagowa amadi yayi ya amsa tareda mikawa amir hannu sukayi musabaha,

"Mama ce ta aikoni tace kayi hakuri anty nadiyan zata fito yanzu"

Murmushi amadi yayi har lokacin yana rikeda hannun amir,

"Karka damu abokina, ai babu wani abu sai dai kawai yayarka bata sona ta tsaneni babu namijin da take jin haushi ahalin yanzu kamar ni"

"Ba tsanarka tayiba, kawai dai halin rayuwa ne ya mayar da ita haka" amir yabashi amsa,

"Amma dagaske wai ta taba aure?"

"Ehh tayi aure harda yaranta twins, sun rabu da mijinne"

Jijjiga kai amadi yayi, "nasan dai ba laifinta bane sai dai laifin mijin saboda nadiya tanada kalar mata nagari"

"Hakane, gaskiya kam laifin ba a ita bane a mijinta ne kuma cousin dinmu ne ma amma yanzu babu aure a tsakaninsu saboda saki uku yayi mata, kaga kuwa duk macen da irin wannan kaddarar ta hau kanta dole ta nisanta kanta da maza musamman ma anty nadiya wacce ko kadan bata tsinci wani dadiba acikin rayuwar aure.."

Amadi ya dago kenan da niyyar sake yin magana sai gata ta fito fuskarta adaure tasha kunu sai faman cika take yi tana batsewa saboda tilastata din da mama tayi ta fito ba ason ranta ba,

Hannun amir amadi ya saki yana murmushi, "abokina sai mun sake haduwa, meye ma sunanka?"

"Sunana amir"

"To amir sai mun hadu next time, nagode"

Wucewa cikin gida amir yayi ita kuma ta karasa fuskarta babu fara'a,juyawa yayi ya dora hannunshi asaman mota ya jingina yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi,

Ba karamin kyau yaga ta kara yiba domin tayi kumatu ta yi haske, tana sanye da atamfa kalar ruwan toka da hoton dutsin guga ajiki, ta yafa mayafi ash colour tasaka flat din takalmi baki,

Haushi taji saboda ganin sunyi anko da amadi, ji takeyi kamar ta koma gida ta sake wasu kayan,

"Meye kuma harda sako kaya kalar nawa?" Yafada cikeda tsokana yana kallonta, sake daure fuska tayi,

"Ni ban ma san kalar kayan da kasako kenan ba.."

"Bawani nan kin sani kawai dai kidai nagane so kikeyi muyi anko"

Sake k'uluwa tayi nan ta juya tana harare harare shikuma abin dariya yake bashi, sake niyyar tsokanarta yayi ya kalleta,

"Har kin dawo daga unguwar? Ai da kin yi addressing dina naje na dauko ki"

"Nagode.." Tafada batare data kalleshi ba saboda ta gane tambayar rainin hankali yayi mata tunda ai yana gani ta fito daga cikin gida,

"Ina twins dina?" Ya tambayeta,

"Dama kanada twins ne?"

"Au da ke baki saniba?"

Shiru tayi masa, dan haka ya kalleta yayi dan murmushi,

"Kizo mu shiga mota karki gaji da tsaiwa ni kinga nasaba tsayawa a aji"

"Basai na shiga ba, nifa aiki nakeyi ka fito dani.."

"Daga dawowar taki daga unguwa kika hau aiki?"

Sake yin shiru tayi dan haka ya kalleta yana duba agogon dake daure a hannunshi,

"Nima ba zama nazo yiba dama ganinki kawai nazo nayi sannan naga gidanku, tunda nagani shikenan zanje natafi amma karki dauka natafi kenan, no i will be back soon, ko yanzu dai nasan kinyi believing cewar bazan taba barinki ba har sai kin zama mallakina koda kuwa bakya sona tunda ni ina sonki shikenan.."

Juyawa tayi ta kalleshi fuskarta a tamke,

"Nagode da sona da kakeyi amma kasani auren matar da bata sonka babban kuskure ne, sannan budurwa itace tafi dacewa dakai ba bazawara mai yara har biyu ba, Allah ya kiyaye hanya.."

"A'a ni bazawara ce tafi dacewa dani ba budurwa ba saboda manzon Allah ma da bazawara yafara kinga kenan idan nayi haka na dabbaka sunna babba.."

"Allah ya kiyaye hanya.."

Tun kafin ya amsa tayi gaba abinta, binta da kallo yayi yana jujjuyawa kalmominta acikin ma'auni,

Duk maganganun da take fada masa yana ji acikin ransa cewar akwai wani abune da yake damunta acikin zuciyarta wanda yakeda alaka da wannan sannan kuma ga maganar da amir ya fada masa dangane da ita cewar bataji dadin rayuwar aurenta nafarko ba, to indai hakane bawai sonshi dinne batayi ba kawai dai akwai wani abune wanda ta ajiyewa ranta,

Waya yayi mata ta dauka dakyar murya a dakile,

"Please turo min amir zamuyi sallama"

Katse wayar tayi ta kalli amir, "kaje yana kiranka"

"Wai waye wanda yazone?" Mama ta bukata,

"Wallahi mama wani classic guy ne anty tasamu.."

Daukar takalmi tayi ta jefeshi yayi saurin fita yana dariya,

A tsaye jingine da mota yasamu amadi,

"Abokina yi hakuri nasake fitowa dakai ko"

"A'a wallahi babu komai"

Kallonsa amadi yayi, "amir ni dagaske nake son yayarka amma kuma taki kwata kwata bani hadin kai mu fuskanci juna ban san dalili ba, shin mijinta nafarko ya cutar da itane?"

"Gaskiya bakai kadai yaya nadiya ke yiwa hakaba, kaga bayan mutuwar aurenta manema da yawa sun fito suna sonta amma taki tace ita karatu zatayi saboda kamar yadda nafada maka abaya ko kadan bataji dadin aureba,

Wannan dalilinne yasa yanzu bata sha'awar sake yi kwana kusa saboda kasan bahushe yace naji dadi shine gari ba na saba ba, abubuwan da anty nadiya tagani agidan aure suna da yawa, taga rayuwa kala kala daga karshe suka rabu da mijin babu arziki, to kaga wanda yaga haka ai fiyeda irin wannan ma zai iyayi"

Jijjiga kai amadi yayi, "na fuskanceka amir, nagane dalilin nadiya na tsanata da kin amsar soyayyata, nikuma nayi maka alkawarin mutukar na auri yayarka bazata yi kuka daniba sai ko na farin ciki, bazan wulakantata ba, zan kula da ita sannan zan bata gatan da bata samu a aurenta na farko ba.."

"Allah yasa, Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Amin"

Hannu yasa a aljihu ya dauko kudi sabbi fil yan 500 na dubu biyar yabawa amir yace ya siyawa twins sweet daga nan ya shiga motarshi yatafi yana mai jin son nadiya yana sake ratsa duk kofofin jinin jikinsa,sannan yanajin wani tausayinta yana shigarshi,

Tunda amir ya kawo sakon mama ke kallon nadiya tana son jin yanda zata karbi zancen amma ko uffan batace ba shikuwa amir sai yabon amadi yake tayi yana cewa mama wallahi guy din ya hadu sannan ga hankali ga class gashi dan gayu.

  Tunda yatafi nadiya bata kirashi ba ganin haka yasa shi ya kirata, kamar koda yaushe shiru tayi masa har fadeela ta shigo ta haye jikinta tafara yimata surutu jiyo surutun fadeela da yayi yace tabashi ita, mikawa fadeela wayar tayi ta kara mata ajikin kunnenta,

"Momy waye?"

"Dady ne" yabawa fadeela amsa ai kuwa nan ta hau tsalle saboda tazata dadyn tane duk da tafara mantawa dashi....


*_Ummi Shatu_*🏻
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
        _(Labarin k'auna)_


   *_BY_*

*_UMMI A'ISHA_*

® *HASKE WRITERS ASSO.*  _Home of perfect & expert writers_


    _Jinjina ga babbar yaya anty maijidda musa, nagode da kokarinki agareni, Allah yabarmu tare.._

   *42*

aishaummi.blogspot.com


    *T*salle fadeela tahau yi tana yiwa amadi surutu, nan yasamu abokiyar hira tanata yimasa labarin school dinsu harda su abcd da sauran karatun da ake koya musu a makaranta,

Ita kanta nadiya sai da abin ya bata mamaki irin yanda amadi ya biye fadeela taketa yi masa surutu, shima fadeel ya shigo nan fadeela tabashi wayar tana cewa,

"Ga daddy"

Karba shima yayi nan hirar takoma amadi da fadeel, daga karshe ita nadiya ma baccine ya dauketa tabarsu sunata faman surutu bata san lokacin da suka gama ba,

"Ina momyn take?" Amadi ya tambayi fadeel,

"Gata nan tana bacci"

"To kyaleta karka tasheta",nan yayi sallama da yaran ya kashe wayarsa.

  Tun daga nan kullum idan ya kira wayar dasu fadeel suke shan hirarsu suyi tayi masa surutu suna sashi dariya,

Satinshi biyu da zuwa yasake shiryawa ya dawo acikin weekend ranar asabar, sai kawai waya yayi mata yace yana waje, amir ta kira tace yaje da bako awaje saboda ita tana kwance cikin bargo tana baccinta,

Amir na ganin amadi ne yamaza ya koma cikin gida yafadawa mama, nan mama tace  ashigo dashi falon baki,

Amira mama tasa tayi masa girki nan Amira ta shiga cikin kitchen ta dora,

Dakyar nadiya ta tashi tayi wanka ta shirya bayan mama ta leko tayi mata kaca kaca, shiryawa tayi cikin leshi dark brown da mayafinsa ta fita,

Lokacin da zata shiga sai ga Amira itama rikeda faranti zata shiga, bata hanya tayi ta fara shiga sannan tabi bayan amiran,

Sai da Amira ta gaisheshi sannan ta tashi ta fita kallon nadiya yayi yau dinma fuskarta adaure,

"Wannan kanwar taki tanada hankali kamar amir.."

Shiru tayi masa bata tanka ba,

"Ina twins dina.."

"Basa nan sunje islamiyya"

Murmushi yayi bai kara cewa komai ba illah kawai kallonta da yake yi,

Babu wanda ya kara magana haka suka cigaba da zaman kurame sai da suka dade ahaka sannan amadi yayi magana saboda yasan ita dai ba magana zatayi ba,

"Nadiya....,ina so kiyi hakuri ki bani dama saboda komai arayuwa da kika ganshi kaddara ne sannan kuma bawai yana nufin cewa saboda mutum daya yayi maka butulci kowama butulu bane, a'a ita rayuwa ahaka take tafiya, yayinda wani ya bata maka sai wani ya dad'ad'a maka, nidai indai nine nayi miki alkawarin bazan taba cin amanarki ba.."

Duk wannan maganganun da yayi bawai sunyi tasiri agareta bane kawai dai ta daukesu a matsayin zallar karya irinta yaya kabeer,

"Dan Allah nadiya kibani dama domin na nuna miki irin son da nake yimiki"

Har lokacin dai bata ce dashi ko ci kanka ba,shiru yayi yazuba mata ido kawai yana kallonta,

"Bakaga an kawo maka abinci bane.." Tafada batare data kalli gefen da yakeba,

"Kin damu da naci ne? Ai baki damu da koshina ko yunwata ba.."

Bata sake tanka masa ba dan haka yajawo farantin abincin nan yabude yaga potatoes mix da wata hadaddiyar sos wadda tasha curry da hanta sai kamshi take,

Kwallo biyu kacal ya dauka ya debi sos din yafara ci,

"Kanwarki ta iya girki, ko kece kika yi?"

"Bani bace.." Tafada tana sake hade rai,

Shiru yayi yaci gaba da cin abincin yana binta da ido,

Ihun sallamar su fadeel ce ta cika musu kunne sai gasu sun shigo cikin falon aguje suna ihu wai dadynsu yazo,

Zuwa sukayi suka rungume amadi suna ihun murna, amir dake biye dasu yana cewa "karku bata masa kaya ku cire takalmin"

Kasancewar milki colour din yadi ne ajikin amadi,

Tunda su fadeel suka dawo amadi yasamu abokan hira bai sake bi ta kan nadiya ba, mama ma tashigo sun gaisa daga nan kuma amir ya rakashi wurin abba suka gaisa ai nadiya ji tayi kamar zatayi kuka da bakin ciki saboda ita bata da burin sake yin aure kwana kusa,

Fita yayi zai tafi yana rikeda su fadeel amir yana binsu abaya, boot din motarshi ya bude yace amir ya kwashe kayan ciki yakai gida na twins ne yakawo musu, ita kam nadiya tana tsaye tana kallonsu kayane sosai yasiyo irinsu bobo, biscuit, chocolate, indomie da sauran kayan makulashe na yara,

Bin amir sukayi zuwa cikin gida dan haka amadi ya matsa kusa da ita,

"Baby zan tafi.." Wani haushi taji ya rufeta saboda ta tsani baby dinnan da yake kiranta dashi,

"Allah ya kiyaye hanya"

"Amin nagode da addu'a, sai yaushe?"

Jin tayi masa shiru yasashi yimata sai anjima yatafi,

Haka sukaita fama koda yaushe yana kiranta awaya sannan yana tura mata da kati,

Har yanzu ita bata ji alamun zata soshi ba saboda zuciyarta ta dade da cire soyayya daga cikinta,

Tana kwance taji yana kiranta awaya, dauka tayi bayan tayi tsaki,

"Baby kina lafiya?"

"Lafiya"

"Dama fada miki zanyi zanzo ranar Thursday ko Friday"

"Bana nan"

"Ina kika tafi?"

"Basai kajiba, sai anjima yanzu aiki nake"

Kitt takashe wayar bata san mama na tsaye tana jinta ba,

"Ke nadiya wai meyake damunki ne? Ashe dama bakida wayo? Allah ya dubi zuciyarki da irin halin da kika shiga yakawo miki wanda yake sonki tsakani da Allah shine kuma zaki butulce masa?

To wallahi ki zauna kiyi karatun tanutsu saboda wannan yaron da gaske yake sonki idan har kika wulakantashi kika koreshi to bazaki samu wanda yakaishi ba agaba,

Kuma wallahi idan har ke bazaki aureshi ba to ni ashirye nake da in bashi Amira ya aura, wallahi indai bazaki aureshi ba ki fada min sai ince masa yazo ya auri Amira, haba yaro mai mutunci mai son yayanki, ya dauki yaranki kamar nasa amma kekuma babu wanda kike ciwa mutunci sai shi, to yakamata ki yiwa kanki fada.."

Juyawa mama tayi tafita tabar nadiya tana kuka, ita kwata kwata yanzu auren ne bata so,sannan maganar mama ta tsaya mata arai wai zata bawa amadi Amira idan ita bata sonshi,

Koda yasake kiranta yace zai zo cewa tayi to, ranar kuwa na zuwa sai gashi yazo da misalin karfe 12 narana,shiryawa tayi cikin wani material ja mai kyau ta fita,

Acikin mota ta sameshi dan haka ta tsaya daga waje tana faman ciccin magani, ta cikin mirror ya hangota yayi murmushi ya bude ya fito, tana ganinsa tajuya tafara tafiya batare da tayi magana ba, binta yayi abaya tiryan tiryan har zuwa cikin gidan falon baki,

Zama tayi anesa dashi ranta ahade, suna zaune haka shiru husna tashigo dauke da faranti kato wanda aka doro kayan abinci aciki,

Fried rice da hadadden salad wanda yaji kwai da sauran kayan hadi sai juice,

"Zo muci abincin" yafada cikin tsokana,

"Na koshi" tabashi amsa, murmushi yayi yafara cin abincin yana kallonta tareda nazarinta sam shi abinda take yimasa baya bata masa rai bare ya daga masa hankali asalima hakan sake burgeshi yake yana kara rura wutar sonta acikin ranshi,

Suna nan zaune zaman kurame har yagama cin abincin ya kalleta,

"Baby ko babu komai ai yakamata ace mun gaisa ko?"

"Mantawa nayi" tafada tana dauke kanta, murmushin da yasaba yi kowanne lokaci yanzun ma shi yayi,

"Na sameku lafiya?"

"Lafiya"

Shiru suka yi na dan wani lokaci,

"Ina budurwata Amira yau ban ganta ba?"

"Tana ciki" ta amsa masa fuskarta adaure,

"Wannan ciccin maganin da kikeyi yakamata ki daina shi saboda nima yau ba wurinki nazo ba wurin Amira nazo domin na sauya shek'a....".




*_Ummi Shatu_*🏻
🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹
        _(Labarin k'auna)_


   _*BY*_

_*UMMI A'ISHA*_

® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_

    _Special gaisuwa ga aminan kwarai abin alfaharina, Pherty Xarah, Fido sodangi, Kausar m Hassan, Khaleesat Haidar, Mom Shakur, Sadiya I Bala,Khadija Sidi, Teemah Cool, Hafsat Bunxa, Aisha Dansabo,Zee Ruma,da duk wadanda ban ambata ba, ina alfahari daku kawayena..._

    *43*

aishaummi.blogspot.com


   *J*i tayi gabanta yafadi bata san daliliba, saurin kallonsa tayi nan taga shi ba ita yake kallo ba ma sam, wayarshi yake kallo yana daddannawa,

Maimaita maganar take yi acikin zuciyarta nan take kuma maganar da mama tafada ta sake dawo mata inda mama take cewa idan har bata sonshi bazata aureshi ba to zata bashi Amira,

Faduwar gabanta ce ta tsananta nan tasake kallonsa still dai wayarshi yake kallo ba itaba,

"Dama Amira ai itace tafi dacewa dakai baniba, Allah yabada sa'a.." Tafada cikin k'uluwa tareda tashi zata fita,

"Amin, dan Allah ki turo min ita idan kin shiga ciki.." Ya fada da niyyar sake tunzurata, bata ko waiwayo ba tayi gaba abinta amma kuma haka kawai sai take jin wani irin haushi yana bakuntar zuciyarta,

Cikin dakinta ta shiga nan taga Amira tana zaune tana gyara kayan sakawar su fadeel tana shirya musu shi acikin wardrobe, kamar bazata yi magana ba sai kuma tace da Amira,

"Amira kije Ahmad yana kiranki.."

"To anty.." Amira tafada gamida mikewa da sauri,

"To Kodai dama yarinyar nan tasan da zuwanshi ne?"

Ta tambayi zuciyarta, zama tayi taci gaba da aikin da amiran tatafi tabari.

Amira nashiga falon baki ta iske amadi azaune,

"Yaya Ahmad ina wuni?" Tafada cikin ladabi,

"Lafiya Amira, yasu mama?"

"Suna nan lafiya"

"Yawwa dan Allah so nake ki shirya min su fadeela zamuje unguwa dasu.."

"To yaya Ahmad"

"Yawwa nagode"

Fita tayi zuwa dakin mama inda Maman ke shiryasu bayan tayi musu wanka nan Amira tafadawa mama sakon amadi na ashiryasu zai kaisu unguwa,

Kayansu Amira tasa musu tayiwa fadeela kwalliya sosai takama mata gashinta da ribom kalar kayanta pink din riga da bakin jeans skirt, shikuma fadeel pink din t shirt da bakin jeans ta fesa musu turare,

Kama hannunsu tayi takaisu wurin amadi tace gasu nan sun fito,

Kallon yaran kawai ya tsaya yana yi domin ba karamin burgeshi suka yiba ji yake aransa inama yaranshi ne,inama shine ya haifesu shida nadiya amma kowaye ya auri nadiya dafarko yayi masa overtaken ne kawai da tuni yanzu yaran nan nashine,

Kama hannunsu yayi suka fita yayinda Amira ita kuma tafara tattare kwanukan abincin da yaci.

  Nadiya kam tana daki bata san abinda yake gudana ba amma jitake aranta amadi yama yi mugun raina mata hankali, daga ganin kanwarta sai yace ita yake so yanzu?

Tsaki taja tayi juyi, "koma menene shi yajiyo dai dama ni ba sonshi nake yiba.."

Shigowar Amira ne ya katse mata tunani, "su fadeel sunbi yaya Ahmad unguwa"

"Kuma meye nawa ni aciki?" Nadiya ta bata amsa cikin fada, fita Amira tayi daga cikin dakin, jin karar shigowar massage awayarta yasata dubawa,

  _Wasafa nake yimiki babu wata shek'a da na sauya, so karki fara kishi da kanwarki dan naga har kishi ya bayyana acikin idonki karara,munje unguwa da twins dina nasan ke ko nace kizo ki rakamu ba zuwa zakiyi ba shiyasa banyi inviting dinki ba, sai mun dawo,1,4,3.._

Gyara kwanciyarta tayi tana hararar wayar kamar yana wurin, "ruwanka kuma"

Amadi wurin wasan yara ya nufa dasu fadeel, kowa yagansu zaiyi tsammanin cewar yaranshi ne gashi suma sun fara shakuwa dashi sosai,

Wasa suka rinka yi cikin farin ciki shikuma yana yimusu pics wani lokacin kuma ya shiga yayi musu tare, shi kansa bai san adadin yawan hotunan da yayi musu ba,

Sai da sukayi wasa mai isarsu suka gaji tikis suka fara kiran yunwa sannan ya daukesu zuwa wani restaurant dake gaba kadan da wajen wasan yaran,

Fito dasu yayi suka shiga ciki yayi musu order din abinci, amala da miyar ganye da kaza, shi yarinka basu abincin har suka koshi sannan yaci yabiya kudin abincin suka fito,

Maimakon yakaisu gida sai ya nufi supermarket dasu nan suka shiga ya lodo musu kayan dadi kala kala yafito yana rikeda fadeela daya hannun kuma ledar da ya iyo shopping ce fadeel kuma yana biye dasu,

Kamar a mafarki kabeer ya hango yaranshi wani rike dasu lokacin da yake packing acikin harabar supermarket din, duk da yadade rabonshi da yaran domin ba zuwa ganinsu yakeba amma ai bazai iya mantasu ba, cikin gaggawa ya fito daga cikin motarshi ya nufi wurinsu amadi,

Amadi yana kokarin bude motarshi kabeer ya isa wurin,

"Fadeel,fadeela...."

Kabeer ya kira sunan yaranshi yana karewa amadi kallo,

"Bawan Allah kai kuma waye da zaka dauko min yara ka kawosu nan wurin batare da izinina ba?" Kabeer yafada cikin gadara,

Kallonsa amadi yayi "banfa ganeka ba, waye kai please"

"Ohhh tambayata ma kake ko waye ni? Ok to nine mahaifin wadannan yaran kai kuma waye"

"Allah sarki, ni nine wanda yake shirin zama babansu ta hanyar auren mahaifiyarsu"

Ai take zuciyar kabeer ta tsananta bugu kishi ya bayyana a fuskarsa karara, haushin amadi ya kamashi musamman ma da yaganshi handsome babu alamun kauyanci ko shirme atare dashi,

"To bani yaya na inyaso kaje ka auri uwar tasu ita kadai amma yaya tunda nawane babu wanda zaiyi min gadara dasu"

Murmushi amadi yayi wanda ya bayyanar da beautiful point dinshi,

"Amma dai kasan ai ba kai kadai ka haifi yaran ba ko? Dan haka tunda bakai kadai ka haifesu ba to baka da iko dasu kai kadai, idan yaranka kakeso ka karba kaje gidansu nadiya ka karbesu acan, amma nidai yanzu bazan baka yaraba yanda nafito dasu sai na mayar dasu wurinda na daukosu.."

Kabeer najin haka yatada fada yana daga murya kamar wani zautacce,

"Wallahi sai kabani yarana saboda bakai ka haifa min suba, kai fadeel kuzo mu tafi nine ubanku ba wannan ba"

Zuwa yayi zai kama hannun yaran anan suka fashe da kuka suka kankame amadi suna makale kafada alamun bazasuje wurinsa ba abinda yayi mutukar sake daga hankalin kabeer,

Nan mutane suka fara taruwa kabeer sai fada yake yana zagin amadi kamar wani marar hankali, ko takansa amadi baibi yasaka su fadeel a mota yashiga yatashi motarsa yabar kabeer yana cewa,

"Wallahi yarana zan karbo, sai anbani yayana.."

Wannan shine mafarin nadamar kabeer saboda yahadu da yayanshi na cikinsa amma sunki zuwa wurinsa daga yakai hannu zai tabasu sai su saka kuka.

  Nadiya na daki azaune bayan tayi wanka ta shirya tana kwalliya su fadeel suka shigo dagudu, fadeel ne mai kokarin dauko ledar siyayyar da amadi yayi musu,

"Momy kinga uncle ya siya mana, kuma mun hadu da wani a supermarket sunyi fada da uncle yace wai shine babanmu.."

Fadeela tafada tana zama akan cinyarta, sake tambayar fadeel tayi nan yafada mata kamar yadda fadeela ta fada,

Tashi tayi tafita waje wurin amadi, yana saman motarshi azaune,

Tsayawa tayi ajikin motar tana son ta tambayeshi abinda su fadeela suka fada mata amma takasa saboda basa doguwar magana dashi.

Zuwa can tadaure ta kalleshi tace,

"Naji su fadeel suna fada min wani zance"

"Name?" Ya tambayeta,

"Wai kun hadu da abbansu a supermarket"

Shiru yayi mata baiyi magana ba,

"Ya kayi shiru?"

"Ehhh"

Yace da ita yana kokarin dirowa daga saman motarsa,

"Dagaske ne mun hadu dashi may be ma kiganshi yazo anjima.."

Sai da taji kanta ya sara saboda ita yanzu bata son duk wani abu wanda zai hadata da yaya kabeer,

"Zanje in tafi amma wannan shine tafiyata ta karshe bazan sake dawowa gidanku ba har sai naji matsayina awurinki, dan haka nabaki dama ki zauna kiyi shawara da zuciyarki sannan ki yanke hukunci akan maganarmu, idan har zaki aure ni kifada min idan bazaki aure niba karki boye min ki sanar dani gaskiya, nabarki lafiya"

Bai jira amsar da zata bashi ba ya wuceta yaje ya bude motarsa ya zabureta yabar wurin.....


*Fatan Alkhairi ga k'awar kirki maryama qaumi...*

  _Gaisuwa mai yawa ga masoyan littafin mijina sirrina, khairat dan dawaki,heedah, hajjaju chuchu, Nasma, kadija mai kano, Billy reality, mom amir,ummy aysha, meenah 4eva da duk wata masoyiyar MS.._




*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment